← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 150

Sashe 145

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hajja Nana da Innayi ce zaune da Khausar aɗaki yayin da Innayi ta zuba mata abinci ta bata taci Momy kuma na riƙe da jiriri tayi masa wankan Yamma ta saka shi cikin wasu fararen kayan sanyu masu masifar taushi pink and white collar.
Anutse Moddibo ya shigo ya same su Kai tsaye bakin gadon ya wuce gefenta ya zauna.
Kallonsa hajja Nana tayi tare da cewa.
“Wai kai kam baka jin kunya ne?”.
Juyawa yayi ya kalleta kana yace.
“Kin iso da sa ido ko? Idon ki be iya gani bakinki yayi shiru ko?”.
Hararansa tayi tare da faɗin.
“Ba dole ba idan bani nake taka maka birki ba babu mai taka maka birki”.
Kallonta yayi tare da cewa.
“Toh sai kiyi mugani in birkin zai taku”.
Anutse Khausar ta kallesa kana ta kalli Hajja Nana tace.
“Yah Mu'allim rabu da ita”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Aima na rabu da ita?”.
Khausar kuwa nutsuwarta ta tattara kana tace.
“Yah Mu'allim gashi har gobe suna in Allah ya kaimu”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh”.
Ahankali ta langwaɓar da kai tare da cewa.
“Kuma banji ka faɗa min sunan yaron ba”.
Murmushi yayi kana yace.
“Kuma tun a asibiti kafin ayi mishi wanka na masa huɗu ba tun kafin ki farfaɗo”.
Murmushi tayi kana ahankali tace.
“Kuma Yah Mu'allim baka faɗa min ba".
Juyawa yayi ya kalli Asma'u kana ya kalli Asiya dake cewa.
“Ai dai kam bamu san sunan yaro ba gashi har gobe Suna”.
Didi kam ido ta zuba mishi tana kallonsa Momy kuwa sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana sawa Jaririn safan hannu tace.
“Toh menene sunan”.
Sunkuyar da kansa ƙasa yayi kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Sunan shi Jameel”.
Cikin tsananin jin daɗi Asma'u ta kallesa tare da cewa.
“Allah sarki Yah Moddibo Ubangiji Allah ya saka da Alkhairi Allah yabar zumunci ayyah Yah Jameel ɗina Allah ya raya shi Allah ya mishi Albarka”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ameen ya Allah Asma'u, Allah yasa ya biyo halin takwaransa”.
Ya ƙare maganar yana Murmushi.
Innayi ce ta amshi zancen da cewa.
“Naji Ibraahim kuna na kiranshi da *Keyan*”.
Kai Modibbo ya jinjina tare da cewa.
“Eh laƙanin kenan. Amman asalin sunan Jameel, Allah ya raya mana shi yayi nagarta irin ta mai sunanshi”.
Cikin tsananin jin daɗi Asma'u tace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”.
Khausar na Murmushi tace.
“Ameen ya Allah yasa ya biyo halin takwaransa Allah yasa yayi Ilimin takwaransa”.
Cikin jin daɗi Didi tace.
“Ka kyauta Babana Allah Ubangiji ya raya mana Jameelu”.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”.
Cikin tuno da Jameel Hajja Nana tace.
“Ameen ya Allah ai Jameelu mutumin kirki ne”.
Asma'u kuwa cikin sauri ta ɗauki waya tare da kiran Ummi Ummi na ɗauka tace.
“Ummi albishir”.
Daga ɗaya ɓangaren Ummu tace.
“Goro”.
Cike da farin ciki Asma'u tace.
“Yah Jameel ya samu takwara”.
Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
“Hmmm Asma'u kenan kece baki sani ba amma ainin tun ranan Aliyu ya faɗa min”
Murmushi Asma'u tayi kana tace.
“Ummi shine baki faɗa min ba ranan muna hira ina cewa Ala'andi wani suna za'a sawa yaron kikayi shiru ashe duk kin sani”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Na sani mana tun ranan ya faɗa min”.
Murmushi Moddibo yayi tare da cewa.
“Ai TOH na rigaki yin albishir ɗin”.
Dariya ta sanya tace.
“Wallahi Yah Moddibo Ina sauri in rigaka ashe ka rigani”.
Haka sukayi yinin ranan anata shirye-shiryen suna, nan washe gari suna akayi raɗin suna da hidindimu kamar yanda al'adan masarauta take.

