← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 112

Sashe 47

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai dai nan itama Nawaz suka isa kofar gidan aminiyar ummi, sauka tayi ta bashi kudin ya bata chanji sannan ta nufi cikin gidan.
A rufe ta tarar da Kofar Dakin matar, ai kuwa Kamar ta zunduma ihu ta fita da sauri Saboda Kada Mai adaidaitar ya tafi, don idan yatafi zata sha wahala kafin ta samu wata, ai kuwa babu shi a gurin sai dai alamun tayar shi..

Wani dan shaye-shaye ne ya fito daga gate ɗin commercial wanda ke baya, Ganin Nawaz da yayi a tsaye ne yasa ya ƙarasa kusa da ita Yana ciccijewa irin yadda yan shaye-shaye sukeyi, haɗe da yin murmushi "ke cika ya akayi ne? Ko kina buƙatar chaji ne?

Zaro ido Nawaz tayi Sannan ta Fara dana sanin fitowa daga gida, domin gurin da take ko kasheta yayi Babu wanda zai sani

*Wallahi kaina ciwo yake yi, wata me kitso ce tabi da zazzamge mini kai*

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 46*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Ja baya tayi bata Kula shiba, ai kuwa mutuminka sai ya daɗa matsawa kusa da ita "cika ina magana fa amma kin wani shareni"

Sosai tsoro ya kama Nawaz Amma bata nuna mishiba saboda kada yaga lagonta...

Ɗago kan da zatayi taga inna talatu tana sauka a kan machine.

Da gudu ta ƙarasa kusa da ita"inna sannu da zuwa! Na shiga gidan naga dakinki a rufe, Allah ne yayi zamu haɗu...

Shima ɗan shaye-shaye sai yayi gaba abinshi ganin inna tazo, dama don ya ganta ita kadai ne..

Murmushi tayi "yarinyata gaskiya naji daɗi sosai dana ganki, yaushe kuka dawo?

Umminki batace min ga Ranar da zaku dawoba. Inna talatu tace tana sa key a cikin padlock ɗin tana murɗawa, aikuwa Kofar ta buɗe Sannan duka suka shiga ciki.

Bayan Nawaz ta ɗan hutane inna ta kawo mata snacks da drinks donta samu ta ci, bata wani ci da yawa ba saboda zuciyarta na raya mata da kyar Idan inna zata yarda ta Zauna a gurinta ba Tare Da kowa ya sani ba.

Ko Bayan ta gama ci inna tace "Nawaz Yanzu kin Dena zuwa gurina, amma da duk ranar juma'a sai kin zo kinyimin week end.
"Inna kiyi hakuri Wallahi abubuwa ne sukayi min yawa saboda ko kafin mu tafi chan Maiduguri ɗin na samu aikin koyarwa a makarantar HAYATUL ISLAM"

Koda naji! Ai nasanki Akwai Zumunci dole dama akwai abinda ya hanaki zuwa, to ya aikin naki yanzu?

Wallahi yanzu banma san a Wane babi nakeba, don ko excuse ma ban amsa a gurin Malam Abdullahi ba nadena zuwa.

"Oh Nawaz manya, yaushe Ita ummin naki zatazo? Ko zatazo anjima ne saiku koma tare?

To Anan ne Nawaz ta kwashe duka labarinta tun daga kan Ranar da umma ta Turo ayi mata fyaɗe har zuwa yau data gudo daga gidansu Aayaan, Sannan ta ƙara Mata da cewa "kuma inna Gaskiya Ni na kasa gane me Aayaan yake nufi dani, saboda saikiga yanata shishshige min, nikuma banaso gaskiya.

Mamaki ne tsububu a idon inna "Lallai ladidi! (tana nufin umma kishiyar ummin Nawaz)
"Yanzu har rashin imanin ladidi yakai ta Turo Yan iska suyi miki fyaɗe? To ta Allah ba Tata ba, kuma Wallahi munanan zakiga mummunan matakin dazan dauka a kanta...
Dafa Nawaz tayi "kada kiji komai kiyi zamanki anan, "ita Rahma inbanda abinta ai yanzu ne ya kamata ta jaki a jiki saboda ki samu sauƙin abinda kikeji a zuciyarki, amma shine ta sakar wa duniya ke, ba tare data san kosu su waye ba.....
"Ki barni da ita saita kirani tana neman ki Ido rufe tukuna zanyi mata tsiya....

