← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 150

Sashe 123

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Suna shiga Falon dai-dai lokacin Asma'u da Khausar na kitchen Khausar har mamakin kanta take saboda ƙosai da kunun gyaɗan da taci da safe, kana yanzu kuma Asma'u da kanta ta tuƙa mata tuwan Semovita da miyar ɗanyen kuɓewa aƙaramin dining Dake kitchen ɗin suke zaune.
Khausar kam ta kasa daina mamakin kanta yanda take cin tuwon sosai kallon Asma'u da itama tayi wani irin kyau na ban mamaki tayi ta fito a asalin amarya tace.
“Wallahi Asma'u har mamakin kaina na keyi rabona da abinci hakafa nafi wata huɗu”.
Murmushi Asma'u tayi tare da cewa.
“Ikon Allah baby ɗan albarka yasan yazo garinsu kenan”.
Murmushi Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ta ɗan kalli cikin,
dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamarsu Didi sun shigo gidan cikin wani irin...

By
*GARKUWAR MARUBUTA*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HCji7xLpR1VEJGYcZJMP6k

KAZAURE COLLEGE OF NURSING SCIENCES (KCONS)
Lafiya Uwar jiki, Kuma sai da lafiya ake morar rayuwa. Kazaure College Of Nursing Sciences (KCONS) ta kawo muku ingantaccen tsarin koyar da jinya da unguwar zoma, mun himmatu wajen samar da kwararrun ma'aikatan jinya da unguwar zoma a fadin Nigeria da ma matakin duniya baki daya, a KCONS mun tanadar muku kwararrun malamai, ingantaccen yanayi da tsarin koyo da koyarwa kai harma da tsarin e-learning, ka zalika akwai tabbataccen tsaro a dakunan kwanan dalibai maza da mata, bugu da kari kudin makaranta dai-dai aljuhu, KCONS munanan a lamba 5 layin fadar sarki dake kan hanyar kano zuwa daura a Kazaure jahar Jigawa, za'a iya samummu a shafikanmu na facebook da instagram @KCONsciences domin bayani, za'a iya tuntubanrmu a wadannan lambobin, 07066542055, 08035298851, ko shafin mu na yanan gizo @ http://kcons.edu.ng/admission KCON sciences kan turbar aiki da kwarewa muka shahara.

