← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 112

Sashe 104

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama ya ɗaga labulen ɗakin umma ya shiga ciki Ummin Nawaz na biye dashi, umma ko sakin baki da hanci tayi tana kallonshi kamar a Cikin mafarki, bata daɗa tabbatarwa cewa ba mafarki take ba saida taji yace "Butulu! Hakan da nazo na sameki ya daɗa tabbatar Min da gaskiyar Komai,"

Girgiza kanshi yayi sannan yaci gaba da cewa "Hmmm! Ban taɓa tunanin cewa da makiyiyata nake zaune ba saida Allah ya fallasa min komai, ya fito da Komai a fili kuma ina ƙar.........

Kuyi hakuri da jina da kuka yi shiru, munyi sha'ani ne Kusan kashi uku a jere, yanzu haka ma bamu gama ba, Don haka nake ƙara baku haƙuri ba lallai ku riƙa jina kullum ba sai in Allah yasa na samu lokaci

Matar Rasheed ❤️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*87*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Kuma ina ƙara yiwa Allah godiya daya lalata Abin ba tare da nima na cutar da wani ba, kin cuceni! kin cuci Rahma, kuma duka akan Abinda Allah be haramtaba, daga baya kuma kika maida kiyayyar taki kan me sunan mamana.
Tunda Madina ta buɗe ido a cikin duniya take cikin kuncin rayuwa, Abin be tsaya nan ba har saida kikasa ƴan uwanta na jini suma suka tsaneta, yanzu to wa gari ya waya..? Waye ya koma Abin tausayi kuma abin ƙi ga kowa? Ke kanki kinsan idan ƴan Uwanki sukasan da wannan maganar to kin zama Abin gudu, babu wanda zai yarda ki raɓe shi.

Waigowa yayi ya kalli ummin Nawaz sannan yace "wai ko Rahma kinsan cewa ita tasa akamin asirin da zai tafi da hankali na yasa na manta komai da kowa? Sannan bata tsaya iya nanba saida tasa aka min shashatau akan ku ta yadda zan watsar da lamarin ku baki daya! Kuma fa wai duk hakan akan kishi tayi shi?"

"Kayi hakuri ranka ya daɗe! (Dama tun tuni haka take ce mishi), nidai na yafe mata kuma zansa Nawaz ta yafe mata, sannan kaima ina rokonka Alfarma akan ka yaf........"
"Dakata Rahma! Wai ke kuwa wace irin zuciya gareki wadda bata fushi? Ni dai bazan iya yafewa ba, idan ma na yafe to taje na saketa domin bazan iya ci gaba da zama da ita ba"

"Innalillahi wa'inna alaihi raji'un, haba Abban Nawaz meyasa zaka yanke hukunci cikin fushi, ya kamata ace ka samu lokaci kayi tunani tukun kafin kace komai game da wannan maganar"

"Wane tunani kuma zanyi banda wanda nayi a baya? Ai iya tunanin da nayi da ƙuncin dana shiga sun isheni, Kuma Ni Sam ba'a cikin fushi nakeba, domin da a cikin fushi nake Wallahi zan iya rufeta da duka har saita dena motsi, Rahma wai ko kinsan me na gani?, Kinsan halin dana shiga? Kisan irin ciwon da zuciyata ta ƙunsa? Haka fa rayuwata ta koma banida maraba da mahaukaci, in banda Allah ya haɗani da malamin kirki mutumin ƙwarai, wanda yasan meye malinta kuma yake amfani da ilimin da Allah ya bashi wurin temakon al'umma da yiwa addini hidima, shine fa ya tsaya tsayin daka sai daya karya duka sihirin data yi min, amma ai da tuni na dade ta fara hauka tuburan"

"Abban Nawaz don Allah adena tone tone, muma masu laifi ne a gurin Ubangiji, ya kamata ka yafe mata dalilin hakan sai Allah ya ƙara shiryata kuma kaima ya yafe maka."

