← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 150

Sashe 67

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty Hajara, Aunty Ruƙayya, Asiya atare suka saki murmushi kana suka miƙe cike da gamsuwan cewa ba Jameel bane kawai dai kamanni ne, domin da Jameel ne bazai ce zai Auri Asma'u ba wannan kalmar kaɗai ta gamsar dasu cewa ba Jameel bane, domin idan M. Jameel ne babu ta yanda za'a yi yace zai Auri ƴar uwarsa ƙanwarsa da suka kasance uwa ɗaya kana suka sha nono ɗaya, da wannan
gamsassun hujjoji suka bi bayan Ummi zuwa bedroom.
Innayi kam murmushi tayi cike da gamsuwa cewa lalle wannan ba M Jameel bane kamanni ne kawai, fuskarta ɗauke da amintaccen murmushi ta kalli Dr Jameel tare da faɗin.
“Toh an baka”.
Saurin kallonta Moddibo yayi babu walwala atare dashi yace.
“Kece me bada Asma'u koni ne mai bada ita?”.
Still Innayi na murmushi tace.
“Kaine Mai bada ita amma kaima ai ina da iko akan ka”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Eh kina da iko akaina Innayi, amma ai shi Aure ɗan bincike ne sai na bincikesa nasan ingancin sa tukunna kafin na bashi Asma'u”.
Asma'u kuwa tun lokacin da yace yana sonta data daskare zaune, sai yanzu taji tayi azamar miƙewa sabida jin kuzarinta ya dawo,
Da gudu ta miƙe tabar wajen yayin da Khausar ta miƙe tabi bayanta.
Cikin lumshe idanu Moddibo yabi Khausar da kallo har ta ɓacewa kallonsa idonsa na kanta wani sassayyan numfashi ya fesar tare da lumshe ƙwayar idanunsa.

Zakariyya kuwa tunda suka shigo idonshi na kan Aseeya gaba ɗaya ya gaza ɗauke idanshi a kanta.
Ibraahim kuwa shiru yayi yana kallonsu kawai.

Ganin duk sun watse yasa Innayi maida kallonta kan Moddibo kana tace.
“Bismillah kuje kuci abinci naga kamar abinci kuke ci na tada daku”.
Kai suka gyaɗa tare dayi mata sallama kana suka tafi.

Suna shiga Falon Dr Jameel ya kamo hannun Moddibo tare da langwaɓar da kai kana cikin sanyin murya da neman alfarma yace.
“Na roƙeka da girman Allah Moddibo kada ka faɗi wani abu da zai zubar min da kima da daraja a idon Ummi”.
Kallonsa kawai Moddibo, Ibraahim, Zakariyya sukeyi Shi kuwa cikin sanyi da neman alfarma ya cigaba da cewa.
“Na lura tana kallona da kima da daraja kuma Wallahi har cikin raina ina ƙaunar Asma'u kuma Aurenta zanyi”.
Cikin sauri Moddibo ya tari numfashinsa ta hanyar cewa.
“Gaskiya ayanayin kan nan dana lura da kai. Wallahi bazan baka Asma'u ba, Asma'u nine nan mai bada ita,Tana da mahaifi, Lallai Mahaifinta shine zai bada ita.
Amma bisa yaƙinina zai bada ita. Ni kuma bani da yaƙini akan ka”.
Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai zafi yana tuno yanayin munanan halayyar Dr Jameel kai ya girgiza kana yace.
“Baka da tsarkakan da zan baka tsarka-kakkiyar yarinya saboda Asma'u tsarka-kakkiyar ce.
Kallonsa kawai Dr Jameel keyi cikin rauni da nadama ɗabi'unsa da yakega zasu kasance mihsi barazana daga mallakar ƴarinyar da yakeji in bai setaba zai zauce.

