← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 150

Sashe 45

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi kuwa Modibbo ratsasu yake a hankali tare da bin hanyar da bata nan ya zo ba, tafiya kaɗan yayi ya ɓullo kan fadar.
Wanda tuni wasu hadiman sun kuma maye gurɓin waɗancan da suka tafi wurin dokin.
Jiyo alamun takun mutanene yasa ya ɗan juyo, ainkuwa zugar tawagar da ya barine suke biye dashi cike da girmama.
Bai fahimci komaiba a cikin abinda suke mishi, kawai dai yana bin hanyoyin da ya saba gani a mafarkansa ne, hakan yasa ya fara taka steps ɗin.
Da sauri wanda yake bakin ƙofar ya tura ƙofar tare da sa hannun sa ɗaya a ƙirji ya ɗan rusunar da kai, ɗai hannun kuma yayi masa alamun bismlillah ga hanya ka shiga.

A hankali yake takun cike da kamala da haiba, ya kutsa kanshi cikin tamfatsestsen falo na al'farmar da ƙasaita. Wanda komai na cikinsa ja ne, sai ratsin baƙi, bisa alamu kalan tutar ƙasarsu ce.

Babban falone wanda a ƙalla zai iya ɗaukan mutun sama da ɗari.
Yana shiga Sarkin Dawaki na biye dashi a baya.
Da sauri ya kalli gefen damanshi jin muryar yaron nan da suka haɗu a jirgi na cewa.
“Alhamadullah Abeey kaga ga wanda nacema mun haɗu dashi a jirgi, mai kama da Ibrahim”.
Faɗin hakane yasa duk suka kalleshi sai kuma suka kalli inda yake nuna musu.
Da sauri wani Kekkyawan Mutun mai cikar haiba, kamala, haɗi da ƙasaita ya miƙe tsaye cikin shiga ta al'farmar dake nuni da shine Sarkin masarautar ƙasar Marocco.
Miƙewarsa tsayence tasa dukkan sauran mutanen kama daga Waziri, Galafima, Wambai, Ɗan Maliki, Sarkin gida, Sarkin fada, dama gyara kimtsi Sarkin zagi kab suma suka miƙe tsaye cike da zubawa Modibbo idanu tamkar zasu ɗagashi sama da idon.
Dr Jameel kuwa, muƙut ya haɗiye wani yawu mai haɗe da mmki dan jarabar neman mata shi bai barshi yayi wani tunani kan kamannin Modibbo da Ibarahim ba koma yace da kawunshi ba.
Sai kuma yace.
“Har nan”.
Moddibo kuwa Jabeer bin Jabeer daya dawo gabanshi yana miƙa mishi hannu ya zubawa ido tara da bashi hannun.

Shiko Jabeer jawoshi yayi har zuwa gaban Sarkin tare da cewa.
“Ganshifa ko makaho ne ya shafa fuskarsa ya shafa taka ko ta Ibrahim yasan wannan mallakinmu ne shi, Abeey ba dama na gaya makaba”.
Ya ƙare mgnar da kallon Sheikh Jabeer .
Shi kuwa Sheikh Jabeer wani Gwauron numfashi ya fesar tare da yiwa Ɗan aminin nashi nuni daya zauna.
Cike da kaɗuwa Sarkin Mouleey ya zauna kana yayiwa dukkan fada alamun su zauna.
Haka kuwa duk suka zauna.
Dr Jameel ne ya ɗanyi gyaran murya tare da rusunar da kai cikin ladab yace.
“Ayi min izini in tashi zan shiga wurin Didi in duba Rahman".
kai Sarkin fada ya gyaɗa masa tare da nuna masa hanya alamun yaje.
Cikin sauri Dr Jameel ɗin ya miƙe da tare da kamo hannun wani ɗan yaron da bazai gaza shekara gomaba yace “Muje”. Ya ida maganar tare da jan hannunsa suka juya zasu fita.
Da sauri Modibbo ya miƙe tare da bin bayan Dr Jameel.
Cike da mmki ya tsaya ganin fadawan da suka zagayeshi da sauri kana sunkayi mishi zobe tare da baza manyan rigunansu.
Suka tareshi baya iya ganin Dr Jameel.
Cikin sanyin murya yace.
“Yah haka Ku buɗe min hanya mana zan tafi”.
Da sauri ya juyo jin Muryar Sarkin Zagi na cewa.
“Gyara kimtsi bisa umarnin mai martaba kuyi mishi jagora sashi na musamman”.
Kafin ya fahimci mai kalaman Sarkin zagin ke nufi, sai ji yayi anja hannunsa ba tare da an cire ƙawanyar da ankayi masaba, yaji sun fara tafiya dashi.
“Ikon Allah wai na zaune ya daɗi".
Shine abinda yake faɗi a ransa yana mai ƙoƙarin ɗago kanshi sama, wai ko zai samu yaga gabanshi amman ina.
A hankali ya fesar da numfashi sabida tariyo masa da mafarkansa da kwakwalwarsa tayi masa.
Taku yaci gaba dayi da bin sawun Sarkin gida dake jansa wanda ta cikin ƙaton falon sukabi ta wata babbar ƙofa, tafiya mai tsawo sukayi kana yaji sun fara hawa steps jim kaɗan kuma yaji sun ɓulo ta wata kusurwar, ɗan gajeren tsaki yaja.
sabida jin tafiyarfa taƙi ƙarewa, kuma mutumin nan yayi mishi riƙon babban ɓarawo, ga ƙattin fadawa da suka zagayeshi.
“Toh wai me haka”.
Ya faɗa dai-dai lokacin da yaji, an ajiyeshi bisa wata ƙasaitacciyar kujera.
Sai kuma yaga duk sun janye ƙawanyar da sukayi mishi kana suka juya suka fita.
Da ido ya rakasu har suka je bakin ƙofa ga mmkinsa sai yaga mutumin nan da ya riƙo hannunsa yaja ƙofar da ƙarfi ya ruf....

