Sashe 19
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Bunayya na shiga falonta ta kalli Amina dake zaune kan 2sitter gyara zama Amina tayi tare da cewa.
“Mommy wai ɗazu hayaniyar me nake jine ina waya da Uncle Naseer ne yana gaya min tsarin ginin gidansa da ake gyarawa a cikin Abuja yace min in anyi aure zamu zauna a nan na wata ɗaya zuwa biyu kafin mu tafi India, shiyasa ban fito ba”.
Cikin jin dadi tace.
“Alhamdullah kice dai abu yanata kankama”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“ Eh Ummah Amman Hayaniyar me akayi ɗazun”.
Taɓe baki Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Ooo Kakar Khausar ce kuma yau tazo tana ta bala'i, banma san bala'in da take ba na dai ji tana cewa Khausar bata da kunya zata kalli tsabar idonta tace batason mijin da ta zaɓa mata tana da wanda take so, to bansan ya ake ciki ba dai. Ni dai tsoro na kaddai Nasseru take so?”.
Gyara zama Amina tayi tare da Girgiza kai kana tace.
“Ba dai Uncle Naseer ba Dan ko magana bata mishi, sai in shi ya mata, shima kuma baya mata magana sosai da nace masa bana so.
Sai dai ko ina wani can daban wayasan mata”.
Cikin jin daɗi Hajia Bunayya tace.
“Ato da sauƙi”.
Ita ko Amina gyara zama tayi tare da cewa.
“Uncle Naseer Kam yanzu ma wayar da muke yine, ya hanani fita.
Kuma cewa yayi anfara hada kayan lefe sannan kuma idan an tashi da kayan lefe da kayan gishi da goro da sadaki da kayan rufi duk za ahaɗa rana ɗaya za akawo”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da Jinjina kai.
Ajiyar zuciya Amina tayi kana ta cigaba da cewa.
“Kuma yace nan da wata ɗaya za'a ɗaura Auren mu sannan ana gama bikin a Abuja zamu tare baza mu wuce wata biyu ba in yayi yawa ne uku zamu wuce India sannan zai nema min admission In cigaba da karatuna”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da ran gaɗa guɗa kana tace.
“Alhamdulillah burina ya cika haka nake son ji da ace mun na cewa batun wannan yaron Jameel gashi ƴan Kidnapping sun kashesa a wofi”.
Kai Amina ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai dai kam Umma Allah ya rufa mnaasa asiri da na nacewa batun Malam Jameel da yanzu na zama matar Mamaci ina takaba”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.
“Aikam Allah ya tsareki yaje can Allah ya jikansa da Rahma”.
Cikin sanyin murya Amina tace.
“Ameen dai tun da yana da kirki Allah ya jikansa Allah yasa ya huta amma dai na kama dahir dana kama Uncle Naseer”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Kin kama dahir kam”.
Asiya ce da bata cika shiga mgnar suba, tunda Hajia Bunayyah tace mata zata tsine mata in tana damunta da batunsuji tsoron Allah, a hankali ta ninke hijabin da tayi salla dashi tare da miƙewa ta fito falo tana maiyi musu addu'ar shiriya.
Ita kuwa Amina da baki ta nunata.
Shashar uwa sai dariya tayi.
Suna cikin hiran wayar Hajiya Bunayya ya hau ruri tana dubawa taga Hajiya Lami cikin sauri tayi Picking tare da kaiwa Kunnenta Hajiya Lami najin tayi Picking batare da tayi Sallama ba ta fara kora mata jawabin abinda Samira ta faɗa mata.
Zare ido tayi cike da damuwa tace.
“Subhanallah toh Meyesa haka?”.
Cike da damuwa Hajiya Lami tace.
“Ban saniba amma ki shirya da daddare bayan sallar Isha'i ki rakani”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh nima zanje dama in Faɗa masa maganar Amina don tuni anfara hada kayan lefe, Gishiri, Goro, kayan rufi, da sadaki duk lokaci ɗaya za'a kawo kinga hankali ya kwanta”.
Jinjina kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“A hankali ya kwanta kam bari sai nazo ɗin dai”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Toh sai kinzo ba komai ki kwantar da hankalin ki”.
Aɓangaren Innayi kuwa har maghariba bata ji motsin Moddibo ba sosai hankalinta ya sake tashi.
Wunin ranan yini tayi tana kuka wanda lokaci ɗaya zazzaɓi ya kamata baki daya tunaninta ya ta allaka akan idan ta mutu ya Moddibo zai kasance awannan gari ya zaiyi.
Wasa-wasa har aka Idar da maghariba da Isha'i har misalin goma ba Moddibo ba labarinsa cikin sanyin jiki da tashin hankali ta miƙe ta nufi sashen sa tun kafin ta ƙarasa hawa barandar ta jiyo sheshsheƙan kukan sa cikin sauri ta ƙarasa hawa barandar tare da Murɗa Kofar falon tashiga kan Sallaya ta hangosa yayi Sujjada yana sheshsheƙa.
Cikin sauri ta zauna gefensa Muryanta na rawa tace.
“Subhanallah haba, Aliyu!, Haba Aliyu!!. Meyesa haka Aliyu ka ɗauki dangana mana kuka shine abinda zakayi ta raka Jameelu dashi arayuwar ka wannan soyayya itace zaka nunawa Jameelu kenan?”.
Anutse ya ɗago daga Sujjada tare da yin tahiya kana yayi sallama yana sheshsheƙa kana ya daga hannunsa biyu sama cikin raunin murya yace.
