← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 112

Sashe 90

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin wani lokaci jikinshi yayi wani irin zafi rau, haƙoranshi har haɗewa da juna sukeyi, sanyi sosai yakeji amma ya kasa tashi ya ɗauki bargo ya rufa.

Itakam Nawaz tanata barcinta wanda bata samu tayi da dare ba, sai bayan kamar awa biyu wani irin fitsari ya tasheta daga barcin da takeyi, koda ta tashi zaune bataga Aayaan kusa da ita ba, Hannu tasa ta janyo towel ɗin daya zame daga jikinta sanda tana barci ta ɗaura Sannan a hankali ta miƙe tsaye, takawa ta farayi a hankali Amma tana ɗan jin zugi a HQ ɗin ta, a haka ta daddafa ta shiga bathroom ɗin tayi fitsarin ta fito, ga mamakin ta ganin Aayaan tayi a ƙudundune saman carpet yana rawar sanyi, sannan tanajin gunjin numfashinshi irin wanda zazzaɓi yayiwa mugun kamu.

Neman zafin da takeji tayi ta rasa, ita kanta Batasan sanda ta isa gareshi ba Tare da ɗago kanshi tana cewa "yaya meya sameka?
Rau haka taji jikinshi kamar garwashin wuta, rasa yadda zatayi tayi sai kawai ta fashe da kuka tare da cewa "nashiga uku! Don Allah meya sameka?

Ganin bazai bata amsaba yasa ta samu gefen shi ta kwanta inda ta shige cikin ƙirjinshi ta rungumeshi gaba ɗaya, cigaba da kukan tayi Saboda bata sanma me zatayi ba.

Hankalin Aayaan yayi mugun tashi sanda yaji maganar Nawaz a kusa dashi saboda yasan ba wani iya takawa zatayi ba dakyau, ya kamata ace shi zaiyi jinyarta bawai ita tayi tashi ba, yanaso yayi mata magana Amma ya kasa saboda yadda bakinshi yayi mishi Nauyi, daurewa yayi ya buɗe bakin a hankali Tare Da cewa
"Dear bakida Lafiya shine kika tashi"
NAWAZ taji alamun yana magana Amma bataji me yace ba saboda Yadda muryarshi tayi ƙasa, "yaya I'm sorry pls, ka taimakeni ka tashi daga kasan nan ka hau Saman gado...
Ganin cewa ko yayi maganar baji takeyiba yasa ya fara girgiza mata kai Alamun ta gane ba zai iya ba.

"Bazaka iya ba?"
"Ɗaga mata kai yayi Alamun "eh", sosai tausayinshi ya kamata, gaba ɗaya ma neman haushinshi da takeji tayi ta rasa.
Yanzu burinta be wuce taganshi ya tashi ba, ace ingarman mutum Irin wannan ne kwance yana rawar zazzaɓi? Lallai koma menene ke damunshi ya Isa Abin dubawa.

Ahaka tana tunani barci yayi awon gaba da ita, sai Misalin ƙarfe shida da wani Abu ta tashi, shima tana cikin barci taji Kamar Ana kissing ɗinta, a hankali ta buɗe idonta wanda yake cike da barci, fess ta saukesu a saman fuskar Aayaan wanda yake yi mata wani kyakkyawan murmushi.
"Dear tashi kiyi sallah mun makara" Maida idonta tayi ta rufe Saboda tuna Abinda ya faru Tsakanin su jiya da dare da tayi, da sauri kuma ta kuma buɗe idon tare da cewa "mafarki nayi ko gaske?"

"Kinganni banida Lafiya Koh? To gaskene! Da gaske nayi zazzaɓi na wucin Gadi" Amma Yanzu naji sauƙi

Maida Idonta tayi ta rufe tare da cewa "Allah ya ƙara sauƙi amma Naji tsoro sosai wallahi"
A hankali kanta a ƙasa ta tashi tare dasa ƙafarta a saman carpet da niyyar sauka daga kan gadon, ai kam bata Ankara ba taji Aayaan yayi sama da Ita tare da cewa "Ayyah Madam ɗina nasona Ashe?, muje Kiyi alwalar to"
Sai a cikin bathroom ɗin ya Sauketa tare da kunna mata tap ɗin sink "kiyi alwalar sai in maidake kiyi sallar"

"Nifa zan iya tafiya da kaina! Ka tafi kawai" Nawaz tace domin ta kasa sakewa sam

"Just keep quiet and do what you Are here for"

Shiru tayi tai alwalar, fara takawa tayi da kanta saboda ita sam ba wani ciwo takeji na azo agani ba, "ɗage ta sama yayi tare da cewa "meyasa kikeson tsokana tane?, Uhhm?"
Ita kunyarshi takeji amma shi ba zai gane ba, sai yayi ta ƙara sa tanajin kunyar.

