Sashe 22
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawayene ya ziraro daga idonta, bata samma ya zubo ba saboda gaba daya ruhin ta baya tare da ita, tunaninta yafi tafiya kan mummy SARFRAZ saboda shi kadai gare ta sannan bata bari yayi nesa da ita amma gashi sanadinta hakan ta faru, kuma tasan takira wayoyinsu har ta gaji...
Abu taji ana goga mata a fuska, firgigit ta dawo hayyacinta, Aayaan ta gani durkushe a gabanta rike ta very neat hankie yasa a fuskarta yana tsane mata hawaye.
Gira ɗaya ya ɗaga mata "why are you crying? Keda tun ɗazu ake jira ki tashi shine kuma zaki tashi da kuka?
Wani hawayen ne ya ƙara zubowa daga idonta "bansan wane hali SARFRAZ yake ciki ba.......
Ita kanta bata san sanda maganar ta fito daga bakintaba kawai dai taji ta gama faɗa ne.
murmushi yayi mata me kyau "look insha Allah Babu abinda zai sameshi kin ji? Saboda tun tuni aka Turo Ambulance ta kwashe waɗanda suka ji ciwo aka kaisu asibiti don abasu taimakon gaggawa, waɗanda suka rasu kuma ankaisu mutuary kafin ƴan uwansu suzo su daukesu.
And please ki kwantar da hankalinki everything will be right insha Allah, Yanzu me zakici? And kuma nasan jiya daƙyar idan kinyi sallolinki koh?
Mamakine ya kamata "au dama sojoji suna sallah, lallai Allah al Hakeem ne, ai ita tasha faɗa da harbe harbe be barinsu su tuna da sallah, to kuwa indai hakane sun isa a Sara musu.. Nawaz ke zancen zuci
Husky voice dinshi ta daɗa ji yace "sister bakice komai ba.
" To ameen Allah yasa yana raye, sannan ruwan alwala zaka fara bani inyi sallolin saboda tun sallar azahar ɗin jiya ban kuma yin Sallah ba.
"Okay bari nazo" fita waje yayi be daɗe ba ya dawo rike da bottle water Guda biyu.
Bata ruwan yayi sannan yace kiyi alwalarki a gefen nan kawai basai kin fita ba, akwai maza da yawa a waje.
Idan kuma za kiyi easing kanki ne to sai in raka gurin da zaifi _safe_.
Da sauri tace "A'a banaji Nagode, be kuma cewa komai ba ya juya ya fita daga ɗakin....
Gefe ta samu tayi alwalar sannan kuma ta koma ta zauna tana tunanin dame zata rufe jikinta tayi sallah, dai dai nan Aayaan ya dawo,
Be kula taba ya wuce ya bude wata luggage 🧳 me jikin sojoji ya ciro wani farin plain din zanin gado, hannunshi yasa ya yaga shi biyu, ajiye ɗayan yayi a gefe sannan ya miƙa mata dayan,
"Ki rufe jikinki da wannan sai kiyi sallar,
Amsa tayi "Nagode"
Fita ya kuma yi, tashi tayi ta fara jero sallolin da ake Binta haɗe da yin addu'ar samun sauki da rangwame agurin Ubangiji Allah,
Ta kusa idarwa Aayaan ya shigo riƙe da bowl guda biyu,
A gefenta ya ajiye shima ya zauna,
Bayan ta idar ta kalleshi a sanyaye tace "ina kwana"
Murmushi yayi "lafiya lau, ya fargaba? Allah ya tsare gaba kuma yasa dan uwanki yana raye...
"Ameen, Nagode Allah ya saka da Alkhairi, kulawar da taimakon da kamini.
Murmushi ya kuma yi "kada ki damu Saida na rantse akan zan taimaki kasata kafin nan na zama cikakken soja, kuma aimu dama bayin kune masu kula daku....
Zaro ido Nawaz tayi "wai!!! nifa Wallahi bance hakaba.
Murmushi yayi bece komaiba, bowl ɗin ya tura mata gabanta "idan kika gama ci colonel yana kira" sannan ya tashi ya fita.
