← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 112

Sashe 99

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro ido Sarfraz yayi "wai yaya kana nufin asibitin da pharmacy ɗin da Almas ɗin duka nakane?"

"No more questions, eh duka nake nufi"

Jinjina kai kawai SARFRAZ yake yi yana jinshi kamar a saman iska, lallai shi ɗan gata ne, ace wanshi ne keda duka wannan abubuwan, ai wallahi sai yayi dinner na murnar be mutu ba, yanzu daya mutu shikenan.

Suna shiga gida sukayi kicibis da colonel zaune a Babban falour tare da mummyn Sarfraz da mummyn Aayaan da Ummin Nawaz dasu baffa harda Daddy shima.
Da sauri colonel ya miƙe "Allah Nagode maka, Allah nayi maka alƙawarin gobe zan yanka raƙuma guda goma nayi sadaka da naman"

A saman kujera Aayaan ya kwantar da Nawaz Sannan ya ƙarasa gaban Colonel suka rungume juna, fashewa da kuka colonel yayi "my son da ace ka mutu bansan ya zanyi ba, ina sane fa naki zuwa gidan nan jana'iza, saboda bazan iya jure ina kallo a saka a cikin kabari a binneka ba, yanzu haka su Naufal da Fudail ne suka koma suka cemin wai ance ka tashi baka mutuba, amma dai basu ganka ba, shiyasa fa na iya zuwa."

"I'm sorry daddy, haka Allah ya tsara sai muyi tayi mishi godiya tunda da sauran numfashi "

"Kowa mamakin irin shakuwar colonel da Aayaan yakeyi, amma Mummy batayiba saboda tasan Yadda colonel ɗin suke da daddyn Aayaan kafin ya rasu..

Zaune kawai Colonel yake amma hankalinshi na kan mummy, ya rasa meyasa har yanzu ta ƙi amsar shi a matsayin mijin aure, yayi mata hannunka me sanda har ya gaji ya fito fili ya faɗa mata amma tace ita bazata iya aurenshi ba tana Matsayin ƙawar matarshi ba.

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*83*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Tsaff mummy na ankare da kallon da colonel yakeyi mata, tasan jimawa da sukayi basu haɗu bane shiyasa daya ganta yanzu ya kasa kauda kanshi a kanta.

"Ai ko mutuwa zakayi saidai kayi, babu yadda za'ayi in aureka bayan Ni ƙawar matar kace, aima cin amana kenan!" Cewar mummy cikin zuciyarta tare da jin takura da kallon da colonel ɗin keyi mata

Duƙawa Aayaan yayi ya ɗauki Nawaz da ledar kayan ciye-ciyen ta, "Son ai daka barta anan ɗin tunda barci takeyi"

Sarai Aayaan yasan ba barci takeyi ba, yasan kunya ce tasa ta kasa buɗe idonta, "No Mummy bari kawai na kaita ɗaki saboda nan kinga akwai hayaniya da yawa"

"Okay to cikin yana nan kuwa?" Cewar mummy tana kallon move ɗin Aayaan ɗin, yadda taga ya kaɗa kai ya juya a raunane yasa ta gane cewa babu cikin tunda tafi kowa sanin halin ɗan nata.
Zuciyarta kamar zata fashe, taso ace an haifi cikin, to Amma tunda Allah yasa shi Aayaan ɗin be mutu ba ai hakan ma ya wadatar, tasan cikin ɗan ƙanƙanin lokaci za'a kuma samun wani cikin duba da yadda suke kwakwumewa juna.

*Aayaan....*
Yana shiga ɗakin ya ɗora ta a saman gado "Sweetheart tashi kici Abincin" zaune Nawaz ta tashi tana murmushi

"Yaya wai meyasa kowa sonka yakeyi? Farin jininka yayi yawa Gaskiya, amma kuma a hakan ne ka zauna har zuwa yanzu bakayi Aure ba?"

Rungumeta a cikin ƙirjinshi yayi Sannan yace "eh mana! Dole naƙi yin Aure tunda ina jiran my Sweetheart"

Daɗi sosai taji maganar tayi Mata, ita ba mace bace mai son a riƙa yaba mata ba, amma kuma duk sanda Aayaan zai yabeta saita ji ta kamar ta tashi sama tayi shawagi tsabar murna.

