← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 150

Sashe 29

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Barka dai Aliyu ya gajiyar hanya tun ɗazu nake ta kiranka, shiru”.
Cikin lumshe ido yace.
“Alhamdullah Abba phones ɗin ne suna cikin jaka”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke cike da kulawa yace.
“Amma to ya hanya”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Lafiya lau hanya Alhamdulillah Abba gashi har na isa nayi sallar maghariba, yanzu wanka zanyi kafin sallar Isha'i ta gabato”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Alhamdulillah ahuta gajiya amma kafin nan ka kira Innayi da Malam Arɗo da kuma Ummin ka dan hankalinsu ya kwanta”.
Kai ya gyaɗa cikin alamun gajiya yace.
“Toh Abba Insha Allah zan kira”.

“Wanne hotel ka sauƙa”.
Abba ya tambaya.

Ɗan guntun numfashi ya fesar tare da cewa.
Sofitel Mouley Youssef na sauƙa Abba dan naga Hotel yanada Kekkyawan tsari kuma a binciken da nayi naga yafi kusa da Companyn' namu”.
Cikin gamsuwa Abba ce.
“Sosai ma kuwa, anan kusa da shine ma gidana yake inda nake sauƙa in nazo. Kaima dan ba'a gyarashi bane shiyasa”.
Miƙe tsaye yayi da wayar saƙale a kafaɗarsa yace.
“Amman yanada tsada kam”.
Shi kuwa Abba gyara zama yayi tare da cewa.
“Ka zauna anan zuwa lokacin da za'a gyara gidana dake nan bayan hotel ɗin ƙadan, sai ka koma can, zan turo maka mai gadin gidan zai zo ya kawo maka key ɗin motar da zaka rinƙa zirya dashi, zai kuma nunnuma maka duk abubuwan da suka dace”.
cikin gamsuwa yace.
“Toh Abba sai yazo”.
Daga nan sukayi sallama.
Yana katse kiran yayi dearling number Innayi lokacin da kiran ya shiga Innayi na kan Sallaya bayan ta idar da sallan maghariba tana ganin kiran tace Alhamdulillah kana ta ɗaga tare da kaiwa kunnenta tace.
“Moddibo”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da komawa yayi bakin gadon ya kishingiɗa kana yace.
“Na'am Innayi”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyin murya tace.
“Fatan ka isa lafiya?".
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah”.
Numfashi ta fesar kana tace.
“Masha Allah cikin Rabat kake ko kuma cikin gefenta kake?”.
Cikin alamun gajiya yace.
“A'a cikin Rabat nake a tsakiyar garinma kuwa”.
Kai ta gyaɗa cikin sauke numfashi tace.
“Wace Unguwar?”.
Hannu yasa tare da shafa sumar kansa kana yace.
“Tsetse amman a hotel ne”.
Kai ta jinjina tare da sauke numfashi tace.
“Ayyah Tsetse kuma kai bansan Unguwar ba”.
Ware ido yayi tare da miƙewa daga kishingiɗar da yayi da mamaki yace.
“Dama to kinsan Rabat ne bare kisan Unguwannin su?”.
Cikin sauri ta girgiza kai kana tace.
“Um-um bansani ba amma ban taɓa jin sunan bane”.
Ahankali yace.
“Ayyah yanzu ina so inyi wanka ne”.
Kai ta gyaɗa cike da kulawa tace.
“Toh shikenan ahuta gajiya”.
Daga nan ya kira Ummi da Malam Arɗo bayan sun gama gaisawa ya shiga toilet, da ido yabi turaren wanka Maclean brush towel pich colour yana kallo komai na ciki sabone Anutse ya fara wankan lokaci ɗaya yaji tsikar jikinsa na miƙewa sabida wanirin sanyin na ratsa baki ɗaya ilahirin jikinsa, cikin sauri yaja dogon tsaki Aransa kana yace.
Anya wannan aljanar yarinyar zata bar rayuwata ta nitsu kuwa, yarinya sai mata da nacin tsiya.
Towel ya janyo ya ɗaura kana ya ɗaura alwala ya fito dai-dai lokacin aka kira sallar Isha'i jikin Dressing mirrow ya nufa ya shafe jikinsa da mai kana ya fesa turare sa masu daɗin ƙamshi kana ya buɗe jakarsa ya ciro Jallabiya Sky blue me taushi kana ya ɗaura hirami kamar ɗankwali ya riƙe farin carbin sa sosai yayi kyau tun da aka sace M Jameel aka kashe sa bai sake yin wankan daya nutsu irin na yau ba yana fita ya nufi Masallaci akayi sallar Isha'i ana idarwa yayi adduo'i kana sai da aka wawwatse kafin ya fito ya nufi cikin ƙoƙarin shiga ya haɗu da mai gadin na fitowa.

