← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 150

Sashe 3

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana ya juya ya fita kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ɗin motarsa kana ya shiga gate din farko ya daga sautin muryarsa tare da yin sallama.
Cikin sauri Innayi ta fito ganinsa yasa ta saki Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Alhamdulillah dama yanzu nake tunanin in kira ka dan. Moddibo tun safe daya fita bai dawo ba, duk da cewa dama yanzu bai cika dawowa da wuri ba”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana yace.
“Ki zo mutafi”.
Saurin Kallonsa tayi kana tace.
“Ina zamuje”.
Cikin sanyin Murya Malam Arɗo yace.
“Wajen Moddibo zamuje yana asibiti”.
Da sauri ta dafe ƙirjinta sai kuma ta juya ta nufi cikin gida hijabinta ta ɗauko ta sanya kana ta rurrufe kofofin gidan kafin ta fita.
Bayan sun fara tafiya acikin motar Malam Arɗo ya kalli Innayi kana yace.
“An samo gawar Jameelu fa!”.
Cikin tsanananin ruɗu da tashin hankali ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.
“Gawar Jameelu kuma?”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.
“Eh gawar Jameelu aka samu sun kashe sa”.
Atake hawaye suka shiga zubowa Innayi cikin tashin hankali da jimami ta saki sassayan kuka tare da addu'o'i.

A dai daren wannan ranar haka kowa ya kwana cikin ƙunci da raɗaɗi azuciya.
Asp da tawagarsa sun koma gida bayan sun gama dukkan abinda ya dace na bincikensu, haka zalika Lamiɗo ma ya koma gida Abba kuwa kwana yayi da gawar Jameelun sa agabansa batare daya rintsa ba.

Asma'u kuwa Hajiya Turai ta jata zuwa ɗakinta Anan ta kwana duk da cewa ba tayi bacci ba.
Bashir kuwa aɗakin ƙannen M Jameel ya kwana tare dasu Aɓangaren Moddibo kuwa haka ya kwana cikin wani irin yanayi shi ba bacci ba kuma kuma shiba Ido biyu ba ba kuma a sumeba.
Ana kiran Assalatun Farko acikin kunnen Moddibo sannu Ahankali ya fara bude idanunsa da yaji sunyi masifar nauyi har ya sauƙesu akan Ummi dake riƙe da hannunsa Idanunta abushe alamar ko rintsawa ba tayi ba bare kuma bacci.
Cikin wata murya mai cike da karaya da kuma rauni yace.
“Ummi”.
Kallonsa Ummi tayi tare da faɗin.
“Na'am Aliyu”.
Girgiza kai yayi yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi yace.
“Ummi J ɗina”.
Cike da tausayawa ta rintse Idanunta kana tace.
“Aliyu kayi haƙuri”.
Cije Lips ɗinsa yayi tare da damƙe hannunta acikin nasa kana yace.
“Ummi J ɗina”.
Jinjina kai tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Kayi haƙuri kaje kayi sallah duk abinda kake ji Aranka kana so ka faɗa min ka faɗawa Ubangiji”.

Cikin sauri Malam Ahmad dake tsaye ya ƙara so bakin gadon tare da riƙe hannun Moddibo cikin sanyin murya yace.
“Kayi haƙuri kaje kayi alwala”.
Kallon Malam Ahmad Ummi tayi kana tace.
“Toh ni yanzu zan tafi gida”.
Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.
“A'a ki bari mu tafi gidan Alhj Bashir yanzu”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“A'a mu tafi gidanmu dai”.
Girgiza mata kai yayi kana yace.
“A'a gidan Alhj Bashir zamu je acan fa za ayi jana'izar mu tafi can ɗin!”.