"My soulmate I so much love you, wallahi har yanzu zuciya bata dawo dai dai ba, na rigada na shiga damuwar da ban taɓa shigan taba."

"Nafiki sonki, shiyasa Allah yasa na dawo, amma kuma mun rasa little Aayaan"

"Hmmm Allah ne kawai ya dubeni da idon rahama yasa baka mutu ba, amma da Yanzu nabi titi"

"Dear ki dena wannan maganar, in'sha Allah muna tare har abada, yanzu dai ƙoƙarta ki samu kici Abincin kada yunwa ta illata min ke"

Murmushi Nawaz tayi tare da miƙewa tana yin hanyar bayi don ta wanke baki, bata Ankara ba tajita a sama cikin iska "dear ina kusa amma sai kiyi ta wahalar da kanki" Aayaan yace yana direta a gaban sink, toothpaste yasa mata a brush sannan yace "open Your mouth" A hankali Nawaz ta buɗe bakin saboda taso ne ace ya barta tayi da kanta.

Sosai jerarrun fararen haƙoranta suka birgeshi, tsaff dasu gwanin sha'awa, sosai siriyar hushiryar dake tsakanin haƙoran ta ƙara ƙawata su.

Tsaff ya wanke mata bakin ya ɗauraye, kuma daukota yayi ya dire a tsakiyar gado Sannan ya buɗe mata madarar ya miƙa mata "fara shan wannan saboda hanjinki ya warware, amsa tayi tasa a bakinta, saida tasha kusan rabi Sannan ta fara cin naman kazar..

Bata wani ci da yawa ba tace ya isheta, "to yanzu babu ke babu yin Barci sai anjima tunda kinga bakici abinci da wuri ba, bazai yiwu ki kwanta ba saiya faɗa Miki"

"Wallahi yaya barci nakeji sosai " cewar Nawaz tana kwanciya a saman cinyarshi

"Oya tashi ki zauna! Ko kinaso kiyi ƙaton ciki ne? Ɗagota yayi ya zaunar da ita.

Laptop 💻 ɗinshi dake gefen side drawer ya janyo, buɗe ta yayi ya kunna yana ɗan danne danne, be lura ba ashe har Nawaz tayi barci a zaune,

Murmushi yayi ya gyara mata kwanciya, shafar fuskarta yayi yace "sleeping beauty kawai!!"
Tsayawa yayi da danne-dannen system ɗin, tunawa yayi da CCTV carema a cikin babban falour, sosai yaji yanaso yaga abinda ya faru sanda akace ya mutu.

Be jira komai ba ya janyo wayar ya jona sannan ya kunna media ɗin, duba date ya farayi yana wucewa har Saida ya iso date ɗin yau sannan ya tsayar,
Bega kowa ba illah tsirarun mutane da suketa shiga suna fita, forwarding yayi Sannan ya tsayar da sauri ganin an shigo da akwatin gawa, hankalin kowa a tashe, wasu ma kuka sukeyi bilhaƙƙi.
Sosai ya maida hankali yana kallon cikin laptop ɗin, shine kwance cikin akwatin baya ko motsi, tasbihi ya riƙa yiwa Allah tunda ya fara kallon har zuwa inda aka fara yi mishi wankan gawa, wani irin tsoron Allah ne yaji yana ƙara shigar mishi zuciya "lallai mutuwa wa'azi ce babba.
Sanda aka fara sa mishi likkafani Saida yayi kuka "lallai mutum ba a bakin komai yakeba, shine kwance sai yadda aka juyashi?" Tsoron Allah ne wanda be taɓa jin irinshiba ya dirar mishi a cikin zuciyar shi...

Yana kallon kowa ta cikin laptop ɗin, addu'a suke tayi mishi , masu kuka ma suna tayi,

Tunani ya fara akan ina Nawaz, saboda tunda ya fara kallo be ganta ba ko sau ɗaya ba, kafin ya fara ba kanshi amsa sai ganinta yayi ta fito tana layi. Tana tsaye sai kuma ta koma, fitowar da zata kumayi shine ta fito riƙe da bindiga tana nuna musu, tundaga fasa TV da tayi har zuwa sanda ta kori kowa ta dawo tana jijjigashi zuwa chanza mishi kaya, maganganun da takeyi da kukan datakeyi duk babu abinda be gani ba, "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un?" Mutun ba'a bakin komai yakeba...

