← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 112

Sashe 81

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun gama wayar ne Amma take shaidawa Mummyn SARFRAZ da Mummyn Aayaan Abinda ya faru.

Mummyn SARFRAZ daɗi ne ya rufeta sosai, har ji takeyi kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha saboda farin ciki, take ta tuna labarin da Nawaz ta bata na irin cutarwar da Umma tayi musu, daga ƙarshe ma duk cutarwar bata yi mata ba saida ta sa yan shaye-shaye suyi mata fyaɗe, dabadon Allah ya kare taba da yanzu ba'a san a Wane hali takeba.

Sosai Mummyn Aayaan taketa jimami, wayarta ta ɗauka don kiran Aayaan ta sanar dasu, aikam babu shiri Mummyn SARFRAZ ta hanata "kada ki kira yara suna can suna farin ciki ki tada musu da hankali akan wata muguwa chan"
Buɗe baki Mummyn Aayaan tayi tana mamakin kalaman Mummyn SARFRAZ, "tabbas nasan zakiyi mamakin maganganun dana faɗa, amma zaki dena mamakin muddin na feɗe Miki biri har wutsiya"
Tsaff Mummyn SARFRAZ ta kwashe komai data sani game da umma ta faɗawa Mummyn Aayaan, "girgiza kai kawai Mummyn Aayaan takeyi don tama kasa magana, jin Abin takeyi kamar almara, "lailai Akwai mugaye a duniya" abinda ta iya faɗa kenan.
"Don Allah gobe da safe mu shirya muje inaso inga idon mara imanin"
"To kada ki damu In'sha Allah da sassafe zamu shirya muje tare dasu Amma kafin su tafi" Cewar Mummyn SARFRAZ

Achan gidan su Ummin Nawaz kuwa sam bata lura da halin da jamila take cikiba saida ta natsa ta ɗan huta tukuna taga Jamila da ciki riƙi-riƙi...
"Jamila aure tayi bayan mun tafi? Sai kuma tayi shiru data tuna duka dududu watansu nawa da tafiya da har Jamila zatayi ƙaton ciki haka?

Umma na sharar ƙwalla tace "yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba, yarinyar nan a makaranta fauziyyah taje ta tawo da ita da wannan ƙaton cikin...

Salati Ummin Nawaz ta Fara tana sallallami, gaba ɗaya ta ruɗe kai kace Nawaz ce ɗauke da cikin "Yanzu Jamila kinyiwa kanki damu iyayenki da ƴaƴanki gata kenan? Bayan dokar Allah da kika keta kin jefa kanki a rayuwar wahala da ƙunci ga tarin zunubai da kika jibgawa kanki, to yanzu yakike so ayi, me kikeso muce wa shi Abinda zaki haifa, bayan haka ma shi meye makomarshi a idon duniya??

Fashewa da kuka Jamila tayi tana girgiza kai tare da cewa "nashiga uku, wayyo Allah na, Allah kasa in mutu lokacin dazan haihu"
Toshe mata baki ummin Nawaz tayi tare da cewa " bakida hankali ne Jamila! Meye kike kirawa kanki mutuwa? Ba gara ki rayu ba kiyita neman Allah ya yafe miki ba"

Umma ma kuka takeyi kashirɓan tana danasanin lalata rayuwarta da tayi, tunda take da ummin Nawaz bazata iya nuna Abu guda ɗaya tace tayi mata shiba, amma duk da haka kishi ya rufe mata ido ta riƙa Neman Yadda zata halaka ta da ƴar ta.
Garin haka kuma ga lalurar data janyo wa kanta....

