← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 112

Sashe 84

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah Maman sudeis da Fatima kuyi haƙuri, Wallahi zan gyara kuma In'sha Allah harshi saina nemi daya yafemin, amma Idan kukace babu ku babu ni ya kukeso nayi a ƙasar nan? Don Allah kuyi haƙuri"

"Munji amma gaskiya mu muna nan akan bakar mu har sai munga chanji tukuna, idan bamuga chanji ba to kada ma ki tunkaro mu don bazamu riƙa kula wadda Allah ke fushi da itaba.

" Yanzu dai ɗebo mana maganin mutafi tunda dai mu munsan daraja da martabar mijinmu" cewar Maman sudeis tana daɗa yin miri-miri da ido.

Simi-simi Nawaz ta fita zuwa store inda Aayaan ya ajiye mata kwalin magungunan, babban mazubi ta samu ta zuba musu da yawa sosai, duk sunsata a vibration tama rasa meke mata daɗi.

A chan ɗakin kuma Nawaz na fita Fatima ta tuntsire da dariya "kai Gaskiya Maman sudeis bakida dama, ji yadda kika hargitsa ƴar mutane!"

"Haba Fatima ai gyara nayi, kuma naga ke kika bani himma ma akan yin gyaran, ya za'ayi mutum yana mata wahala kamar bawa amma ace babu ta inda yake samun relief daga gareta, kinsan Allah tsoron Allah nema ya mishi yawa amma da ba haka ba.
Yadda muke a ƙasar nan ta Nasara da ba sai dai ya riƙa leƙa gidan karuwai ba, wasuma fa kina kallo da matan nasu har biyu ko fi ma amma suna bin matan banza.

Kama haɓa Fatima tayi tare da jinjina kai Sannan tace "gaskiya ne fa wallahi, Allah dai ya duba yasa ta gyara"

"Kima barni da ita zataci ƙwal ubanta ne, da kanta zata nemeshi idan taji wuya"

Fatima zatayi magana Nawaz ta dawo, miƙa musu package ɗin tayi "gashi"

Mazewa Maman sudeis tayi ta amshe Tare Da cewa gobe kisa ya kawoki gidana ki amshi wani magani, Nasan zai taimaka miki sosai, idan ma dai wani ciwon ke damunki ke koma aljanu ne duk Allah zai warkar miki dasu Idan kika fara sha"

"To Nagode sosai, sai mun zo In'sha Allah "

Fatima ce tace "Ni kuma inaga sai jibi idan mun haɗu a school"
(Dayake Makarantar kwana hudu ce, monday zuwa Alhamis ne akeyi musu karatu, juma'a asabar da Lahadi kuma Babu, saboda masu zuwa wajejen Addini)

"To Allah ya kaimu lafiya" cewar Nawaz tare da ɗaukar doguwar riga a Saman kujera tana sawa don ta rakasu zuwa ƙasa..

Koda ta raka su, wani me cab ne ya karaso kusa dasu ya gaishesu tare da cewa "Captain yace a kaiku duk Inda zakuje"

Kallon Nawaz Maman sudeis tayi ta balla mata harara sannan tace "mijin marainiya kenan! Idan ya mutu lokacin zaki san meye duniya"

Cikin motar suka shiga ita kuma ta koma ciki, zuciyarta fall tunani kala kala.

Maman sudeis ce tace "driver kaimu Lacosté pharmacy"
"Yes ma'am" drivern ya amsa.

Dayake chemist ɗin beda nisa sosai cikin ƙasa da minti shabiyar suka kai, ce mai suka yi ya jirasu zasu siyo maganine.

Koda suka shiga cikin pharmacy ɗin direct Wajen keeper suka wuce "don Allah maganin sha'awa nake nema (libido booster)"

"Na ƙarawa ko na ragewa?" Keeper ɗin ya tambayeta

"Na ƙarawa, inda halima inason me mugun ƙarfi ne"

"Okay to Akwai duk kalar da kikeso" miƙewa yayi ya ƙarasa gurin canter ɗin dake zagaye da pharmacy ɗin.

Wata madaidaiciyar roba ya ɗauko a gefen wasu magunguna ya mika mata.

