← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 112

Sashe 9

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maggi safraz ya dauko, guda nawa zan bare?
"10"tace a takaice, haka Yayi tajan ta da hira har saida ya samu ta saki ranta..
har saida suka koma suna rigerigen zuba abu, gurin sauri nawaz a Kai hannu tukunya ta kone,
Dasauri safraz ya kama hannun Yana firfitawa sai faman Sannu yake mata.
Amsar hannunta tayi gami da cewa kadan ne pah..

Misalin 11:43am
sun gama abincin, warmers safraz ya kwaso ya kaiwa nawaz ta jujjuye a ciki,
mum anyi mata rice and beef stew d'in datace, su kuma tayi musu chicken biryani.

wanke Hannu tayi a dish washer na kitchen d'in sannan ta goge fuskar ta....
warmers d'in suka kwasa zuwa dining suka jera...

kallon safraz tayi "Dan Allah inaso nayi barci, ko kadan ne?!

murmushi yayi "to kije ki kwanta mana, cewa tayi ai bansan inda zan kwantaba..

cewa Yayi kije d'akin da kika kwana,
d'akin safraz ta nufa ta shiga, a falour Ta kwanta Saman three sitters couch....

tana kwantawa barci yayi awon gaba da ita.

Bayan Kamar minti goma safraz ya shiga d'akin, ganinta Yayi kwance tana barcinta peacefully.
Karasawa yayi Yana Kallonta, "datasan dakinane nasan bazata yarda ta shigoba balle harta yi barci a cikiba.
murmushi ya kuma yi "kalleta Mai kyau Dan Allah...

zama yayi ya zuba mata ido yanata kallo, ita kuma Sai barcinta takeyi hankali kwance

motsi yaga tayi, da sauri ya tashi, .
cigaba da barcinta tayi Shikuma ya zauna yana tunanin me zaiwa wadanda sukaso ketawa malamarsa haddi..

anan shima barci ya daukeshi.....

♾♾♾♾♾♾♾♾

umma nagani zaune gaban wani farin tsoho fuskarshi duk buyagin gemu.
fauziyya ce tayiwa bokan bayanin komai sannan tace suna sone a rufewa Nawaz baki yanda bazata iya fadan komai a kaiba
Nan bokan yadanyi siddabarunshi yace komai ya kammala.

godia sukayi mai sannan umma ta ciro kudi ta ajiye a gabanta sannan suka tashi suka fita...

saida sukayi tafiya mai Nisa sannan suka Isa titi, kasan cewar a sabuwar unguwa gidan bokan yake..

gida suka koma suna farin cikin anrufe bakin Nawaz (inba bata ba ace wani Wanda bai iya yiwa kanshi abubane zai iya yi maka, kana zaune a gurin yayi shirme Amma ka yarda

♾♾♾♾♾♾♾♾

sai wurin karfe 1:25pm mummy ta tashi daga barci, kitchen ta duba bataga Nawaz ba sannan duka dakunan gidan ta duba Amma batanan.

d'akin sarfraz ta tura ta shiga, "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un mummy tace ganin.......

please nagaji kuyimin afuwa...

*OUMMOU MUHSIEN* 😍*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 9*

✍🏻 by oum aeyman

Supreme writers association....

Ganin sarfraz Hankalinshi kwance yanata faman barci......

Hancinshi ta matse iska ta daina shiga, Dasauri ya bud'e ido ya tashi......

Mitstsike idonshi Yayi sannan yace mummy kin tashi ashe😳
Mum tace "ban tashiba Kai yakamata in tambaya koka tashi?

Murmushi yayi "mum menayi kuma?
Cewa tayi "kazauna tambayata Bayan kacemin 1:00pm kakeda lecture kuma gashi yanzu 1:30pm

Kayi sauri ka tashi ka shirya, kasamu kaci abincin ko kadanne saika tafi....

Cewa Yayi to mum, sannan ya fita.

Juyawar da Mum zatayi kawai ta hango nawaz sai faman barci takeyi, duk ta saki jiki..
Karasawa tayi tad'an tasheta kad'an, bud'e ido tayi suka had'a ido da mum, da sauri ta tashi domin Sam ta manta ba'a gida takeba.....

Mum tace meyasa kikazo d'akin safraz?
Maimakon kizo nawa, inma bakyason nawa ai akwai d'akuna da yawa....