Zare idanu Asma'u ta miƙe tare da kallon Khausar tace.
“Kamar su Didi ce suka shigo?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa.
“Ehem sune ya akayi?”.
Yarfe hannu tayi sai kuma ta girgiza kai kana tace.
“Wayyo Allah nikam zan fita ta ƙofar kitchen bana zaton zan iya haɗa ido da ita”.
Dariya ce taso kufcewa Khausar amma sai ta daure bata yiba tace.
“Meyesa?”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Asma'u ta ɗan kalli ƙofar tare da faɗin.
“Wallahi kunyar su nake ji”.
Baki sake Khausar ke kallonta kafin tace.
“Dallah tafi daga nan muje ki gaishesu idan yaso sai mu tafi gidan Ummi tunda su suna nan”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh shikenan ”.
Kana suka fito Falon Khausar ce agaba Asma'u na biye da ita cike da kunya.
Didi na kallon Asma'u ta miƙa mata hannu tare da faɗin.
“A'a ɗiyata ƴar Albarka Masha Allah fatan mun same ku lafiya?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa batare data kalleta ba kana ta gaishesu ɗaya bayan ɗaya.
Anutse Khausar da cikinta ya ƙara bayyana dabida samun cin wadataceccen abinci ta juya jin Lalla Hafsat na cewa.
“Ƙanwata ya dai an samu anci abinci kuwa?”.
Murmushi Momy tayi tana kallon Lalla Hafsat tace.
“Dama bata ci abinci ko?”.
Kai Didi ta gyaɗa cike da tausayi tace.
“Ina kuwa take cin abinci sai dai tai ta shan fruits”.
Mommy na kallon Khausar dake sunne kai kana tace.
“Ikon Allah nan kuwa tunda tazo cikinta bai huta ba haba ashe shiyasa take ta ci ba sausauci”.
Asma'u ce ta karɓi zancen da cewa.
“Yanzu ma tuwo da miyar kuɓewa tana ɗa a kitchen kamar me”.
Khausar kuwa ɗan hararan Asma'u tayi.
Didi kam da mamaki ta kalli Khausar tare da faɗin.
“Ikon Allah Alhamdulillah ai haka akeso”.
Murmushi Lalla Khadijah tayi kana tace.
“Ai dama wani cikin hakane in Kaje unguwa sai kiga Kaci abinci idan kuma agidanka ne ba zaka iya ba”.
Ahankali Khausar ta sake kasa da kanta cike da kunya wani irin masifeffen kunya ne ya mamaye ta jin yanda ake ta maganar tana da ciki.
Batare data ɗago kanta ba ta riƙe hannun Asma'u tare da cewa.
“Mu tafi”.
Miƙewa Asma'u tayi kana suka shiga bedroom ɗin Khausar ta dauko mayafinta kallonta Momy tayi tare da cewa.
“Ina zaki je?".
Tana ƙoƙarin gyara mayafinta tace.
“Zamuje gidan Ummi ne”.
“Toh kin tambayi mijinki ne?".
Cewar Momy.
Murmushi Didi tayi kana tace.
“A Babu Matsala ai taje tunda ziyara ne”.
Miƙewa sukayi suka fita kai tsaye Side ɗin Hajiya Bunayya suka shiga bakinsu ɗauke da sallama.
Falon shiru ba kowa sake sallama Khausar tayi da ɗan ƙarfu.
Asiya dake bedroom ɗin tun ɗazu suna kukane tashin hankali d suke cikine ya hanata fitowa, jiyo muryar Khausar ɗin ne yasa tayi saurin miƙewa ta fito idanunta cike da hawaye ga kumburar da sukatu Khausar ta rungumeta tare da cewa.
“Oyoyo Khausar sannu da zuwa fatan kunzo lafiya? ya gida yasu Didi da kowa da kowa?".
Khausar na sake ruggume ta tace.
“Duk lafiya lau".
Ta ƙare maganar tana kallon idanunta da Fuskanta da suka kumbura alamar taci kuka da damuwa tace.
“Addah Asiya lafiya kuwa?”.
Ɗan Murmushi tayi tare da cewa.
“Lafiya lau Khausar ”.
Kai Khausar ta girgiza tana nazartan yanayinta tace.
“Amma Addah Asiya kamar kuka kika yi fa dan Allah ki faɗa min dakuwarki na tabbatar akwai abinda ke damunki”.
Araunane Asiya ta maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tace.
“Amina da Umma ce babu lafiya shiyasa hankalina yake tashe”.
Da damuwa Khausar ta kalli Asma'u da itama ita take kallo kana tace.
“Subhanallah me ya sami Aminan?”.
Ahankali Asiya tace.
“Bata da lafiya ne”.
Da sauri Khausar ta ɗan kalli Falon tare da cewa.
“Toh Ina take?”.
Bedroom ɗin Hajiya Bunayya ta nuna mata tare da faɗin.
“Tana ciki”.
Cike da kulawa da tarin tausayi tace.
“Toh mu shiga mana”.
Kai Asiya ta gyaɗa kana tayi gaba Khausar da Asma'u na biye da ita.
Suna shiga Idanunsu ya sauƙa kan Hajiya Bunayya dake zaune gefen gado tana sharɓan Kuka cikin sauri Khausar ta ƙarasa shiga kana ta zauna gefen Amina ta riƙo hannunta acikin nata cikin raunin ganin halin da Amina ke ciki tace.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Amina meyesa meki?,me yake damunki?,Ya ilahi ya mujibud da'awati ya hayyu ya ƙayyum meye haka yake damunki?”.
Ƙasa furta komai Amina tayi sai hawaye dake ambaliya saman fuskarta kallonta ta mayar kan Asiya kana ta cigaba da faɗin.
“Addah Asiya meke damunta?”.
Kai Asiya ta girgiza tare da cewa.
“Muma bamu san meke damun Amina ba”.
Muryanta na rawa tace.
“Yaushe taxo to?”.
Kai Asiya ta girgiza tare da faɗin.
“Abin sai ahankali Khausar am”.
