← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 112

Sashe 56

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya fara magana tana sauraron shi, tabbas Aayaann soyayyar Gaskiya yakeyi mata domin gejin da yakai ba kowane namiji bane zai kai wannan gejin kuma ya rabu dake salin alin ba, kuma duk abinda ya fada Gaskiya ne Domin ita kanta shaida ce, saboda sanda suka haɗu a daji koda wasa be taɓa yunƙurin taɓa mata jikiba, sai yanzu da suka chakudu da juna.
Hamdala taketayi a zuciyarta da Allah yasa har Yanzu tana nan a matsayin ta na budurwa, don a yanda zuciyarta ta karaya bata taɓa tunanin Aayaann zai rabu da itaba. Haƙiƙa taji daɗi da Allah yasa Aayaann nada hangen nesa, girmanshi taga ya Karu a idonta sosai, ga kuma wata Irin kunyarshi dataji ta rufeta.

Yanzu fa ko hijab tasa kenan a banza tunda babu inda be taɓa ba ajikinta, itakam yazatayi da wannan Abin kunyar?

"Inna batada da yara ne? Aayann yace yana komawa gefenta..
A hankali Nawaz tace yaranta uku, biyu mata ɗaya na miji, su matan sunyi Aure namijin ne Karami shi beyiba tukuna.

"To miji fa" Aayaann ya kuma jefo mata wata tambayar. "Tanada shi amma yana Niger tare da ɗan innan, saboda tacemin Tare sukaje ganin gida shine ta barsu acan ita ta dawo...

"Allah sarki! Allah ya dawo dasu suma lafiya" cewar Aayaan yana kai hannunshi saman side table, purse ɗin dake ajiye ya dauko Tare Da zage zip ɗin, ƴan dubu daya ya gani guda takwas sun zubo mishi, murmushi yayi Sannan yace yau Kuma ruwan kuɗi akeyi kenan.

Ita dai Nawaz bata kula shiba, ita jirama takeyi ya ɗauke kafarshi daga jikinta ta tashi ta gudu amma yaƙi.

"Purse 👛 ɗin waye Wannan?.
"Tawa ce" cewar Nawaz a hankali

"Ashe ke hajiya ce, to nawa za'a bani a ciki?.

"Nima fa Inna ce ta bani dubu goma da zata tafi, tace in dauki dubu biyar ko zan sayi Wani abun, dubu biyar ɗin kuma wai wata zatazo ta amsa....

Ɗan murmushi yayi " to in dauki dubu daya aciki?

Cewa tayi "ko duka ka ɗauka ma Babu komai"

Sosai Aayaann yakejin daɗin hirar da sukeyi, amma kiran sallar dayaji ne ya tayar mishi da hankali, kenan isha'i tayi gashi basuyi magrib ba, da sauri ya miƙe Tare Da cewa ina bayi muyi wanka!
Itama miƙewa tayi ta kwasa da gudu ta shige bayin Tare Dasa sakata, " wane irin muyi wanka, hmm ya Aayaan da gaske yake yi, nikam bazan iya wannan abin kunyar ba Wallahi.

Dariya yaketayi don ta bashi dariya sosai, kuma childish behavior ɗinta yana birgeshi, fita daga faloun yayi zuwa tsakar gida.
Sosai gidan ya burgeshi, ɗan daidai kuma daga ganinshi na Masu matsakaicin ƙarfi ne, ko ina tsaff a gyare, sam Babu kazanta a Cikin gidan.

Kofar dayaga alamun kitchen ne ya nufa ya shiga, buhun coal yagani a gefe ga kuma sauran kayayyakin amfani suma a shirye suke tsaff.
Ashanar daya gani a saman table ya dauka don so yake ya hura wuta ya dora Musu Ruwan wanka don garin Akwai sanyi, yasan koda shi Zai iya yi dana sanyi ita bazata iya yi ba.
Tukunya dake kan mangal ɗin ya kama da nufin ya sauke ta ƙasa sai yaji da zafi alamun akwai Abu a cikin ta, buɗewa yayi yaga Ruwan zafine cike alamun ya tafasa har ya gaji.

Tsakar gida ya fito ya ɗauki bokiti ya juye Ruwan Sannan ya dauka ya nufi falourn don kaiwa Nawaz, ganinta yayi ta shige bayin da sauri hannunta riƙe da Flask ɗin Ruwan zafi.

