Sashe 54
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Achan gidan inna kuwa, inna ce zaune anayimata kunshi irin ɗan jere, Nawaz ta kafa ta tsare akan itama sai anyi mata.
"Ke kam Nawaz Nima da badon bikin da zani gobe ba da bazanyi ƙunshin nanba, kuma nace ki bari idan zaki tafi gida zan kirata tazo tayi miki harda baƙi zatayimiki na Sudan a bayan hannu,
Chuno baki Nawaz tayi "Nidai inna don Allah tamini yanzu harda baƙin Wallahi inaso, Kuma idan Zan koma ɗin ma sai a kuma kiranta tayi min sabo" dariya Inna tayi "Shikenan tayi Miki duk wanda kikeso"
Ai kuwa Nawaz harda tsallen murna, wayar mai lallen ta amsa tana kallon photunan ƙunshi kala kala a wayar, tama rasa wanda zata zaɓa.
Me ƙunshin ce tace "kibari a gama Mata, Ni nasan wanda zan yi Miki, kada ki damu na amare zan Miki, barin gaki fara, nasan idan nayi miki mijinki bazai gane kiba idan kika koma gida.
Zaro ido Nawaz tayi, kadafa itama wannan tana zarginta tana da aurene saboda cikar da tayi, sai Kawai tayi murmushi taja bakinta ta tsuke.
Inna kam murmushi tayi, duk da bawai tasan Aayaan bane amma tasan Dole idan yaga Nawaz ya ruɗe koda shi ƙarfe ne kuwa.
Hankalin Nawaz be kwanta ba har Saida taga an gamawa Inna an fara jera nata, sai murmushi takeyi domin akwaita dason yin lalle kamar aljana.
Tunda kinga yamma tayi Yanzu sosai, ja kawai zanyi miki zuwa gobe da sassafe sai nazo nayi Miki flawar Sudan ɗin itama sai in haɗa miki da chilli rani.
Murna Kamar Nawaz tayi mene, fuska Kamar gonar auduga, sai washe haƙora takeyi kamar mai tallan MacLean.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Haidar ne wanda fitowar shi daga yiwa wani surgery kenan, yayo hanyar ɗakin SARFRAZ Don ya duba jikinshi, Yadda yaga Hassu tayi zaune lakadan a kasa ne ya bashi dariya, sai kace wadda akaba gadi.
Da sauri ya ƙarasa kusa da ita "haba Hafsatul ikraam, kiyi hakuri mana, ɗan naki ya kusa samun sauƙi fa, Wallahi Nayi Miki alkawarin cewa Komai zai zama Kamar ba'a yiba.
Shagwaɓe fuska Hassu tayi "Ni so nakeyi na ganshi" murmushi haidar yayi "Idan kika ganshi zaki tafi gida?"
Aida sauri Hassu ta miƙe wallahi hardai ka bari na ganshi Allah zan tafi.
Gaba haidar yayi tare da cewa to kuzo muje, ammafa kada kuyi magana.
"Bazamuyi ba" cewar Hassu tanaji Kamar ansata a Aljannah
buɗe dakin yayi suka shiga ciki, abin gwanin Ban tausayi gaba ɗaya kan SARFRAZ an nadeshi da bandage ga Wasu Irin wayoyi da aka jona mishi kala kala, wai nan akwai ta abinci data Iska ta Wadda ke fitar da fitsari da bayangida.
Sai dai har wata ƙiba yayi ga haske ɗaya ƙara yi, duk baƙin da yayi a rugar su hassu ya washe ya koma usulin SARFRAZ ɗinshi.
Shafa mishi fuska Hassu tayi Tare Da cewa a ranta gashin ƙasumbarsa yayi yawa, Dalilin haka sai ya zama Wani babban mutum. Bandi ma dai sai kallonshi yakeyi yanajin daɗi a ranshi yasan cewa in'sha Allah wata rana SARFRAZ zai koma dai dai, to amma zai iya tunasu kuwa?
"To kuzo mu tafi gida, dama na duba ruwan ne, naga zai isa har na dawo, muje gida nima na ɗan samu nayi wanka naci abinci sai in dawo anjima.
Rimi Rimi Hassu tabishi Babu ko musu, dama ita burinta taga SARFRAZ, kuma ta ganshi yanzu babu sauran matsala.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Yadda Aayaan ya faɗa haka suka dauko hanya misalin ƙarfe Bakwai, koda Mummy taganshi sanda yake shiryawa ce Mata yayi kiran gaggawa akayi mishi daga NMS Barrack dake Zaria.