Umma wadda tunda suka shigo bata furta komai ba illa hawaye da yaketa kwarara daga cikin idonta, bata taɓa jin kunya da nauyi irin na yau ba, lokaci ɗaya tsana da ƙyamar kanta da ayyukan ta suka saukar mata, nadamar da tafi wadda tayi a baya ita ta cika cikin ƙwaƙwalwarta.

Sosai ta ƙara fashewa da kuka jin irin kalaman da mijinta keyi akanta, lallai ta tafka babbar asara a rayuwarta, yanzu bazata iya nuna wani abu me kyau da zatace itace ta aikata shiba domin kiyamarta, gaba ɗaya ta shagala da duniya wadda kuma ba matabbata bace.

Cikin gunjin kuka tace "Muhammad Nagode maka sosai, Allah ya saka maka da Alkhairinsa, kuma hukuncin daka yimin wallahi na chanchanci fiye da haka, amma Nasan adalcinka ne yasa haka domin Ni shaida ce akan kyawawan dabi'un ka .... Nagode sosai sosai, amma ina ƙara baku haƙuri dukanku musamman Rahma da Nawaz, na cutar dasu iya karfina, sannan mama (tana nufin mahaifiyar Abban Nawaz) sai kai, Don Allah ku taimakeni ku yafe min dukda cewa banida tabbacin cewa Allah zai yafe mini"

Da sauri ummin Nawaz ta katseta da cewa "A'a umma kidena cewa haka! Domin wallahu gafurur Raheem,"

Abban Nawaz ne yayi saurin katse ummin Nawaz da cewa "kuma shadidul iqab ba"

Ƙara rushewa da kuka umma tayi tana girgiza kanta cike da nadama da dana sani!

Sallamar inna talatu (kawar ummin Nawaz wadda Nawaz ta gudu gurinta) ce ta cika tsakar gidan..

Jikin ummin Nawaz ne ya hau rawa sanin cewa talatun ta dawo da Jamila ne, saboda sanda zata tafi maiduguri gaisuwar Aayaan, (lokacin da aka ce ya mutu) takaita can don bataso masu zuwa gurin umma su ganta da ciki, domin abin har Ita da Nawaz zai yiwa illah.

Da sauri ta tashi ta fita daga ɗakin Umma ba tare data nemi izinin kowa ba, da ido tayiwa jamila nuni akan ta shige dakinta, "Rahma ki barsu su karaso Kawai domin abinda na shuka shi nake girba, shine fa mahaifinta to boye boyen me za'a yi?" Abinda Umma tace kenan bayan ummin Nawaz ta fita...

"Meye boye boye? Kuma meye Abinda kika shuka?" Abban Nawaz yace tare da ɗaga labule don ganin su waye a tsakar gidan

Wani irin sarkakken tari ne ya sarƙe shi sanda ya sauke idonshi akan Jamila "innalillahi wa'inna alaihi raji'un, Yanzu yata ce dauke da cikin shege? Ko aure tayi sanda bananan?"

Kowa shiru yayi an kasa samun wanda zai bashi amsa, illa Umma data goge hawayen idonta taci gaba da cewa "Ni Nasan da wuya idan Allah zai yafe mini, barakar dana jawo da gurɓata abubuwan da nayi sunyi yawa"

Be tanka ta ba illah janye jiki da yayi ya shige kuryar dakin ummin Nawaz sannan yasa sakata ya rufe kofar.

Bakin ciki ne fal zuciyarshi yana taradadin meye ma ya hadashi da umma da har yayi sha'awar aurenta?

Ummin Nawaz kuwa jinta takeyi Komai ya dagule mata, Ummah kuka jamila kuka, shikuma ya shige ɗaki ya kulle,. Bata gama wannan zancenba saiga fauziyyah ta shigo da sallamarta a bakinta.
Turus tayi ganin yadda Kowa yayi tsuru tsuru, kallon ummin Nawaz tayi tace "Ummi meye ya faru?"