Dan duddubawa tayi sannan ta bashi kuɗinshi ya basu receipt suka fito.

"Maman sudeis kada dai kice wannan shine maganin da kikace Nawaz tazo ta amsa gobe" Fatima tace tana zare ido.

Basarwa maman sudeis tayi tare da cewa "shine mana, amma zan chanza mishi mazubi kuma zance kada ta bari oganta ya gani, ko akwai matsala ne"

Kyalkyalewa da dariya Fatima tayi tare da cewa "zanso ace wata ƙawata me suna *Khadija Sunusi Lawal* amma *Seema* muke ce mata tana kusa, Wallahi da kinga tausayi, bazata bari a bata ba, cewa zatayi kada ki bata wai Allah zai tambayeki, kuma ma zata ƙara da cewa idan ke akayi miki haka fa?

Amma da *Safiyyah Hassan (Ummi)* ce da Kinga dariyar mugunta, ai so zatayi ma taga yadda za'a ƙare idan tasha .

"Ke Nifa yau ko *Yaya Muhammad Katsina* ne zaizo kasar nan bai isa ya hana naba Nawaz wannan maganinba" Maman sudeis tace suna shiga cikin motar.

*A Chan Royal Shire Hotel........*

Nawaz ce zaune ta rafka uban tagumi gaba ɗaya Abin duniya ya ishe ta, ta wani fannin su Maman sudeis gaskiya suka faɗa mata, domin a wannan ƙarnin da muke ciki babu namijin dazai zuba miki Ido ya kyakeki ba Tare da yayi miki wani abu ba, kuma ace kalau yake, balle Aayaan kowa ya kalleshi yaga lafiyayyen namiji meji da gwarzontaka.

Hannun Aayaan da taji ya cire mata tagumine yasa ta dawo daga tunanin da takeyi "sannu da dawowa" tace a ɗan firgice

"Bazan amsa ba sai kin faɗa min abinda yasaki wannan tunanin!"

"Su Maman sudeis ce da Fatima suke fushi dani"

"Lalala Gaskiya dole ki shiga damuwa, aminanki ne fa, ke kam me kika yi musu?"

"Saboda Kai ne, amma pls kada ka tambayeni dalili yanzu, zan faɗa maka daga baya da kaina"

"Okay to bazan tambayeki ba amma gobe zamu shirya muje mu basu haƙuri Koh"

"Eh In'sha Allah, thank you"

"Muje muyi wanka lokacin sallah ya kusa, inaso idan munyi Sallah zamuje wani park" Aayaan yace yana daukar Nawaz Tare da ɗaga ta sama.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*Zaria Nigeria......*

Tuni Inna zuwairah ta koma gida domin hassu komai ya koma daidai, kuma Mummy batabar Sarfraz haka ba saida tasa family Doctor ɗinsu yaci mishi sannan kuma yayi mishi bayanai da yawa akan yadda ake bin mace, bawai da garajeba.
Zamansu ya dawo dai dai gwanin sha'awa, don hatta da shaƙuwa sun ƙara fiye da tada, sai dai har yanzu hassu takanji fargaba idan taga ya nufota da bukatar shi.
Duk kwana uku sai sunje gidan Mummy sun gaisheta inda itama Hassu ɗin a wannan Monday ɗin me zuwa Za'a maidata makaranta don har an samu tsohuwar da zata riƙa zama a gidan.
SARFRAZ ba kunya gareshiba dama! don haka shima dagewa yakeyi akan sai hassu ta sake dashi fiye da Yadda suke a yanzu, duk maganar da tazo bakinshi ta Rashin kunya faɗa mata yakeyi, tun tana jin kunya wani zubin ma guduwa takeyi, to yanzu harta dena sai dai tayi Banza dashi.

*Ta ɓangaren Umma kuwa* ta samu lafiya sosai sosai fiye da sanda fauziyya ke kula da ita, domin yanzu ummin Nawaz raba dare takeyi tana yin addu'oi a cikin Garin ganyen magarya da sassaƙenshi wanda take haɗa wa da zuma tana wanke mata ciwon dashi, kuma kullum gidan tsaff yake babu datti domin ciwon ma ya dena wari dalilin ganyen magaryar da ake sa mishi.

