← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 150

Sashe 2

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Ahmad na ɗagawa Abba yace.
“Malam kazo da Fatima da yaranta!?”.
Cikin tsinkewar zuciya Malam Ahmad dake Bedroom ɗinsa ya miƙe tare da cewa.
“Meya faru Alhj Bashir ka faɗa min”.
Girgiza kai Abba yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.
“Ga gawar Jameelu na agabana”.
Cikin tsanananin tashin hankali Malam Ahmad ya dafe bango tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha”.
Katse kiran Abba yayi cikin sauri ya fito falon tsaye ya samu Ummi riƙe da waya a hannunta cikin ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin sa yace.
“Fatima Lafiya!?”.
Ahankali Ummi ta juya ta kallesa tare da cewa.
“Yan zun nan Abban Jameel ya kirani, to kuma ya yanke gashi kuma ina ta sake kira naji line Busy”.
Da ƙyar ya haɗiye wani abu mai masifar ɗaci kana cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yace.
“Toh kada ki damu kizo muje muji meke faruwa”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Sannan ta nufi hanyar fita.
Kallon Bashir da Asma'u dake tsaye yayi kana yace.
“Kuma kuzo mu tafi”.
Kai suka gyaɗa kana suka bi bayansa suka fita.

Suna isa falon suka samu Hajiya Turai da Hajiya Karima da ƴaƴan Hajiya Karima na kuka cikin sauri Ummi ta ƙara sa shiga falon tare da tsayawa agaban Abba kana tace.
“Abban Jameel meye faru?”.
Ahankali ya ɗago ido ya kalleta, sai alokacin yaji kuka ya kufce masa ganin Ummi agabansa baki ɗaya ta gigice jikinta na rawa.
Cikin rawan murya tace.
“Abban Jameel meyafaru!?”.
Kasa cewa komai Abba yayi sai kuka da yake tamkar ƙaramin yaro.
Da sauri Ummi ta juya tare da kallon yanda su Hajiya Turai ke kuka cikin rawan murya da yanayin tashin hankali tace.
“Ku faɗa min mana meke faruwa!?”.
Tayi tambayar baki ɗaya ilahirin jikinta na rawa.
Asma'u da Bashir dake tsaye Atare suka fashe da matsanancin kuka ganin yanda ƙannen M Jameel ke kuka.
Ahankali Malam Ahmad ya matso kusa da Ummi tare da cewa.
“Fatima ki zauna”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“Ni bazan zauna ba kafaɗa min abinda ke faruwa”.
Cikin sanyin murya Lamiɗo yace.
“Maman Jameel kiyi haƙuri ki zauna”.
Kallon sa tayi tare da cewa.
“In zauna?”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh”.
Cike da tausayawa Malam Ahmad ya janyo hannunta tare da zaunar da ita.

Abba kuwa kallonta yayi cikin tsanananin fargaba da tashin hankali yace.
“Fatima”.
Cikin rawan murya da raunin zuciya tace.
“Na'am Alhj Bashir”.
Cikin sauri Abba ya kalleta wannan shine karo na farko arayuwar sa da yaji ta kira sunan shi kai tsaye.
Jinjina kai tayi Idanunta tsaye akansa tace.
“Eh Alhj Bashir ka faɗa min menene? kafaɗa meke faruwa”.
Rintse idanunsa yayi yana jin kansa na sarawa Araunane yace.
“Fatima Jameelun mu”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh nasani akan Jameelu ne to Menene ya faru?”.

