Sashe 97
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiri ne ya kama Nawaz kafin su ƙaraso kusa da ita, baya tayi zata faɗa, amma tana ƙoƙarin tsaida kanta daga faduwar, sai ya zamana kamar tana layi, Aayaann dake jingine da kujera ne ya gane faduwa zatayi amma take ƙoƙarin hana kanta, cikin Rashin kwarin jiki ya tashi da sassarfa ya nufi inda take.
Dai dai nan itama Aseey ta lura da abinda zai faru, dagudu ta ƙarasa dai-dai zuwan Aayaan gurin, dai dai lokacin kuma Nawaz ta yanke jiki ta fadi amma kafin takai kasa Aayaan ya tareta da ƙirjinshi.
Kowa tsaye yayi yana kallon Aayaan ɗin cike da mamaki, mutumin dake shirye cikin likkafani amma yanzu gashi tsaye har yana iya taimakon wani mai rai.
Aseey kam da sauri ta rungumeshi haɗe da Nawaz ɗin, itama Mummy kansu tayi tana kabbara, baffan Aayaan ne yace "ku lura fa! Kunsan ba kwari ne da Ayatullah ɗin ba, balle ita kuma Nawwarah ɗin.
Sakin shi sukayi badon suna soba domin gani suke zai bace, suna sakinshi shima yayi baya zai faɗi, kawu da baffa ne suka rike shi gam, harda taimakon Aseey.
Kwantar dashi akayi a saman carpet sannan aka cire Nawaz da itama ke sume a ƙirjinshi.
"Innalillahi wa'inna alaihi raji'un!!! Mummy tace tana tafa hannu ganin jini yana bin ƙafar Nawaz yana sauka a ƙasa, hankalin kowa saida ya tashi ganin jinin jajir dashi, Ummin Nawaz ɗin tafi kowa shiga tashin hankali saboda yadda tasan tasha wuya sosai akan zubar jini, tayi ɓarin ciki da zubar jini yafi sau biyar..
Ruwa Aseey ta miƙo aka yayyafa musu amma shiru babu wanda ya tashi, sai dai duka suna numfashi, waje Sarfraz yayi cikin ƴan kai gawa yana cewa don Allah waye Doctor a cikinku?
Kusan mutum biyar ne suka ɗaga hannu "kuzo muje, don Allah ana buƙatar taimakonku aciki"
Bin bayanshi sukayi ahankali suna tunanin kodai Aayaan ɗin be mutu bane da gaske kamar yadda sukaji wasu na faɗa?, hankalinsu ya tashi matuƙa ganin yadda su biyun suka galabaita sosai, da sauri wani daga cikinsu ya rubuta magunguna a takarda ya miƙawa Sarfraz yace "kayi sauri ka Kawo waɗannan magungunan saboda da alamun guba a Tare dasu duka"
Jikin SARFRAZ har rawa yake tsabar tashin hankali, tsoro yakeyi kada suga samu kuma suga rashi, be ɗauki mota ba Kawai ya samu wani zaune akan mashin yace mishi "taimaka ka kaini asibiti"
"Wai da gaske be mutu ba!" Mutane keta tambayar Sarfraz
"Eh be mutu ba ya tashi" Cewar Sarfraz dai dai sanda mutumin yaja mashin ɗin da gudu zuwa hanyar babban titi.
Mamaki ne ya kama kowa jin wai Aayaan be mutu ba, wasu har cewa sukeyi ƙaryane, kuma wai baza su tafi ba suna nan sai sunga yadda za'a ƙare.
A cikin gidan kuwa an samu an kai su Nawaz da Aayaan cikin ɗaki kan gado, duba Aayaan ɗin sukayi sosai inda suka tabbatar da guba ce ta sarƙafe huhunshi kuma duka jikinshi ya amshi gubar shiyasa har numfashinshi ya ɗauke na wasu awanni donma Allah ne yasa jininshi ya yaƙi gubar amma da bazai tashi ba.
Kan Nawaz suka koma suna duba me yasata zubar jini haka, cikin idonta suka bude, sai tafin hannnunta da jijiyar wuyanta.
Amma mama itama fa alamun poisoning ne tare da ita, me taci ne?
