← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 150

Sashe 44

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman haka nan yaji wani irin amintaccen nitsuwa da salama a ranshi.
Haka nan yake jin farin ciki, tafiya mai nisa sukayi kafin suka wuce Sheikh Zayed hospital tafiya kamar na kimanin minti goma suka yi suka isa Fadar masarautar ƙasar Marocco baki ɗaya.
Ta cikin jahar Rabat suna isa Dr Jameel Yayi Hong ganin motarsa yasa aka buɗe masa gate ɗin.
farko yana shiga Moddibo ya mara masa baya tare da rumtse idanunsa da ƙarfi sabida harbawar da zuciyarsa tayi kamar zata haɗin ƙasa. Da sauri ya kuma buɗe idanunsa tare da sauƙesu can sama kan tambarin masarautar.
Lokacin ɗaya yaji jikinsa ya fara tsuma, kana duk tsikar jikinsa ta miƙe tsaye.
Da sauri ya kutsa kai cikin tare da bin Dr Jameel bamba to bamba yana shiga yaji zuciyarsa ta buga da Masifaffen ƙarfi wani irin tsuma yaji jikinsa nayi amaimakon yabi motar Dr Jameel da kallo sai ya kuma bin Cikin masarautar Da kallo daga kan dogon ginin zuwa shimfiɗeɗɗen kwalta da kuma yanda tsarin yake baki ɗaya ginin zagaye yake da bishiyoyin dabino ta ko ina masu tsawo, da sukayiwa illahirin ganinsa ƙawanya.
Ahaka suka isa wani babban gate Dr Jameel yayi hong aka buɗe masa yana shiga Moddibo ya mara masa baya.
Shi kuwa Dr Jameel sabida wayar da yakeyi yasa hankalin sa baya kai kan Modibbo ba.
Sassayyan numfashi Modibbo ya saukeganin yadda hadiman ke zirya da hidima.
Yayinda su kuwa
Fadawa da hadiman basuma ga fuskarsa amman a zatonsu tare yaje da Dr Jameel shiyasa basu hana shi shigaba.

Suna shiga gate na biyu suka isa dai-dsi kan wani RounAbout mai masifar kyau tsakiyar farfajiyar fadan. Yayinda hanyoyi guda huɗu suke zagaye dashi, kana gefe-da gefen ko wacce hanya bishi yoyin yan gajjerun dabino ne, masu ɗauke da yaya ringis a kai.
Kana tsakanin, wanda yake miƙe da ta inda su Modibbo suka fuskanta kuwa wani babban baranda ne wanda yake da staps goma sha biyu, a staps ɗin forko Hadimai ne, guda biyu gefen hagu da damansa, sai kuma a steps na shida suma hadi mai biyu sai ana sha biyu su kuma hadimai bibbiyu ne hagu da dama, wata babbar ƙoface mai kyan gani da daukar hankali da kuma taswirar manomi a cikin kekkyawar gona.
Daga nan cikin RounAbout ɗin kuwa a yalwace yake da shuke-shuke na dukkan samfurin kayyakin da ƙasar suke nomawa kasancewarsu manomane, daga tsakiya kuma
Mutun butumin wani ingarman Doki da linzaminsan cikin ado na ƙawa kasan dokin kuma zagaye yake da Grass Capet sai kuma mutum-mutumun mutane biyu da fatanya a hannunsu sai na ɗawisu a gaban dokin.
Sai kuma ƙanan tituna da suka rabu kusan kashi takwas da alamu duka cikin Masarautar yake daga saman RounAbout ɗin anrubuta Barka da zuwa Masarautar Mouley da Larabci.
Daga gefe Dr Jameel Yayi parking yana Parking ya fito shima Moddibo ahankali ya ziro ƙafarsa ya taka ƙasa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafa ƙahon zuciyarsa sabida jin yadda tsikar jikinsa ya tashi yammm tamkar wanda aka watsawa ruwan ƙankara atsakiyar hunturun sanyi.
Cikin sauri Dr Jameel ya juya ya kallesa cike da mamaki yace.
“Yah Salam biyoni nan kayi bawan Allah Meyesa zaka bini har nan? Kasan inane nan kuwa? kasan meya kawo ni nan? kasan me nazo yi? Nace kama san ina ne nan kuwa? Nanfa ba cikin asibiti bane”.
Moddibo kuwa kasa cewa komai yayi saboda yanda tsikar jikinsa ke tashi baki ɗaya ya rasa yanda zaiyi sai kawai ya ƙanƙame jikinsa yana karkawar tamkar mazari.
Cikin sauri Dr Jameel
ya juya banyansu jin wata murya cikin karaji na cewa.
“Jama'a ku lura *Rinƙas* ya kunce ina Sarkin dawakai yake? *Rinƙas* ya kunce jama'a ku kauceeeeh”.
Cikin tsanani sauri fadawa da sauran jama'a dake zirya a tsakikar suka fara mannewa a jikin bishi yoyin dabinon domin sanin irin gagarumar illar da Rinƙas keyi a duk sanda ya kubce kuma babu mai iya sarrafa shi cikinsu sai sarki Dawaki ko Mai martaba Youseep Mouleey da kansa.

