← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 112

Sashe 49

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jama'a wai kam Babu Wanda ya taɓa cigiyar umma, anya kuwa? Kodayake dama ai mutum mai baƙin hali bashida farin jini, amma dai yau Ni zan leƙa ko don naga ƙwaƙwaf!

Sauri sosai umma da fauziyya sukeyi a cikin dajin, wanda gaba da bayan shi babu alamun gida sai dai bishiyoyi da ciyayi kala-kala kuma ga magriba ta sanyo kai don garin har ya fara duhu.

"Fauziyya wai har Yanzu bamu iso bane? Nifa na fara gajiya! Cewar umma wadda gaba ɗaya ta tattare zaninta gefe guda saboda Uwar tafiyar da suka sha.

"Umma kiyi hakuri mun kusa saura kaɗan, muna wuce waccan bishiyar kanyar Zaki hango bukkarshi, fauziyya tace tana nuna saitin bishiyar da yatsanta.

" To Shikenan! Wallahi tafiyar ce ta isheni, tundazu fa muke tafiya amma munki kaiwa sai kace waɗan da zasuje ƙarshen duniya..

Kallon Umma fauziyya tayi sannan tace "to umma naga ai biyan buƙata yafi dogon buri!
"Nima ai don burina ya cika ne shiyasa na yarda nayi wannan Uwar tafiyar amma wallahi da Babu abinda ya isa yasa nayi ta.

Saida suka daɗa tafiyar kimamin minti goma tukuna suka isa bukkar,
ita kaɗai ce a cikin dajin, babu gida gaba babu a baya, amma dayake zuciyarsu ta bushe babu ko alamun tsoro suka duka suka shige cukin bukkar, zaune yake baƙikƙirin dashi Hakazalika idanunsa ma jajaye ne gwanin ban tsoro.

Gefe suka samu suka zauna tare da cewa "ran boka ya daɗe"

"Hahahahahahahaha haha "ya saki wata Uwar dariya Kamar kukan jaki "kada kuce zakuyi bayani! Na rigada nasan Abinda ke tafe daku.
kinasone ayiwa ƴar kishiyar ki asirin baƙin jini Yadda Babu wanda zai taɓa aurenta, sannan Abu na biyu shine, kinaso Yadda suka tafi suka barmiki gida ke kaɗai, to a rufe bakinsu kada su dawo Sannan a shashantar dasu game da gidan...

Zaro ido umma tayi "ya akayi ka sani?
Daɗa kyalkyalewa da dariya yayi Sannan yace "au an faɗa miki Ni na wasa ne? To bari kiji idan ma kinzo da wasa to Gara ki shirya kisan ba gurin wasa kika zoba.

Yanzu abinda za'ayi shine zaki kawo ƙasar da aka gina fadar Sarkin sin tun karni na takwas, sai kuma ruwan tekun ƙarshen duniya, da kuma gashin girar gawar fir'auna dake ajiye a gidan tarihi a ƙasar masar, muddin waɗan nan abubuwan suka haɗu to zakisha mamaki domin sai dai yarinyar ta mutu a haka, don babu wanda Zai taɓa jin sonta koda dai dai da girman kwayar zarra ne a zuciyarshi, kuma su da dawowa gidan nan har abada, ke ingaya miki ko kashe su kikeso ayi tsaff zan aika su lahira ba Tare Da Wani shamaki ba, mufa nan babu wasa a harkar mu sam.

Sosai farinciki ya kama umma jin bayanan da boka ya gama faɗa, amma damuwarta ɗaya a ina za'a samo Kayan daya lissafa, cewa tayi "boka Kada a kashe su, nafison su rayu Amma cikin ƙasƙanci da tozarci Yadda da kansu sai sunyi dasunsanin zuwansu duniya... To kuma matsalar duka abubuwan daka lissafa banida haryar dazan iya samosu!

Wani yare boka yayi tare da zazzare idanuwanshi masu kama da bushasshiyar gauta (ɗata) Sannan yace "a cikin rafanai an samu Wanda yace zaije yanzu ya dawo cikin minti biyar ya Kawo komai amma da sharadin za'a yanka mishi baƙin raƙumi...