A saman carpet ya ajiyeta ya sa mata doguwar rigarta sannan ya yane mata kanta da mayafi Sannan yace "to Bismillah"

Tada iƙama tayi shikuma ya tafi kitchen don ya haɗa mata tea me zafi saboda ta gasa mararta, bashida magani wanda ya danganci condition ɗin da Nawaz take ciki a cikin first aid box Dinshi, kuma Abin yazo mishi a bazata shiyasa be shirya komai ba.

Sanda ya kawo mata clove tea ɗin ya Tarar harta idar da Sallah, ɗaukarta yayi ya ɗora ta a saman cinyarshi tare da kafa mata kofin a bakinta "Bismillah"
A hankali ta fara sipping ɗin tea n, sosai yayi mata daɗi Saboda yasa zuma da yawa a ciki, saida ta kusa shanyewa tace ya isheta, murmushi yayi ya shanye sauran tare da ajiye cup ɗin a saman side drawer.

Ɗaukarta yayi ya ɗora saman gadon tare da rungumeta a Cikin ƙirjinshi "Sleep" Abinda yace mata kenan ya shiga duniyar tunani "me zanyiwa Nawaz a duniyar nan na biyata? What will suite her? "
Sosai yake Duba meya dace da Ita, komai ya kissifa a ranshi sai yaga beyi mishi ba, yayi kaɗan ko kuma darajar ta tafi Abin.

A haka shima barci ya dauke shi dama ita Tun tuni tayi nata barcin. Bashi ya tashiba sai wajejen ƙarfe Goma, koda ya tashi ita bata tashiba sai barcinta takeyi hankali kwance, a hankali ya gyara mata kwanciya Tare Da ƙara rufeta da duvet.

Tashi yayi saboda yaje CLINIC ya siyo mata magunguna duk da ya lura jikin nata Alhamdullillah, zazzaɓi ne kawai yake damunta sai kuma zargin da yakeyi akan ta saboda zazzaɓin da yayi.

Yana tunanin idan Hakan ta kasance shikam ya zaiyi da farin ciki?

Yana buɗe kofa sukayi ido huɗu da fatima zata danna ƙararrawa, gaisheshi suka fara yi a ɗan daburce ita da Maman sudeis dake tsaye bayanta, murmushi yayi musu Sannan ya amsa tare dace musu "sannunku da zuwa, ina abokina?"

"Aikam gashi yana barci, dama yau munyi zamuzo mata yini ne, to kuma mun kira wayarka amma ba'a picking shine mukace bari mu tawo kawai" maman sudeis tace tana ɗan murmushi.

"Ayyah wayar na ɗayan bedroom ɗinne, dayake ba'a nan muka kwana ba, kushiga tana ciki tana barci ne.

Nuna musu ɗakin da take ciki yayi Sannan ya fita ya barsu a falour, maman sudeis ce tace "Anya kuwa Fatima ba'a kashe boss ba? Naga yanata murmushi, kuma wane barci ne har shadaya saura?

"Uuhmm nidai Babu ruwana, kinganki dasa ido, kin tasa Yar mutane a gaba"

Miƙewa Maman sudeis tayi ta shiga bedroom ɗin da Aayaan yace Nawaz na ciki, Yadda taga Komai a yamutse yasa ta yafito Fatima da hannu Alamun tazo.

Bin bayanta Fatima tayi itama ta shiga ɗakin, bin ɗakin suke da kallo Domin suma ya tafi da imaninsu, zanin gadon da Aayaan ya ajiye a gefe sanda ya chanza ɗayan Maman sudeis ta ɗauka tana kallo, ƙwalalo Ido tayi tare da cewa Fatima dama nace Miki...........

