← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 150

Sashe 107

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Gembila*
Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajja Nana da Hajja Umma ce kwance akan gadon Momy yayin da Aunty Aunty Ruƙayya da Ummi ke kwance tsakiyar bedroom kan katifa data shimfiɗa musu Momy dake zaune gefen katifa ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummin Jameel ku kwanta kun ɗebo gajiyar hanya”.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“Ai Momyn Khausar bazan iya bacci ba yau sai na baki labari”.
Murmushi Momy tayi tana gyara zamanta tace.
“Allah ko?”.
Ɗagowa Aunty Ruƙayya tayi tare da faɗin.
“Ai dai kam Momyn Khausar sai mun baki labari ,Muna tafe da labarai kala-kala munga alfarma, Isa, Wadata, Kawaici, kara, Mutuntaka, Munga iyayen Moddibo, Mahaifinsa, Mahaifiyar sa,Yayunsa, Ƙannensa, Kakarsa, munaga baki ɗaya Family sa masu mutunci kamala da kawaici”.
Zama Momy ta gyara tare da cewa.
“Abin al'ajabi yaron nan suka zo suka rayu da Innayi anan babu wanda ya taɓa tunanin yana da dangi”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Kin ganni nan Momyn Khausar koni kaina ban taɓa sani ba Jameel dai kusan rasuwarsa ya fara cemin ya samu labarin inda ƴan Uwan Moddibo suke amma be faɗa min ba ni kaina na shiga mamaki”.
Juyawa Momy tayi tare da kallon Ummi tace.
“Allah Ubangji ya rufa asiri Allah ya basu zaman lafiya, amma yau hankalina gaba ɗaya ya tashi yanda naji Khausar nata kuka, kawai daurewa nayi na rufeta da faɗa saboda Kukanta yana son sakani kuka”.
Sai kuma ta sauƙe Numfashi fuskarta ɗauke da damuwa ta cigaba da cewa.
“Bare kuma acan bata da kowa sannan Mijinta ba sonta yake ba ita ta daurawa kanta da kanta Ni abinda yake tayar min da hankali kenan Moddibo bawai son Khausar yake ba”.
Cikin sauri Hajja Nana da bacci ya fara fusgarta ta miƙe zaune idanunta akan Momy tace.
“Waya ce miki baya sonta in faɗa miki Aysha kiyi shuru da bakinki babu Munafukai aduniya sama da wannan yarinyar da yaron bata nuna mana saboda Jameelu zata Auresa ba to ƙarya take suna soyayya wannan abin nasu ƙaryane ace babu soyayya ke kinga abinda suke wlh ita kanta Khausar tana matuƙar sonshi so na gaskema kuwa bare shi uban gayya kam ai ko tattabara sai haka”.
Cikin mamakin maganarta Ummu ta zuba mata idanu sai kuma ta juya ta kalli Aunty Ruƙayya da take cewa.
“Kai gaskiya Momyn Khausar al'amarin Moddibo ya sunce min ƙwaƙwalwata da tunani idan kinga abinda Moddibo ke yiwa Khausar wallahi ³ gaba ɗaya sai kin faɗa Duniyar da bakiyi zato da tunani ba”.
Cikin mamakin kalamanta Momy ta gyara zama tana sauraren ta Aunty Ruƙayya kuwa cikin farin cikin yanda Moddibo ya karɓi Khausar hannu bibbiyu ta cigaba da faɗin.
“Abinda Moddibo ke yiwa Khausar ya wuce akirasa da so sai dai Ƙauna kai baza ma kasan da me zaka Misalta shiba saboda ko kallon Khausar yake yi kallone da yake cike da tsantsar soyayya,kulawa da tausayi Momyn Khausar ki cire tunanin da kike yi ba cewa wai Moddibo baya son Khausar ni inaga akwai abinda M Jameel ya sani shiyasa yace a haɗa Auren khausar da Moddibo”.