Moddibo kuwa jin yadda ake gudu da kuma ganin yadda kowa ke neman mafaka ne yasashi cewa *Rinƙas*
Yayi mgnar a fili a cikin ransa kuma ya kuma sake cewa.
“Rinƙas a na”.
Yayi mgnar tare da saurin juyawa sabida jin wani irin takun aukuwar ingarman doki lafiyeyye ya nufo kanshi gadan-gadan yana wani irin gigitaccen suƙuwansa da harba iska tare da barbaza gezan kwataccen dogon gashin dake kan wuyansa.
Gab-gagab Gab-gagagab Gba-gab, ya nufosa haiƙan ƙadaran.
Dr Jameel kuwa wani irin gigitaccen kara ya sake tare da artawa a guje, ya nufi kam ƙofar fadar.

Yayinda gaba ɗaya hadimai da bayi kuwa duk suka ɗaɗdaura hannayensu a kai tare da rumtse idanunsu baki ɗaya sabida gaba ɗaya sun gama sadaukarwa sai dai a dauke nuƙurƙushesshen gawar Modibbo.

Shi kuwa Modibbo juyawa yayi ya kalli gabas da yamma Kudu da Arewa na cikin masarautar gaba ɗaya jama'ar da ke ziryar duk sun manne da jikin bishiyoyin kai kace kadangarune.
Wanda ke gefen damansa ya kalla yadda ya zare ido tamkar zai fiddasu waje.
Bayanshi ya juya ya da sauri jin kukan wani mutun.
Da sauri ya juyo kan zaburarran dokin da yaji an kira da Rinƙas ɗin da yayiwa farin sani a mafarkansa.

Sai kuma ya kuma kallon dottijon da kallo ɗaya zakayi mishi kasan cikekken mahaukacine tubran.

Rinƙas kuwa wani irin gigitaccen haniniya da sukuwa mai bada sautin takunsa mai jawo hankalin mutane, yayinda daga can baya kuma mai gadin sashin dawakanne ke ihu da kururuwa tare da yin mgn cikin tashin hankali yake cewa Modibbo.
“Ka gudu! Nace ka gudu zai kasheka fa".
Sai kuma ya ƙara ɗaga murya tare da cewa.
“Sarkim Dawaki taimakon gaggawa”.

Dai-dai lokacin kuma Rinƙas yayi wani iri-iri haniniya tare da harbin iska kana ya baza gashin kan wuyanshi tare da zura ƙafafunsa na gaba suka tafi suuuwwwh kan Modibbo.

Shi kuwa Modibbo cikin tariyo yanayin da yake rayuwa da dokin a mafarkansa na tsawon rayuwarsa.
Ya ture hular kansa tare da girgiza kansa yayi yadda dokin yayi, kana ya saita ƙwayar idanunsa, cikin tsakiyar idanun dokin.
Tare da ɗaga tafin hannunsa na dama ya saita kan goshin dokin.
Wanda hakan ne kuma yasa dokin sakin wani hargitstsen haniniyar da saida ta ratsa kunnuwan tsarki da tawagarsa dake cikin fadar suna zaman yiwa Sarki Jabeer Nuruddeen Gwadabe sallama dan yau yake shirin komawa Nigeria.

Juyowa mai martaba sarki Youssef Muhammad Mouley yayi tare da kallon gefen da Sarkin Dawaki yake tare lunshe idanunsa wanda hakan kaɗai ya wadatar ya gane nufin Sarkin.

A can waje kuwa gaba ɗaya jama'ar idanu suka zubawa Modibbo da Rinƙas suna kallon sarautar Allah, shi kuwa Modibbo.
Lumshe idanunsa yayi tare da buɗasu cikin na dokin.
Wani irin ɗaga sawu sama dokin yayi alamun sarawa da kuma cikekkiyar sanayya yayi Modibbo, kana yayi ƙasa dasu a hankali ya manna goshinsa da tafin hannun Modibbo.

