← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 150

Sashe 73

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Morocco*
Bayan an idar da sallar Maghriba matan da sukayi mata lallene suka shigo suka haɗa mata ruwan da zatayi wanka ruwane me masifar kyau da ƙamshi koda tayi wankan ta fito wani irin sheƙi da ƙamshi take bazawa lallen ya kwanta akan farin fatar ta da yayi smooth ta dawo kamar wata tarwaɗa fatan ta sai haske da ƙyallin Amarci yake.
Already tayi alwala kafin ta fito zama tayi awani kujera suka fara turara mata jikinta da turare bayan sun gama suka fara turara mata gashinta da wasu masu daɗin ƙamshi nan da nan gashin ya dauki sheƙi da haske..
Kai tsaye ta nufi bedroom ta gabatar da sallar Maghriba kana tana zaune har aka kira Isha'i ta idar Misalin ƙarfe goma Ummi ta kalli Khausar hannunta riƙe da Damun data dama kana tace.
“Gashi ki karɓa kisha”.
Ahankali Khausar ta ɗaga idanunta ta kalleta cikin yanayin kasala da baƙon lamarin dake ratsa jikinta ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Ummi wallahi cikina ya ƙoshi bazan iya shaba”.
Ummi na kallonta tace.
“Bana son haka Khausar kar kiyi min musu tun bayan la'asar nace Asma'u ta faɗa miki kisha.
Ni nayi tsammanin kinsha ashe baki sha ba”.
Karɓa tayi cikin kasala da sanyi ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Wallahi Ummi baki daya shi yake cika min cikina shiyasa ko abinci bana iya ci aɗuramin wannan aɗuramin wancan abarni haka mana In huta”.
Harara Aunty Hajara ta watsa mata cikin ɗaure fuska tace.
“Zaki karɓa kisha ko kuma saina ɓata miki rai”.
Cike da tsoronta ta karɓa tasha kamar zatayi kuka...

Hajja Nana dake kallonsu tace.
“Hmmm Allah ya kawo saukin wato wai yanzu duniya ta kai duniyar da har ɗuwawu yana da kwallinsa wai in zaku Aurar da ƴaƴa kuyi ta musu shungullah da hidima”.
Murmushi Innayi tayi tare da faɗin.
“Toh ai tun zamanin mu da ɗin ma ana gyara kam sai dai inke bakiyi gyara ba amma tun da kam ana gyara”.
Wani kallo Hajja Nana ta watsa mata tana gyara zama tace.
“Kyanuna min gyara kema Baiwa kikace kinsan gyara bare mu matan Sarakuna”.
Dariya Innayi tare da shewa ta tafa hannu kana tace.
“Da ne nake baiwa yanzu kin manta agaban idonki aka ƴantani ai yanzu dai-dai nake dake”.

Zare idanu Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Za dai kiyi dai-dai dani amma bazaki taɓa dai-dai dani ba ai wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa”.
Kallon Hajja Nana Khausar tayi kana tace.
“Kiyiwa Allah da Annabi Hajja Nana kada araba hali dake a ƙasar da ba naki ba nan fa ba muhallin ki bane ba kuma cikin ƙannenki kikeba”.
Cikin sanin halin Hajja Nana Innayi ta kalli Khausar cike daso tace.
“Yi shiru abunki barni da ita, ai in da sabo tuni na saba”.

Baki sake Hajja Nana ke kallon Khausar kafin ta harareta da faɗin.
“Iyyeee kaji shegiyar Yarinya.
Toh naji ke kam muhallinki ne ai nan ɗin gidan Ubanki ne ko da zakice ba muhalli na bane”.
Lumshe idanu Khausar tayi tare da tura bakinta kana tace.
“To ko ba gidan Ubana bane ai gidan mijinane kam”.
Tafa hannu Hajja Nana tayi tare da Salati ta sanar da Ubangji kana tace.
“Eh ba shakka ba ƙarya wato ɗazun da yazo zugaki yayi ya Fom-famkaki ya zizzira miki”.
Cikin lumshe ido Khausar tace.
“Me kuma zai zira min?,Ya ziramin kamar wata rijiya”.
Ummi da Aunty Rukayya da Hajja Umma kam dariya sukeyi dramer Khausar da Hajja Nana baya ƙarewa.
Hajiya Bunayya kuwa Ayatsine ta kalli Khausar tare da jan tsaki kana ta kawar da kai gefe...