Sun daɗe Anan zaune ummin Nawaz tace bari taje ɗaki itama ta gyara ɗan abubuwan da ba'a rasa ba, amma idan ana buƙatar wani abu ko kuma umman zata hau poo a kirata.
Dama Inna talatu a ƙage take, suna shiga ɗakin ta fara masifa "gaskiya Rahma bakida zuciya a cikin kirjinki, yanzu fisbilillah duk cin zarafi da cin mutuncin da matar nan tayi miki shine zaki zage kina bauta mata haka? Yanda nayi imani da Allah haka nayi imani cewa dakece hakan ya faru dake dariya zatayi, ƙilama saita zuba ruwa a ƙasa tasha saboda farin ciki.

"Haba ƙawata, aini duk abinda kikaga ina yi mata to inayine saboda Allah da kuma saboda mijina Muhammad, kuma ai zaman tare ya wuce komai, naga koda a gidan haya muka haɗu zan iya yi mata ma Abinda yafi haka balle kuma Wadda muka haɗa miji"

"Lallai Rahma! Wallahi zuciyarki mai kyau ce, Allah ya ƙara miki haƙuri da kyawawan ɗabi'u"
Murmushi ummin Nawaz tayi tare da cewa "Ameen" sannan ta maida kanta taci gaba da kakkaɓe ƙurar da take kakkaɓewa.

"Kafin isha'i nakeso na tafi gida" cewar inna talatu

"To bari muyi Sallah saina rakaki, ai wallahi kimmayi ƙoƙari sosai, Nagode Allah ya bar ƙauna da zumunci "

"Ameen" Cewar inna talatu itama ta miƙe tana gyara wasu abubuwan

*England........*

Koda suka tashi daga barci dare ya riga da yayi sosai, Aayaan ne yace ya kamata su ƙara yin wanka saboda yanaso suje wani store dayayi mata oder ɗin kaya ta online tun suna Nigeria .....

Fir Nawaz tace itafa atafalfal bazata ƙara yin wanka ba, kuma a zancen gaskiya tanaso tayi wankan kawai dai bataso yace zaiyi mata ne..

Tsaff ya gane me take nufi shiyasa shi kuma ya dage akan dole fa sai anyi wankan nan ko kuma ido ya raina fata.

Dataga abin da gaske ne sai kawai tace to ta yarda don alamun su fara nuna mata zata jawa kanta idan bata haƙura da iya wankan ba to zata iya jangwalo me gaba ɗaya.

Tanaji tana gani yanzuma Aayaan ya dage yana mata wanka, rabi taɓe-taɓe rabi shiririta quarter ne wankan, yauma dai kamar kullum Idonta a rufe yake gam.

Tana cikin jacuzzi ɗin shima yayi nashi wankan sannan ya nannadota ya fito daga bathroom ɗin, haka ma yanzu duk shi ya shafa mata mai yasa mata undies, duk dai abinda ya kamata haka ya gama yi mata amma koda wasa ta ƙi yarda ta buɗe idonta.

Shikam ko a jikinshi domin nishaɗinshi ma yakeyi.

Yanzu ma yayi yayi ta buɗe idon taƙi, yayi dabarar namma taƙi, ganin bafa zata buɗe ba. Yasa ya ciccibeta ya ɗora saman gado tare da zuge zip ɗin rigar daya sa mata yana ƙoƙarin cire mata bra.
Babu shiri ta buɗe ido tare dacewa "nifa da barci ne ya fara ɗaukata shiyasa banji sanda kake cewa in buɗe ido ba"

"Kin rigada kin makara, domin na kai bango, bazan iya hakuri ba a halin yanzu, i am sorry"

Kuyi hakuri da wannan 🙏🙏

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*70*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Fashewa tayi da kuka tare da cewa "Nidai gaskiya na gaji da garin nan ka maidani gida"
Tashi zaune Aayaan yayi tare da maida mata ZIP ɗin ya rufe "meyasa ba kya son garin nan?"