Shi kuwa Modibbo shafa sumar gaban goshin yayi tare da fesar da sassayyan numfashi.

Mutumin dake gefen sane yayi wani irin sake baki tare da furta Yah Salam.
Dan sai lokacin ya samu damar ƙarewa fuskantar Modibbo kallo.

Dokin kuwa cikin nuna alamun shaƙuwa da sanayya mai tarin yawa, ya rinƙa karkaɗa jelarsa tare da baza gashin wuyansa da sakin haniniya kana ya fara zaga Modibbo tamkar maiyin ɗawafi.

Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen murmushi yake tare da jujjuyawa yana kallon duk inda dokin yayi.

Saida ya zagayashi sau uku, sai kuma ya dawo gabanshi.
A hankali ya sunkuyo haka yasa Modibbo sumbatar wuyan dokin.

Dai-dai lokacin kuma sarki Dawaki ya buɗe ƙofar fadan ya fito da sassarfa ya fara taka steps din.

Shi kuwa Modibbo ɗan buge goshin dokin yayi sai ga dokin yayi ƙasa a hankali ya kwanta tare da karkarɗa jelarsa alamun so yake Modibbo ya hau kanshi.

Ya ilahi ya mujibatda'awato. Yah Salam, shine kaɗai abinda gaba ɗaya al'ummar dake kewaye da bishiyoyin suka fara faɗa tare da sauƙowa suka nufo Modibbo.

Shi kuwa Modibbo gashin saman wuyan dokin ya kamo tare da ja,
Haka yasa dokin miƙewa tsaye cike da biyayya.
Shiko Modibbon a hankali ya lumshe idanunsa, sai kuma yayi gaba dokin na biye dashi tamkar raƙumi da akala.
Duk da babu linzami a wuyan dokin.

Shi kuwa Modibbo ido a lumshe ya juya gefen hagunsa ya fara tafiya yana mai kallon taswirar hanyar inda zaije ya ɗaure dokin na dawo masa filla-filla kamar yadda yake gani a mafarkansa.

Wannan al'amari yayi masifar sa mamaki da kaɗuwa a zuƙatan al'ummar waje.

Dr Jameel kuwa ido ya zubawa Modibbo.
Yayinda sauran Hadiman kuwa gaba ɗaya hannun suka rinƙa ɗaurawa a ƙirzansu suna ɗan ronƙofowa kaɗan sunayiwa Modibbo wani irin gaisuwar ban girma.

Sarki Dawaki kuwa cike da al'ajabi da ta'ajjudin ganin yadda wani ke sarrafa Rinƙas ban ya sani duk duniya shida Abualeey ne kaɗai ke iya sarrafa dokin wato sarki Youseef, ko Ibrahim Mouley baya matsowa kusa dashi, kana ya sani kusan mutum uku ya kashe a cikin masarautar.

Hakane yasa ya fara sassarfa, amman ina ya kasa iso Modibbo da dokin domin shima da sassarfan yake tafiya ganin dokin na sonyin sukuwa.

Kana gaba ɗaya mutanen kuma yuuuh sukayi suka bi bayan Sarki Dawaki domin al'ajabin wannan al'amarin.

Tafiya mai nisa sukayi kana Modibbo yayi kwanan gefen yamma nan ma tafiya mai tsawo sukayi kana suka ɓullo kan wani ƙaton farfajiya wanda a ƙalla dawakai sun kai ɗari uku zuwa huɗu ke wurin.
Duk inda ka wulga idonka iya ganinka dawakaine a wurin. Shi kuwa Modibbo wata yalwatacciyar hanya yabi tare da ratsa tsakiyar dawakan ya wuce.
“Iko sai Allah”. Mutumin nan dake ya shelanta tsinkewar Rinƙas da gudu ya nufosu tare da maɗaukakiyar mamaki a fuskantar.

Shiko Modibbon ratsawa ya rinƙayi har ya isa inda nanne tirken dokin. Ɗaureshi yayi kana ya juyo.
Juyowarsa kuwa itace tasa numfashin Sarkin Dawaki kusan ɗaukewa a fili yace.
“Yah salam”. Sabida ganin kamannin fuskantar Modibbo tayi masifar girzashi, kawai sai ya ɗaura hannunshi na dama kan ƙirjinsa ya ɗan rusunar da kai, yayinda gaba ɗaya sauran ma haka sukayi.
Chapter 44 · 0% Book details