Kallonsa mai gadin yayi cike da girmamawa yace.
“Aliyu Youssef Mouley?”.
Ya faɗin sunan da sigar tambaya tare da duba hoton Modibbo da Abba ya tura mishi ta whatsapp.
Kai Modibbo ya haɗa mishi tare da bashi hannu.
Cikin fara'a mutum miƙo hannunsa tare da cewa.
“Assalamu alaikum Yah Mouley”.
Rumtse ido Modibbo yaui domin tunowa da Jalaladdeen ne kaɗai ke kiransa da wannan suna. Sai kuma ya ƙara rumtse idanun da ƙarfi, sabida tunowa da tsawon lokacin da baiji motsin Jalaladdeen ba, tun kafin a sace. Jameel, ya tabbatar babban abune kaɗai zai iya ritsa Jalaladdeen da har zai iya hanashi nemansu na tsawon wannan lokacin.
Cikin sauri ya buɗe idanunsa tare da gyaɗa tsayuwarsa yana jan Carbin hannunsa jin Mutumin na cewa.
“Sunana Habibullah nine mai gadin gidan Alh Bashir kuma nike kanshi in yazo duk inda zaije nike kaishi kuma nida matata ke zaune a BQ ɗin gidan”.
Kai Modibbo ya gyaɗa masa tare da cewa.
“Eh Abba ya gaya min”.
Jinjina kai mai gadin yayi tare da cewa.
“Ganan abinci na kawo maka”.
Kallonsa Moddibo yayi da mamaki yace.
“Abinci kuma?”.
Kai mai ya gyaɗa alamar Eh.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da kallon womers ɗin hannunsa yace.
“Toh daga ina aka samu abincin?”.
Murmushi mai gadin yayi kana yace.
“Ai akwai abokin Alh anan lokacin da Marigayi Jameel yazo har ya koma daga can ake kawo masa abinci”.
Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyi yace.
“Ayyah yayi kyau angode”.
Sannan yayi gaba, mai gadin kuma na biye dashi.

Bisa kujerar ya zauna shi kuwa Habib kai tsaye dining area ya nufa kana ya ajiye mishi ɗan kondon da kulolin ke ciki, kana ya dawo gabanshi tare da miƙa mishi key ɗin mota tare da cewa.
“Ga wannan da ita zamana fita, in kuma baka son draving ga number'n ta sai ka Kur'ani, zanzo in kaika duk inda kakeso”.
Ya ƙare mgnar tare da miƙa masa hannunsa alamun ya bashi wayarsa ya saka mishi number's.
Wayar ya miƙa mishi ba tare da yace komai ba.
Shi kuwa Habib number's sa ya sawa wayar Modibbo kana ya miƙa mishi.
Amsa yayi tare da ajiye wayar.
Shi kuwa Habib sallama yasa kana ya miƙe ya ficee.

Shi kuwa Modibbo a hankali ya miƙe jin yadda cikinsa ke ƙugi alamun yunwa.
Dinning table ya nufa, kujerar yaja ya zauna tare da zuba abinci kana ya fara ci bayan ya gama ne ya dawo falon.