“Ya Allah Ubangiji kasa mafarki nake, Allah kasa in farka daga wannan hautsinennen mafarkin da nakeyi”.
Ahankali Innayi ta matsa kusa dashi tare da Kallonsa cikin sanyin murya tace.
“Haba Aliyu Meyesa kakeyi yin haka? ka kwantar da hankalin ka babu abinda ya gagari lamarin Ubangiji”.
Domin Ita batasan cewa yaji maganar da sukayi da Hajja Nana ba.
Ahankali ya ɗago idanunsa da suke kada sukayi jawur tamkar garwashi cike da mamaki take kallon yanda idanunsa suka sauya launi Muryanta na rawa tace.
“Aliyu lafiyar ka kuwa?”.
Kai ya Girgiza tare da cewa.
“Bakomai”.
Ya faɗa tare da lumshe Idanunsa domin ya rasa ta yaya zai fara tambayarta shin inane asalinsa shin waye mahaifinsa su waye ne tushensa, yanaso ya tamyan amma ya najin tsoro da fargaba da taraddadin ya tambaye, ya zama cewa kalaman da Hajja Nana ta faɗa da kuma zarginsa na tsawon shekaru ya zama gaskiya hakan yasa yaji tsoron tambayarta kamar yadda ya saba, haka ya meda tambayar cikin ransa, sunkuyar da kansa ƙasa yayi.
Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da rarrashin sa domin duk azatonta mutuwar Jameel ya tuna cikin rarrashi ta cigaba da cewa.
“Aliyu kayi haƙuri kowa da irin ƙaddarar da Ubangiji yake masa Addu'a zamu masa”.
Sunkuyar da kai Moddibo yayi hawaye ya cigaba da kwaranya daga Idanunsa.
Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da cewa.
“Kada kayi kuka Aliyu ko wani irin matsala ka shiga arayuwar duniya kada ka butulcewa Ubangiji da irin wannan kukan, babu abinda zai kawo maka banda tashin hankali da damuwa”.
Ta ida maganar tana zubda zafafan hawaye, kukan abubuwa biyu ne suke haɗe mata alokaci ɗaya kalaman Hajja Nana da kuma halin da taga Moddibo aciki yayi masifar ɗaga mata hankali.
Anutse Moddibo yasanya tafin hannunsa yashiga share hawayen fuskarsa muryarsa na rawa yace.
“Toh shikenan Innayi nayi shiru dan Allah kema ki daina kuka Ubangiji Allah yarufa mana asiri”.
Cikin muryan kuka tace.
“Ameen ya Allah”.
Miƙewa tayi tare da fita ba daɗewa ta dawo hannunta riƙe da Warmers din abinci ta ajiye masa agabansa kana tace.
“Gashi kaci abinci”.
Kai ya Girgiza kana yace.
“A'a Innayi bazan ciba aƙoshe nake”.
Jinjina kai tayi tare da miƙewa ta dawo hannunta riƙe da wani bowl dake ɗauke da Fruit ta ajiye masa kana tace.
“Toh kaci wannan”.
Kai ya gyaɗa kana ya fara ci ahankali.
Ganin ya fara ci yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa.
“Toh sai da safe”.
Sannan ta fice domin bata da nutsuwa atare da ita.
Washe gari Da safe Ganin Moddibo bai zoba yasa Abba yashiga motarsa kai tsaye gidansu Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ya fito daga bakin gate ɗin farko ya tsaya yayi sallama Innayi dake Alwalan sallar Walha ta miƙe bayan ta ida ta nufi ƙofar tare da amsa masa Sallamar.
Bayan sun gaisa Abba ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Dama Moddibo ne nake son ganinsa kuma bai zoba”.
Cikin sanyin murya Innayi tace.
“Hmm Moddibo ai jiya wuni yayi aɗaki yana kuka babu inda ya fita”.
Cike da alhini Abba yace.
“Subhanallah ni kuwa dama al'farma nazo nema Aliyu yamin taimako”.
ya ida mgnar cikin alamun neman al'farmar.
Haka yasa Innayi ta ɗan juyo ta kalleshi da kyau kana a hankali tace.
“Alhji Bashir ai ka wuce haka, kawai Umarni zakiywa Aliyu, kamar yadda kakeyiwa Jameelu da izinin UBANGIJI kuma zai cika maka umarninki. Aliyu ɗan ka ne, kadama kacemin komai kawai ka bashi umarni yamaka duk abinda kakeso ni kam na amince duniya da ƙiyama”.
Cikin jin daɗi kara da kawaicinta gareshi yace.
“Nagode da mutuntaka Allah ya bar zumunci”.
Amin tace tare da juyawa
tayi gaba.
Abba na bin bayanta zuwa falon Moddibo tsaye Abba ya gansa afalon yana ƙoƙarin fita.
Cike da ladabi yace.
“Ha'a Abba kazo ne?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh naga shiru-shiru Aliyu ba kazo ba tun jiya”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da faɗin.
“Eh dama yanzu nake shirin fita zan biya ta gidan Ummi sannan na ƙara so wajenka”.
Ahankali Abba yace.
“Allah sarki to zamu tafi tare”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh”,Sannan suka fita.
Cikin sanyi da
disesshiyar murya yace
“Abba na rasa ta ya zan gayawa Innayi batun
tafiyar nanfa”.
Juyowa Abba ya ɗan yi
ya kalleshi na second uku kana yace.
“Munyi mgnar da Innayi tace, babu matsala duk abinda ya dace in saka kayi min ta amince”.
Cike da mamakin amincewar tan yace.
“Ta yarda”.
Ka Abba ya gyaɗa mishi yana mai ci gaba da tuƙi.