Bayan sallar la'asar manyan Fada ne a zaune saboda Aranar Abualeey yake son yin Murabus ya barwa Moddibo sarauta.
Bayan an zauna an cika a Fada anyi komai an taru Sarkin Al'adun Fada ne ya juya ya kalli Moddibo dake cikin wani irin shiga na alfarma da kawa da yayi masifar fitar da ainihin kyawunsa da ƙwarjinsa kana yace.
“Alhamdulillah kamar yanda al'adun Fada take sarki yana da dama da iko da zai yi Murabus tun yana da rayuwarsa ya danƙa Mulki a hannun ɗan sa da yake ganin zai iya gadon mulkinsa kana zai iya kula da Masarauta yanda ya kamata dan haka Sarki Youseef Mohammed Aliyu Mouley ma yayi alƙawari zai maida Sarauta ahannun ɗan sa Aleeyu Youseef Mohammed Aliyu Mouley”.
Cikin jin daɗi Manyan cikin Fada da Manyan Masarautu na gefe-gefe wanda baki ɗaya sun san da Maganar an samu sa hannunsu tun watanni hudu da suka wuce kowa cikin jin daɗi da farin ciki yake faɗin Alhamdulillah.

Cike da girmamawa Sarkin Fada ya juya ya kalli Moddibo tare da cigaba da cewa.
“Kuma a wannan ranane za'a ƙara wa Sarki Aleeyu Youseef Mohammed Aliyu Mouley mata kamar yanda atsarin Masarauta sarki bai kasancewa da mace ɗaya sai an masa biyu aranan da za'a danƙa mulki a hannunsa”.
Cikin sauri Moddibo ya ɗaga kansa ya kallesu sai kuma ya saki wani Murmushi dashi kaɗai yasan ma'anar sa juyawa yayi ya kalli Abualeey dake cikin matsanancin farin ciki kana ya kalli Sarkin Fada tare da cewa.
“Ina son magana da mahaifina”.
Kai Sarkin Fada ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan ba damuwa”.
Kana suka shiga ɗakin Sirri Shida Abualeey, Waziri, Galadima Wambai Garkuwa...

A dai-dai lokacin kuma acikin gida Khausar ce cikin shiga ta alfarma sanye take cikin wani lafiyayyan Abaya Pinch colour mai masifar taushi da santsi da yasha duwatsu kana ta ɗaura Alkyabba ta Masarauta fari ƙall mai masifar taushi wanda al'ada ce ta Masarauta wanda ranan da za'a naɗa mijinka a Masarauta zaka sa.
Shima Jaririn sanye yake cikin shiga na alfarma wasu picnh colour kayane tausasa kana aka daura masa ƙaramin Alkyabba fari irin na jarirai.
Sai hotuna suke ta ɗauka dasu Lalla, Khadijah Lalla, Hafsat Asiya, Asma'u, Dija, Rahama, Raudat Asma'u kuwa kai tsaye take turawa cikin group ɗin su na class mate ɗin su da suka gama makaranta.
Nan da nan cikin group ɗin ya kace me da surutu kala-kala kowa na tofa albarkacin bakinsa wata ƙawarsu wacce lokacin da suke makaranta bencinsu ke kusa da nasu Khausar mai suna Hawwa Idris ne tace.
“Ikon Allah wai Khausar ce haka🤔 girma yazo rawan kai ya gudu?”.
Tayi typing da emotion na mamaki dariya Asma'u ta tura mata tare da cewa.
“Gashi kuwa kinga zahiri”
Cikin Mamaki tayi voice dan gani take typing ɗin bai mata sauri kana tace.
“Masha Allah shiyasa akace arayuwa kada ka taɓa wulakanta mutum domin baka san baiwar da Allah ya mishi ba wai yau Khausar ce matar Sarkin Morocco kuma Malam Moddibo?”.
Hoton dariya Asma'u ta sake tura musu tare da faɗin.
“Aikam ikon Ubangiji yafi gaban haka?”.
Wata mai suna Jidda ce tace.
“Aikuwa dai muma Allah yasamu Adamshin ku Asma'u ku kam kunji daɗin rayuwarku”.
Murmushin Samira Sani ta turo tare da cewa.
“Uhmmm kuma ku godewa Allah a yadda kuke ɗin”.
Da sauri Khadijah Sule tace.
“Sosai ma kam Samira am”.
Amin kuwa cikin sanyi da nadama tace.
“Alhamdulillah ai in Allah ya baka lfy ka gode masa”.
Haka dai suka cigaba da hira acikin group ɗin kowa na faɗin albarkacin bakinsa.

_Daga can gefe kuwa su ne Rafi'a,Tutus kitchen, Mom sayyeed&Noor Tatti Dija chiroma, ne da suka halarci wajen sunan ne suke ta Video da hotuna suna turawa cikin Group ɗin SAKAYYA Team Moddibo da Khausar kam baki yaƙi ruhuwa duk farin ciki ya cika su ganin irin gift da Khausar ta bayar akawo musu._

_Daga can gefe kuma ƴan karatun bati siddan na Allah ya isa kenan da basu biya kuɗi ba suke wiƙi-wiƙi da ido duk hakki ya hanasu sakewa da samun nitsuwa..._
Chapter 145 · 0% Book details