Asma'u kuwa ka faɗan Khausar ta dafa tare da faɗin.
“Allah yaja da Zamanin Matar Sarki”.
Murmushi Khausar tayi tare da Fari da idanu kana tace.
“Aaa faɗawa tsohuwa dai taji”.
Cikin mamaki da sarewa da halin Khausar Hajja Nana tace.
“A lallai kin samu baki Munafuka, ai ɗazu kam kuka kika tayi sai da na rarrasheki.
Amma yanzu saboda kinga kuna tare shiyasa kike min haka toh zasu tafi kuma har nima tafiya zanyi na fasa zama, tunda kwaye min baya zakiyi”.
Dariya Asma'u ta sanya tare da faɗin.
“A'a Hajja Nana baza ayi haka ba dan Allah kiyi haƙuri ki zauna”.

Mutsike idanu Hajja Nana tayi tana hararan Khausar tace.
“Wallahi bazan zauna ba tafiya zanyi waɗannan fitsararrun ai in mutum ya zauna babu abinda ba zasuyi agaban idanunsa ba”.
Jin abinda tace yasa Khausar langwaɓar da kai cikin sanyin Murya tace.
“Don Allah dan Darajar Annabi Hajja Nana na mu zauna mana kada ku tafi ku barni ni kadai”.
Sai kuma ta maida idanunta kan Ummi tare da cewa.
“Ayyah Ummi dan Allah za'a bar Asma'u anan ina?”.
Sai ta kuma juyawa ta kalli Hajiya Bunayya kana tace.
“Umma dan Allah ki barmin Addah Asiya”.
Cike da tsanarta Hajiya Bunayya tace.
“Eh dole abar miki su dole sai tunda su ba aure zasuje suyi ba”.
Araunane ta girgiza kai tare da faɗin.
“Ayyah ba haka bane dan Allah Ummi ku bar min su”.
Kai Ummi ta girgiza kana tace.
“A'a Khausar kada muyi haka dake.
Kada ma mufara haka dake”.
Rau-rau tayi da idanunta yayin da ruwan hawaye suka cika alamar gan take da fara kuma.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da faɗin.
“Um-um ki kwantar da hankalin ki kada kiyi kuka ai Asma'u kuna tare”.
Murmushi tayi Ummi kuwa miƙewa tayi ta nufi bedroom ɗin ta...

Agefen Moddibo kuwa tun da ya koma sashen sa ya samu Ibraahim da Zakariyya suna zaune batare daya kalli inda suke ba ya wuce bedroom ɗinsa ya kwanta akife kana ya runtse idanunsa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake wani irin Masifeffen feeling yake ji na fitar hankali.
Ji yake tamkar ya ɗaura hannunsa aka yaita zunduma ihu ko zaiji sassaucin abinda yakeji.
Wani irin tsuma jikinsa keyi da dama da zai iya yin sex da katifar koda zaiji sassaucin abinda yake ji juyi kawai yake akan katifar cikin tsananin feeling dake addabar sa yayin da *A* ɗin sa ya miƙe tunda yake bai taɓa jin azabebben feeling irin na yau ba baki daya na yau ya bambanta da duk na sauran lokutan da yake ji.