Kafin ummi ta furta komai umma tace "Mugun Abin dana aikata shi ya dawo min kuma nake amsar sa koda ban shirya ba, Abban ku ya dawo kuma yace na tafi gidan mu, sannan yaga cikin dake jikin Jamila

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Yana mikewa daga sujudar ya ƙarasa gaban Nawaz, haɗe hannuwanshi cikin nata sannan ya fara magana kamar zai fashe da kuka "dear Nagode, Nagode, Nagode sosai Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, kin bani farincikin da ban taɓa zaton Akwai koda rabin shiba cikin duniyar nan, yanzu kuma ga wani, dama ashe little Aayaan ɗin mu yana raye?" Ɗaga hannuwanshi yayi sama tare da cewa "ya Allah Nagode, Alhamdulillah ala Ni'imatullah," sauke hannuwanshi yayi yana kallon Dr Uthman wanda Fuskarshi ke kunshe da wadataccen murmushin taya abokinshi murna.

"Old friend murnar ta isa haka, pls a ɗauki madam aje a cigaba da kula da ita, Nasan kasan duka Abinda Ya dace, so kaga ba saina ɓata bakina ba"

"Hmmm Nagode Uthman! Agaida min da Madam da mama, kace in'sha Allah zan shigo na gaisheta," ƙarasawa yayi gurin Nawaz be jira komai ba ya sunkuci kayarshi yayi waje rungume da ita, ko a cikin motar ma rabin jikinta na cikin jikinshi.
Kasancewar itama Nawaz ɗin ba daɗin jikinta take ji ba saboda ga jirin har Yanzu be sake taba, ga heartburn da faduwar gaba, sai hakan yasa batada wani karsashi, shiyasa ma ta zubawa Aayaan ɗin idanu yake Abinda yaga dama.
A motar ma be barta ta huta ba, sai lissafo mata abubuwa yakeyi yana cewa zataci, sai dai ta girgiza mishi kai alamun a'a.

Da taga bafa zaiyi shiru ba saita yanke shi da cewa "kaza zanci da yoghurt da ice cream sai kilishi"

Jin tayi magana sai yaji kamar an mishi bushara da gidan Aljannah, sauri ya ƙara don ya isa restaurant ɗin da yake ganin ya dace da abubuwan da yake da bukata.

Da kyar ya fita ya barta ita kadai a cikin motar, shi a nashi da akwai hali goyata zaiyi ya tafi da ita, cikin ƙasa da minti goma sai gashi riƙe da manya manyan shopping bags guda uku, back seat ya zuba su sannan ya shiga driver side ya cigaba da tuƙi, Allah Allah yake su isa gida domin yaba Mummy da Aseey Labarin ashe little Aayaan Yana nan.

Dakyar yayi parking ɗin motar sanda suka iso gidan tsabar zumudi, buɗe gefenta yayi ya sunkuceta duk uban Mutanen dake cike a harabar gidan be damu ba, cikin usulin main falour ya nufa ɗauke da ita, wasu dasu kasan Abinda Ya faru ne suka fara tambayar shi "ya mai jiki?"
"Da sauƙi" yana ci gaba da durfafar faloun, cikin Sa'a kuwa babu wasu mutane masu yawa, mummy ce sai Aseey sai muhsien sai Colonel da wata kanwar marigayiyar da yayar Colonel, sai wata Yar dattijuwa wadda ba yace wacece ba.

Yana karasa shiga ya kwantar da Nawaz a saman three sitters sofa dake facing ɗin Mummy, gyarata yayi sai kace wanda ya kwantar da jinjiri yana tsoron kada ya fado ƙasa "Mum and Dad please ku tayani murna" Sosai sunan da Aayaan ya kirasu dashi ya dake su, Colonel addu'a ya hau yi a cikin zuciyarshi kan Allah ya tabbatar da hakan, ita kuma Mummy ji tayi zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, Cikin rashin Sa'a kowa ya saci kallon kowa ai ko sai suka haɗa ido, da sauri Mummy ta kauda kanta Saboda wani kwarjini da taga idanun colonel sunyi mata.

"Son bakada hankali ne anyi rasuwa ko uku ba'a yiba zakazo kana cewa a taya ka murna?" Cewar Mummy Wadda ta faɗa da biyu ne, tana nufin kada ma colonel ya soma tunkarar ta da wani zancen yana sonta zai aureta.
Chapter 104 · 0% Book details