← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 150

Sashe 56

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Hajia Bunayyah ta zubawa Didi, idanu sabida a zatonta, lamarin zai zo da gardama ne, ta yadda zasu koma Nigeria da Khausar, ga mamakinta sai taga Didi ta gaza ƙarasa kalmar bakinta, sai juyawa tayi ta fuskanci alƙibla, tare da yin sujudul Shukur cike da yalwataccen farin ciki da yasa hawaye fara zubomata.
Wani irin malolon bakinci ne, ya takari ƙahon zuciyarta, sai kuma tayi ƙasa da kanta, jin Didi na cewa.
“Alhamdulillah wannan mgnar itace mafi daɗi a cikin dukkan bayanan da kikayi mana Innayi kin gama min komai a rayuwata".
Lamiɗo kuwa sassayyan numfashi ya fesar hakama Bappa Jimeta da kuma Abban Jameel. Hajja Nana kuwa ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe tare da gyara zamanta cikin jin daɗin nagartar ahlin Modibbo, yanzu matsalarta ɗayace, ta yaya Modibbo zai karɓi Khausar wacce irin tarba zaiyi mata a matsayinta na matar da aminshi ne yayi mishi zaɓinta, bawai dan ita ɗin zaɓin rashi bane, gouron numfashi ta kuma fesarwa tare dayi mgnar zuci.
“Dole in sa ido kafin komawarmu inga irin tarɓa da kuma yanadin da yaron nan zai amshi Khausar a matsayin mata, muddin naga abinda bai minba, ko alamu. Tozarci ko cin fuska, Allah shine shaida wlh bazan bar jikata a wulaƙanta min ita a ƙasar da bata da kowa nata ba.”
Sai kuma ta juyo kanta ta kali Niyna kakar Modibbo kenan mahaifiyar Abualeey, cikin kamala kawaici mutuntaka gami da aminci tace.
“Ku shirya idan Allah ya kaimu gobe da yamma akwai taro na musamman, wanda dama an shiryashi tun kwana uku baya, don zamu gabatar da Aleey a gaban family'nsa, tuni Fada take amsar bakunar ƴaƴanta da jikokinta na nesa dana kusa, domin wannan shine buri da fatan dukkan ahlinmu. Toh Alhamdulillah gabatarwa ta ƙara armashi tunda da matar Aleey ta aure ta sunnan ma'aki S.A.W. za'ayi taro".
Sai kuma ta kalli Jakadiya tare da cewa.
“Jakadiya a sanarwa sarki shiri a shirya gangamin gabatarwar da na aure. Kana ki gayawa Gimbiyya Lailai ta tanadi kayan amarya dana ango, a kuma fidda ƙoren al'ada”.
Cikin biyayya da girmamawa Jakadiya ke amsawa da.
“An gabama Gimbiya Shatu”.
Sai kuma ta kalli Sarki Youseep Mouleey tare da cewa.
“A sanarwar faɗa gobe babu zama, kana taron na family ne, idan Allah ya kaimu jibi kuwa za'a gabatar da Aleey a Fada, da kuma bayyanenne matsayinss”.
Yah Salam Didi kam sai wasu hawayen farin cikin ne ke zuba mata wani ba korar wani.
Galadima kuwa da Waziri kawai murmushi sukeyi kai kace anyi musu bushara da al'jannane.

Sheykh Jabeer kuwa a gyaran murya yayi tare da kallon matar amininsa Marigayi Sarki Muhammad Mouley, da ɗan murmushi a fuska yace.
“Da dai kada a yawanta bidi'a a lamarin, kuma da an sirranta shi ko”.
Cikin sauri Galadima yace.
“Yah Sheykh ai Aleey ya sirrantu tsawon shekaru talatin ai yanzu kam lokacin bayyanar sa ce tayi, dole ya fito ko domin girgiza zuƙatan sauran ɗan burbushi magauta duk da dama suna zaton haka tunda kowa yasan labarin wasiƙar da Innayi ta bari kafin tafiyar kuma a san shi ba a tsinci gawarsa ba kamar yadda ake tsinta na yayunshi da suka gabata, masu fariyar dole sarauta ta bar hannun ahlin Aliyu Mouley, su san cewafa ga wani Aleey mazan”.
Murmushi mai ɗan sauti Sheykh Jabeer yayi dan shi kansa al'amarin yana tsumashi yana tuna mishi irin magautan da suka fuskanta a masarautar Joɗo, shida har tsuntsuwa aka meda mahaifiyarsa. *A Littafin GARKUWA sai gashi kuma ƴar shima ta faɗa irin gidan*
Innayi kuwa cikin yaƙini tace.
“Da izinin Allah su da Aliyu na sai dai kallo basu da zarrar iya cutar dashi”.
Cikin gamsuwa Sarki Youseep Mouleey ya gyara zamansa tare da fuskatarsu kana yace.
“Aje a fara shiri”. Daga nan aka watse taro cike da jin daɗi.