Cewa tayi d'akin sarfraz 😳❓
mummy wallahi bansan d'akin shi bane 🤨.
Kuma aishi yace nazo nan😔

"kada ki damu my dear ☺, nasan halin sarfraz zaiyi fiye da hakama.
yanzu kizo muje kici abinci kiyi sallah koh?

"to" tace sannan ta Mike tabi Bayan mummy.

A dining suka tarar da sarfraz har Yayi serving dinsu, mummy ta balla mishi Harara "wayace maka yanzu zamuci daka wani zuba mana ❓

cewa Yayi ai nafiso taci da wuri saboda mu tafi da wuri kada na rasa lecture na🤨..

Mum tace ban gane ku tafiba 🤔

cewa Yayi "dama dazu da Muna girkine tacemin Dan Allah idan zan tafi makaranta zata bini in siyan mata kayan kwalliya da hijab shine nace mata to.
kallon nawaz yayi "koh malama 😋😉❓

☹ 'bata rai nawaz tayi "yaushe nace maka haka 😟?

fuskar mamaki sarfraz yayi "haba malama fisbilillahi Don kinajin kunyar mum saiki chanza magana 😉😎

Cewa tayi "Allah niban ce maka hakaba 😡

mum tace "shikenan yi sauri kici abincin kiyi sallah kibishi kada ya rigaki,

"Mum Allah niban ce mishi hakaba 😦

mummy tace " shikenan, koda bakiceba tunda Yayi niyyah saikije ya siyan miki d'in, yi sauri my daughter ☺

nawaz ta cika tayi bam ji take Kamar ta zabga ihu, Shiko sarfraz murna fal cikinshi.....

bini bini ya kalleta Yayi mata gwalo 😛😋😜...

sunkuyar dakai tayi takicin abincin, mum ce ta ta'ba ta "my daughter kici abincin mana!

Charaf sarfraz yace "mum tun dazu tacemin Idan muka fita in siya mata ice-cream 🍦 da chocolate 🍫, wai su take sha'awa yau...

OK "tunda bakyajin cin abincin to yi sauri kije kiyi sallah kafin ya gama.....

Tashi tayi ta nufin d'akin mum,
Tana shiga tace "wayyoo oh ooo 🤯
wai me wannan sarfraz d'in yake nema danine ❓

ya daukeni tamkar sa'ar shi, to kuwa zan koya mishi hankali, wallahi donma Ina jin kunyar mummyn shine.....

Bathroom ta shiga donyin alwala, amma me?
Jikinta ta gani a 'bace, cewa tayi na shiga uku, baka kyautamin ba coz bakazo a lokacin daya daceba...

inani inayin menses a gidan mutane, mutanenma irin sarfraz ❓

cire pant d'in Tayi ta wanke, sannan ta dauki tsohon nata data cire ta mayar....
gyara fuskarta tayi, sannan ta fita falour...
"yauwa malama kin fito a daidai nima na gama.

murmushin ya'ke tayi sannan tace hmm, wani sabon flat shoe mum ta mika mata "kisa wannan koh!

Murmushi tayi "nagode mummy,
Mum tace "you don't have to, and kuma batun hijab zaki zauna a mota saiya amso miki kisa koh?

murmushi ta kumayi ''to mummy "

to to Kuyi sauri kunga har biyu tayi, har parking lot ta rakasu sannan ta koma d'aki,,

Suna fita daga gidan sarfraz ya kwashe da dariya 🤣😂🤣😂😂🤣😅"ya kikaga salon nawa?

Harararshi tayi ''wallahi kaima zakazo Hannu, saboda kasan mum zata goyi bayanka shine kaketa yin karya kana jonawa Dani koh?

malam saukeni anan 🤨....

Hmmm ki sauka mana, kinga saiki tanadarwa mummy Amsar tambayoyin dazata miki Idan kika koma😎

domin a gabanki tace asiyo kayan da yawa kuma itama tace na siyo mata grapes 🍇...

balla mai Harara ta kumayi "naga alamun kama manta ni malmarkace koh?

kashe mata ido Yayi 😉"kin manta ni kuma yayankine koh❓

enough!!!!!! 😡😡😡😡
daga yau nafasa y'an uwantakar, ko dolene?