Daɗi Nawaz ta riƙa ji akan ta samu ƴanci Yanzu bamai yi mata dole,

Spare ɗakin da Nawaz take zama idan tazo mata week end nan ta tafi don dama inna cewa takeyi ɗakin Nawaz ɗin ne, ai kuwa a gyare ɗakin yake tsaff kamar akwai me zama a ciki.

Ita kuma inna saita shiga daki ta zauna a bakin gado tana jimamin abinda ya faru, wayarta ta ɗauka ta danna number ummin Nawaz don taji ta bakinta...

Ƙara biyu ana Uku ta dauka "Assalamu alaikum Barka da Yamma ƴar Uwar Alkhairi " cewar ummi tachan ɓangaren

"Wa'alaikumus salaam masoyiyar kwarai! Wai kam lafiya? Naji kwana biyu wayar ki bata shiga idan na kira?

"Lafiya lau Wallahi an ɗan samu matsalar wutar nepa ne, amma an gyara, kuma dama Nima itana neman Yadda zamu haɗu saboda akwai maganganun da nakeso mu tattauna.

"Okay to Ina jinki, fatan dai lafiya?" Inna tace tana daɗa gyara zamanta a saman gadon da take zaune...

"Kinsan anyi bikin Nawaz kuwa? Kuma Yanzu hakama tana tare dasu amma batasan da hakan ba!

😳😳😳 Zaro ido Inna tayi Babu shiri don kalmar tayi mata nauyi sosai, ya za'ayi ayiwa Mutum Aure ba Tare Da Sanin shiba?

"Tsaya ƙawata kidena ma wannan zancen taya za'a yiwa ƴata irin wannan mummunan abin?

Ƙasa da murya ummin Nawaz tayi "wallahi dagaske nakeyi, amma matsalar duk daga gurin baffa ta faro, don zuwa yayi sukayi magana da kakan Nawaz ɗin, wato sirikina, Ni kaina Lokacin na shiga tashin hankali mara misaltuwa amma kinsan dai halin baffa kaifi ɗaya ne baya chanza magana....

"Na fahimceki! To amma meyasa ba'a sanar da ita ba?

Shiru ummi tayi, sai kuma tace "Nima dai na rasa dalili amma Farko baffane Yace kada a bari ta sani..

Nan dai suka tattauna akan maganar sosai, saidai Koda wasa inna bata furta Cewa Nawaz tana gurintaba....

Ko Bayan da sukayi Sallama kasa tashi inna tayi a inda take "ita dai Nawaz haka tata kaddarar take? Amma Wallahi baffa ya bani mamaki ya za'a yiwa yarinya auren Dole kuma ba Tare Da Sanin taba?

Sannan an dauketa an damƙa Musu ba Tare Da anyi Mata wani cikakken gyaran jiki ba, ga mazan yanzu da dambanzan jaraba da fitina, duk kansu a waye yake sun riga da sunsan komai.

Sosai Tayi niyyar zage damtse don gyara Nawaz ciki da bai, kuma bazata bari kowa ya san tana gurintaba har sai sanda ta gamsu ta tsuma ta da kyau da gyara yadda duk jarabar shi saidai yayi ya gama.

°°°°°

Ta chan gidan kuwa, koda Aseey ta fito Daga wanka bataga Nawaz ba sai bata damu ba don a tunaninta ta fita falour ne.
Shiryawa tayi ta fita ta kira su Mummy Don aci abinci, kowa Yana dinning amma banda Nawaz, Mummy ce tace "kije ki kira Nawaz mana! Nifa Kunyar nan ta isheni haka, ace Mutum yayita ƙunshe kanshi a ɗaki bazai fito yasha Iska ba, kuma akan laifin daba nashiba. Amma idan taƙi ki rabu da ita kada ki matsa mata.

Duk inda Aseey ke tunanin Nawaz ta shiga saida ta duba amma ba Nawaz ba alamunta, cike da fargaba ta karaso dining area ɗin tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un wallahi babu inda ban Duba ba amma Babu Nawaz Babu alamunta..