Ummi ce ta gyara zama tare da cewa.
“Nima abinda nayi tunani kenan ina ga tabbas Jameel yaga Moddibo nasan Khausar ne Shiyasa ya haɗa abin domin gaskiya abinda Aliyu ke yiwa Khausar soyayya ce mai zafi da zurfi atare dashi”.
Baki sake Momy ke kallonta cikin mamaki tace.
“Moddibon yake son Khausar?”.
Cikin tabbatar Ummi ta gyaɗa mata kai tace.
“Babu shakka babu tantama babu Haufi acikin wannan al'amarin wallahi akwai soyayya mai ƙarfi tsakaninsa da yarinyar nan ita kanta bata sani ba shi kuma bai fito fili ya faɗa mata ba al'amarin su soyayyace mai ƙarfi”.
Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe kana tace.
“Ikon Allah amma abinda Mamaki”.
Hajja Umma dake kwance tayi murmushi tare da faɗin.
“A akwai soyayya kam dan lamarinsu yafi ƙarfin ace wanzar da wasiyyane kawai bama so bane soyayya ce ta gefe duka biyu”.
Cikin sauri Ummi tace.
“To ai shi Aliyu idan yasan wasiyyar ma daga baya ya sani don har aka ɗaura Auren nan har muka je baisan da batun wasiyyar ba”.
Kai Aunty Ruƙayya ta jinjina tare da faɗin.
“Kinga kuwa ran farko da yaga Khausar irin rungumar daya mata?”.
Murmushi Momy tayi tare da sunkuyar da kai tana jin wani irin sanyi nutsuwa da Salama.
Aunty Ruƙayya Kuwa ahankali tace.
“Wallahi rungumar daya mata sai da gaba ɗaya falon ya ɗauki tafi zaki rantse da Allah uwace da ɗan ta ya ɓace tsawon shekaru ta gane sa haka ta rungumeta kamar ma ya manta da akwai mutane acikin Falon itama Khausar ni har taban kunya yadda ta lafe a jikinshi kai kace furanninesu”.
Fuska ɗauke da farin ciki Momy tace.
“Moddibon?”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Tabbas kuwa Moddibon shi ɗin dai”.
Hajja Nana dake jinsu tace.
“Tabbas Moddibon kuwa bakisan fitsaran yaron bane ya tsefe idanunsa yo wannan ƙasurgumin tuzurun ai sai abinda Allah yayi”.
Zama suka gyara suka cigaba da bata labarin abinda ya faru Hajja Nana ma cikin gyara zama ta riƙa basu labarin yanda yaje dining ya same su da Khausar filla-fillah duk abubuwan da suka faru acan sai da suka bata.
Haka nan Momy taji wani irin nutsuwa da Salama har misalin ƙarfe biyu suna zaune suna hira juyawa Ummi tayi tare da kallon Momy tace.
“Nikam Momyn Khausar kina zaune Lamiɗo fa kin barshi shi kadai”.
Dariya tayi tare da faɗin.
“A'a haba yau kam ai nace masa Hajiya Bunayya taje ta sameshi nikam ai ina tare da baƙi”.
Da mamaki Aunty Ruƙayya tace.
“Kamar ya Hajiya Bunayya taje ta sameshi ba tare sukayi tafiyar ba?”.
Still Murmushi tayi kana tace.
“Inma tare da ita akayi tafiyar ba ai bata gan shiba bai gan taba ko?”.
Haɓa Ummi ta riƙe tare da cewa.
“To ai kema baki ganshi ba”.
Momy na dariya tace.
“A'a duk da haka dai suje na turata ni kuma inji da baƙina mana”.
Ƴar dariya Ummu tayi tare da faɗin.
“Eh lallai kam hakane”.
Daren wannan ranan haka suka rabata cikin hira.

