Sashe 108
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita dai aje wayar tayi ta fita don zuwa yiwa jamila wanka domin ta juye ruwan, bilhakki take kula da jamila Kamar yadda zata kula da Nawaz hakan yasa cikin lokaci kankani jamilan ta maida jiki sosai kuma ta samu lafiya illah damuwa da tasa kanta a ciki, kuma damuwar tanada nasaba da meye makowar Rayuwar ta anan gaba, me zata cewa wanda zai zama mijinta game da rayuwarta, hakan yasa lokaci zuwa lokaci ummi ke samunfa tana kuka.
Itako umma kullum tana Cikin hijabi riƙe da charbi tana istigfari da tuba, mamakin ummin Nawaz kullum baya barin zuciyarta domin kullum cikin hidima take dasu, babu Abinda ta rage illah karawa ma datake yi, kuma haka fauziyyah ma Kusan kullum ummi saita kirata a waya taji ya ƙarfin jikinta.
A yanzu ji takeyi da za'a bata Aljannah guda ɗaya ace taba wani kyauta to babu makawa ummin Nawaz zata ba, domin ta rufa mata asiri duniya da lahira.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Su Mummy sun sauka a gida Lafiya, Aseey ce keta hidimar gyara gidan donma anci Sa'a maiyi musu girki ta dawo, miƙewa Nawaz tayi don ta taya Aseey Saboda suyi saurin gamawa, namfa Aayaan ya riƙe ta kan cewa taje ta kwanta wai Little Aayaan yana buƙatar hutu.
Ihu ta fara ta nufi ɗakin Mummy "yiiii wayyo, Ni wallahi bazan iya ba" da sauri mummy ta buɗe kofa cikin tarardadi tana tambayar Nawaz cewa meya faru take kuka?
"Mummy ni wallahi bansan me yaya Aayaan yake nufi daniba, tunda akace cikin nan yana nan ya hana ni yin komai hatta alwala shi yake min, dana tashi zanyi aiki saiya hanani"
"To daughter Yanzu wannan ɗin kikewa kuka?"
"Mummy wallahi jikina ciwo yakeyi kuma na gaji da zama"
"To yanzu bari zanyi mishi magana ya riƙa bari kina alwalarki da kanki"
Tsalle Nawaz tayi "Mummy nifa ba alwala kadai ba harda abubuwa da yawa"
Tsallen da Nawaz tayi saida mummy ta jishi a cikin ranta, domin itama a nata gurin matakin da Aayaan ya ɗauka akan Nawaz ɗin yayi mata dai dai, Domin bazata iya jurar rasa cikin a karo na biyu ba, kuma ga Nawaz mayyar aiki ce sam bata gajiya barin ma taji labari akan girki.
Lallabata tayi da cewa zatayi wa Aayaan ɗin magana, sai sannan NAWAZ ta wuce ta tafi daki ko kallon inda Aayaan yake bata yiba irin ita ta samu yancin nan.
Ɗaukar waya Mummy tayi don ta kira ummin Nawaz daga nan ta kira mummyn sarfraz don taji ya suke, aikuwa murna taƙi barin fuskarta sanda taji cewa gobe su ummin Nawaz zasu sauka a garin kuma ƙarin daɗin shine Abban Nawaz ya dawo.
Koda ta kira mummyn sarfraz ta faɗa mata gameda zuwansu ummin Nawaz Maiduguri sai tace itamafa ata bau bau sai taje, yadda ta yanke zance ma shine zata shirya taje gun ummin Nawaz ɗin taji yadda za'a yi tafiyar don tana ganin tare zasu tafi kawai.
*Zuwa maiduguri da sukayi ya gyara abubuwa da yawa* *kuma ya haifar da farinciki Sosai a zukatan duka ahalin*
Domin Abban Nawaz yaga mijin Nawaz inda take yaji ya shige mishi zuciya, kuma baffa yacewa Abban Nawaz ya maida umma dakinta tunda tayi nadama kuma ya gaggauta yafewa Jamila.
Koda Nawaz taga Abban ta haka ta tafi ta faɗa jikinshi ta riƙa kuka har Saida Aayaan yaji kamar yaje ya ɗauketa a gurin. Sosai duka ahalin suka samu kusanci da juna domin a gidan su Aayaan suka sauka duka, sai daga bisani aka zazzaga dangi.