Miƙewa sukayi a tare, kamarya? Ina ta shiga to?
Aikuwa duka suka bazama lungu da saƙo na gidan amma zance ɗaya ne, babu ita.

Sosai suka shiga tashin hankali sunata salati da sallallami, Mummyn SARFRAZ ce tace "to ko guduwa tayi?"

Da sauri Aseey ta shiga dakinsu tana dube dube, sai daga Baya ta fito idonta Duk yayi ja, "Wallahi guduwa tayi! Kuma bata ɗauki komaiba sai wayarta, harta kuɗin da Aayaan ya bata ɗazu da suka yi sallama bata daukaba...

Tare su Mummy suka dada rafka salati haɗe da cewa "ita kuwa ina zata haka, Aseey kodai kinyi Mata Wani Abin ne?

😳😳 zaro ido Aseey tayi "Shikenan kuma!!! Wallahi Ni nasan dama wannan Abin a kaina zai ƙare, ku kanku da muke cikin gidan tare zargina kukeyi balle shi uban gayyar, Allah dai ya fidda Ni.

Mummy ce ta kuma cewa "to koshi ya ɓata mata rai kafin su rabu?

Duk ran Aseey a jagule tace "Ni ban saniba, sannan don Allah taya zakuce ko Wani abu nayi mata? Yanzu Aayaan yanajin wannan Kalmar taku akanta zai tsaya, kuma Mummy kinsan dai Yadda Aayaan yake da tijara idan aka taɓa abinda yakeso...

"Af wato ke Yanzu fushi ma kikayi!? har kinada Lokacin yin fushi ga ƴar Mutane tayi ɓatan dabo.

Mayafi kowa ya ɗauka suka fita cikin layin ko Allah zaisa su ganta ƙilan wani abu ta fita ta siyo, sosai suka zagaya duka layin amma babu alamunta.
Basu suka dawo gida ba sai wajen Biyar saura, a hakan ma don sun gama cire raine, koda suka koma gidan Babu Wanda yabi takan abinci domin yunwar ma nemanta sukayi suka rasa. Iya fargabaar tafiyar Nawaz ce ke musu yawo a kwakwalwar su.

°°°°°

🤣Shi kam Alh Aayaan ana chan ana fama, bai san wainar da Nawaz ta soya taba Aseey ajiyaba😂😂 sai Wajen ƙarfe Shida aka gama taron, Sannan ne yayi hamdala don yasan Yanzu zai samu Lokacin kanshi...

Gurin Colonel yaje sukayi Sallama akan idan an kwana biyu colonel ɗin zaije chan Maiduguri gurinshi, dayake Aayaan ya amshi hutun wata uku da yake amsa duk Shekara.

Mota ya ƙarasa ya shiga Inda securities ɗinshi suka dau hanya, "Daniel idan kaga wani store me kyau kafin mu karasa gida notify me pls"
" Yes Sir" cewar Daniel Yana daɗa zuba idanuwan shi bisa titi.

A daidai *M.R.G Plaza* sukayi parking, Sannan Aayaan ya shiga ciki, gurin ɗan kunne da sarƙa da zobuna ya ƙarasa inda yayi selecting ɗin wasu special na Gold Wanda ya siyesune a Matsayin kyautar da zaiba Nawaz idan yaje gida, tunda yasan ya ɓata mata rai kafin ya fita.... Biyan kuɗin yayi sannan ya koma mota suka dauki hanya, sai kuma suka kuma tsayawa a *A.M CAFE* Inda ya tsaya ya siyar ma MUHSIEN chocolate da ice cream, Basu kuma tsayawa a ko ina ba sai a Kofar gidan su sarfraz Wanda a Yanzu suka yada zango.

Cikin gidan kuwa kowa zaune yake yayi jugum kamar yan zaman makoki, domin Mummy tayi yunkurin kiran baffa ta faɗa mishi Amma Mummyn SARFRAZ ta hanata tace Gara a Bari Aayaan ya dawo tukuna.

Ita kam ta ɓangaren Aseey ba'a cewa komai, tasan Aayaan da ɗaukar zafi kuma ba Lallai ya fahimceta ba, zaune take Kawai Amma zuciyarta sam babu daɗi.
Chapter 47 · 0% Book details