← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 150

Sashe 27

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhamdulillah cikin kwanaki huɗu bizi'nsa ya fito da yake business bisa ne ba wuya.
Alhamdulillah ranar Al'hamis da misalin ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga daga Abujam Nigeria.
Zuwa Rabat babban birnin ƙasar Marocco kenan

A hankali ya fesar da wani irin zazzafan numfashi dai-dai lokacin da tayun jirginsu ke raɓuwa da ƙasar Nigeria, rumtse idanunsa yayi da karfi sabida wasu irin zafafan hawaye da yaji suna tsastsafo mishi ta cikin dukkan jijiyoyin idanunsa.
Wani irin yanayin da bai taɓajiba duk tafiye-tafiyen da yakeyi yaji yana dabaibaye rayuwarsa haka kawai yakeji kamar ya bar kasar kenan bari na har abada.
Lokaci ɗaya tunanin Jameel ya dawo masa, wanda hakan yasa yayi saurin jingina bayansa da kujerar jirgin.
Yana mai jin wani irin sassayan kuka na taso mishi daga can cikin ƙahon zuciyarsa, hakanne yasa ya fara karatun Alqur'ani mai girma a hankali.

Yayinda mutanen cikin jirgin kuwa kowa keta hidimar gabansa.

Shi kuwa Modibbo tunda ya zauna bai ɗago kansa ya kalli kowaba.
Sabida yanayin da yakeji.

A hankali dai tafiya ta fara nisa, tuni sun kutsa cikin sararin samaniya jirgi ya kama hanyarsa.

Koda akazo tambayarsu me yake buƙata.
Cewa yayi baya buƙatar komai.

A ƙalla sunyi tafiyar awa uku a sararin samaniya.
Zuwa yanzu kam mafi akasarin matafiyan kowa ya nitsu hada-hadar ta ragu matuƙa, wanda zuwa lokacin kuma sauran musu 57 minutes su dira cikin birnin Rabat sabida daga Abuja zuwa can tafiyar awa uku da minti hamsin da bakwai ne cib-cib.

A hankali ya gyara zamansa tare da kallon farin matashi da ya zo ya zauna gefensa wanda bazai wuce sa'anan ba.
Murmushi matashin yayi tare da miƙa masa hannun yana mai mishi wani irin kallo mai cike da tambayo al'ajabi da kaɗuwa.
Shima ɗan murmushin yayi tare da bashi hannu sukayi musabaha.
“Jabeer bin Jabeer Joɗa. Wanda ya kira kansa da Jabeer ɗan Jabeer Joɗa ɗin ya kare mgnar cike da masifar mamaki da zurawa fuskar Modibbo idanu yana matuƙar mamakin kamanninsa.
Shi kuwa Modibbo cikin yanayin sanyi yace.
“Aliyu Youssef Muhammad Mouley”.
Cikin tsananin bayyanar mamaki ya zazzaro idanu waje tare da juyowa garesa da kyau cikin alamu rawan jiki ya juya harshe zuwa larabci yace.
“Yah Salam toh kuma yaushe kazo”.
Cikin ɗan sanyi Modibbo shima juya harshe ih zuwa asalin amintaccen larabci yace.
“Nazo kuma? Nida ƙasata, me zanje yi a Marocco dai zaka ce”.
Kai Jabeer bin Jabeer Joɗa ya jujjuya tare da juyawa yayi mishi mgn da hausa yace.
“Kamar yaya ƙasar kuma?”.
Ga mamakin Jabeer sai yaji Moddibon na bashi amsa da harshen hausa.
“Sabida ni ɗan Nigeria ne girman Nigeria”.
Da sauri Jabeer yace.
“A'a wannan ai ko makaho ya shafa yasan kai ba ɗan Nigeria bane kuma ma sunan da ka fadi ai ya isa shaidar inda ka nufa komawa zaka yi ba zuwaba”. Ya ƙare mgnar da iya haƙiƙanin gskyrsa da rawan jiki.
Cikin ɗan ƙosawa da surutun sa Modibbo yace.
“To sabida me?”.
Da sauri Jabeer yace.
“Sabida kafi kama da Larabawa”.

“Toh gashi kuma kaima da larabawan kake kama”.

Gyara zama Jabeer yayi tare da cewa.
“Kuma ni dai ba fullatanine”.
A hankali shima Middibo yace.
“Minfu mi pullo”.
To zuwa yanzu kam mamakin Jabeer ya tsananta.
Ya buɗi baki da niyar zaiyi wata mgnar kenan aka kirashi a baya bisa dukkan alamu Kakanshi ne da sauri ya tashi ya nufi can bayan.

Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da numfashin gajiya da surutun da Jabeer ya sashin.
Tare da fara karatun Alqur'ani mai girma.

Jim kaɗan da tafiya Jabeer sai gashi ya dawo zama yayi bakinsa cike da tarin mgn to amman samun yana karatun Alqur'ani mai girma yasa dole ya haɗiye dukkan rogowar mgnarsa da tarin tambayoyinsa.

A hankali Moddibon ya ɗago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar Rarat da suka iso tsakiyarta.
Wanda tuni an sanar musu.
Haka nan yake jin wani irin salama da kwanciyar hankali kana da nutsuwa tunda suka shiga yankin ƙasar Marocco yake jin wani irin sanyi da more happy Wanda har ya iya jure surutun Jabeer.
Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙara ware manyan idanunsa yana kallon garin ta window'n jirgin.
Haka nan yakeji tamkar yabar damuwarsa baki ɗaya acikin Nigeria ya kuma saki dukkan ƙuncinsa a cikin Taraba.
Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake bin tsarin dogayen benayen gidajen garin da kallo kana sassayan muryarsa na ratsa kunnuwansa yana jin sautin karatunsa da yakeyi jikin suratul Kahf.