Ganin Yadda aka haɗu guri ɗaya yasa Aayaan ya zame ya kira colonel ya shaida mishi cewa yayi sauri yazo yanaga hakansa zai cimma ruwa in'sha Allah.
Su kuwa su Naufal da fudail ganin sarfraz da bandi sai ya zama kamar Sallah a gurinsu, duk da cewa su sarfraz ɗin sun girmesu amma suna jin daɗin zama dasu sosai.
Hassu kuwa tunda suka haɗu da Nawaz ta like mata, itako Aseey duk murnarta ta koma ciki domin baban Muhsin ya kirata yace ta tabbatar ta koma gida jibi shima yana hanya.
Aayaan sanin cewa ga Abinda Ya shirya na Mummy da colonel sai ya sa securities dinsa sukaje suka kwaso kakannin Nawaz na uwa dana uba, sai nashi kakannin na wajen mahaifi, be tsaya nanba saida yayiwa sarfraz kara shima ya kwaso nashi, inda yace kowa ya kira sauran ƴan uwa a shaida musu cewa gobe wajen ƙarfe goma akwai walima a gidan.
Aikuwa sosai aka taru inda su Mummy da Aseey suketa mamakin wace walima za'a yi wadda basusan da Ita ba, kuma su basu tanadi komai ba ga mutane sun fara taruwa.
Abinda basu saniba shine Aayaan duk ya bada order ɗin duka abinci da snacks da drinks ɗin da za'ayi amfani dasu a kusan restaurant guda Biyar.
Gurin ƙarfe tara da rabi kuwa gida duk ya cika da abinci, mutane sai kai komo sukeyi inda gidan yayi tanƙam da mutane daga ɓangaren duka ahalin.
Wurin karfe goma da wasu Yan mintuna colonel ya sauka, dakinda su kakanninsu suka yada zango nan Aayaan ya raka colonel.
Bayan sun gaisa ne Aayaan yake musu bayanin cewa colonel tun bayan rasuwar abbansu yakeson mummy amma taki bashi dama, ga kuma yanzu Allah yayiwa mai dakinshi rasuwa kuma ya kuma dawowa nanma tace a'a itafa bata yarda ba,
Sosai kakan Aayaan ya gyara zamanshi, "to Amma Ayatullah meyasa Ni baka taɓa fadamin ba?"
"Ita ta hanamu baffa, ko yanzu ma bata saniba"
Shima kakan Nawaz Sosai yayi mamakin wannan karfin halin na mummy, Anan suka yanke hukunci shadaya na bugawa za'a daura Auren colonel da Mummy.
Ganin Maganar ta koma ta manya yasa Aayaan yayi sif ya fice ya basu guri, shikuwa Colonel jinshi yake kamar wanda aka ɗauka aka saka a cikin aljanna, shikuwa wace irin Sa'a ya taka yau kuwa? Yanzu wannan dalleliyar balarabiyar ce zata zama mallakin sa? Lallai kuwa ya godewa Allah, kuma shima zaiyi bajinta.
Kamar yadda sukace kuwa shadaya na bugawa aka Daura Aure, Mummy na can tana hidima da mutane Aseey ta tawo da gudu tana cewa "mummy! Mummy!! Bakiji abinda naji bane?"
"Ooh Aseey Don Allah Ni banji komai ba, ki bari na gama da mutane sai ki faɗa min koma menene "
Matsawa kusa da Ita Aseey tayi sosai sannan tace "yanzu fa Naji ana sanarwar an daura auren ki keda daddy colonel, wai ashe abincin bikinki kike rabawa"
Tsaye Mummy tayi chak kamar gunki, ji tayi komai na jikinta ya dena aiki......
😂😂😂😂😂😂😂
Matar Rasheed ❤️*🎀 🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*91*
*SECOND TO THE LAST PAGE 😭😭*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Ko motsa yatsanta ta kasa yi sai zallar gudun da zuciyarta takeyi, wata Irin fargaba ce ta kama ta wadda ko a aurenta na fari bata ji irin taba.
