← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 150

Sashe 36

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa yayi ya fita kai tsaye sashen sa ya nufa zaune ya samu Hajiya Bunayya da waya maƙale akunnenta tana magana da Hajiya Lami ganinsa yasa tayi saurin cire wayar kana ta katse ta juya ta kallesa zama yayi tare da tsira mata ido tamkar shine rana ta farko da yafa ganinta acikin rayuwarsa.
Ganin kallon da yake bin ta dashi ne tace.
“Ya dai Mai martaba naga kana ta kallona lafiya kuwa?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana cikin tsira mata Ido yace.
“Wai me yake faru tsakanin Naseeru da Amina ne?”.
Cike da farin ciki tace.
“Meye kuma yake faruwa Lamiɗo banda lamarin Aure da muke fatan zai tabbata tunda sun daidaita kansu”.
Wani irin kallo ya watsa mata kana yace.
“Sun dai-dai-ta kansu Meyesa ban sani ba”.
Zare ido tayi tare da ɗage hannunta sama tace.
“Lalala nima Wallahi ban saniba sai kwanan nan bai kai sati ba Amina take cemin wai zai aiko ya gama haɗa kayan Aure su goro da kayan gishiri da kuma sadaki”.
Ido kawai Lamiɗo ya tsira mata bako ƙyaftawa ta cigaba da cewa.
“Hatta kayan rufi ya gama haɗa komansa yana so ayi auren nan da mako biyu nanne nasan da maganar toh tsoron yi maka magana nake ta yanda zan tunkare ka da maganar”.
Cikin wani irin yanayi Lamiɗo ya tsira mata ido tamkar mai son fahimtar wani abu.
Marerece fuska tayi kana tace.
“Ya dai ka zuba min ido Lamiɗo ka yarda dani ai danasan da maganar dana faɗa maka nima abin ya daure min kai shiyasa ban faɗa maka ba”.
Sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ta cigaba da cewa.
“Domin nasan da farko Khausar Naseeru yake so to amma shi Naseeru da kansa ya sameni yace Khausar tace bata sonsa to shi ya hakura sannan Gimbiya Dadu ma tace ya nemi Amina ƴar Uwarfashi Lamiɗo ya fesar kana yace.
“Allah ya kyauta amma batun kice baki sani ba zancene Bunayya magana kike”.
Cikin sauri ta kallesa kana tace.
“Wallahi tallahi Lamiɗo ban saniba”.
Cikin yanayin ɓacin rai da takaici yace.
“Dakata Bunayya kada ki rantse dan na lura kamar baki san girma da darajar rantsuwa ba idan kika ce baki sani ba magana ya ƙare”.
Cikin tsinkewar zuciya take kallonsa.Cike da ɓacin rai ya cigaba da cewa.
“Idan kika faɗa kona yarda ko kar nayarda wannan tsakanina ne dake akan abinda kinsan ƙaryane kinsani sannan nasani kuma inada tabbaci da yaƙinin ke kika ƙulla wannan alamarin”.
Cikin yanayin tashin hankali da damuwa tace.
“Fisabilillah taya zan ƙullah”.
Ƙwaffa yayi kana yace.
“Bunayya gani kike kamar bansan komai akanki ba ko?”.
Atake zuciyarta ya tsinke zufa ya fara wanke mata fuska duk da sanyin irin na garin Gembila cikin sauri tace.
“Toh yanzu dan Allah ni menayi?”.

Kai ya girgiza still Idanunsa na kanta yace.
“Hmmm jiki magayi tunda haka kika zaɓawa kanki, duk abinda ya kasance ku kuka da kanku acikin al'amarin nan ya kamata ace komai zakiyi kiyi shawara dani”.
Kasa cewa komai Hajiya Bunayya tayi sai zufa dake wanketa cike da takaici ya cigaba da cewa.
“Amatsayina na mijinki kuma Uba ga Amina amma bakuyi shawara dani ba sai kuka tura Iyayena ta yanda zasu tsareni acikin maganar tunda haka kuka zaɓa magana ta ƙare, kowa ya ɗeɓo da zafi bakinsa!!!”.
Cikin ɓoye tsoronta tace.
“Naseeru fa shiyace ya daina son Khausar”.
Cikin sauri ya katseta ta hanyar cewa.
“Khausar ko baice ya dena sontaba Ni kaina inada nufin bazan bashi Auren Khausar ba, tunda kuma yazo ya zagaya kukayi haka ke kika sani ƴa ƴarki ce shi kuma ɗan uwana ne babu abinda zance”.
Marerece murya tayi kana tace.
“Ni dai wallahi babu abinda na sani aciki kuma itama Amina tace in faɗa maka Babansa yace zai zo gobe”.
Wani kallo ya watsa mata Afusace yace.
“Idan kinga dama kice masa yanzu yazo aɗaure ba haka kike so ba?”.
Asanyaye ta kallesa kana tace.
“Toh fisabilillah dan Amina za tayi Aure shine zai zama laifi ko kuma so kake itama tayi ta zama kamar yanda Asiya take zaune?”.