Shiru kawai Ummi tayi ahankali.
Moddibo da har yanzu hannunsa ke cikin nata yace.
“A'a Ummi dan Allah muje gidan Abba”.
Kai ta gyaɗa masa cikin sanyi tace.
“Toh shikenan”.
Batare da an sallamesu ba suka fita Moddibo da Malam Ahmad suka shiga gaba Ummi tashiga baya Anutse Malam Ahmad yayiwa motar key kana yaja suka bar Asibitin kai tsaye gidan Abba suka nufa suna isa Malam Ahmad ya danna hong ta cikin ƙaramin ɓulin. Mai gadi ya leƙa jin ana ta danna hong ganin motar da tazo jiya da safe ne yasa ya koma cikin gida tare da sanarwar Abba yaga motar da jiya tazo yauma ta dawo.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh kaje ka buɗe musu Maman Jameel ne yanzu aka sallame su daga asibiti kaje ka buɗe musu”.
Kai ya gyaɗa sannan ya buɗe musu gate din suka shiga bayan Malam Ahmad yayi Parking suka fito kai tsaye falon Abba suka shiga.
Zaune suka samesa shi kaɗai a falon hannunsa riƙe da Carbi ya tsirawa kwalin Gawar Jameel Ido.
Ahankali Ummi ta ƙarasa tare da zama agefen kwalin shima Moddibo zama yayi agefen kwalin Malam Ahmad ma ya zauna agefen kwalin sai ya zamana sun saka kwalin Atsakiyar su.
Moddibo kuwa kallon kwalin yayi kana ya kalli Ummi cikin raunin murya yace.
“Ummi yanzu J ɗinane aciki?.
Ummi da gaske J ɗina ne ya rasu!?”.
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
“Da gaskene Moddibo, tabbas Jameelu ne yarasu Jameelu ya tafi yabar mu bari na har abada, ba zamu sake ganinsa ko jin sautin muryarsa ba sai dai ahoto”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da ɗaura kansa akan kwalin ya fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya cikin sheshsheƙan Kuka yace.
“Yanzu shikenan J ɗina mun rabu har abada bayan yana burin yin Aure ya zauna gida ɗaya da Ummi da ƙannensa yanzu shikenan wannan burin ya tafi”.
Ya sake Rungume Kwalin tare da cewa.
“Yanzu shikenan J ya tafi ya barni shin dawa zan rayu duk wani farin ciki ne da walwala na J ɗina ne shin waye zai fahimcini a duniya? J ɗina ne kaɗai yake iya fuskarta halin da nake ciki shikenan sun rabani da aminina kuma farin cikina!”.
Wani irin tausayinsa ne ke ratsasu Abba kam kasa daure wa yayi ya sunkuyar da kansa ƙasa hawaye na zuba.

Cikin sheshsheƙa Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon Ummi idanunsa cike da ruwan hawaye yace.
“Shikenan Ummu sunyi mai kisan gillah, sun hanashi shan ruwa, ya mutu da kishi da begenmu, yana ganin muna kiransa amma bashida damar ɗauka, Ummi ashe duk kiran da mukewa J yana kallon kiran mu!”.
Sai kuma ya kife kansa akan kwalin hawayen sa na sauka akai yace.
“Ummi J yana ganin kiran mu amma bazai iya ɗagawa ba Ummi sun azabtar da J ya mutu da tsananin begenmu da muradin son kasancewa damu Ummi sun cutar da J mutumin da koda ƙwaro baya iya cutarwa bare bil adam shin wani irin zunubi suka aikata!”.

Jin ankira assalatu yasa Malam Ahmad sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Moddibo kayi haƙuri ku tashi muyi alwala mu tafi masallaci”.
Ahankali Moddibo ya ɗago kansa akan kwalin daya jiƙe da hawayensa cikin ransa yace shikenan J ya tafi yabarni bari na har abada shikenan ni kaɗai zan rayu.
Hajiya Turai ce ta shigo falon tare da jan Ummi suka tafi ɗakinta Anan sukayi sallah.

Dole Gawar M Jameel yanda ya kasance a kakkarye ahaka aka yayyafa masa ruwa madadin wonkan kana aka kaisa makwancinsa na gaskiya.
Jana'izar data samu halarta ɗumbin jama'ar domin kafin gari ya waye mutuwar ta zagaye cikin Gembulan da kewayenta har Taraba Yola da dai sauransu.