Moddibo kuwa cikin yaƙini da gaskiya ya cigaba da faɗin.
“Saboda Faɗin Allah ma ɗaukakin sarki ne, cewa. Mazinaci baya Aure sai Mazinaciya ƴar uwarsa Asma'u kuwa tsarka-kakkiya ce ba Mazinaciya bace kai kuma kafi kowa sanin kanka”.

Ahankali Zakariyya da tausayin Dr Jameel ya gama cikawa zuciya ya kamo hannun Moddibo suka zauna kana cikin nutsuwa yace.
“Kayi haƙuri Moddibo ai abu da yawa yana zama sanadin shiryuwar mutum kada kayi mamaki Auren Asma'u ya kasance hanyar shiryuwan Dr Jameel”.
Kai Ibraahim dake gefe ya jinjina tare da cewa.
“Hakane Yah Aleey tunda har yace yana sonta da dai ashige masa gaba ba ba mamaki wannan abin da yake rashin mata ne”.

Dr Jameel kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya kalli Moddibo kana yace.
“Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! In dai za'a bani Asma'u Ni dai nayi al'ƙawari zan rabu da duk wata ƴa mace”.
Ganin gaskiya acikin ƙwayar idanunsa yasa Moddibo fesar da numfashi tare da cewa.
“Shikenan ka fara rabuwa dasu tukunna idan na gamsu ka rabu dasu.
Ni kuma zan baka ita In dai har na gamsu”.
Cike da farin ciki Dr Jameel ya gyaɗa kai kana yace.
“Ni kuma nayi maka al'ƙawari daga yau daga yanzu na rabu dasu”.
Ya ida maganar tare da zaro wayarsa kana ya shiga contact tare da blooking ɗin Number duk ƴan matan sa kana ya nunawa Moddibo.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Toh Allah yasa kayi iya deleting ɗin su acikin Mind ɗin ka da zuciyarka kamar yanda kayi awayarka”.
Asanyaye Dr Jameel ya furta.
“In sha Allahu babu kowa a raina”.

Juyowa Modibbo yayi ya kalli Ibarahim dake miƙa mishi woyoyinsa,
Murmushi Ibraahim yayi tare cewa.
“Tun da safe Abualeey ya bani su yace amman in bari sai dare in baki”.
Murmushi Modibbo yayi tare da cewa.
“Ummm yayi kyau”.
Cikin wasa Ibraahim yace.
“Nasa maka caji ne dan naga sun mutu sabida kiraye-karen da akayi ta maka”.
Miƙewa yayi tare da cewa.
“Yoh ba dole su mutuba moko guda”.

“Eh amman ai yanzu duk a cike suke”.
Cewar Ibraahim.
Kai Modibbo ya gyaɗa mishi yana mai kunna woyoyin nasa.

Acan ɓangaren su Khausar kuwa tunda suka shiga bedroom take sakin murmushi idanunta akan Asma'u da duk tayi zuru-zuru da ita kana tace.
“Asma'u Wallahi wannan ba Yan Jameel bane”.
Kallon mamaki Asma'u tayi mata Still hawaye na bin fuskarta tace.
“Kamar ya zakice ba Yah Jameel bane”.
Hannunta Khausar ta riƙe tare da cewa.
“Asma'u jikina ya faɗa min ba Yah Jameel bane.
Ki sani da Yah Jameel ne ko cutan hauka yayi ba zai kalleki yace yana sonki amatsayin matar Aure ba”.
Sai kuma ta sake damƙe hannun Asma'u acikin nata cikin son tabbar mata da gaskiya ta cigaba da cewa.
“Ki tuna fa Nono ɗaya kuka sha mahaifiya ɗaya ce ta haife ku fa wallahi Asma'u ba Yah Jameel bane, kawai ni inajin farin ciki araina ne. Alhamdulillah bazan rayu Ni kaɗai aƙasar nan ba zan rayu tare dake, zai ɗakko min ke ya dawo min dake ƙasar nan mu rayu tare”.