"calm down little sister nasan Rankine ya baci, Amma dazaran kinsha ice-cream you will be alright.... 😇

banza tayi dashi batace komaiba,, ,
baiji dad'in shirun data yiba domin yafiso ta tayashi suyi tayi ...

a classic boutique yayi parking, cewa Yayi tsaya inzo, kada pa ki fito a haka.. ...

kauda kanta tayi gefe "alamun batajin abinda yake cewa

cikin boutique d'in ya shiga, Kamar 13mins saigashi ya fito rikeda Manyan shopping bags 🛍.. .
motan ya shiga ya d'ora duka kayan a cinyar nawaz sannan ya Fara driving.

Hanyar kasuwa taga yayi ba hanyar school ba, cewa tayi "sarfraz makarantarfa? Ko so Kake karasa lectures?

murmushi yayi "nifa yau banada lecture, dama saboda inzo gidanku nayi wa mum karya, kuma saigaki Allah ya kawomin Ke a sadaka.. .

"hmm 'karya dai haramun ce kuma Ina kyautata zaton tun kana yaro kasan haka!

"Nasani Amma saiki Duba dalilin yin karyar tawa, inasone naje naga kanwata kuma hakanan freely bazai yuwuba.. ..

Harararshi nawaz tayi sannan tace "okay fine do what ever you like!

fresh vitamins Yayi parking, cewa Yayi ''zo muje tare,
da gayya ta Mike zata fita Haka kodon taji me zai ce mata,
da sauri yace "kiduba jakunkunan akwai hijab kisa kafin ki fito, yaza ayi ki fito haka?

dariya tayi aranta sannan ta koma tasa hijab d'in , tana fitowa mai stall d'in yace hajjaju me za'a zuba miki?

Harara sarfraz ya balla mishi "malam concentrate on me not her, "Ke kuma koma mota. ...

zuba mini pomegranate da pear da apple da grapes da banana da lime da lemon da kuma pineapple and watermelon.. ...

Polythene bags ya dauko yanata packaging dinsu da sauri.. . Sannan ya mikawa sarfraz, yayi service dinshi ya shiga mota. ....

malama kinga mutum yanata kallonki, aiya kamata ki koma dakanki kafin wani yace miki

Banza tayi dashi, domin abin nashi ya Fara bata tsoro, saikace wani mijinta

sahad stores ya wuce da ita nanma hanata fita tayi..

ai kuwa Yana fita taga chanji a cikin bags d'in kayan, waje Ta leka ko zata hango Wanda zata aika, wani saurayi ta hango zaune kusa da exit.

fita tayi kusa dashi "Barka dai Dan uwa, "Barka hajiya...

Dan Allah kozaka taimaka ka samomin yaro nadan aikeshi ciki?

dariya yayi, hajiya ki aikeni mana!
murmushi Nawaz tayi "habadai da girmanka?

Allah ki aikeni wallahi ni dako ma nakeyi anan ,,,

d'ari bakwai ta mika mishi, "Dan Allah ka shiga ciki ka siyomin always pad, idanma baka ganeba zaka iya cewa abaka pad, saika ri'ke sauran chanjin,..
cewa Yayi hajiya nagode, sannan ya tafi

tana tsaye a gurin Bayan minti Kamar hudu saigashi ya fito rikeda karamar bakar Leda "hajiya gashi
Amsa tayi "nagode Dan uwa na, tajuya zata tafi

da sauri yace "hajiya chanjin pah?

murmushi tayi mai "babu komai ainice nace ka rike,

kwandonshi dake jingine a gefe ya dauka, nagode kingama gida zani domin wani zubin Sai in yini anan amma dakyar zan samu d'ari biyu Sai dai in Allah ya hadani da irinku....

murmushi tayi mai "to shikenan ka gaida gida nagode, har tana Daga mai hannu..

duk abinda ake sarfraz na gani, da sauri ya tawo Amma sai dai kafin ya karaso ya riga ya tsallaka titi..
jiyayi Kamar ya zabgawa nawaz Mari,
"who the hell are you, nace ki zauna a mota shine kika fito?

tukunama waye wancan d'in?
cewa tayi "ya birgenine shine na fito mu gaisa,.

kam bala'i, wallahi bazai yuwuba idan na karyashi sai Inga ta inda zai fito daga gida balle kiganshi harya birgeki...

hanyar titin yayi zai tsallaka, da sauri ta rike rigarshi ta baya...
Chapter 9 · 0% Book details