Didi ce zaune a bakin gadon ta na alfarma yayinda
Lalla Khadijah da Hafsat dake zaune a gabanta cikin tsananin happy tace.
“Didi kin ko tuna cewa gobene birthday ɗin Aliyu”.
Kai ta jinjina tare da kallon Rahama da ta miƙe zaune tana mai danna wayarta tace.
“Didi kice inyi gayyata ta mu samman”.
Ta ƙare mgnar tana shiga group ensu na Mouley family.
Didi kuwa cikin jin daɗi tace.
“Ai kuwa Rahama ki gayyata ta musamman domin bikine na musamman.
Sai kuma ta kalli Hafsat tare da cewa.
“Ki kira ƙawarki Islam kuje Ryad square shopping mall. Ku ɗebo dukkan abinda ya dace, kama daga na amarya da shi Aleey.
Daga nan in kun taso ku biya Marocco Mall ki ku zaɓo dukkan abin buƙata na al'adun amaren masarautar Mouley, Hafsat so nake komai ya zama na musamman ne”.
Cikin sanin manufar mahaifiyar tasu ta ce yanzuma kuwa Didi.

Khadija kuwa da sauri tace.
Amman sai munje munga amaryar kafin mu tafi”.
Gyaɗa musu kai Didi tayi tare da cewa.
Nima yanzu zan tafi sashin Niyna dan ance min su Goggonku Salma da Zakariyya sun iso”.
Daga nan ta miƙe ta fita.
Rahama kuma tana gama fesa labarin hidimar da za'ayi a masarautar tasu gobe misalin ƙarfe huɗu na yamma.
Ta kuma shiga group ɗin na ƙawayenta.
Nan ta fesa musu.

A masauƙinsu Khausar kuwa bayan su Ummin da Innayi sun dawo cikin farin ciki Ummu ta zauna kusa da Khausar dake riƙe da kwanon ƙasaitacciyar mace da Ummin ta dama mata tun kafin su tafi.
Ƙwaffa tayi tare da cewa.
“Wai Khausar har yanzu baki shanye damun nan ba?”.
Fuska ta ɗan kwanɓe tare da cewa.
“Allah ko Ummi abun babu daɗin”.
Da sauri Asma'u tace.
“Ni dai Wlh yayi min daɗi gaba ɗaya gumbunan da da garukan ɗaɗine dasu, wani garɗi kamar na dabino da aya da kwakwa harda ɗanɗannon zumafa a ciki, Ummi gashi da zaƙin su ƙungiyar alewa da kuma mazarƙwaila”.
Da sauri Ummu tace.
“Toh sha zumami kice mana wanda aka ɗan sha ɗin ma kece kika shanye. da kike koro jawabi haka”.
Yar dariya tayi tare da rufe idonta kana tace.
“Sai daifa gsky kuma duk da kayan dadin akwai itatuwa da jijiyoyi dan naji ƙamshi jijiyar ilanwaddihi ma da ma kwaranyi wanda kike yawan aikena in amso miki wurin Innayi”.
Harara Ummi ta cilla wa Asma'u tare da cewa.
“Dama ai mgni kam bazai yi ɗaɗiba, maza Khausar kafa kai ki shaye”.
Cikin rumtse idanun ta kafa kanta ta fara sha.
Saida tasha kusan rabi kana ta janye kwanon tare da kwaɓe fuska tace.
“Wlh Ummi ni dama can kayan zaƙi bai cika dakuna ba, nafi son abun yaji-yaji kiga mana kazar nan da kika dafa min duk da babu daɗi amman dana zumbuɗa yaji na cinyeshi fes. Kuma Kinga Wanda Aunty Hajara ma ta kawo min na cinyeshi. Shi kam ma yafi rashin daɗi dan da ƙyar naci tanata zagina wai dubu ashirin da takwas ta biya AYSHA ALIYU GARKUWA ta dafa minshi wai zuciyar farin ragone”.
Haɗe fuska Ummi tayi tare da cewa.
“Kuma wannan ɗinma sai kin shanyeba”.
Jin haka yasa ta kafa kai ta shanye, tare da ajiye kwanon kana tace. “Alhamdulillah na gama”.
Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.
“Yanzu muka dawo daga sashin kiran da akayi mana, munje bisa jagorancin innayi”.