Babu yawa Amin afuwa.

*MATAR RASHEED* ✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*76*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

"Fatima dama nace Miki an kashe boss, kalli kiga" Cewar maman sudeis tana nunawa fatima stain ɗin dake jikin zanin gadon

"Ni dai ajiye mu fita kada ta tashi ta gammu kisa muji kunya" Cewar Fatima tana yin hanyar fita daga faloun.

Shara da kakkaɓe-kakkaɓen ƙura sukayi mata da ƴan gyare-gyare amma iya falour da kitchen sai ɗaya bedroom ɗinsu wanda suke kwana da.

Maman sudeis ce tace "Anya kuwa fatima bazamu dafa musu wani Abu ba! Nasan ba wani abu suka ci ba kuma Dole bakinta babu daɗi"

"Eh ya kamata amma kamar me"

"Mu fara duba freezer muga abubuwan dake ciki, Kinga sai musan me ya dace a girka"

"To" Fatima tace tare da miƙewa Sannan suka nufi kitchen Dukansu.....

Bubu abinda babu a cikin freezer ɗin, nadaga kaji, kifi dasu vegetables.

Kaji biyu Maman sudeis ta ciro da kayan lambu sai catfish guda uku manya, kifin taba fatima tace ta gyara ita kuma ta daɗa ɗauraye kazar ta ɗora a wuta tare dayi mata haɗin tafashe.

Sosai aikinsu yayi nisa inda har sun gama pepper chicken da roast fish, fried rice ɗinne basu gama ba, babu Nawaz babu alamunta, hakan ke nuna har yanzu bata tashi ba, shima kuma Aayaan har yanzu be dawo ba.

A ɗaki kuma tashin Nawaz kenan daga barci taga babu Aayaan, sosai taji daɗi Saboda zatayi komai a sake tunda shi ya kase gane tana jin kunyar shi, miƙewa tayi a hankali ta fara tafiya, ita kanta mamakin ya akayi batajin irin mugun zafin nan takeyi, tasan dai tanajin zugi amma ba Irin wanda take tunani ba "kenan Sarfraz mugunta yayiwa hassu, tunda har fa ɗinki akayi mata" bathroom ɗin ta shiga a hankali tare da kunna tap ɗin water heater.
Bath ta cika da Ruwan zafi Sannan ta sirka zuwa yadda zata iya shiga, cire rigar jikinta tayi sannan ta shiga cikin Ruwan a hankali, daɗi sosai Ruwan yayi Mata, tayi kwance luf a ciki dumin na ratsa ta tako ina.

Saida ta canza ruwan har sau uku Sannan ta haƙura tayi wanka ta fito, zanin gadon dake gefe ta ɗauka ta koma bayin ta tura shi cikin washing machine ta zuba ruwa da liquid soap.

Bedroom ɗin ta dawo ta samu mai a cikin drawer ta mutstsika a jikinta sannan ta feshe duka jikinta da turare, rasa kayan da zata sa tayi saboda babu kaya a cikin wardrobe ɗin.

Tana tunanin fita zuwa ɗauko kayan saboda kada su haɗu da Aayaan kila yana falour ko kitchen, gashi kuma towel ne Kawai a jikinta, shiru tayi naɗan wani lokaci inda daga bisani ta koma bathroom ɗin ta ɗauko doguwar rigarta ta mayar jikinta tunda dama Sallah kawai tayi da ita bawai tayi datti bane.
Tufke gashin kanta tayi daya dameta a fuska Sannan tayi hanyar fita falour saboda cikinta ya fara kiran ciroma, mamaki abin yaba Nawaz ganin maman sudeis da Fatima hakimce a kujera sunata shan hira "lah! Ikon Allah! Don Allah yaushe kuka zo gidan nan? Ina yayan yake?"

"Hmmm Madina kenan, nifa har yanzu na kasa yarda ba ciki gareki ba, wannan uban barci kamar barcin mutuwa" Cewar maman sudeis tana kannewa fatima ido
Ita kuma Fatima tace "Tun ƙarfe goma muna nan gidan fa, yayan naki kuma ya fita tun sanda mukazo"

"Kai dan Allah! Shine ko ku tasheni!"
Chapter 90 · 0% Book details