← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 112

Sashe 15

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

dariya yayi ya rungume mum "whoooooah saini sweetien mamanshi nagodema Allah daya bani Ke a matsayin mahaifiya.....

tashi Yayi "mum bari na koma gurinta, sai ince tashigo d'aki kafin dad ya dawo,

mum tace "kada ka damu yau zanyi wa dad dinka maganarta, kaga koda ya ganta babu Matsala....
murmushi yayi "to mum nagode, bari naje.....

fita daga d'akin mum yayi yanajin gaba d'aya Allah ya yaye mishi damuwarshi.

a sofa ya ganta zaune ta tasa uban awara tayi Tagumi,
harya karasa gurinta bata San yazoba.

ta'ba hannunta Yayi, firgitgit ta dawo hayyacinta "murmushi yayi mata "ya akayine?

chino baki tayi Kamar zatayi kuka "bakai bane Daga nace maka zanci awara shine zakaje ka kwaso min duka awarar nan sai Kace Wanda mutum ishirin zasuci.

yanda tayi maganar ta burgeshi, "okay to yanzu ya kike ganin za'a yi?

"ni naci guda Hudu kuma na koshi, yanzu kaima kaci idan ka rage kuma kasan zata lalace.

"A'a sai dae muci tare domin guda Hudu tayi miki kadan, yanzu ki kara nima kuma zanyi taci har saina koshi.....

murmushi tayi"dagaske kaima zakaci?
"Eh zanci duk da dai ban ta'ba ciba nasan zan iyaci saboda Ke.

d'aya ya dauka ya gutsiri kad'an, Ahankali yake taunawa, dakyar ya hadiye domin ji yake kamar ƙwai amma wani iri.

tausayi ya bata "dena ci kada kayi amai, bari na kara guda biyu Sai asa sauran a fridge, gobe sai aba almajirai tunda kaga bananan.
amma kuma gaskiya idan na kuma cewa ka siya mini abu kada ka siyo Mai yawa, domin asara batada dad'i kuma babu kyau zubar da abinci.

to Insha Allah zan kiyaye, sannan kuma ko wannan awarar da kika gani ba siya nayiba kyauta Mutumin ya bani .

in an amazed tace "kamarya kyauta?

Tashi Yayi ya zauna a kusa da ita ya dau awara guda daya ya nufi bakinta dashi "kedai bud'e in baki idan kin koshi zan baki labarin abinda ya faru duka,
Bud'e bakin tayi ta gutsuri kad'an, be dauke hannunshi ba Yana cewa "ki kara mana..
dad suka gani akansu tsaye,
murmushi dad yayi "A'a sannunku da dare, SARFRAZ bakuwa mukayine?
SARFRAZ Yayi murmushi "Eh dad ai tun tunima tananan,
Ita kuwa Nawaz ji tayi Kamar ta zabga ihu, saboda wata irin kunya data kamata.........

OUM AEYMAN CE.........*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 17*

✍🏻written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji (*Matar Rasheed*)

Supreme writers association..... (SWA)
we write with the ink of era... That's era is our ink...

We satisfy, entertain and touches our readers mind....

Saboda wata irin kunya data kamata.

D'aki dad yawuce, da sauri SARFRAZ ya Mike ya shiga d'akin mum....

"mum wallahi yanzu dad ya dawo kuma ya ganni inaba Nawaz abu a baki...

"wallahi SARFRAZ gaba d'aya kazama mara kunya cewar mum tana hararar shi.....
Ni wuce ka fita ka bari guri.....

Sime Sime ya fita, bega Nawaz a inda ya barta ba, dube dube ya farayi Yana tunanin ina ta shiga......

Motsi ya jiyo a kitchen, nan yagane tana ciki,.
Shiga kitchen d'in Yayi "malama kin koshine?

Kallonshi tayi kamar wadda aka ce babanta ya mutu
ba'a saniba, namma kabiyonine ka bata min sunan?

Cikin damuwa SARFRAZ yace "menayi kuma malama?

Ba'a saniba, kuma Insha Allah gobe karfe shidan safe nabar maka gidanku inyaso duk abinda zakayi sai kayi.....

Sanda zaka bani warar Kamar kada na Amsa, Amma sai naga idan ban amsaba Nayi maka wulakanci....

kuma kaga tawowar daddy maimakon ka Dena bani amma sai ka'ki fadamin yazo...