Zaro Ido umma tayi, ga ƙoshi ga kwanan yunwa! "To Ni yanzu ina zan sami baƙin raƙumi?
"Kada ki damu, Akwai aljanin da zansa Wanda zaiyi shigar Mutane yaje chan Niger ya siyo, Yanzu kuɗin Kawai zaki bada..

Ɗan murmushin samun nasara Umma tayi "to boka nawane kuɗin?

Washe baki boka yayi Sannan yace ba wani yawa ne dasuba, dubu ɗari shida ma ya isa! Kuma ina Daɗa tabbatar Miki da cewa har dai akayi aikin nan to su da samun farin ciki kar harshen rayuwarsu....

Shiru Umma tayi Sannan tace "gaskiya kuɗin hannuna dubu ɗari da saba'in ne kuma Gashi inason aikin cikin gaggawa!

Washe baki boka yayi tare da cewa "kawo ɗari da saba'in ɗin, inyaso gobe saiku dawo kafin nan ma na gama haɗa maganin Kawai saiku tafi dashi idan kunzo....

Sosai Umma taji daɗi harda yi mishi godia Sannan suka tashi suka fita daga bukkar, ita dama fauziyya Yar kallo ce, Babu abinda ta furta illa dai sai taji Abin Kamar yayi yawa, Domin Nawaz bafa Ita ta zaɓar wa kanta Uba ba, kuma ai ummi ce kishiyar umma ba Nawaz ba, yaza ayi a hanata yin aure.

Ƙunɗinbala tayi tace "umma sai naga abin kamar yayi yawa! Naga Babu ruwan Nawaz, ba Gara koma meye ayiwa ummi ba Tunda ai Ita ta Aure Miki miji ...

Kama haɓa umma tayi "Lallai fauziyya! Yaushe kika koma Malama? Ni kike wa wa'azi? To lallai raini ya Fara shiga tsakaninmu, nanfa umma ta fara faɗa, inda take shiga batanan take fitaba...

Hakanan fauziyya Tayi gum da bakinta bata kuma cewa komaiba...

Ni kam matar Rasheed nace " mara rabo dai yashiga uku, boka ya zurma umma kuma ya amshe Mata kuɗin ta da imaninta. Kuma dai Nawaz naga amarya take a Yanzu, don haka umma kin makaro🤪🤪

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Sosai inna tayiwa Nawaz wayau domin dama tasan Nawaz ɗin bawai ta cika shiga Cikin kawaye da yawa bane, balle ace tasan magungunan mata ba.

Bokitin maganin ta ajiye a gaban Nawaz "yata ga magani na Kawo Miki, inaso ki Maida hankali Wajen shanshi domin maganin sammu ne, kuma Tunda kikacemin umma ta Turo ayi miki fyaɗe naji zuciyata ya kasa Zama guri ɗaya, Domin Duk Wanda Zai iya sawa ayi maka fyaɗe to Babu abinda bazai Iya yi maka ba, don haka ki dage sosai da shansa.
Har mazarkwaila ma nasa Miki aciki saboda kiji daɗin sha, kuma akwai na gari shi da nono akeshanshi, saboda shi na kambun baka ne da maita, gobe idan Allah ya kaimu zanje kasuwa sai insiyo mana nono galan ɗaya, Sai Musa a fridge duk sanda zamusha sai mu ɗiba.

Wani sabulu a cikin ƙaramin bokiti ta mikawa Nawaz ɗin "Kinga wannan shima na sammu ne, domin a cikin hadin harda ganyen magarya da ƙaiƙayi koma kan mashekiya aka zuba, zaiyi Miki magani kuma zai gyara Miki fata sosai.

Insha'Allah hardai kina gidan nan saikin gaji da magunguna, domin so nakeyi kome umma zatayi yazama tayi a banza, kuma Sannan inaso ki dage dayin azkhar sosai, kinji daughter?

Godiya sosai Nawaz tayi mata, Tare Da ƙara jin ƙaunarta a Cikin zuciyarta, tasan cewa babu wanda zai iya yi mata haka idan aka cire ummin ta.

Sam magungunan basu damu Nawaz ba, shan abinta take tayi domin dama ita bame gudun magani bace, don iya ranar ta kusa shanye wanda inna ta dafa, barin akwai zaƙi🤩...