Cikin bowls ɗin tabi da kallo, bowl ɗin farko farfesun naman kaji ne sai na biyu wani abu kamar koko kamar Golden morn gashi nan dai, cokalin dake ciki ta dauka takai bakinta.
Jin ɗanɗanon tayi kamar ansawa kunun alkama madara, kaɗan tasha ta matsar dashi gefe, shima farfesun bata wani sha da yawa ba.
Zanin da tayi sallah ta dauka ta rufe kanta dashi sannan ta miƙe tayi hanyar fita, a hankali ta buɗe labulen ta fita..
Sojoji ta gani bila adad wannan yayi chan wannan yayi nan, wasu kuma na gefe suna duba bindigogi wasu kuma suna wajen motoci irin na yaƙi
Aɗan gaba ta hango wasu a gaban manyan tukwane, " oh wai dama mazane suka dafa abincin, hu'umm sojoji na ƙoƙari...
Duk ta hargitse ta rasa inane tent ɗin colonel ɗin, ɗan gaba tayi kaɗan sannan ta fara waige waige, kallonta sojojin suka farayi suna mamaki "wannan daga ina kuma! Kayan sojojin is familiar to them kuma gata karama, su sam basu taɓa ganin taba ma..
Wani ne ya nuno ta da bindiga "hey you, from where?
Fitsari ne taji yana kokarin zubowa , jikinta sai rawa yakeyi.
Batasan sanda ta ɗaga hannuwanta sama ba ta rufe ido, itafa yanzu gaba ɗaya jinta take kamar ba ita ba Duniyar ma ta isheta.
Muryar Aayaan taji yana cewa "kai mara hankalin inane? Macen kake nunawa bindiga? Me aka fara faɗa mana kafin mu fara aiki?
Natsuwa kowa yayi, hakan ya nuna yanada wani babban matsayi, shikuma da sauri yace "I'm sorry sir, wallahi wasa nakeyi mata, naga ta fito ne tana raba ido kamar tanajin tsoro
"Okay shine kake so ka daɗa razanata koh? To da ta faɗi fa?
Kuma kar kaga kamar nabar maganar i will get back to you.
Gurin Nawaz ya ƙarasa wadda har yanzu idon ta na rufe,
"Open your eyes" ya fada cikin soft and husky voice dinshi.. ke kin cika tsoro Wallahi....
A hankali Nawaz ta buɗe idon ta amma har yanzu jikinta rawa yake kamar ace kyak ta ruga da gudu...
Gaba ya shiga tabi bayan shi da sauri har ɗakin colonel ɗin...
Bayan sun zauna ne colonel ɗin ya kalleta cikin kulawa yace "my daughter how was ur night?
"It was...... Kasa ƙarasawa tayi sai kuma ta kalli Aayaan.
Murmushi colonel yayi "yea u are right Aayaan ya kamata na tambaya ya kika kwana ba ke ba.
Smirking kawai Aayaan yayi amma bai ce komai ba,
"Yauwa daughter kina ganin daga nan zuwa gurin da ƴan ta'addan suke zai Kai kilometer nawa?
"Ehm gaskiya da nisa kuma bazan iya tantance kilometers nawa bane, amma dai tun magrib na gudo sannan kuma gudu nayi ..
"Sir and kuma ni na ganta ne misalin 2:28am kaga ta kwashi kusan 7hours kenan tana tafiya.. cewar Aayaan
"Yea u are right, Amma banji daɗi da ba'a Turo mana da 🚁 helicopter dinba, naso ace zuwa yanzu mungama abinda zamuyi saboda kowa a shirye yake.
"Sir kada ka damu insha Allah ko wane jinkiri za'a yi mu zamuyi nasara. Cewar Aayaan yana kallon colonel ɗin
Ita dai Nawaz mamakin yanda Aayaan ya shaku da colonel takeyi, kuma duk tanajin abinda suke cewa cikin fahimta.
Colonel ɗin ne ya kalleta "daughter Dake zamuje kema kiga yadda za'a yi musu koh?
Zaro ido tayi waje kuma ta kasa furta koda kalma guda ɗaya.....