"Ashe haka Nawaz taji! Lallai Nawaz nada haƙuri domin ita kanta da ta taɓa aure abin ya bigeta balle wadda bata taɓa aureba kuma bata samma wanda aka aura mata ba"
Da kyar ta dawo cikin hayyacinta, ba tare data cewa Aseey komai ba Kawai ta miƙi hanyar sasan da su baffa suka sauka, so take taje taji waye ya shirya mata wannan manaƙisar.
Tsabar saurin da takeyi yasa lafayarta ya fara warware wa da kanshi, bata jira komaiba ta ƙarasa cireshi da kanta, Nannaɗe shi tayi ta ɗora a saman kafaɗarta tana ci gaba da tunkarar sashen.
Warwarewar da lafayar tayi sai ya ƙara bayyanar da duka surar mummyn a fili, barin ga kuma saurin da takeyi hakan yasa duka jikinta ke juyawa tako ina musamman mazaunta, kuma dama su take ɓoyewa kullum cikin lafayar, sai lafiyayyen gyararran gashinta daya sauka har gadon bayanta.
Colonel ne tafe da Aayaan suna maganar yadda za'a bullowa Mummy, basaso taji zancen a bakin wani, sunfi so su faɗa mata da kansu Saboda Abin zaifi zuwan musu da sauƙi. Aayaan ne ya taɓa Colonel yana nuna mishi Mummy Wadda ta nufosu cikin wani irin sauri, "Daddy da Alamu wani yaje ya faɗa wa mummy"
Cirko cirko sukayi suna jiran mummy ta karaso gurin su saboda suga yadda za'a kare, abinda basu sani ba shine sam Mummy bata ma gansu ba, gaba ɗaya hankalinta da tunaninta duka yana hanyar kofar ɗakin su baffa.
Ganin ta wucesu batace musu komai ne yasa suka gane bata gansu ba, zata ɗaga labulen ɗakin su baffa kenan taji baffa yana cewa "Aini mehtab ta gama yimin komai a Rayuwa, tunda nake da ita ban taɓa yin abu tace baiyi ba, tun Muhammad yana raye ko kara na ajiye bata tsallake wa, kuma har bayan ya mutu bata rage komai daga abubuwan da take yimin ba, Allah dai yayi mata Albarka ya albarkaci Aurensu, yasa shine hanyar da zata shiga Aljannah.....
Jin wannan Maganar da baffa yayi akanta sai mummy taji gaba ɗaya gwuiwarta ta sage, bata da wani sauran kwarin gwuiwar zuwa ta samu baffa tace mishi batason auren, juyawa tayi da nufin ta koma daki domin zuwa yanzu ta amince cewa Auren ta da colonel A Rubuce yake.
Ganin colonel tayi tsaye shida Aayaan, da alamun ma ba Yanzu suka ganta ba, ji tayi bazata iya cigaba da tsayuwa a gaban suba, wai wannan Abin Kunyar har ina! Fisbilillah ace kamarta ce wai akaiwa auren dole, ta gefen su Colonel ta wuce ba tare data ce musu komai ba.
Hakan saiya darsa wa colonel tsoro a cikin zuciyarshi, yaso ace tayi masifa,tayi jaraba Saboda ta fitar da duka damuwar ta, wannan shirun yana nufin Akwai sauran rina a kaba kenan.
Da ɗan sassarfa ya ƙarasa kusa da ita tare da ɗan shan gaban ta "Pls ki tsaya ki saurareni, wallahi shirun nan ƙona ni yakeyi, koma me zakice pls kice.
Kaucewa tayi zata cigaba da tafiyar ta, besan sanda yasa hannunshi ya riƙe damtsen taba "pls ki saurareni, beat me, slap me or do anything you like, wallahi mehtab da gaske ina sonki, kuma bawai nayi miki karfa karfa bane saboda na nuna baki isaba, ƙaunar kice tamin yawa a cikin zuciya ta.
Wani iri mummy taji a damtsen ta, wani yamm gurin yakeyi mata, ƙoƙarin kwace hannun ta tayi ya kuma riƙe wa da karfi, "pls ka barni mana"
"Promise me bazaki tafi ba koda na sake ki"
"Eh bazan tafi ba, sakeni"