Sannan ummin Nawaz ta gyarawa Jamila ɗakin Nawaz ta maida ita chan, sam bata bari kowa ya ganta, domin yanzu ma cikin ya daɗa fitowa sosai Kuma Gashi Yanzu ana Yawan zuwa gidan don ganin jikin umma.

Ko gidan ka Shigo bazaka taɓa cewa akwai mara lafiya ba, Domin hatta da ɗakin umma kamshin turaren wuta yakeyi kala kala..

Ita kanta umman sau uku Ummin Nawaz take yi mata wanka, haka take kullum tsaff da ita, babu me cewa ma tana fama da wata lalura idan ba ƙafar ka gani ba.

Abin duniya ya ishi umma, kullum cikin dare saitayi kuka ta godewa Allah, tana tuba zuwa ga Allah akan ya yafe mata sannan yasa idan ta roƙi ita Rahama ɗin da Nawaz suma su yafe mata, abinda take yi mata ko ɗan uwa wanda suka fito ciki ɗaya da ita yake yi mata tasan wata rana dole saiya nuna ƙosawa, amma ita sam bata nuna wata damuwa kullum ma ƙara zage damtse takeyi

Mummyn Aayaan kam ganin ummin Nawaz bata komaba yasa itama tayi zamanta gidansu SARFRAZ, sai dai lokaci bayan Lokaci tana zuwa gidan su Nawaz ɗin su wuni Tare Da ummin Nawaz ɗin, Dalilin haka ne ma yasa ta Saba da Inna talatu sosai har zuwa gidanta ma yakeyi wani zubin itama tayi mata yini.

*ENGLAND........*

Da sassafe suka shirya don zuwa gidan maman sudeis, sosai Nawaz take farinciki Idan ta tuna Maman sudeis tace zata bata maganin dazai taimaka mata.

Doguwar riga tasa baƙa Sannan ta yafa mayafinta, ita Aayaan yaba motar yace ta tuƙa su yanason yaga ko tana gane abinda yake koya mata (kusan sati ɗaya kenan daya fara koya mata motar, amma da dare suke fitowa saboda titin yafi rashin hayaniya)

Mamaki sosai Aayaann yayi ganin yadda Nawaz ɗin take tuƙin a nutse, ƙarfin halinta yana matuƙar birgeshi matuƙa, kuma hakan yana ƙara sa tana birgeshi sosai.

Har bakin kofar gidansu Maman sudeis ita ta tuƙa Sannan tayi parking, shikuwa Aayaan daɗi ne Kamar zai kashe shi, sai tafa mata yakeyi yana cewa good job my extraordinary wife.

Zama yayi a waje ya jirata bayan ya bata kayan daya saba haɗowa sudeis yace takai mishi saita kawo mishi sudeis ɗin ya tayashi hira.

Aikam sunsha hira ita da Maman sudeis kamar basu bane suka rabu jiya cikin ɓacin rai, koda zata tafi haka ta ɗauko mata maganin bayan ta canza mishi roba tace mata ta riƙa shan guda biyu da safe, biyu da rana, biyu da yammah..

Godiya sosai Nawaz tayi mata tare dayi mata Alƙawarin zata riƙa sha kullum.

Lokacin da Maman sudeis ta rako Nawaz ne Aayaann yake ce mata "mun tuba a yafe mana, bazamu kuma ba duk da bamusan laifin da mukayi ba"

Dariya tayi tace mishi " Babu komai ai an yafe muku, sai dai ku kiyaye gaba..

Koda zasu koma gida ita ta tuƙa su har bakin hotel ɗin su.

Bayan sunje gida ne Nawaz ta samu guri ta ɓoye maganin inda Aayaan bazai ganiba kamar yadda Maman sudeis ta buƙata, amma saida tasha guda biyu.

Ranar monday da kyar Nawaz ta yarda taje makaranta saboda wata iriyar muguwar kasala da take damunta, ga yawan mutuwar jiki kuma bini bini tayita hamma.

Koda taje Makarantar ma babu Abinda ta iya tsinanawa inbanda kwanciya da tayi a saman desk, tayi hamma tare da miƙa yafi sau hamsin, itafa Bama ta gane me ake koya musu sam.
Chapter 84 · 0% Book details