Murmushi yayi sannan ya fita zuwa bayin tsakar gida, shima bayin tsaff dashi sai kamshin IZAL yakeyi.

A gurguje ya watsa Ruwan Sannan ya kama gefen wandon shi inda ya bata ya wanke Sannan ya maida Kayan jikinshi tare da fita daga bayin.

Yana shiga faloun ya tarar itama Nawaz fitowarta kenan, sanye take da hijabi amma yadda yaga fuskarta jike da ruwa ga sajenta da gashin goshinta sun kwanta sunbi jikin fuskarta saboda ajike suke.

Murmushi yayi jin alwalarshi ta karye, "dama nasan za'a rina, dole fa na ɗauki mataki wallahi, don inba haka ba kwaɓa ta zatayi ruwa.
Da anashi yaso ya jasu jam'i ne amma yanzu ya sadakar yasan bazaima iyaba.
Cewa yayi ɗan bani dadduma, da sauri ta ɗauka a inda ake ajiyewa ta tawo kawomai, rintse ido yayi Ganin yadda jikanta yake zuyawa a cikin hijabin.

Yana amsar daddumar yayi waje da sauri, buta ya ɗauka ya tari ruwa Sannan ya shiga bayi, bayan ya fito ya daura alwala ya tada sallah.

Addu'oi sosai yayi wa Ubangiji na nuna mishi Nawaz da yayi Cikin sauƙi ba Tare da Wata dabara tashiba, a hankali ta mike ya nufi kofar faloun ya daga labule, dinɗin yaga ɗakin kasancewar Garin yayi duhu, "sweet heart pls kizo ki rakani anguwa!

Nawaz tana zaune cikin dakinta ta jiyo shi, a hankali ta tashi jiki Babu laka Sannan ta fito falourn ta nufi Hanyar kofar, tare suka fita daga gidan zuwa kofar gida.

Da sauri Aayaan ya zagaya ya buɗe Mata kofa, Saida ta shiga sannan ya mayar ya rufe tare da zagayawa shima yana shiga gefen driver.

Koda ya zauna ita ya kalla yace "inane Hanyar titi? Da hannu Nawaz ta nuna mishi don ita gaba ɗaya kunyarshi takeji kamar ta ruga a guje haka takeji.

Saida suka fita titi Sannan ya kuma ce mata "ina zan samu store ɗin magunguna"

"Kayi gaba muje idan anzo gurin zan nuna maka, "alright thanks" cewar Aayann yana ci gaba da tukin sa...

Sunyi tafiya sosai sannan yaji shirun ya isheshi, "sweet heart babu ko ƴar hirar soyayya? Namfa garin kune ya kamata ki riƙa nunamin gurare kina faɗa Min sunan su amma kinyi shiru.

"Yauwa ga pharmacy ɗin" Nawaz tace da sauri tana nuna gurin da yatsanta ta jikin glass don ta katse Maganar da yake yi..

Parking ɗin motar yayi sannan ya fita daga motar ya shiga pharmacy ɗin, ba'a fi minti Bakwai ba ya fito riƙe da wata ƙaramar roba a hannunshi.

Saida ya shiga motar ya zauna Sannan ya buɗe robar tare da zazzago wasu ƙananun kwayoyi guda biyar ya watsa a bakinshi, Ruwan dake ajiye a gefe ya dauka ya ɓalle murfin Sannan ya kafa kai, saida ya shanye ruwan tukuna ya cire robar a bakinshi ya jefata waje.

Ita dai Nawaz tana zaune tana kallonshi...

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Yauma Kamar kullum hassu ce zaune a bakin ɗakin SARFRAZ tayi tagumi Tare Da zubawa ɗakin idanu, sam bata gajiya da zuwa Asibitin, har likitoci sun gane ta, dasun ganta zasu Fara tsokanarta suna dariya.
Gani tayi Kamar SARFRAZ yana motsi, ai babu shiri ta mike ta karasa kusa da Glass ɗin tana kura ido don Ganin da gaske ne ko kuwa gizo ne, saboda ance sai nan da sati biyu ko uku zai tashi..