Kasa cewa komai Abba yayi kawai sai ya fashe da matsanancin kuka yayin da hawaye ke bin kuncinsa Shar-shar-shar.
Cikin raunin murya yace.
“Fatima ga Gawar Jameelun mu”.
Atake maganar ya daki dodon kunnenta kana ya ratsa ƙwaƙwalwar ta zuwa zuciyarta saurin kallon Abba tayi tare da sakin Murmushi kana ta juya tare da kallon su Hajiya Karima dake kuka cikin wata dakakkiyar murya mai cike da ƙuna tace.
“Toh kukan me kukeyi!?,
Juyawa tayi tare da kallon Abban M Jameel kana tace.
“Har kaima kuka kakeyi!?Haba Alhj Bashir Addu'a ya kamata ka masa amma ba kuka ba!, Su mata suyi kuka kaina kayi Yanzu ina yake?”.
Cikin sheshsheƙan Kuka Abba ya nuna mata kwalin da ya tsarsa kana yace.
“Gashi can”.
Saurin Kallon wajen tayi Zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi still Muryanta adake da wani irin bushewa da hurawar zuciya tace.
“Gawar ne kuma acikin kwali”.
Cikin wata raunan'niyar murya ya Girgiza kai kana yace.
“Kiyi haƙuri kiyi ta maimaita Addu'a”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin La'ilaha Illah anta subhanaka inni kuntu Minal Zhalimin Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha³”.
Ahankali ta gyara zamanta tare da naɗe ƙafafunta tare da sakin murmushi kana ta fuskanci gabas yayin da Idanunta suka kaɗa sukayi jawur jikinta na wani irin tsuma na tsananin tashin hankali cikin raunin murya tace.
“Ya Allah kaine ka bani Jameelu, kai kasa ya zamemini Garkuwa, ya Allah kajiƙan sa da rahma, ya Allah kasa ya huta Alfarman Annabi da Alkur'ani, Allah kayi mana SAKAYYAH akan dukkan waɗanda suka cutar damu ya Allah kayi mana SAKAYYAH”.
Kusan a haɗe baki daya mutanen falon suka amsa da Ameen.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ne ya kufcewa Asma'u da Bashir musamman Asma'u numfashinta har fisga yake baki ɗaya Falon kaurewa yayi da koke cikin rawan murya Ummi tace.
“Ina gawar yanzu Jameelu na ne haka acikin kwali?”.
Jinjina mata kai Abba yayi tare da cewa.
“Eh shine”.
Still Muryanta adake tace.
“Wani irin mutuwa yayi da har gawarsa zata ƙankace ya zauma acikin kwali”.

Asp dake tsaye ya kalli Ummi cike da tausayawa yace.
“Hajiya kiyi haƙuri ya riga daya bushe, shiyasa ana taɓa shi ya kakkarye!”.
Ahankali ta juya ta kalli Asp kana tace.
“Toh ya akayi kuka tabbatar Jameelu na ne?”.
Cike da tausayawa Asp ya ƙara sa gaban Kwalin kana ya buɗe mata ahankali Ummi ta tsirawa jerarrun gabɓan gawar dake cikin kwalin ido ahankali ta sauƙe Idanunta akan zara-zaran yatsun, hannunsa da suka bushe kana ta tsirawa zoben hannunsa ido.
Cikin wani irin yanayi na ƙunan zuciya da sadaukarwa tace.
“Hmmm!”.

Ahankali Asp ya sake nuna mata takalmin M Jameel dake cikin leda da kuma wayoyinsa cikin sanyin murya yace.
“Ga takalmansa da kuma wayoyinsa duk agabansa muka samu sun ajiye masa da goran ruwa.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.
“Tabbas Jameelu na ne”.
Ahankali ta matsa jikin kwalin sosai tare da sanya tafin hannunta ta rufe kana ta sunkuyar da kanta akan kwalin cikin Muryan ta daya fara karaya tace.
“Babana bazan yi maka kuka ba, sannan baza zubar maka da hawaye ba, kana bazan yi maka Ihu da kururuwa ba, amma zan ƙarashe baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu'a, zan ƙare rayuwata da ƙunan rashinka zan ƙare rayuwata babban giɓin rashinka”.