Fuskarshi yakai saitin fuskar Nawaz ya zuba mata Ido, "yaushe Nawaz ta fara sonshi haka? Shikam me zeyi yaji daɗi a cikin ranshi? Farin cikin da yake ciki ya kasa barin zuciyarshi ta huta, lallai Allah maji rikon bawa ne, tunda yake be taɓa kawo cewa Nawaz zata iya yin quarter ɗin Abinda tayi ba, lallai dole ayi mata alluran barci, ɗagota yayi ya haɗa da ƙirjinshi ya matseta wai ko zai samu relief, amma inaa wani irin maganaɗisun ƙaunarta ne da sonta ke ƙara shatata a cikin zuciya, ruhi da gangar jikinsa, jiyakeyi kamar numfashinshi zai ɗauke.

A Yanzu kam Aayaan gani yakeyi shima idan babu Nawaz bazai iya Zaman duniya ba, a yadda yakeji a ranshi ma gani yakeyi numfashin ma da yake shaƙa Nawaz ce ta nemar mishi alfarma, yasan mata da mugun tsoron gawa amma ita sam bataji tsoron Shiba, saima dakumarshi data riƙa yi tana rungumar shi.
"Shikam me zaiyi wa Nawaz ya biyata, ya tabbata da badon Allah yaba Nawaz ikon yin hakan ba da tuni yana cikin Rami ya fara kumbura.

Kwantar da ita yayi cikeda kulawa kamar kwai, sannan ya tashi ya shiga bathroom ya ɗauro Alwala, nafila ya riƙa jerowa yana yiwa Allah godiya da kirari Sannan yana ƙara yiwa Nawaz addu'oin gamawa da iyaye da duniya lafiya, a yadda yakeji da shine me mukullin Aljannah da kyauta zai bata kawai yace ta shiga ta huta.

Sai tsakiyar dare Sannan ya dena yin sallar ya nufi gado ya kwanta, janyota yayi saman ƙirjinshi yanajin zuciyar shi kamar zata faso ta fito waje, lallai Nawaz ɗaya ce Tamkar da dubu, wato sosai ta iya harbi amma sai tayi tamai alayen cewa bata iyaba.

Koda asbah tayi shi ya fara tashi, rasa Yadda zai tashi Nawaz ɗin yayi domin a yadda yakeji yanzu game da ita bazai iya ɓata mata raiba, abinci ma da ana taunawa mutum to da tauna mata zaiyi ya haɗiye sai dai ya shiga cikinta direct (```Nikam Matar Rasheed nace dama ya lafiyar kura balle yanzu```)

Haɗe bakinsu yayi guri ɗaya yana bata French kiss, mutsu mutsu ta fara tare da buɗe idonta ahankali, tsaff ta sauke su a kan fuskar Aayaan da yake yi mata wani irin ƙayataccen murmushi wanda ke ɗauke da faassarori daban daban, "sweetheart I'm sorry! Natasheki Koh?"
Murmushi itama Nawaz ɗin tayi ba tare data ce komai ba.

"Lokacin Sallah ne yayi shine nace bari na tasheki"

"Ka manta bana Sallah"
Kamar saukar Aradu haka yaji maganar Nawaz

"Don Allah kiyi hakuri wallahi na manta ne" duk sai yayi fuskar tausayi

Tashi zaune Nawaz tayi tana dariya mara sauti "my reality ji yadda ka tada hankalinka kawai don ka tashe ni daga barci! Ni daɗi naji sosai sanda nayi ido huɗu da kyakkyawar fuskarka, wallahi yaya baka san irin kaunarka da Allah ya dasa a cikin ruhina bane, ina kaunar ka kamar na mutu"

Tausayi sosai taba Aayaan domin yagani da idonshi, yasan ƙaunar da take yi mishi pure ce babu algus a cikin ta
Chapter 99 · 0% Book details