Sosai tayi mishi addu'oi ita da Aseey, mandiya Ashley kuma sannan ko barci bata tashiba.
Ta chan gurin Nawaz kuwa tun shida me lallen tazo, don itama tunda taga Nawaz taji tayi mata har addu'a taketayi azuciyarta Allah yasa su Zama kawaye, shiyasa bata tsaya Wata Wata ba tazo da wuri, tasan Nawaz ɗin zataji daɗi..
Misalin ƙarfe tara har ƙunshi ya bushe an wanke, wai hmm Nawaz kam zama tayi kamar wadda ake daurawa aure yau, farar Fatarta ta amshi ƙunshin sosai sai Wani sheƙi takeyi.
Ita kanta hadiya mai ƙunshin Saida na riƙe hannun tana kallo, don gani tayima Kamar bata taɓa yin lalle mai kyan Shiba..
Zuwa lokacin kuwa inna harta gama shiryawa, domin itace ƙirjin biki saboda Yar kanwarta za'a aurar anan Nagoyi (chan cikin Zaria) kuma gobe ne ɗaurin aure. Achan zata kwana, taso suje da Nawaz amma ganin hadiya sai Nawaz tace innan ta tafi su zasuzo gobe tare da hadiya yinin bikin.
Mai napep abokinta ta kira har ƙofar gida, saboda Akwai kayayyakin da innan zata tafi dasu, basu suka koma cikin gidan ba Saida sukaga napep ɗin tasha kwana.
Sosai suke ta hira da hadiya, don itama a ƙalla zata iya kaiwa ishirin da biyu a shekaru.
Wurin ƙarfe Uku da rabi hadiya tace zata tafi saboda zataje tahfiz sai ƙarfe Shida zata dawo, Nawaz tace mata su tafi tare ta nuna mata inda akeyin washing And setting tanaso za'ayi mata straighting ɗin gashinta.
Tare suka tafi, Saida hadiya ta nuna mata saloon ɗin Sannan ta wuce makaranta.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Shikam Aayaan sai wajen ƙarfe huɗu ya shigo Zaria, map ɗin motar yasa aka kunna sannan ya amshi tuƙin saboda yanaso ya kula sosai, location ɗin da ola ya Turo mai yake tabi ahankali.
Mamaki Abin yaketa bashi sanda yaga layin su sarfraz yake nuna mishi, ai kuwa yaci gaba da kallo yana bi, sai kuma yaga ya chanza hanya, a daidai gidan nafisa yaga locator ɗin ya tsaya.
Shiru yayi yana kallon gidan domin Kamar ya taɓa ganinshi, da sauri yace "gidan nafisa kawarta"
Fitowa Daga motar yayi yanayin Wani shu'umin murmushi "Daniel pls go And knock the door"
Ƙarasawa Daniel yayi ya ƙwankwasa kofar, ba'a jima ba saiga yaro ya fito yana kallonsu.
Kiranshi Aayaan yayi "maminka tana nan? "Eh tananan" yaron yace yana kallon Aayaan.
Kaje kace mata wai mijin Aunty Nawaz yana waje. Aida gudu yaron ya kwasa ya shiga gida, ba'a Fi minti Uku ba saiga Nafisa ta leko sanye da hijabi.
Murmushi tayi ganin dagaske Aayaan ne "ina ƙawar tawa?
Tambayar da tayi sai da Aayaan yaji zuciyarshi ta buga, Kada dai ace bata nan ma!
Muryar Nafisa ya jiyo tana cewa "yi hakuri bamu gaisaba, ina yini, yasu inna?
"Lafiya Lau Alhamdulillah ya yara"
Murmushi Nafisa tayi"yara suna lafiya, ina muhsin? Ko yana gurin inna? Ashe a gidan inna kuka sauka?
Wani daɗi Aayaan yaji ganin bema tambayetaba ta sashi a kan hanya, (mutum Idan ya cika surutu sai dai a barshi)
Ai kuwa suna chan gidan inna, dayake Ni banma je gidan innan ba tafiya ta kamani, to Sai yau na dawo kuma nakira Number mutuniyar taki bata shiga ba, gashi Bansan gidan innar ba shi ne nace kila Idan nazo zaki Iya kwatanta min!
