← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 150

Sashe 37

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai Mommy ta gyaɗa tare da kallon Haiydar tace.
“Sannu Babana mu gani”.

“Mommy Ummina tace in gaisheki”

Jinjnna kai Mommy tayi kana tace.
“Ina amsawa”.
Hannun Asma'u Khausar taja suka shiga Bedroom ɗinta suna shiga Khausar tace.
“Fisabillah baki zoba sai yanzu ko dai kwana zamuyi?”.
Zare ido Asma'u tayi kana tace.
“Mu kwana kuma wa zai taya Ummina aiki da safe?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi sai kuma tace.
“Don Allah Asmeey mu kwana zan kira Ummi mu roƙeta”.
Kai Asma'u ta girgiza kana tace.
“A'a keto muje mu kwana mana”.
Ware ido Khausar tayi tare da sanya dariya tace.
“Caɓɓ lallai kam”.
Murmushi kawai Asma'u tayi kana ta zauna abakin gadon.
Khausar kuwa fridge ta buɗe ta ɗauki Plate ta sanya Faro water da Ayaba ta mikawa Asma'u.
Karba Asma'u tayi tana ɓare Ayaban tace.
“Ke dai bakya rabuwa da Ayaba aɗaki kina nan kamar biri”.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Wallahi kuwa Ina son Banana yana min daɗi”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ai lallai dai kam”.

*Morocco*

Aɓangaren Moddibo kuwa haka yaita fama bayan minti talatin cikin yake sake Murɗansa yana kallon gari yayi duhu maghariba ta kawo kai har wasu massallatai sun fara kiran sallah amma ya kasa miƙewa saboda yanda ciwon cikin ke kartansa jin ciwon ya lafa yasa ya miƙe tare ya fita yaga wajen shiru alamar duk ma aikata sun tattafi sai securities da mai bawflowes ruwa kasancewar karfe biyar da wasu Mintuna ake tashi ma tsaye wajen motarsa yashiga yaja ya fita a gate one.
Ya miƙe titin ya fito gate ɗin La riva restaurant dake Opposite da Company yazo Dai-dai wajen Traffick sun tsaida shi saboda sauran motoci da suke wucewa ahankali yasa hannunsa ya dafe fuskarsa ta gefe yatsunsa na dafe da kuncinsa ya tsansa ɗaya kuma na cikin bakinsa kana ya fito da fuskarsa ta wajen motar yana ɗan shan Iska jikin katangar Company sa yana shaƙan iskar bishiyar dabino dake zagaye da Company wanda ta ko ina sune da gudu yaga wata mota ta gilma ta gabansa wacce ta fito daga gefen yamma zata yi gabas kana shi kuma yana gefen kudu ne idan ya samu dama zaibi arewa ganin wulgawar motar yaga fuskar J ɗinsa ne aciki cikin sauri ya zare Idanunsa sakamakon kallon fuskar J ɗinsa aciki Motar cikin wani irin sauri ba tare da anbasa hanya ba ya figi motar ya karya kwana yabisa har ya kusa bige wata mota.

Da mugun gudu yake bin motar kana ga cunkoson ababen hawa kasancewar maghariba ta kawo kai ƴan kasuwa sun taso ga kuma ma'aikata sun tattaso daga Office kowa na burin komawa gida wasu kuma na ƙoƙarin su samu masallacai dan kada su rasa jam'i hakan yasa cunkoso yayi yawa ga kuma duhun gari gudu yake yana bin bayan motar ga kuma cun kuson motoci da suka taresa ya cusa ta nan yaga antaresa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake tun lokacin daya zare idonsa har yanzu bai maidasu daidaiba saboda idanunsa sun gane masa Allah ya nuna masa fuskar Jameel ɗin sa ne yasani Koda amagagin mutuwa yake ya tabbatar fuskar Jameel wulgawa daya zaiyi ya gane yasani wannan fuskar Jameel ɗinsa ne baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kana yana maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yana cigaba da dannawa motocin gabansa hon baki daya mutane Kallonsa suke wasu kuma na cewa wannan kam lafiyarka ina zakaje haka kamar zaka tashi sama shidai haka ya cigaba da tafiya ya kutsa tanan ya kutsa tacan garin hakane ya bigewa wani motarsa mutumin na cewa Kai lafiya amma ina tuƙi kawai yake da gudu baki ɗaya hankalinsa baya jikinsa wani mai Napep ne ya tare gabansa madadin ya kalli gabansa amma baki ɗaya idanunsa na kan motar daya yaga J ɗinsa aciki yana samu ƙaramar ɗin ya kauce masa ya cigaba da bin bayan motar yanda yake gudu da masifaffen ƙarfi haka zalika motar da yake bi ɗin ma take gudu hakan yasa yasake tabbatarwa kansa J dinsa ne kenan gudunsa yake ko kuma yaya ahaka suka isa wani roud about nan yaga ya ɗauki hanyar da zata sa dashi da flyover gudu yake da ƙarfi haka shima wancen ke gudu duk da gudun da yake amma ya kasa kamo wancan motar saboda shima gudun yake ga kuma motoci dake tsakaninsu amma yana iya hangosa kasancewar be wuce motoci biyu zuwa uku bane agabansa sunzo daidai kan Flyover yasamu yabi sama Shima Moddibo cikin sauri yabi sama kasancewar ba cunkoso sosai numfashi mai karfi ya sake kana ya hau kan Flyover yabi sana kafin ya isa tsakiyar Flyover shi kuma wannan har ya sauƙa ya ɗauki hanyar Unguwar Mellila shima Moddibo cikin sauri yabi wannan hanyar tafiya kaɗan sukayi yaga motar ta wuce wani asibiti cikin gudu shima ya wuce tafiya kaɗan suka ƙara yaga motar taja kwana adai-dai wani tamfatsetsen gini mai masifar kyau da girma bisa duk kan alamu asabiti ne saboda sunan dake manne asaman ginin idanunsa ya ɗaga yaga sunan dake manne ajikin ginin *Youssef Mouley Hospital*.
Mai motar kuwa yana danna hong aka buɗe masa gate yashiga kafin ya juya akalar motarsa ya ƙarasa wajen kuma a maida gate din ana ƙoƙarin rufewa da wani irin sauri ya danna hancin motarsa cikin gate din.