Ayyah "wallahi malama nima bansan sanda dad ya shigoba, wallahi sanda kika ganshi nima lokacin naganshi.... Na rantse da Allah

kinsan nima bazan so hakaba, ai babu dad'i, Dan Allah kiyi hakuri...

Kallonshi tayi, naji! zanje nayi wanka na shirya, inaso nayi barci.....

To muje d'akin mum domin ta tafi d'akin daddy.... Cewar sarfraz yana murmushi...

Gaba tashiga yabi bayanta, har bedroom d'in mum ya rakata....

kama kwankwaso tayi "to katafi nagode saida safe,...

murmushi yayi "to Allah ya tashemu Lapia, sannan ya Mike ya fita parlour....

inda ta ajiye doguwan rigar da Mum tabata ta Duba, nan taga panties da ragowar pads dinta..

cire kayanta tayi sannan ta daura towel ta shiga bayin,

tafi Kusan minti ishirin tana wanka sannan ta wanke pant dinta da skirt, tayi disposing d'in pad d'in data cire...

wani towel taga anyi hanging, shi tajanyo ta tsane jikinta dashi, sannan tasa sabon pad Ta fito daga bayin....

Gefen gado ta zauna tayi shiru, na Kusan minti uku, sannan ta Mike...

Gaban dressing mirror Ta karasa Don shafa lotion......

motsi taji a bayanta, koda ta waiga bataga kowaba... juyawa tayi ta dauki cocoa butter ta fara shafawa a fuska sannan hannu.....

SARFRAZ dake la'be Bayan labule yabi bayanta Wanda gashi ya barbaje da kallo.....
dai dai nan ta Fara shafawa a cinyarta, tadanyi sama da towel d'in

duk abinda take SARFRAZ Yana Kallonta,
jiyayi tsigar jikinshi ta fara tashi "meyasa nashigo d'akin nan? Ina zaune Lapia zan tayarwa da kaina hankali.....

gaba d'aya ta tattare towel d'in a kwankwasonta tana shafawa a duka cinyarta....
Gaba d'aya mood d'in SARFRAZ ya chanza, haushin kanshima yakeji....
Mikewa Yayi ta nufi inda doguwar rigarta take, dai dai santar inda SARFRAZ yake a la'be.....

rigan ta dauka ta juyata daidai, Hannu tasa zata zare towel d'in, da sauri safraz ya rufe idonshi domin a halin yanzu shiyasan irin abinda yakeji.....

rigan tasa sannan ta koma gurin mirror d'in, taje kanta tayi sannan tayi parking dinshi in a Messy bun...

turare ta fesa kad'an sannan ta dauki karamin gyalen rigar ta yane kanta dashi....

cire zanin gadon tayi ta karkabe, sannan ta mayar tayi tucking dinshi....

Hawa gadon tayi "mtsews ace mutum ya nemi wayarshi ya rasa, fisbilillahi yanzu da tananan ai da Nayi game yanda banajin barcin nan....

shiru tayi tana tunani, can kuma tace "wai Anya SARFRAZ dinnan kanshi d'aya?
Nidai Kamar mai aljanu, inba mai aljanuba, kawai saika dauko Mace ka ajiye ta a gidanku kana mata hidima.....

amma nasan jininmu ya hadu domin wallahi da Wanine yakemin abinda SARFRAZ yakemin da yasha wahala wallahi....

Jifa irin tambayoyin da yakemin "yaya ake wankan janaba?
Yaya ake kwanciya da Mace?
Wace macece tafi dad'in muamula?

wallahi nidai wadannan tambayoyin na gwammaci na mutu bansan Amsar suba da in yi tambaya akansu....

Itama mamanshi ta yarda Dani daga zuwa, da ace ni mayya cefa?

uhhmm koda yake gobe dai zan tafi in huta da farintar SARFRAZ....

dariya ta kyalkyale da ita "oh shima harda zuwa gidanmu, ita kuma umma harda yin ba'kin ciki batasan ma karamin yaro bane....

Duk wannan sambatun da takeyi SARFRAZ Yana jinta, Abu d'ayane ya dameshi, jinshi da yake Kamar bashiba ga wani nauyi da idonshi ya mishi yana jinshi Kamar d'an Maye, photon jikin Nawaz ne yaketa mishi yawo a zuciya....

Gashi ya gaji da tsayuwa, so yake ya samu ya kwanta inda hali ma ya kwanta kusada Nawaz....