Nidai cewa nayi "zaki yabawa Aya zaƙin ta"

Ita kuma ta ɓangaren inna daɗi taketaji kasancewar bata sha wahala ba, kuma inda abinma yazo mata da sauƙi bata daɗe Da dawowa daga Niger ba, duk ta tawo da magunguna kala kala,
Ashe zasuyi mata amfani....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Sosai zazzaɓi ya rufe Aayaan domin harta duvet ɗin daya rufa dashi Saida yayi zafi, gakuma wani uban sanyi da yakeji.

Mummy ce tsaye a bakin kofa tanata bugawa "Aayaan! Aayaan! Aayaann!!! Please kazo ka buɗe min kofa, please my son!

Aayaann Yana kwance ya jiyo Muryar mummy, hakanan don Babu yadda ya Iya yasa ya miƙe jikinshi yana rawar sanyi yaje ya buɗe ƙofar

Sosai tsoro Ya kama mummy, Domin bata taɓa zaton abun har yakai hakaba!
Kamashi tayi nanma taji jikinshi rau Kamar garwashin wuta. "Aayaann Yanzu fisbilillah Abinda kayi ka kyauta kenan? Kasan bakada lafiya shine ka Shigo ka rufe kanka a ɗaki? Ko abinci fa baka ciba, Yanzu don Allah ki yadda jikinka yayi zafi, ya kakeso nayi? Da ɓacewar Nawaz zanji ko da ciwonka?

Fashewa Aayaan yayi da kuka "Mummy don Allah kicewa Aunty Aseey ta fitomin da matata, idanma tayi hakane don ta gane ko inasonta da gaske, to ace Mata wallahi ina sonta kuma ina ƙaunarta.

Sosai tausayin Aayaan ya kama Mummy, lallai wanga Abu babbane, ta manta rabon da taga hawaye a idon Aayaan amma yau gasu nan suna kwarara, Sam bataga lefin shiba don dama Mutane da yawa sukance duk Wanda Bai taɓa yin soyayya ba to Idan ta kamashi Abin Baya yin kyau.....
Patting bayanshi takeyi a hankali"I'm sorry Aayaan, Insha'Allah i Will do My very Best don ganin matarka ta dawo, kuma Aseey ma zan tsawwala mata yadda Idan tasan inda Nawaz ɗin take Dole ta faɗa min..

Hakuri Mummy taketa bashi, shikuma ya dunkule Guri ɗaya a jikin mummy Kamar zai koma ciki.

Çikin hila da dabara irin ta iyaye mummy tace "Aayaan nifa haihuwar farko inasone Nawaz ta haifi Mace saboda insa mata sunan twins ɗina, hope zaka bani?

Mummy Kawai kiyi iya kokarinki na Ganin Nawaz ta dawo domin jikoki ma saikin gaji dasu, harda ƴan bibbiyu zata riƙa haifar Miki, ammafa idan ba Nawaz bace ta dawo bani Babu yin Aure don haka ki taimaka ta dawo ko don ki samu jikokinki...

"Daɗi Kamar ya kashe Mummy, dama dabara tamishi don taji cewar wai shi ɗin macen ne ko kuwa Kawai ya faɗa ne?

Yanzu ta gane Cewa bacin raine yasa yacewa Aseey haka,

Mummy kenan! Hankali dai ya kwanta tunda anji Aayaan lumui yake......

Aseey kam itama haɗa kayan ta tayi akan gobe idan su Mummy suka shirya zasu koma Maiduguri ita kuma ta tsaya a Kano ta hau jirgi ta koma gida, don taga alamun wannan zuwan kamar Babu Sa'a...

Ina jiran sharhi

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 48*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Sosai Mummy ta kwantar wa da Aayaan hankali, inda tace mishi kada suyi garajen faɗawa baffa cewa Nawaz batanan har sai sun koma Maiduguri, Saboda su Fara zuwa gidan su duba da kansu, idan kuma akaci Sa'a chan taje Shikenan...

"Aayaann promise me you will not cry again" Mummy tace tana goge mishi Fuskarshi da tafin hannunta.

Gyaɗa Kai Aayaan yayi tare da cewa "mummy bansan ma sanda nayi kukanba, kawai nima zubar hawayen naji.
Chapter 49 · 0% Book details