Misalin ƙarfe shida saura minti uku rak.
Jirginsu yayi sauƙar angulu a cikin babban Airport dinsu.
Rabat Sale international airport.
Wanda dai-dai lokacin kuma ya dire ayar ƙarshe ta Suratul Kahf ɗin tuni kuma jirginsu ya dai-dai-ta da'irar tsayuwarsa.
Da sauri Jabeer ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar kallonshi gefen damanshi ganin har an buɗe ƙofar jirgin.
Juyowar da zaiyi kuwa sai ganin Middibo yayi a tsaye yana jawo jakarsa daga drower dake samansu.
Da sauri ya miƙe shima, sai kuma yaji ana kiransa a baya, da sauri ya nufi bayan.
Shi kuwa Modibbo agogon dake hannunsa ya kalla, da ɗan hanzarin sa ya nufi wajen sabida ƙaratowar lokacin sallan magrib.

A hankali ya fesar da sassayan numfashi, dai-dai lokacin da ya taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin Rarat, duk da dai duk Arfica ne amman ƙasar Marocco sunyi mana rata zarrama mai girma, sunada ci gaba na musamman.
A hankali ya furta.
“Yah Salam”.
Sabida wani irin ni'imtaccen iskane mai cike da salama ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake.
Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe ajiyar zuciya ya shaka, like ɗan da ya daɗe baiga mahaifiyarsa ba, kuma yayi kuka.
A hankali yaci gaba da taka steps din yana sauƙo ƙasa.

Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙafarsa kan ƙasar Marocco cikin yankin Rarat.
Wani irin tsuma yaji naman jikinsa nayi tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin tsuma.
Wanda ya ta'allaƙa hakan da tsananin yanayin sanyin garin ne.
“Alhamdulillah!!!”.
Ya furta a saman lips inshi sabida, tunda Allah ya halicce shi bai taɓajiba irin yanayin da yakeji a yanzu, ko Saudia yaje bayajin yanayin nan.

Yana mai shaƙar sassayan iskan garin ya fara bin ayarin sauran matafiya.
Yayinda can gefen kuma manyan motocine na al'farma wanda bisa dukkan alamun wani babba akazo ɗauka.

Su kuwa a cikin yanayin gajiya suka ƙaraso inda masu tarɓarsu suke.

Ɗan dube-dube ya yayi.
Da sauri ya nufi wani Balarabe dake jingina da Taxi yana riƙe da ɗan allon tarba wanda aka rubuta Aliyu Youssef Muhammad Mouley.
Yana isa yayi masa sallama.
Cike da tsananin girmamawa Balaraben yayi saurin buɗe masa marfin motar tare da cewa.
“Marhababuka”.
Kai ya jinjina masa cike da gajiya da ƙosawa.
Yasan Taxi Abba ne ya turosa.

Da sauri shima ya shiga Taxi ɗin kana yaja suka fita daga cikin Airport ɗin.
A hankali yayi miƙa tare da jingina bayansa da seat ɗin dai-dai lokacin da suka ratso ta cikin unguwar Ben slimane.
Anƙuwace ta masu alfarma, haka yasa tsarinta na musamman ne.
haka nan yaji yanayin Weather yayi masa masifar daɗi da kyau.

Gashi yanayin damuna ne Iska mai sanyi da ratsa jiki na kaɗawa gashi duk ta inda ka wulga ido bishi yoyin dabinone masu kyan tsari ke rausayawa sunyi kore shar dasu iska na kaɗawa suna rangaji ga kasar garin ajiƙe yake alamun anyi ruwa.

Ƙarfe shida da minti sha biyar dai-dai mai Taxi ɗin ya juya hancin motarsa kan wani gini mai kyau da ɗaukan indo wanda a samansa aka rubuta.
Belere Hotel Rabat.
Kai da ganin masifar kyau da tsaruwan hotel ɗin kasan zaiyi masifar tsada.
Cikin taushin murya ya kalli Balaraben dake riƙon.
Tare dayin mgn da larabcin.
“Muje wani wanda bai kaishi ba”.
Cikin sanin darajar aiki mai Taxi ɗin ya ɗan kalleshi ta madubi tare da cewa.
“Toh".
Daga nan ya juya akalar motar ya ɗauki hanyar da zata sadashi da unguwar Sidi bettache.
Tafiya kaɗan sukayi suka fito kan babban titinsu.
Da sauri Modibbo yace.
“Masha Allah”.
Dai-dai lokacin da
Idanunsa suka sauƙa akan tamfatsetsen masha'hurin hotel mai masifar kyau da tsari daga can sama tsololuwan ginin an rubuta.
Welcome to Sofitel Youssef Mouley hotel.
Da sauri yace.
“Tsaya mu shiga nan”.
Yayi mgnar still idanunsa na kan sunan hotel ɗin da yayi kama da sunanshi hakan don sunan hotel ɗin yaji yana son sauƙa a nan.
Murmushin mai Taxi ɗin yayi tare da cewa.
“Toh ai wannan yafi wancan tsadama”.
Da sauri ya gyaɗa mishi kai tare da cewa.
“Eh shi yayi”.
Ya ƙare mgnar da lumshe idanunsa jin sautin kiransan salla a masallacin dake cikin hotel ɗin.
Haka yasa shima mai Taxi ɗin saurin shiga.

Numfashi mai sanyi ya fesar tare da buɗe Idanunsa daya lumshe kana ahankali.
Chapter 27 · 0% Book details