Cikin tsawa ya ɗaga mata hannu kana yace.
“Ki kiyayi kanki kada ki yarda kijefi Asiya da mugun furuci, Insha Allah Asiya Ubangiji zai jiɓanci lamuranta Asiya zatayi Aure aure mai daraja da izinin Ubangiji baza ta taɓe ba”.
Kallon yanda yayi kicin-kicin da fuska Hajiya Bunayya tayi cikin fushi ya cigaba da cewa.
“Da yardan Allah tunda tayi haƙuri da jarabawar da Ubangiji ya mata za taci nasara baya ga haka duka-duka nawa Asiya take bare Amina dududu ba shekaran daya gabata bane ta gana Secondary ba?”.
Uffan batace ta lura aharzuƙe yake cikin rashin walwala ya miƙe yashiga Bedroom ɗinsa.

*MOROCOW*

Aɓangaren Moddibo Baki daya kansa ya ɗauki zafi aiki suke gadan-gadan Anutse ya fito daga masallacin dake cikin Company ya nufi ainihin inda ake buga Abaya, kama daga Dubai Abaya, Morocco Abaya, Saudia Abaya, da kuma Turkiya Sai kuma Veils,Bags,shoes da sauransu.
Babba wajene sosai ankafa manyan ijinina sabbi ana ta haɗa su ga manyan-manyan AC dake aiki kana ga sanyin garin dake sauƙa wajen ya ɗauki sanyi baki ɗaya aiki suke gadan-gadan babu kama ƙafar yaro da alama nan da Kwanaki biyar za'a haɗa komai gashi an dakatar da aikin komai sai sabbi dake aiki Saboda sabunta Injina da akayi Ma'aikatan na ganinsa suka nufo sa suna Cikin harshen larabci suke masa Barka cike da mutuntawa da kuma girmamawa shima sannu yake musu yana yaba aikin da suke.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan wanda yake shine Babba yace.
“Alh aiki na kyau yanda ake buƙata insha Allah nan da kwana biyar za'a gama daddasa Injinan da za'a gama aikin”.
Kallon yanayin wajen Moddibo yayi kana yace.
“Masha Allah abu yayi kyau sosai”.
Kai Engineer ya Jinjina kana yace.
“Sosai ma ai saboda ansamu zaƙaƙuran ma aikata kuma baki ɗaya cikin kwanaki Ukun nan da aka dakatar da buga Abaya's,Veils,Jakankuna da Takalma *BASJAM”.*
Ahankali Moddibo ya lumshe Idanunsa Aransa yace Allah sarki Abba gashi ya haɗa sunan sa dana J ɗina a Company sai dai bashi da ikon aiki a Company Engineer ya cigaba da cewa.
“Baki ɗaya har abin ya fara ƙaranta zuwa ƙasashen da ake kaiwa danma ansamu antanadi masu yawa suna zaune amma Alhamdulillah aikin zaiyi gaggawa tunda ansamu zaƙaƙuran ma'aikata”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa saboda sanyin da wajen ke dashi kana yana jin yanda Kasan mararsa ke murɗawa ahankali ya ɗaura tafin hannunsa na dama akan maransa ya danna sai kuma ya cije Lips ɗinsa na ƙasa cikin dauriya ya kalli Engineer tun jiya ya kwana da ciwon cikin kana har yau bai lafaba na awa ɗaya mai kyauba da zaran yayi minti talatin zai sake murɗa masa ahankali ya cije Lips ɗinsa kana yace.
“Abu yayi kyau Allah yatemaka insha Allah nan kusa zamu kammala akoma bakin aiki a cigaba da aiki gadan-gadan”.