Zazzafan Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe idanunta akan Khausar tace.
“Wallahi nifa Khausar har yanzu ban gamsu cewa ba Yah Jameel bane”
Kai Khausar ta girgiza tare da cewa.
“Wallahi Asma'u ba Yah Jameel bane ya za'a yi Yah Jameel yace yana sonki zai Aure ki, Asma'u kiyi tunani mana hakan bazai taɓa faruwa bafa”.
Haka dai sukaci gaba da tattaunawa.
A daren wannan ranan haka suka cika da alhini da al'ajabi...

Acan Side ɗin Didi kuwa zaune suke da ƙannenta da kuma Yayyanta da suka zo.
Baki ɗaya hirar tasu akan Khausar ce suna yabon kyawu da kuma haibar da Khausar tayi kowa na faɗin albarkanci bakinsa.
A wannan ranan haka duka ahalin suka kwana cikin yalwataccen farin ciki.

Washe gari aka shirya taro na alfarma wanda baki ɗaya manyan Fada da kuma manyan Masarautar Morocco ne taro ne wanda yafi na jiya sai dai wannan taro ne na maza zalla saboda an gabatar da Moddibo amatsayin Sarki mai jiran gado kana ana gabatar dashi a baki ɗaya idon Fada sosai Moddibo yayi jawabi daya ratsa zukatan mutane kasancewar shi aka bawa Microphone ya rufe taron da addu'a.
Al'amarin da ya gigita jama'ar masarautar jin yanda ya dinga zazzago addu'oi yana rerawa cikin zazzaƙan muryansa.
Wani irin farin cikine ya mamaye zuciyar Abualeey ya tabbatar da cewa ɗan sa ya samu kyakkyawan tarbiyya da jigon da zai iya mulkar masarautar Mouley.
Cikin jin daɗi yake kallonsa,

Shi kuwa Modibbo addu'oin daya ta jerawa na yayi dai-dai da lokacin da aka kira Sallar Azahar.

Limamin masallacin Fadan dake zaune gefe wanda tsohone tukuf ya tsufa sosai bisa alamu kuma sa yanayin jinya na tsufa.
Cikin jin dadin ya sauke A tare da karɓan Microphone ɗin kana yayi jawabin cewa,
Shi ya fahimci wannan Yariman yana da cikekken ilimin addini dan haka daga yau ya sauƙa daga kan karagata na limanci shine zai cigaba da limanci masallacin masarautar su kasancewar tsufar da ya cimasan da kuma sanyin da muryasa keyi wacce wasu lokutan bata isarwa mabiyan jam'inshi.
koda Modibbo yaji haka yayi ƙoƙarin maida tayin da limamin yayi mishi amman ina yaƙi sabida da gskyarsa sufa tacin mishi.
Sai kallon Modibbo yake cikin so da
Amintaccen murmushi mai cike da yarda da yaƙini kamilin dattijon yake bin Modibbo da Addu'o'i kana ya ɗaura da cewa.
Hakan za'a yi kuwa domin Modibbo ya cancanta sai dai ko in baka kusa ko kayi tafiya ko wani abu dai to sai in jamu.
Daga haka taron ya tashi da yaƙin cewa an bar mishi Limanci...

Aranar Modibbo ne yaja limancin sallar Azahar, wanda baki ɗaya sautin zazzaƙan muryarsa ya cika masarautar.
Wanda baki ɗaya al'umma cikin Masarauta ke yaba zaƙin muryansa.

Bayan an idar da sallar Azahar Direct sashen Didi Ibraahim ya nufa cike da farin ciki ya zauna gefen Didi tare da riƙe hannunta kana yace.
“Didi kinsan waya ja mana jam'i?”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“A'a sai ka faɗa?”.
Cike da matsanancin farin ciki yace.
“Wallahi Yah Aleey ne Kai Didi wlh Innayi ta gama mana dukkan gata na duniya”.
Fuska ɗauke da yalwataccen farin ciki Didi tace.
“Kai Alhamdulillah”.
Chapter 67 · 0% Book details