Cikin matsanancin Kuka Amina ta damƙe hannun Khausar dake cikin nata kana muryanta cike da rauni tace.
“Khausar ki yafemin”.
Da sauri Khausar tace.
“Ni kuma me kikayi min”.
Cikin rawan murya Amina tace.
“Ai ba abinda ban mikiba na cutar dake arayuwa Khausar ki yafemin”.
Cikin sauri Khausar ta girgiza mata kai Idanunta na zubda hawaye.
Hannunta ta ɗaura akan bakinta ta datake wani irin zaro harshe waje kana tace.
“Ba kiyi min komai ba Amina ki daina kuka Allah Ubangiji ya yaye miki abinda yake damunki Allah ya baki lafiya Amina”.
Kallonta ta mayar kan Hajiya Bunayya jin yanda shesh-sheƙa kukanta ke tashi tace.
“Ummu kema kina kuka toh ita kuma ya zata yi aike zaki ƙarfafa mata guwwa!”.
Amaimakon tayi magana sai ta zame ƙasa ta gurfana gwiwoyinta gaban Khausar tare da riƙe hannunta cikin wata raunatacciyar murya mai sanya tausayi tace.
“Khausar ki yafe min nasan na cutar dake a rayuwata na cutar da mahaifiyar ki nasan kin sani na cutar daku”.
Ahankali Khausar ta cije gefen bakinta kana ta jujjuya kanta still hawaye na bin fuskarta tace.
“Bakomai Umma Allah ya yafe mana”.
Kuka sosai Hajiya Bunayya ta fashe dashi tare da cewa.
“Khausar na cutar daku da cutarwa mafi muni azaman da mukayi nasan ke kina zargina ”.
Kai Khausar ta girgiza tare da faɗin.
“Astagfirullah ai nima zargi nake Umma Allah ya yafe min kan zargin dana miki saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce. _Azzannah Zhambu Walau kana haƙƙun_”.
Araunane Hajiya Bunayya ta girgiza kai tare da cewa.
“Ba zargi bane Khausar dagaske ne tunanin ki akaina, ina cutar daku gashi Allah ya muku Sakayyah alokacin da bakuyi tunani ba ba kuma san ina yiba. Allah yayi muku Sakayyah alokacin da banyi Aune ba don Allah Khausar ki roƙamin gafarar wurin Momynki ku yafemin”.
Asma'u kuwa cikin yanayin tsoro take kallon Amina data kasa tantance yanayin da take ciki.
Hajiya Bunayya kuwa cikin tarin nadama ta cigaba da faɗin.
“Kiga yanda Allah ya jarabceni kiga yanda Amina ta dawo kiga abinda Naseer ya mana Naseer yaje ya cutar min da yarinya.
Jiya da yamma yazo ya wurgar mana da ita ya tafi ko shigowa cikin gidan nan baiyi ba.
Ya juya ya tafi yau ya tafi Indi'a yabar mu da jidali Uwarsa da Ubansa sai binmu sukayi da rashin mutunci”.
Nan ra kwashe duk labarin da Amina ta basu na macijin da yake fitowa yasha nononta da yadda ta kasa faɗawa kowa da kuma yadda yake hanata faɗa ta kara da cewa.
“Ashema shine yake juyawa ya zama macijin yayi ta shan nononta sai jiyan duk yake gaya mata ya aureta ne dan tayi tsafi da ita ya samu biyan buƙatar rayuwar duniyar sa, yanzu kuma buƙatarsa ya biya ya haɗota da takardar saki uku yazo ya wurgar mana da ita”.
Hawayen da yaƙi tsayawa Khausar ta share tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Uncle Naseer”.
Sai Kuma ta juya ta kalli Asma'u da itama ita take kallo Asma'u kuwa cikin sanin muguwar ɗabi'arsa tace.
“Hmmmm Uncle Naseer zaiyi abinda yafi haka ma”.
Hajiya Bunayya kuwa cigaba da cewa.
“Khausar nasan Sakayyar abinda nayi miki ne nayi muku sihiri na biku da bita da ƙulli”.
Daga nan ta tsinke da surutai duk wani abu data aikata musu saida ta faɗa.
Khausar kam baki ɗaya ilahirin jikinta rawa ya fara cikin tsananin kiɗima mamaki da al'ajabi gami sa tsoro.
Duk da cewa tana zarginta bata taɓa tunanin abin nata yakai haka ba.
Hajiya Bunayya kuwa miƙewa tsaye tayi sai kuma ta durƙusa tana ƙoƙarin naɗa zaninta tace.
“Khausar kiga yanda tsutsotsi suke cina yanda na dawo”.
Cikin sauri Khausar ta riƙe hannunta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Umma kada ki nuna min Ummu kiyi addu'a Allah ya yaye miki kuma in Sha Allahu nima zan miki addu'a nikam na yafe miki”.
Idanunta ta mayar kan Amina kana tace.
“Amina Allah ya baki lafiya Ubangiji ya yaye miki zan faɗa wa Yah Moddibo ya miki addu'a Allah yaye miki kuma zan sa Dr Jameel zai zo ya duba ku in Sha Allahu Allah yaye muku ya baku lafiya mai amfani mai albarka Allah ya yafe muku shurkar da kukayi”.
Da karfi Hajiya Bunayya ta fisge hannunta dake cikin na Khausar kana tace.
“Um-um Khausar ki bari in nuna Miki abinda ke cina kiga *Sakayya* data diromin”.
Cikin sauri Khausar ta girgiza kai tare da cewa.
“A'a Umma basai kin nuna min ba wannan bai kamata ba ai”.
Ta ƙarashe maganar hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta ganin ta da Amina ke wani irin numfashi tana hura yayin da take zazzaro harshenta waje tana kaɗawa kamar yanda maciji keyi”.
Asiya kuwa ta gaza cewa komai sau wani irin kuka mai cike da ƙuna da ƙuncin zuciya da take yi tamkar ranta zai fita.
Chapter 123 · 0% Book details