Acan Side ɗin Haiydar kuwa kwance suke da Sulaiman yana ta bashi labarin Morocco da kuma Family Moddibo da irin abubuwan da aka gabatar acikin Masarautar.

Acan ɓangaren su Asma'u kuwa bayan ta gama waya da Dr Jameel ne ta juya ta kalli Asiya dake waya da Zakariyya sai kuma ta maida idanunta kan Dija dake kwance ba tayi bacci ba cikin sanyin murya tace.
“Nayi kewan Khausar bari In kirata inji”.
Ajiyar zuciya Dija ta sauke tana gyara kwanciyar ta tace.
“Wallahi kuwa nima nayi kewarta kira mana ita muji”.
Ɗaukar waya Asma'u tayi tare da dearling Number Khausar har tayi ringing biyu ta gama bata ɗauka ba kallon Dija tayi kana tace.
“Ki gani fa har kira biyu bata ɗaga ba”.
Wayar Dija ta ɗauka ta duba lokaci ɗan ware idanunta tayi tace.
“Kina gani ƙarfe biyu na dare nefa ya za'a yi ki sameta kina ganin wannan mijin nata maƙale mata mam-man-ne mata ai da wuya idan ba suna can suna maƙale da juna ba”.
Asma'u kuwa kirji ta dafe tare da ɗan zaro ido sai kuma tayi saurin cewa.
“Haka fa”.
Sai kuma ta janyo wayar ta kashe tare da kallon Dija tace.
“Ai Yah Moddibo duniya ne wani irin kallon da yake yiwa Khausar kamar zai mai da ita cikin zuciyarsa”.
Dija na gyara kwanciyar ta tace.
“Aikuwa Soyayya ce mai ƙarfi Moddibo Namijin Duniya ne”.
A wannan daren haka suka kwana hira.
Acan ɓangaren su Khausar ma suka kwana maƙale da juna.

Washe gari da safe

*Abujan Nigeria*
Bayan fitar Uncle Naseer da kimanin minti talatin Amina ta fara jiyo gurnanin macijin na fitowa tana zaune Jingine jikin kushin wanda tun jiya daya shata jikinta ke mace ta kasa da faɗawa kowa aranta tana ji tana so ta faɗawa Ummanta amma ta gagara tayi waya da Samira Sani ma tayi niyyar faɗa mata amma sai taji bakinta yayi nauyi ta kasa sanar mata tana kwance taji gurnanin Macijin kusa da ita cikin sauri ta miƙe daga kwance ta zubawa Micijin Ido yana isowa kusa da ita kamar jiya ya shiga rigarta ya kamo kan Nipples ɗin ta ya-shash-sha kafin ya kama hanya ya fita tun jiya daya sha bata sake dawowa dai-dai ba tana jin kasala bata da kuzari yanzu ma daya sake tsotsa sai taji gaba ɗaya jikinta ya sake mutuwa ahankali ta kalli bakin Nononta na dama kana ta kalli na hagun taga ɗigon jini kamar na jiya wani irin nauyi jikinta yayi mata ahankali ta sulale ta kwanta wani irin bacci ya ɗauketa...

Acan gidan Lamiɗo kuwa Abualeey, Waziri, Galadima Baban Zakariyya tun da sassafe aka kai musu abinci da komai na buƙata na alfarma kuwa su Asma'u ne suka kai musu Breakfast da komai ba buƙata.

Bayan sun kammala Breakfast Ummi ta kalli Momy tare da cewa.
“Momyn Khausar mufa zamu tafi”.
Da sauri Momy tace.
“Da wuri haka Ummin Jameel?”.
Ummi na murmushi tace.
“Gidan ba kowa nayi missing ɗin ɗan Autana Bashiruna Nasan tun jiya yake tsammanin zan koma yaji shiru yayi ta kirana ma ban ɗauka ba nafi so ma sai naje ya ganni”.
Kai Momy ta jinjina tare da cewa.
“Ayyah Asma'u am ki riƙa ɗan leƙoni kafin kema a ɗauke mana ke kinga ƙawarki kam an ɗauke ta zakuje can ku haɗu”.
Asma'u kam kanta ta sunkuyar ƙasa tana murmushi tace.
“Momy gobe ma zanzo in Sha Allah”.
Cikin sanyi Momy tace.
“Allah ya kaimu”.
Chapter 107 · 0% Book details