"Ai Kusan kwana uku bata ci abinci ba saboda koda yaushe allurar Barci akeyi mata, amma ana sa mata drip sosai. Cewar mummy cike da tashin hankali.
Ɗaya Daga cikin likitocin ne yace "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, allurar barci akeyi mata ko da yaushe? Kasheta kukaso kuyi kenan? Ga kuma Alamun ciki nan tattare da ita, yanzu haka idan ba ayi wasa ba cikin ya lalace shiyasa ta fara zubar jini.
Wata damuwar ce ta kuma kama kowa dake ɗakin, dai dai lokacin SARFRAZ ya shigo riƙe da ƙatuwar leda a hannun shi ta magungunan da akace ya siyo.
Basuyi wata wata ba suka ciri allurar kashe guba sukayi wa Aayaan har guda Uku Sannan akayi wa Nawaz guda ɗaya, saboda sunce allurar barci da aka yi tayi mata ce ta zama makwafin guba a cikin jinin ta.
Sunyi kokari sosai wajen ganin jinin ya dena zuba, amma abun yaci tura, sai kawai suka ce ayita addu'a.
Drip suka ƙara daura musu tare dayi musu wasu alluran a cikin Ruwan, kowa dai zaune yake yana addu'ar Allah yasa duka su tashi, kada kuma Azo ana murna yanzu kuma suyi mutuwar kasko.
*Bayan awa biyu.....*
Har zuwa Lokacin basu tashi ba, sai dai numfashinsu ya dai dai ta, fita sallah mazan sukayi inda matan kuma suka yi alwala a cikin gida, kowa ka kalla sai dai kaga yana mui-mui da baki Alamun addu'a, Aseey kam tana zaune a gefe ta zuba musu idanu tana jan carbi, sosai take jin wata irin ƙaunar Nawaz tana ratsawa ta cikin jinin jikinta tana shiga cikin zuciyar ta, "tabbas Nawaz Alkhairi ce a cikin rayuwarsu kamar yadda mummy take cewa, yanzu daba don itaba da tuni Aayaan ya zama labari"
Ganin Aayaan tayi ya buɗe ido yana yunƙurin tashi, da sauri ta ƙarasa kusa dashi tare da taimaka mishi yana jingina da jikin fuskar king size royal bed ɗin, "ina sweetheart?" Abinda Aayaann yacewa Aseey kenan
Nuna gefenshi tayi da ɗan yatsanta manuniya tace "gata tana barci"
Zuba mata ido yayi yana kallonta cike da ƙauna, ga wani uban tausayinta dake ratsa mishi ruhi, dai dai lokacin su baffa dasu kawu dasu daddyn sarfraz, da Sarfraz ɗin kanshi suka dawo daga masallaci,. "kowa saida yayiwa ubangiji hamdala ganin Aayaan zaune har yana magana, sukam dai sunga Ayar Allah, baffa ma be iya yin shiru ba Saida yace "Ayatullah lallai kaci sunan naka *Ayar Allah* tunda gashi ka ajiye mana Aya mun gani da idonmu"
Duk da halin da suke ciki saida kowa ya dara harda shi uwar gayyar *Aayaan*,
Tea me ɗumi Aseey ta haɗo mishi ta zauna tana bashi a hankali, shan tea ɗin yakeyi amma hankalinshi yana kan Nawaz, kusan minti Talatin da tashin shi amma ita bata tashi ba.
Sosai jikin Aayaann yayi kyau don har bayi ya shiga yayi wanka ya canza kaya harda fesa turare, gefen Nawaz ɗin yazo ya zauna, bayan ya duba mata nata drip ɗin, dayake shi tun tuni ya cire nashi.
Darduma yasa Aseey ta shimfida mishi ya zauna ya fara jero sallolin da ake binshi a zaune, yana ƙara yiwa Allah godiya da yasa numfashin shi be ƙare ba.
Saida a ƙalla yayi Sallah ta yini guda Sannan ya tsaya ya huta, dai dai lokacin suma su baffa suka fita don yin sallar isha'i, mutane kamar mayu har lokacin akwai Wasu zaune a waje basu tafi ba, wadanda suke na jiki kuwa duk Sarfraz ya buɗe musu ɗakin baƙi suna ciki.