Adduar kwanciya barci ta karanta sannan taja light duvet ta rufe jikinta ta d'ora kanta a pillow.

a hankali sarfraz yake tafiya yanaso ya fita a dakin domin halin dayashiga komai na iya faruwa "he's totally in need of her"

Yana bakin kopa Yana tunanin yanda zai bud'e kopar ya fita, yaji motsin Nawaz...

Dube dube takeyi akan gadon domin ji tayi Kamar abu yana yi mata yawo a jiki,
Bataga komaiba ta koma ta kwanta...
kwantawarta keda wuya taji ana yi mata tafiya a gadon bayan ta.
da sauri ta mi'ke tahau zazzage rigar tana bubbuga kafarta.....

tsaka ce (gecko) 🦎ta fado daga cikin rigar, aikuwa da gudu tayi hanyar Waje Tana ihu, tana kokarin bud'e Kopa taji ta kuma ta'ba abu Kamar mutum...
nan takuma dagewa zata zabga wani ihun
Da sauri SARFRAZ ya fito fili had'e da toshe mata baki..

Ganin SARFRAZ ne yasa ta karasa kusa dashi ta rungumeshi tana maida numfashi.

sosai ta kamkameshi jikinta sai rawa yakeyi..

cikin wata irin kasalalliyar murya yace "meya farune?

muryarta na rawa tace "tsaka ce ta shigan mini cikin Rigaa.

Nidai Don Allah ka fitar Dani Daga nan tsoronta nakeji sosai...

Lumshe idonshi Yayi ya dad'a rungumeta, a tunaninshi zai samu sauki Amma Ina jiyake abin Yana dad'a karuwa Kamar ana zuba fetur a wuta...

cikin muryarshi dashashshiya yace "sakeni kigani,

A hankali ta sakeshi, aikuwa tana sakinshi yayi Waje da gudu, itama da gudu ta bishi ta rungumeshi Ta baya tana cewa "Don Allah sarfraz kada ka gudu ka barni wallahi tsoronta nakeji hadda hawaye a fuskarta....

ganin yanda hankalinta ya tashi yasa SARFRAZ yace "to shikenan kada ki damu zauna anan inje dakina in dawo...

ai kuwa jin haka yasa ta dada kamkameshi nidai A'a Don Allah muje tare zan rakaka....

"Nawaz ki sakeni! Da kinsan halin danake ciki da ko kusa Dani bazaki matsoba.

"Eh naji nidai ko wane hali kake ciki naji zan bika... Don Allah...

bece komaiba ya Fara tafiya, binshi takeyi domin hannunta Yana sargafe a kwankwasonshi ..

Suna shiga d'aki ya fad'a gado Yayi ruf da ciki yana mutsu mutsu.....
hankalin Nawaz yayi mugun tashi ganin yanda sarfraz yakeyi...

Kusa dashi ta karasa "meke damunka?
Dan Allah ka fad'a min...

Ahankali ya bud'e ido ya kalleta '' "cikina Nawaz zan mutu, don Allah ki kiramin mum" hankalin Nawaz ne ya dada tashi, gashi kuma yace zai mutu...

Wayar ta dauka ta gama dubawa amma babu mum a sunayen..
cemai tayi dame kayi saving d'in number?

Ahankali yace "my World "
dubawa tayi tayi dialing da sauri, amma sai taji wayar a kashe....

cewa tayi wayar mum a kashe take yanzu yaza ayi?

bata gama rufe bakiba ya janyota ta fada jikinshi ya rungumeta da karfi

Laluben bakinta ya farayi.........

ink d'ina ya kare 🖊

Kubiyoni donjin nawaz kuwa tana kubuta a hannun oga SAFRAZ???

*MATAR RASHEED CE.....*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 18*

🤳written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji

Supreme
Writers
Association
We write with the ink of era.....
That's era is our ink....
We satisfy, entertain and touches readers mind.....

Laluben bakinta ya farayi,
Mai kuma ya tuna Oho, sai ya fasa......

Nawaz data ke kokarin kwace kanta tana rayawa aranta cewa "wai meke damunshine? Ji yanda jikinshi Yayi zafi, sannan ya wani rungumeni salon mamanshi ta shigo ta zata ni yar duniya ce....
Nasan kuma shi cewa zaiyi besan sanda ya rungumeniba....
Chapter 15 · 0% Book details