Lumshe yayi dearling number Abba.
Bayan Abba ya ɗaga sun sake gaisawa ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Toh Abba yanzu me ake ciki idan Allah yakai mu gobe dame dame za'a fara?”.
Kai Abba ya Girgiza cikin yanayin sanyin muryarsa yace.
“A'a Moddibo gobe kam ka huta tun da kaga yau Alhamis gobe kuma jumma'a ne ba aiki a ƙasar tasu dan jumma'a da asabar ne ranakun hutun ƙarshen makonsu, shiyasa dama naso yau ka tafi ka kwana ka huta gobe ma huta sai jibi lahadi in Allah ya yarda zaka fara zuwa Company”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba Allah ya kaimu”.
Ameen Abba ya amsa kana sukayi sallama.

Miƙewa yayi akan kushin ɗin ya lumshe Idanunsa a hankali yayi miƙa da alamun gajiya kasancewar yayi doguwar tafiya sannan dan kusan wuni yayi a zaune, da fari akan ƙarfe tare jirginsu zai tashi. Ashe tun dare sun mishi text sun caza lokacin tashin sun meda sai biyu zasu tashi bai ganiba, saida yazo Airport ɗin, shiko yanaga komawa ciki wani jidaline shiyasa ya zauna anan kawai.
To hakan ne yasa ya wuni a zaune, shiyasa gaba ɗaya gaɓoɓinsa ciwo suke masa ahankali ya gyara kwanciyar sa still Idanunsa na lumshe cikin sauri ya miƙe kana ya tashi ya zauna numfashi mai zafi ya fesar, tsaki yaja kana ya miƙe tare da nufar ƙofan Falon ya fita yana mgnar zuci Mayya jarabebbiya nan ɗinma sai kin adaddabeni.

Ahankali ya tsirawa coumpund ɗin ido zuwa wajen ganin yanda fitilu suka haska wajen kamar rana komai na hotel ɗin abin burgewane da ban sha'awa ne ahankali ya fara taka step ɗin farandar yana sauƙa kallon dattijon mai gadin dake zaune daga can wurinsa ya nufa,
Duk da tarin motocin dake wurin Hausa wurin ya cunkushe ba, yayinda kuma kowa harkar gabansa yake.
Hannu ya mikawa tsohon tare da yi mishi sallama.
Cikin tsananin girmamawa tsohon ma ya bashi hannu tare da zuba mishi ido cikin ƙare masa kallo.
Shi kuwa Modibbo a ya buɗe bakinsa tare da ɗan ɗaga sautin muryansa yanda zaiji yace.
“Baba”.
Miƙewa Dattijon yayi tare da da ɗan rusunawa kana ya ɗan ɗaura hannunsa na dama kan kirjinsa tare da ɗan sunkuyawa cike da tsananin girmamawar da ta fara bawa Modibbo haushi ya za'ayi dottijo kamar wannan yake kishi haka, in Habib ya mishi haka zai iya amsa sabida ya girmeshi.
Numfashi ya fesar tare da ɗan sakin fuska jin dottijon na cewa.
“Na'am Alh ya aka yi?”.
Gyara tsayuwar sa yayi kana yace.
“Baba kana zaune kai kaɗai ne?”.
Kai Dattijon mai gadin ya gyaɗa kana yace.
“Eh Alh gacan abokan aikina yanzu sune a bakin gate, ni sai da safe zan koma can kuma, yanzu anan nake”.
Ya ƙare mgnar yana buɗe wani mutun da yazo shiga, saida mutumin ya shiga kana ya kuma rufewa.
Girgiza kai Moddibo yayi yana kallon kalimin Dattijon numfashin ya fesar tare da cewa.
“Sunana Aliyu Youssef Muhammad Mouley, daga Nigeria amma kakata tana kirana da Moddibo zaka iya kirana Modibbo”.
Jinjina kai Dattijon mai gadin yayi yace.
“Ayyah Alh yayi kyau”.
Chapter 29 · 0% Book details