Wani irin tausayinta ya ratsa baki ɗaya jama'ar dake falon ahankali Malam Ahmad da Lamiɗo suka sanya hannu tare da share hawayen da suka saƙƙo musu.
Cike da rauni Ummi ta cigaba da cewa.
“Babana zan ƙare baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu'ar Ubangiji ya karbi shahadarka Allah ya maka SAKAYYAH tun daga nan duniya akan wa anda suka zalince ka har zuwa ranar tashin Alkiyama. Allah Ubangiji yajiƙan ka da rahma Allah ya gafarta maka yasa kahuta”.
Cikin sauri Hajiya Turai ta ƙarasa kusa da ita tare da Rungumeta ajikinta kana cikin Muryan kuka tace.
“Kiyi haƙuri Hajiya Fatima kiyi shiru”.
Kallonta Ummi tayi still Muryanta adake tace.
“Idan banyi haƙuri ba Hajiya Turai ya zanyi. Ubangijin daya ɗauke Jameelu shi yabani shi kuma shi ya ɗauke sa kana ya fini sanin wanene Jameelu agareni, sannan ya fini sanin Jameelu Allah ya masa rahma”.
Ta ida maganar tare da janye Jikinta daga na Hajiya Turai tare da juyawa ta kalli Abba kana tace.
“Ina Moddibo!?”.
Tana gama fadar haka tayi baya tare da sumewa.

Cikin sauri Hajiya Karima ta mike tare da ɗauko ruwa ta yayyafa mata dogon numfashi Ummi taja tare da buɗe Idanunta kana tace.
“Ina Moddibo yake?”.
Cike da tausayawa Abba yace.
“Moddibo yana asibiti asume tunda abin ya faru daya farfaɗo idan ya kira sunan Jameel zai sake sumewa, yanzu ne da aka samu ya farfaɗo aka masa Alluran bacci”.
Araunane tace.
“Ku kaini inga Moddibo sannan kada aje abinne Jameelu abari sai Moddibo ya farfaɗo yaga J ɗinsa na ƙarshe ya tabbatar cewa J dinsa tafi ya barsa bari na har abada, idan yaga haka zai dangana ya sawa ransa haƙuri amma yanzu dan Allah ku kaini wajen Moddibo”.
Abba ne yace.
“Yanzu zaki tafi can?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh ku kaini wajensa”.
Ahankali Malam Ahmad ya miƙe tare da riƙe hannunta suka tafi.

Asma'u da Bashir kuwa kuka suka sake fashewa dashi har muryarsu baya fita saboda tsananin tashin hankali.
Rintse Idanu Abba yayi cike da tausayawa ya kallesu kana yace.
“Ku daina kukan nan kuyi masa addu'a babu abinda Jameelu ke buƙata awajenmu yanzu kamar addu'a.

Acan asibiti kuwa Ummi da Malam Ahmad na isa a reception suka samu Malam Arɗo tsaye ganinsu yasa ya ƙara sa kusa dasu kana yace.
“Maman Jameelu kiyi haƙuri. Ubangiji Allah ya jikansa da rahma Allah ya gafarta masa Ubangiji ya amshi shahadarsa”.
Cikin sanyin murya tace.
“Ameen Malam Arɗo ina Moddibo?”.
Ahankali ya gyara tsayuwar sa kana yace.
“Gashi can yana ciki”.Ya faɗa tare da shiga gaba Ummi da Malam Ahmad na biye dashi.
Suna shiga ɗakin Ummi ta zubawa Moddibo idanu dake kwance plat Fuskarsa tayi fayau duk da bacci yake amma tashin hankali da fargaba ne kwance asaman fuskarsa.
Ahankali ta riƙe hannunsa acikin nata kana tace.
“Moddibo munyi rashi, rashin da baza mu maimaita gurbinsa ba, munyi rashi rashin da har abada ba zamu mance shiba, munyi rashi rashin da saidai namu mutuwar ne zai mantar mana dashi”.
Moddibo kuwa duk da Alluran baccin dake jikinsa hakan bai hana shi jiyo sautin muryan Ummi ba. So yake ya farka domin kunnuwansa na sauraronta haka zalika yana iya motsa gaɓɓansa sai dai koda ya buɗe idanunsa baya ganin komai cikin wani irin yanayi ya damƙe hannun Ummi acikin nasa, yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.
Kallon Malam Ahmad Malam Arɗo yayi kana yace.
“Toh tunda kunzo bari na wuce na faɗawa Kakarsa halin da ake ciki”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.
“Ya kamata kam aje afaɗa mata sannan itama ataho da ita”.
Chapter 2 · 0% Book details