Muje zuwa, wasa ya jiƙa, karatu dan aka biya kuɗin laranra Littafin yafi ɗadi ba haƙƙin kowa a kanki 1k ne fa kacal ki biya kada ki kiranta na sata 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 ki biya in tura miki littafin ki karanta abinki cikin Salam kana in saki a Group ɗin littafin kusha comments,

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 12*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*TSAYA! TSAYA!!! NACE ki TSAYAKO Sister's* duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing, gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai ba🤗nd wanan new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku, domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso ga number's ɗin da zakuyi mgn bani AYSHA ALIYU GARKUWA, zakuyiwa mgn ba, gaban 👇🏻👇🏻👇🏻Ga ta inda zakuyi magana Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

Cike da matsanancin mamaki Moddibo ya tsirawa ƙofar da suka rufe ido, toh shin me hakan yake nufi, gwauron numfashi ya fesar yayin da abubuwa da yawa suka riƙa dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa, cikin kasala ya jingina bayansa da jikin kujeran kana ya buɗe manyan idanunsa da suka sauya launi.
Ahankali ya shiga ƙarewa tsarin falon kallo, falone mai masifar girma da kyau tun daga farkon falon yake ɗauke da wasu lumtsa-lumtsan kujeru 4couner tun daga farkon Falon har ƙarshesa kujerune zagaye dashi ya kasance kalan Golden ne da ratsin milk kana da ɗigon Coffe ga wasu trust pillow kalan Golden da suka sake ƙawata kyawun kushin ɗin yayin da ƙasan falon ke mamaye da wani lallausan Darduma kalar Golden da ratsin milk kana da ɗigon Coffe daga can saman P.o.p kuwa wasu irin Gloves ne da akayi musu dising na ƙawa da alfarma, yayin da Labulayen suma suka kasance kalan Golden ɗin, daga tsakiyar Falon kuwa wasu stool ne masu azabar kyau guda biyu ɗaya daga farkon falon ɗaya kuma daga ƙarshe kuma jikinsu duk akwai ƴan ƙananan stoll guda huɗu, wanda za'a iya jansu, iya tsaruwa falon ya tsaru kana sai can gefen daga gefe kuma dinning area ne mai ɗauke da dining table shima komai goldie ne, sai daga gefen dama can wata ƙoface dake da ƙawanyar labule, hakama gefen hagu falo ne na al'farmar kai da ka gani kasan babu ƙaranta a cikin lamarin tsarin komai a fili zai nuna maka anci uban kuɗi a Masaarautar daga can tsakiya wani shunfiɗeɗɗen steps ne mai faɗi wanda ake shimfi tattausan Carpet na al'farmar busa alamun akwai wuri na musamman a saman.
Chapter 45 · 0% Book details