SARFRAZ ne ya gaji Aayaan ɗin a Yau, domin tuntuni yayi order ɗin abinci a restaurant dai dai yadda zai isa kowa.
Har zuwa wannan lokacin kowa mamakin wannan abin sukeyi, akwai ma masu tarar Sarfraz ɗin suna ce mishi wai anya da gaske kuwa ya tashi, kodai basaso a binne shi ne?
Murmushi kawai Sarfraz ɗin yakeji tare da cewa "Allah ya kaimu gobe, zaku gani da idon ku"
Saida Aayaan yayi sallar yini uku kamar yadda Aseey ta lissafa mishi Sannan ya fara jero ta yau.
"La'ilaha'illallahu Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam" Nawaz tace tana jujjuya kanta hagu da dama.
Sallame sallar Aayaan yayi ya haye saman gadon kamar walƙiya, har Gware suka kusa yi da Aseey, tallabo kanta Aayaan yayi ya riƙe a hannun shi.
Wata iriyar zabura tayi tare da cewa "wayyo mijina be mutuba, kada ku binne shi"
"Calm down! Calm down!! Gani basu binne niba, ina Tare dake....
A hankali Nawaz ke buɗe ido har ta gama buɗe shi tas a fuskar Aayaan "yaya baka mutu ba Koh"
Murmushi yayi mata tare da cewa"in'sha Allah ina tare dake" sunbatar ta yayi a goshi tare da cire mata allurar dake hannunta Sannan ya rungumeta a cikin faffaɗan ƙirjinshi.
Jinta takeyi very safe, wani sanyi da daɗi ke ratsa wa ko ina a jikinta.
Sam Nawaz ta shafe idonta da toka babu wata kunya, "sweetheart don Allah kada ka kuma zuwa yaƙi"
For the first time da ta taɓa kiranshi da wani suna daya danganci soyayyah kenan, farin ciki gurin Aayaan bazai misaltuba, koda kowa ya shigo ɗakin bata sakeshiba shima be sake taba sannan suma basu damu da hakan ba duba da irin haukar da Nawaz tayi musu, sanda akace Aayaan ɗin ya mutu.
"Aseey kuje ki taimaka wa Nawaz tayi wanka donta kuma samun kwarin jikinta kafin doctor su dawo" mummy tace tana kallon Aseey ɗin
"No mum! Fisbilillah Ina zaune saiki wani ce Aunty Aseey, Ni zan yi mata da kaina Gaskiya "
Be jira me mumy zatace ba ya miƙe rungume da Nawaz ɗin a ƙirjinshi ya shiga bayi, kunya ce ta kama kowa dake gurin, waisu wace irin makauniyar soyayyah sukewa junansu da basa jin kunyar kowane, aikam kafin su fito daga bayin kowa ya gudu ya bar musu ɗakin.
Tun sanda Aayaan ya fara cire mata kaya yaji zuciyarshi ta tsinke ganin pad cike da jini a jikin Nawaz, ita dakeda ciki meya haɗa ta da pad?
Ɓari tayi kenan? Tsoro ne ya kamashi sosai, ya ƙwallafa rai a cikin nan bazaiso ya zube a banza ba, yanaso yaga gudan jininshi wanda yake ɗauke da Babban Tarihi, a ranar daya fara sanin mace a ranar Allah ya assasashi.
Sauri sauri yayi mata wankan Sannan ya rufeta da Babban towel ya daukota zuwa kan gado, kayanta ya buɗe ya ciro doguwar riga yasa mata mara nauyi, so yake yaje asibiti yayi mata scanning donya tabbatar da abinda ke faruwa.
Allah yasa muji Alkhairi.....
*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*82*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Cikin sauri sauri ya gama shirya Nawaz ɗin, ɗaukarta yayi ya tawo falour "yaya ka saukeni kaga ba lafiya ce dakai ba" cewar Nawaz Saboda sosai take tausaya mishi idan ta tuna har likkafani ansa mishi.
"Komai zan iya yi akanki, kuma daga yau kada ki kuma yi min magana Idan na ɗaukeki Saboda Ni sam bana jin nauyin ki"
Gum Nawaz tayi da bakinta saboda yanzu sam bataso tayi mishi Abinda zaiji babu daɗi.