Dariyar ciki Aayaan yayi yana kallon ta, " sir ai wannan matsoraciya ce, yanzun nan ma na tarar Daniel ya nuna mata bindiga bakaga yadda jikinta ke rawa ba....
"Stupid wai ku meyasa bakusan darajar mata bane, kuna mantawa ko yaƙi zamuje garin maƙiya ana faɗa mana cewa kada mu taɓa mata da yara...
Kuma ko ba haka ba an fada muku cewa ku zaku iya yin Abin da Mata keyi ne?
Duk ƙarfin nan da kuke takama dashi to itafa ta haifeku kuma da bata kula da kuba kun isa ma ku rayu balle har ku zama wani abin,
Amma ku yanzu kun maida mata abin tsokana koh?
" I'm sorry sir" Aayaan ya fada cikin girmamawa.
Ita kuwa Nawaz sakin baki tayi tana kallon colonel "wai wane irin muhimmanci sojoji sukeba mata ne, itafa abin mamaki yake bata, ashe shiyasa Aayaan yaketa hidima da ita....
Kallon Aayaan tayi, ɗaga mata gira yayi alamun ya akayi?
Ita dai idan ya ɗaga girar har mamaki yake bata amma yanzu ta ajiye cewa ɗabi'ar shice ya riga ya saba...
Kauda kanta tayi gefe...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Mummyn sarfraz ce zaune taci uban kuka har ta godewa Allah, domin tun a jiya labarin ƴan ta'addan ya isa gurinta tunda gaba daya anyaɗashi a labarai da internet...
Gashi kuma ta kira wayar SARFRAZ harta gaji, da idan ta kira tana shiga dauka ne kawai ba'a yi, amma yanzu idan ta kira sai dai taji ana cewa switch off...
Daddy ne ya kalleta "ɗan Allah Madam kiyi hakuri ki Dena kukan nan, Wallahi Nima zuciyata a karye take kawai dai ina boyewa ne saboda kada abin yayi Miki yawa.
Share majina tayi "haba maigida yanzu ace ga abinda ya faru kuma sai na zauna, yaron nan shi kadai fa Allah ya bamu yanzu ace ya mutu shikenan mu bamuda Magaji kenan kuma bamuda meyi mana addu'a, da acema yayi aure ne to nasan matar ta haihu koma bata haihuba kila tanada ciki.
Amma yanzu babu ko ɗaya, ƙara fashewa tayi ta wani irin kuka mai cin rai, wayyooo Allah na, na shiga uku Allah ka duba halin da nake ciki kada ka rabamu da SARFRAZ,
Shidai dady sai ya zama ɗan kallo don ya rasa ma yanda zai yi mata, gashi shima zuciyarshi sai ƙuna takeyi mishi daurewa kawai yakeyi...
Ganin mummy yayi ta mike zumbur "wallahi can zani Gara naje na duba idan yana raye inma baya raye Gara ko gawar shi na gani, nasan idan na zauna bakin ciki ne zai kasheni.
Shima mikewa yayi yabi bayanta cikin sauri..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Ummin Nawaz ce zaune ta tafka uban tagumi, ƙuna kawai takeji a zuciyar ta, sam ta rasa me keyi mata daɗi a duniya,
Baffa ne yace "duk abinda ya faru Ni naja tunda Ni na matsa akan sai tazo garin nan, nadan da bance ba da babu abinda zai faru amma yanzu sai Allah saboda kuna gama waya da ita aka fara sanarwar yan ta'addan sun kwashe mutane
"A'a baba ba laifinka bane haka Allah ya riga ya tsara, koda baka ce tazoba sai hakan ta faru.
Amma ce tace "Ni wallahi jiran tsammanin nan ya isheni Saboda duk minti ɗaya zuciyata ƙara tsinkewa takeyi, wallahi dama mun bishi can mutuary ɗin...
Jugum jugum sukayi kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarshi.....
Yau dai bamu leka gurin SARFRAZ ba.....
_*MATAR RASHEED*_*🎀🎀SARFRAZ*🎀🎀
*Episode 26*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*