Cikin sauri securities dake bakin gate din suka taso suka yo Kansa.
Shi kuwa mutumin cikin motar tuni yayi Parking ya buɗe motar ya fita da sauri Norses biyu suka biyu bayansa suna faɗin.
“Welcome Sir”.
Security din kuwa kan Moddibo suka nufa suna faɗin.
“Lafiya kuwa?”.
Shi kuwa Moddibo gadan-gadan ya nufi kan security din da sauri suka kauce masa yana shiga yayi Parking kana ya fito da sauri security suka yo kansa suna faɗin.
“Lafiya kuwa?”.
Bai tanka suba yabi bayan mutumin yana cewa.
“J!,J!!,J!!!,”.
Shikuwa Mutumin gaba yayi Norses na biye dashi jin hayaniya yasa ya juya ya kalli bayansa gani yayi Moddibo ya nufo kansa yana cewa.
“J”.
Security kuwa ƙoƙarin riƙesa suke suna faɗin.
“Malam lafiyar ka kuwa ina zaka je?”.
Cikin sauri Moddibo ya hankaɗesu kana cikin fushi yace.
“Ka matsa min anan ka bani hanya, J!J!!”.
Wata matace ta fito daga cikin Hospital din ta ƙaraso kusa da wannan mutum kana tace.
“Dan Allah Dr Jameel kayi sauri kaceci rayuwar ƴata tana cikin hatsari”.
Jin haka ne yasa Mutumin da takira da Dr Jameel ya juya ya nufi cikin asibitin.
Moddibo kuwa da gudu yabi bayan Dr Jameel da already ya shiga cikin reception tamkar wani zautacce haka ya dawo baki daya bashi da wani cikakkiyar nutsuwa Akuma dai-dai lokacin yaji cikinsa ya sake kartawa da masifaffen ƙarfi da gudu ya nufi kan Dr Jameel yana cewa.
“J!,J!!,J!!! Ina zaka je”.
Afusace Dr Jameel ya tsaya tare da juyawa yace.
“Wai lafiya Malam Security ku fita dashi mana me kuke jira ha'a ya zaizo yana mana ihu yana firgita mana marasa lafiya”.
Baki ɗaya Norses da sauran mutanen ido suka zubawa Moddibo.
Cike da girmamawa security yace.
“Yallaɓai munyi ƙoƙarin korinsa amma yaƙi tafiya sai turemu yake”.
Juyawa Moddibo yayi jin J ɗinshi na mgn da larabci wai a koreshi, da sauri ya buga hannunsa aƙirjin Dr Jameel Cikin juya harce zuwa larabcin yace.
“J ni kake cewa akaro?,J nine fa A.J ɗinka ni kake cewa akaro?”.
Cikin fushi Dr Jameel ya fincike hannun Moddibo ajikin rigarsa yace.
“Ka sakeni wanene kai a ina na sanka kaji yanda kake ihu kana gigita mana mutane”.
Ya ƙare mgnar yana yiwa Modibbo wani irin kallo mai cike da tarin mmki da kuma son nazartan abubuwa da yawa musamman kamaninsa.
Shi kuwa Modibbo Cikin rauni da tsanananin tashin hankali da azabebben ciwon ciki Moddibo ya sanya tafin hannunsa ya dafe maransa muryarsa na rawa yace.
“J Nine fa J A.J ɗinka kake cewa baka gane ba Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J nine yau kake cewa baka sani ba?”.
Akuma dai-dai lokacin cikinsa ya sake murɗawa da masifaffen ƙarfi cike da ɓacin rai Dr Jameel ya Kalli security kana yace.
“Ku fitar min dashi”.
Norses ɗin kuwa cikin alamun damuwa suka ce.
“Dan Allah Dr muje ka duba matarnan”.
Juyawa Dr Jameel Yayi Moddibo kuwa ganin haka yasa Cikin wani irin rauni ya kallesa muryarsa na rawa kana numfashinsa na fusga yace.
“Jameelu nine fa aduniya Koda baza ka gane kowaba amma Ni da Ummi da Abba bamu cancanci kamanta damu ba kuma ko me yafaru da kai aduniya Ni dai da Ummi da Abba bamu cancanci ka ce baka gane muba A.J dinka nefa”.
Yana gama faɗar haka ya yanke jiki yayi baya...

*Zakusha Typing errors dan banyi editing ba, wani wurin zakuga kalaman a baude ko baibai*

By
*GARKUWAR FULANI**SAKAYYAH book 2... page 10*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Chapter 37 · 0% Book details