Ai kuwa da gaske motsi yakeyi, ko Bandi bata tsaya fadawa ba ta nufi cikin asibitin tana Cewa Wallahi motsi yakeyi kuzo ku gani, ganin yadda ta kwasa a guje shima sai bandi yabi bayan ta.
Kicibis yayi da likitan da yakeda shifting yau Tare Da Hassu tana cewa, Wallahi motsi yakeyi da harshen Hausa, don tama manta cewa da Bature take magana.

Sauri sauri gudu gudu suka Isa dakin, ai wani uban ihu da hassu ta zabga Saida likitan ya toshe kunne Tare ta Saurin kallon Inda SARFRAZ yake kwance.
Jinine yake fita ta hanci ta baki babu kakkautawa....

Likitan ne ya ƙarasa da sauri ........

*AYAAN YA SAMU DAMA AMMA BEYI ANFANI DA ITA BA, TO KO DAI RABON SARFRAZ CE DUK DA DAI GASHI CHAN RAI KWAKWAI MUTU KWAKWAI*

INA JIRAN SHARHI

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*52*

*NA HAFSAT ALIYU SHUA'IB CHIKAJI* ✍️

Likitan ne ya ƙarasa da sauri tare da tallabo sarfraz da hannunshi sannan ya ɗago kan gadon yadda kan SARFRAZ ɗin zaiyo sama, wayoyin dake jikin kan SARFRAZ duka ya cire Fuskarshi kunshe da murmushi.

Hassu Wadda tun tuni take rusa ihu sai Sannan ta Kalli bandi "bandi kalli fa, wallahi murmushi yakeyi, ace mutum yana aman jini amma yana dariya, gaskiya turawan Nan basuda imani....

Kusa da shi bandi ya ƙarasa tare da cemishi "likita meya faru, naga kana murmushi!" Cikin ɗan turancin daya fara iyawa a gurin masu yi musu lesson.

"Aikinne yayi kyau sosai, kaga wannan jinin daya amayar shine wanda ya maƙale mishi a cikin kwakwalwa kuma da wanda ya zuba a ƙirjin shi dalilin harbin da akayi mishi, yanzu haka muna saran a kowane irin lokaci zai iya farkawa" bayanin da likitan yayi wa bandi kenan da turanci.

Hassu taɗan fuskanci me likitan yace, amma tana buƙatar ayi mata bayani sosai.
"Bandi naji kamar yana cewa aikin yayi kyau?"

"Eh haka yace kuma yace wai daga yanzu zai iya tashi ko Wane irin lokaci"
Dadine ya cika Hassu ta tafi da gudu ta rungume bandi "yaya bandi Allah yasa idan ya farfaɗo kada yace be sanmu ba! "Ameen" bandi yace tare da bubbuga kanta a hankali.

Duk da kasancewar yamma tayi sosai har garin ya Fara duhu amma asibitin fayau yake da haske Kamar Rana dalilin futilun da suka cika yalwataccen harabar asibitin da haske,

Tuni aka kira haidar yazo shima sai murmushi yakeyi Domin yasan idan Aayaan yaji wannan gagarumin labarin abotarsu zata ƙara ƙarfi Fiye da yanzu.

Ya kira wayar Aayaan yafi so hamsin amma taki shiga, "shiru yayi Sannan yace"bafa Wani tazarar lokaci garemu sosai ba, balle ince ko dare ya raba ne, nasan Yanzu bazai wuce ƙarfe tara da wani abuba, amma kila Akwai abinda yake yi ne wanda beson hayaniya.

Farouk ya kira ya sanar mishi Sannan yacewa su Hassu su Wuce su tafi gida, fir Hassu tace ita batasan zance ba, wai bazata tafi ya tashi Babu kowa a kusa dashiba.
Duk yin duniya haidar yayi amma Hassu ta shafawa idonta toka tace Anan zata kwana, Ganin haka da haidar yayi sai yace wa bandi ya zauna su kwana tare.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tada motar Aayaan yayi Tare Da kallon Nawaz yana murmushi "me zakici in siyo Miki?"

"Babu komai" Nawaz tace a hankali.
"Au nama manta, duba back seat ga tsarabar ki nan, maybe ki samu Wani abu da zaki iya ci, hope tsarabar batayi miki kaɗan ba?
Chapter 56 · 0% Book details