Dr Jameel ne ya shi lokacin alwalan sallar Maghriba ganin yanda yake murƙususu yace.
“Ya dai tun ɗazu nazo Ibraahim suka cemin kashiga ciki kana kwance lafiya dai?”.
Shiru Moddibo yayi dan ya tabbatar idan yace zai buɗe baki yayi magana kuka ne zai kufce nasa koda kuka bai kufce masa ba to Muryansa bazai fita.
Sake matsawa jikin gadon Dr Jameel yayi kana yace.
“Lafiya kuwa? Na tafi na Barka ɗazu lafiya kalau kuma yanzu tunda nazo kana kwance”.
Ya ƙara sa Maganar tare da taɓa wuyan zafi rau ya ratsa hannunsa.
Cike da kulawa yace.
“Subhanallah baka da lafiya ne?”.
Araunane Moddibo ya kallesa kana ya girgiza kai tare da cewa.
“Nima ban sani ba”.
Ya ƙare maganar cikin ruwar murya.
Da mamaki Dr Jameel yace.
“Kamar ya baka sani ba baza ka rasa sanin meke damunka ba mana?”.
Shiru Moddibo yayi yana murƙususu.
Ganin yanayin da yake ciki sai ƙaruwa yake yasa Dr Jameel cewa.
“Ko dai zamu tafi asibitine, kaga yanayin ka baki ɗaya jikin ka rawa yake ga zufa da kake fitarwa duk da sanyin da ake”.
Still shiru Moddibo ya masa.
Dr Jameel kuwa hannu yasa tare da yaye blanket ɗin daya rufu ware idanu yayi ganin yanda *A* ɗin sa ya miƙe kamar zai fasa wandon Jeans ɗin ya fito.

Dariya Dr Jameel ya fashe dashi harda riƙe ciki kana yace.
“Ashe dai bani kaɗai bane mayen matan, kaiɗin ma gashinan ka gaza haƙura, yanzu ka dubi yanayin da kake ciki to kai me matsalar ka tunda ga mata an kawo maka zuwa anjima dai kuna tare”.
Hararansa Moddibo yayi kana yace.
“Kai fa ɗan Iska ne”.
Still Dr Jameel na dariya yace.
“Ƴan Iska dai zakace.
ai kai kam ma wa ɗan'nan shaiɗanun idanunka masu cike da shu'umaci sai ka casani, toh ni nama isa inyi ko rabin abinda idonka ke nunawa ne ko amafarki ban isa in aikata abinda zaka aikata ba dan wlh in ka ritsar ƴar mutane zata gane kurenta”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da hararansa kana yace.
“Kamar yaya mene aikata? yanzu Jameel kai duk abinda kake aikatawa kace ko rabin abinda zanyi baza ku aikata ba ko amafarki amman wlh ka cuceni?”.
Kai Dr Jameel ya jinjina tare da cewa.
“Sosai ma kuwa”.
Cikin yanayin gajiya da maganar da kuma feeling dake addabar sa ya miƙe dare da yin miƙa atake *A* ɗin sa ya kuma miƙewa duk da wandon Jeans ne ajikinsa saida ya nuna.
Dariya Dr Jameel ya sheƙe dashi kana yace.
“Toh da ace baka da mata ne sai ince zan baka magani ko kuma In maka allurai dan wlh in ace zaka rayu na wata ɗaya a haka Allah ne kaɗai yasa adadin matan da zaka danne.
to amma Alhamdulillah ba wannan duk cikin biyun tunda ga matarka nan shikenan nan magana ya ƙare”.
Hararansa Moddibo yayi yana ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa.
Murmushi Dr Jameel yayi kana ya ɗage masa giransa tare da cewa.
“Kamayi Sa'a ɗazun na biya sashen Didi naji tana cewa gobe In Sha Allah za'a kai maka matarka sashenta dama already an gama gyarawa”.
Hararansa Moddibo yayi kana ya wuce ya shiga toilet bayan ya fito suka tafi Sallah koda aka idar da Maghriba basu dawo ba sai da akayi Isha'i.
Haka ya kwana baiyi bacci ba sai juyi yake saboda tsananin feeling da fitinar dake addabar sa baki daya ya rasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Zaran ya lumshe idanunsa zai tuna moment ɗin da suka kasance a dining sai ya riƙa jin tafin hannunsa kamar yana yawo acikin nata wani irin azabebben tsuma jikinsa keyi baki daya *A* ɗin sa ya takura sa a duk sanda ya tuna yadda take shafa hannunta bisa sajenshi sai yaji kamar zai zauce...
Chapter 73 · 0% Book details