"Kullum mutum yana daki babu motsin kowa, and kuma Koda na fita ba irin mutanen dana saba gani zan gani ba"

Murmushi yayi "To yanzu dai Nasan daga zuwanmu ba kadaici zallah kikewa wannan ƙorafin ba, tunda har yaushe mukazo da zakice kullum, kawai dai a takaice kice kinaso ki riƙa ganin ƴan Nigeria"

Ɗaga kanta tayi alamar "eh"

"Okay to Yanzu abinda nakeso dake shine ki tashi mutafi store ɗin kinga daga chan ma sai mu tawo da sabuwar laptop Wadda zanyi miki registration a online, gobe saiki fara zuwa"

Zaro ido Nawaz tayi "ina zan fara zuwa?"
"Wata makaranta ce ana ce mata *LIFE SCHOOL* mutane ne kala kala acikin Makarantar, kamar ke Yanzu da kike complain nasan idan kika fara zuwa Makarantar zakiji daɗin ta sosai saboda suna koya yadda zaka zauna da ko wane irin jinsi da yaren ɗan adam, kuma suna koya yadda zaka zama freely ako wace irin ƙasa ka tsinci kanka, ba iya nan ba suna koya kalar dressing ɗin ƙasashen duniya da girke girkensu.
"Hope u're interested?"

Murmushi ne ya kufce mata "yea naji daɗi sosai sosai, thanks alot"

Gira ya ɗage sama "kiss nakeso a madadin godiyar"

"Ni dai Allah zan fasa fitar"

"I'm sorry to, yanzu ɗauko veil a cikin closet ɗin chan mutafi"

"Yaya wai a ina ka samu kayan mata ne? Dazu kasamun wata riga, yanzu ma kasamun wata kuma kace naje na ɗauko veil yanzu.

Gyararriyar ƙasumbarsa ya shafa da hannunshi na hagu sannan yace "yea! Tun kafin mu tawo nasa aka min order ɗinsu a reception sannan aka kawo min su ɗaki aka shirya"
"Kenan wannan ɗakin kane😳😳?

"Yea permanent ɗaki nane duk sanda na sauka a nan ƙasar, gwamnatin Britain ce ta bani shi har sai sanda nayi retire tukuna, idan ma Anan ƙasar na dawo da zama to har saina mutu"

Jinjina kai Kawai Nawaz takeyi tana mamakin Matsayin da akaba Aayaan kuma ba'a cikin ƙasar Shiba.

"Sweetheart muje kada time ya gudun mana, idan muka dawo saiki tambayeni duk Abinda kikeso zan baki amsa In'sha Allah"

Da kanshi ya miƙe ya buɗe closet ɗin ya dauko mata Babban mayafi wanda yake haɗe da ƙaramin hijab, sa mata yayi ya gyara mata Yadda ya kamata sannan ya kama hannunta yace "muje sweetheart"

Binshi ta fara yi ahankali saboda takalmin daya sa mata me uban tsini, hakan da takeyi sai yayi kamar tana yanga ne, card ɗin daya buɗe ƙofar dashi ɗazu sanda suka zo ya kuma sawa a sensor ɗin jikin ƙofar, ai kuwa ƙofar ta rufe ruff kamar ba yanzu suka fito daga cikin taba, button ɗin lifter ya danna ƙofar ta buɗe suka shiga ciki.
Cikin ƴan mintoci suka sauka ƙasa, gani tayi kawai Aayaan ya buɗe wata shu'umar mota ya saka ta a ciki Sannan shima ya shiga.
Mamaki Kusan kasheta yayi, tasan dai tare suka sauka ƙasar nan kuma tunda suka shiga ɗakin be fito ba suna Tare to yaushe ne har ya siya mota kuma?

Gira ɗaya Aayaan ya ɗage mata "Are you surprised? Don't be! Saboda har indigene ɗin ƙasar nan inada shi, kinga kuwa this is nothing Koh?
Ƙifƙifta ido kawai Nawaz tayi tana kallonshi a sace...
Smirking yayi yaci gaba da tuƙi da hannu ɗaya while ɗaya hannun ya riƙe hannun Nawaz yana matsa mata tafin a hankali.
Chapter 81 · 0% Book details