Ya ida maganar tare da juyawa ya nufi gefen dama wanda office, Office ne awajen wani Corridor ya shiga tare da buɗe makeken Office da yafi sauran kyau da tsaruwa sosai Office din ya haɗu table ne kansa ɗauke da system da takardu sai flowers kana daga jikin bango kujera ce mai juyawa daga gaban table ɗin kuma kuma jeru biyu ne sai Cottons sky blue da fari daga gefen dama Ac ne daga ɗaya gefen kuma tamkar falo ne manyan kujeru ne guda bakwai suma Sky blue sai Tv Plasmer ajikin bango da frigde sai kuma showglass dake ɗauke da kofuna ahankali ya ɗauki remote din AC yaƙara gudu duk da kuwa sanyin da ake stugawa yayin da zufa ya shiga tsats-tsafo masa agaba ɗaya ilahirin jikinsa kana maransa na cigaba da murɗawa jikinsa sai zufa yake karyo masa rintse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda mararsa ke murɗawa tamkar zai fita ahankali ya zauna kana ya ɗaura kansa akan Center table dake tsakiyar falon ya lumshe idanunsa sai kuma yayi saurin buɗewa kana ya lashi busassun laɓɓansa baki ɗaya jikinsa ya fara rawa jin yanda maransa ke dunƙulewa yana tsikarinsa cike da damuwa da rauni ya soma faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kana yaja wani numfashi me nauyi ya yunkura da niyyar miƙewa ji yayi bashi da kuzarin da zai iya tsayawa ji yayi tamkar an haɗa maransa da bayansa ana dinkewa ga wani irin harbawa da zuciyarsa keyi da Masifar ƙarfi kwanciya yayi akan 3sitter yayi rub da ciki baki daya ilahirin jikinsa rawa yake ga zufa dake tsats-tsafo masa tamkar babu Ac saboda yanda azabebben ciwon cikin ke gallazarsa yakai kimanin minti talatin yana murƙususu akan kujera kafin ya fara lafawa sannu Ahankali ya fara maida numfashi yana fesaewa.

*Gembila*

Asma'u kuwa ta daɗe tsaye aƙofar gida bata samu Adaidaita ba jin kiran sallar La'asar yasa ta juya da niyyar koma gida tayi Sallah kuma sai tasamu adaidaita shiga tayi tana isa gidan Kai tsaye falon Mommy ta shiga bakinta ɗauke da sallama zaune ta samu Khausar da Haiydar tana riƙe da hannunsa tana yanke masa Farce.
Haiydar kuwa kallon Khausar yayi kana yace.
“Nifa ki kula kar ki yanke min hannu”.
Hararansa tayi sai kuma ta cigaba da yankewa kana tace.
“Tunda dai baka iya ba kona yankekama kai ka jawa kanka”.
Ta ƙarasa maganar tare da sauke Idanunta akan Asma'u data gama shiga falon da sauri ta sake masa hannunsa tare da miƙewa da sauri ta Rungume Asma'u cike da farin ciki tace.
“Oyoyo Asmeey ta”.
Zare ido Haiydar yayi tare da yarfe hannunsa yace.
“Wayyo ta yankeni Wayyo ya tsana”.

Da sauri Mommy ta fito daga Bedroom ɗinta Idanunta akan Haiydar tace.
“Lafiya kuwa”.
Yarfe hannu Haiydar yayi kana ya Marerece fuska yace.
“Mommy ki kallafa Addah Khausi ta yanke min yatsana daga kallon Asma'u”.
Langwaɓar da kai Asma'u tayi kana tace.
“Ayyah Haiydar Sorry sannu bata sani bane”.

Hararansa Khausar tayi tace.
“Rabu dashi ƙato dashi tunda dai har yanzu bai iya yanke Farce ba sai dai in yanke masa aikuwa nata yanke masa hannu”.
Kallonta Mommy tayi kana tace.
“Wato ma da saninki kika yanke sa?”.
Cikin sauri ta girgiza kai tare da langwaɓar da kai tace.
“Wallahi Mommy ban sani ba ganin Asma'u ne yasa na tashi da sauri ashe na yanke sa”.
Chapter 36 · 0% Book details