Da sauri Asma'u tace.
“Ummi kunga Yah Modibbo?”.
Kai ta jujjuya mata tare da cewa.
“Bamu ganshiba, baima san munzoba, innayi ma sunce ta bari sai gobe zata ganshi”.
Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.
“Uhmm me ake ta ɓoyeshi sai kace kuɗine shi ko zinari”.
Zura mata ido Asma'u tayi tare cewa.
“Yoh ba doleba, sun san akwai mai ƙar mishi kallo har gashin ƙeyarsa ta iso”.
Harara ta cillawa Asma'u tare da cewa.
“Waya ma damu da dashi”.
Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
“Yanzu dai tashi kiyi Wonka, tunda dilken ya kai awa biyu a jikinki”.
Da sauri tace to, tare da miƙewa ta nufi bathroom din.

Asma'u kuwa falo ta nufa jin innayi na kiranta.

Zaune ta sameta dasu Hajia Bunayyah da kuma su Aunty Hauwa duk dai waɗanda suka zo tasu.
Gyara zama tayi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya kana tace.
“Idan Allah ya kaimu gobe za'a fara hidimar bikin Khausar da Modibbo kamar yadda al'adar masarautar Mouley takeyi.
Dan haka ku shirya karfe huɗu na yamma ne za'a fara.
Zuwa Maggarib an gama na gobe sai kuma zuwa jibi.
Cikin tsinkewa da lamarin cigaban da Khausar ta samu Hajia Bunayyah tace.
“Uhmm Allah ya kaimu”.
Sai kuma ta yunƙura zata tashi.
A hankali ta koma zaune jin muryar Hajja Nana na cewa.
“Bisa alamu dai Khausar taci ribar ƙin auren ɗan mayu, abu ya haɗu, sunna ta haɗu da farilka, sakekke ya haɗu da sakekkiya, wato bazawari ya samu bazawara ɗan maye da ƴar Mayu, jikar tsarki da jikan sarki”.
Cikin takaici Hajia Bunayyah tace.
“Kamar yaya kuma Sunan ta hadu da farilla?”.
Kai Hajja Nana ta jinjina cikin isa kasaitar data motsomata yau tace.
“Eh ɗan babban Sarkin Mouley na kasar Marocco ya auri jikar babban Sarkin Gombawa na ƙasar Nigeria jihar Gombe, kin san su dama su Khausar kirarinsu Gombawa ɗiban fari ba'a kwana dasu ba a tashi dasu, Gombe doma hamadar sarki lahirar sulaimanu”.
Da sauri Innayi ta kalleta cikin rashin fahimta ita kuwa Hajja Nana cikin ƙasaita tace.
“Yoh da ji kikeyi ku kadaine keda masarauta, to idan baki saniba, Sarki Buba Yero shine tsohon mijina kuma kakansu Khausar, barina Gombe da mahaifin Khausar da bappanta Muhammad, ne yasa masarautar ta koma hannun kaninsu ɗan abokiyar zamata, kuma shi har yanzu jira yake Yayanshi bappan Khausar yaje ya karɓi ragamar mulki dan su masarautarsu sunada imani da ƙaunar juna babu wani tsaface-tsaface, nice na hana sabida ni kwanciyar hankali ƙannena yafi min”.
A hankali Ummi dake jiyo Hajja Nana ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Haba sai haka mana ƙasaita da isar Hajja Nana tayi yawa, ita kanta Khausar ƙasaitarta da kwarjinin ba irin na normal mutane bani, kwarjinin ta yawa gareshi.

Sai kuma ta kalli Khausar da fitowar ta kenan daga Bathroom.
“Masha Allah”. Shine abinda Ummi ta faɗa sabida ganin wani irin sheƙi da ƙellin da fatar Khausar keyi kai kace tarwaɗace, tsabar farin da tayi kace balarabiyace.
Chapter 56 · 0% Book details