Rayuwa tayiwa duk wani makusancin M Jameel ƙunci da zafi musamman Ummi, Abba, Moddibo, Asma'u, Bashir daga Jiya zuwa yau sunyi wani masifaffen ramewa kallo ɗaya zaka musu kasan cewa suna cikin tsananin ƙuncin rayuwa musamman Moddibo baki daya ya fita cikin hayyacinsa duk ya gigice ya sake zama wani shiru.

Misalin ƙarfe biyu na rana bayan andawo daga sallar jana'izar M Jameel Lamiɗo ya koma gidansa kai tsaye falon Mommy ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama.
Anutse Mommy da Khausar dake zaune suka amsa masa Sallamar.
Cike da kulawa Mommy tace.
“Sannu da zuwa yinin yau duk baka nan sau biyu ina zuwa sashenka”.
Zama yayi akan 3sitter tare da sauƙe ajiyar zuciya kana ya jingina bayansa da jikin kushin ɗin tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Eh yanzu na dawo daga jana'iza”.
Cikin sauri ta kallesa tare da cewa.
“Jana'iza kuma?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh”.
Gyara zama tayi tare da faɗin.
“Janaizar waye!?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dafe kansa kana yace.
“Janaizar Jameelu”.
Cikin sauri Khausar ta dafe ƙirjinta tare da kallon Lamiɗo kana tace.
“Abbah waye”.
Kallonta Lamiɗo yayi kana yace.
“Malam Jameelu”.
Cikin tashin hankali Mommy tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Jameelu Yayan Asma'u”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.
“Eh shi ɗin dai Allah ya masa rasuwa”.
Cike da kaɗuwa tace.
“Innalillahi Ayyah Ummin Asma'u Allahu Akbar duniya yanzu yaron nan kashesa sukayi”.

Khausar kuwa tunda ta dafe hannunta aƙirji ta kasa koda ƙokƙwaran motsi ne wani irin bugawa da masifaffen ƙarfi zuciyarta keyi.
Atake wani irin kuka mai tsuma zuciya ya kufce mata cikin sheshsheƙan kuka mai cike da tausayi da tashin hankali tace.
“Abba Yaya Jameel ya rasu!? Abba kashe Yah Jameel sukayi? Abba me yayi musu da zasu kashesa, suka rabasa da rayuwarsa”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh Khausar sun kashesa kisa mafi ciwo".
Sau kuma ya zayyane musu yanda suka samu labarin har suka je wajen da kuma yanda suka samu gawar.
Cike da tausayawa Khausar ke jujjuya kai tana cigaba da kuka yayinda numfashinta ke sarƙewa.

Kallon Mommy da hawaye ke kwaranya daga idanunta Lamiɗo yayi kana yace.
“Tun jiya ne, ai muka samu gasar, ban dai faɗa muku bane, dan kada in hanaku bacci.
Yanzu ku shirya anjima idan anyi Sallar La'asar zan kaiku gidan kuyi musu ta'aziyya”.
Cikin muryan kuka Mommy ta gyaɗa masa kai cike da rauni tace.
“Ayyah Ummin Jameel ta ɗandani mutuwa me raɗaɗi da ƙunan zuciya”.
Ta faɗa tana tuno Ramadan domin ko Rasuwar Ramadan bata samu tayi kuka haka ba bayan Lamiɗo ya sake rarrashin sune ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Bunayya ya sanar mata.
Khausar kuwa Kuka takeyi tamkar zata mace.

Bayan anyi sallar La'asar Lamiɗo ya ɗebe su suka tafi gidan Abba.

Suna zuwa falon Hajiya Turai suka nufa Cikin gidan da falon cike yake da mutane ƴan ta'aziyya duk wanda yaji rasuwar M Jameel da kuma yanda aka samu gawarsa saiya zubda hawaye tare da la'antar wa anda suka aikata masa haka.
Chapter 3 · 0% Book details