Washe baki Nafisa tayi, jin cewa Aayaan zai iya Neman taimako a gurinta "aikuwa dai inna tana hayin ojo ne, idan kasan makarantar commercial to gidansu Yana gefen dama, da dai sanda muke zuwa Blue ɗin fenti ne, amma dayake an Dade yanzu bansan wane kala bane.
Hannu Aayaan yasa a aljihu ya ciro sabbin yan ɗari Biyar Biyar ya mikawa yaron Nafisa, Sannan yasa Daniel ya ciro kwalin chocolate a boot ya bashi, sai godia Nafisa takeyi tana cewa "baka gajiya, to Allah ya saka da alkhairi, Idan kaje kace ina gaida su, Allah ya tsare hanya.
Locator app ya shiga yayi searching ɗin ojo commercial, ya saita suka ɗauki hanya.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Hajiya Nawaz na zaune shigowarta kenan daga saloon tayi wanka, sam bakinta babu daɗi ta kuma rasa me zata ci gashi batason fita waje, miƙewa tayi ta ƙarasa katangar gidan dake haɗe dana inna,
Sallama tayi Sannan tace mamii don Allah Abba yayanan, tachan gidan mamii tace eh yananan inturoshine?
"Eh dama zan ɗan aikeshi shago ne"
"To gashinan zuwa" cewar mamii
Godiya Nawaz tayi Sannan ta juya zata koma tsakar gida don jiran shigowar Abba. Binta nayi da kallo, don wata riga ce play a jikinta doguwa, gata rubber, duk tabi jikinta ta liƙe Sannan kanta babu ɗan kwali sai dai parking ɗin gyararren gashinta da tayi.
Da gudu Abba ya shigo yana dariya, "ina wuni Aunty baturiya"
Yaron Yana sonta sosai domin ƴar baturiya ma yake ce mata, gashi kuma Duk sanda ya siyo mata Abu Shima saita bashi nashi, shiyasa duk sanda ta kirashi yake zuwa da gudu.
Kuɗi ta miƙa mishi "Abba don Allah chocolate Zaka siyo mini a shago, Irin Yar ɗari ɗari ɗin nan guda goma.
"To Abba yace Tare Da yin hanyar soro Don fita daga gidan.
Ɗai ɗai Nan Aayaan sun iso layin yama fito Daga cikin mota yana Bin gidajen da kallo, rasa wanne ne gidan inna yayi Ganin gida Kusan biyar Duk da blue ɗin penti.
Da gudu Abba ya fito yana murmushi don yasan Idan ya siyo Shima zata bashi.
"Abokina zo" Aayaan yace yana ɗaga wa Abba hannu alamun dashi yake.
Karasowa Abba yayi Sannan Yace "Ina wuni"
"Lafiya Lau abokina, don Allah ko kasan gidan Inna acikin gidajen nan?
Da sauri abba yace"inna wadda baturiya tazo gurinta?
"Ya sunan baturiyar"
"Sunanta aunty Nawaz, itace ma ta aikeni na siyo mata chakuleti yanzu, amma fa ita innar bata nan.
Murmushi Aayaan yayi Sannan yace"ina innan tajee?
"Ɗazu ta shigo tayiwa mamii sallama wai zataje biki cikin Zaria kuma wai kwana zatayi..
"Okay, gidan daka fito shine gidan innar ko?
Ɗaga Kai Abba yayi alamar eh, hannu Aayaan yasa a aljihu ya ciro sabbin yan ɗari Biyar ya mikawa Abba Sannan yace ya tafi gida Kada ya siyo, shine mijinta ta kuma ya siyo mata, dubu ɗayar Abba ya mikawa Aayaan Sannan Yace"ga kuɗin to kakai mata,
"Nabar maka" har Abba ya ruga Zai tafi Aayaan ya tsayar dashi, kwalin chocolate yasa Daniel ya ciro ya bashi.
Kallon securities ɗin Aayaan yayi Sannan yace "ku tafi da motocin amma ku bar min wannan, yana nuna wadda tsarabar Nawaz take ciki, zamu haɗu gobe in'sha Allah."
Kofar gidan Inna Aayaan ya karasa ya tsaya, Sannan ya Fara knocking a hankali, Nawaz Dake zaune jin ana Knocking Sai ta zata ko Abba ne ya dawo, dayake kofar takan rufe kanta sai Kawai ta tashi don zuwa ta buɗe.