← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 112

Sashe 105

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ile kuwa sakon ya isa inda takeso, aikam colonel na gane cewa dashi take sai yayi saurin cewa "Ai mutuwar wani tashin wani, yanzu dan anyi rasuwa shi kuma sai ya rufewa kanshi kofar farin ciki? Ta riga ta mutu Kuma ba zata dawo ba, Abin da ya rage Yanzu tsakanin mu da ita shine addu'a da fatan alkhairi da dace da kyakkyawan makwanci."

Tsaff mummy ta gane shima ya rama ne, sai ta ƙasa cewa komai illah "Allah ya jikanta yayi mata Rahma"

"AMEEN'' duka suka furta,
"Son meya faru?"

"Dad cikin jikin sweetheart yananan ashe"

Mikewa tsaye Aseey tayi wadda tuntuni take zaune amma bata furta koda a ba.

Ina ji yiwa kowa Fatan Alkhairi
MATAR Rasheed ❤️....*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*88*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

With high excitement tace "bro da gaske cikin yananan?" Gyaɗa mata kai Aayaan yayi haɗe da ɗaga mata gira, Kamar zata faɗi don sauri haka ta ƙarasa gaban Nawaz tana yi mata magana ƙasa ƙasa daga bisani kuma ta fita daga faloun.

"Allahamdulillah ala Ni'imatuka ya Rahman" Abinda Colonel yace kenan fuskarshi cike da matsanancin farinciki.

Itama mummy saida ta kasa boye farincikin ta duk da bata furta komai ba a matsayin ta na suruka, amma daga kalle ta zaka gane tana cikin farin ciki, suma sauran mutanen gurin Sosai suka nuna farincikin su duk da basusan usulin Abinda ya faru a baya ba.

Ita dai Nawaz Duk kunya ta cikata, yanzu kowa yasan ciki gareta bayan kuma kowa yasan Abinda ke faruwa kafin ayi cikin, daɗa rintse ido tayi tana tasbihi Acikin zuciyarta, tunda akace cikin nanan bataji wani Abu game dashi ba sai yanzu, ji tayi dama zata iya ganin waye a cikin nata, amma tasan in'sha Allah mai Albarka ne tunda Allah ya kareshi daga lalacewa.

Aayaan ne ya karaso ya ɗauketa yana fita daga faloun zuwa dakinsu, Babu wanda ya dube shi balle ya tanka mishi tunda sun riga da sun gama gane halinshi (baya iya boye soyayya ga wanda yake so)

Saida ya tabbatar ya kwantar da ita sannan ya fita don ya koma mota ya dauko abubuwan daya siyan mata a hanya.

Naufal ne tare da fudail suka shigo Harabar gidan, alamun kamar daga kasuwa suka dawo hannunsu ɗauke da manya manyan bamboona, tsabar farin cikin da yake ciki yasa be tuna cewa basusan komai game da cikin ba ya tare su yana cewa "My twins kunsan da mukaje asibiti Ashe cikin be zube ba!"

"Cikin wa?" Cewar Naufal yana shafa kai alumun tunani
"Au ashefa baku saniba ba " cewar Aayaan sannan ya ƙara da cewa "dama kwanaki ne mu dear tayi ɓari, to ashe cikin nanan be zube ba sai dazu da mukaje asibiti akayi mata scanning da wasu tests akace yana nan.

Cikin nuna farin ciki afili Naufal yace "masha Allah, Alhamdulillah, Gaskiya naji daɗi, nima zanyi ƙani, idan kuwa mace ce nayi mata wallahi"

Ajiye bamboon Fudail yayi tare da cewa "to sannu ɗan iya, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi! To idan namiji ne kayi aboki idan kuma mace ce nayi Mata"

Dariya Abin yaba Aayaan, "to to to ya isa haka, bari naje nabar auntyn taku ita kadai"

"Okay Uncle sai mun hadu anjima" cewar Naufal yana ballawa Fudail hararara, nanfa musu yaci gaba, shidai Aayaan yayi saurin barin wajen bayan yasa hannu a cikin ɗaya daga cikin shopping bag din ya ciro babban plastic take away guda ɗaya ya mikawa Naufal tare da cewa "for both of you, kuma saura kuyi faɗa! Nasan halinku"

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Anan wajen fauziyyah ta zube a ƙasa tana rusa ihu, Abinda taketa gudu kenan shi yasa koda yaushe takan cewa umma ta riƙa haƙuri akan wasu abubuwan amma taƙi, har gurin bokayen ƙarya ta riƙa kaita don dai taga babu Abinda ke samun su ummin Nawaz kila ta haƙura amma ta ƙi denawa, kullum ƙiyayyar gaba takeyi, itama saida tayi iya kokarinta wajen dasa mata ƙin Nawaz ɗin.
Yanzu fisbilillah kamar ita ace babanta ya saki mamanta? Ai wannan ma babban abin gori ne Wallahi, ga mazan yanzu da Neman ba'asi, Abinda be kai ya Kawo Bama sai suyi maka gori akai, balle Abu irin wannan, barin yanzu ita kanta auren nata girgiɗi yakeyi.

Inna talatu ce ta kama ta ta miƙar da ita tsaye tana bata baki "Addu'a zakiyi fauziyyah ba kuka ba, domin kowa da Irin tashi kaddarar, fatan mu kawai shine Allah yasa muyi kyakykyawan ƙarshe, kuma wannan kukan da kikeyi ƙara tayar mata da hankali zaiyi.

Jamila kuwa ji takeyi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki saboda kunya da dana sani wadda take ƙeya ce, tuna abubuwan da suka faru a baya ta fara yi, lallai umma itama tanada laifi, domin sanda Nawaz ta fara ganinta ta wanda ya banka mata cikin dake jikin ta saida tayi mata magana akan ta dena kulashi saboda kawarta tace mata ba mutumin arziƙi bane, amma umma tace mata ta rabu da ita baƙin ciki takeyi mata saboda ita ba'a zuwa wajen ta, gashi kuwa yanzu ta tabbatar da gaskiyar Nawaz tunda ya haɗa ta da ribar kwaɗayi ya gudu ya bar ta tana ta fama da wahala da kunya da nadama.

Allah sarki, shiyasa hausawa ke cewa kayi mai kyau zakaga sakamako, idan ma ranka bekai ba duniya zata shaida, yanzu babu Nawaz amma Jamila ta tuna cewa taso ta hana rayuwar ta shiga tasgaron da take ciki a yanzu, a yanda takeji ma da zata mutu Lokacin naƙuda da taso hakan.

ummi kuwa bin bayan abban Nawaz tayi tana tunanin ta inda zata bullowa maganar.

Babu irin bugun kofar da ummi bata yiba amma shiru ko motsin shi taki ji balle tayi tunanin zai buɗe, haka nan ta juyo ta dawo jiki a sanyaye, a cikin ɗakin umma ta tarar dasu duka suna zaune, jamila da fauziyyah sunata jan majina, umma kuma kuka takeyi bilhakki, tana ganin shigowar ummin Nawaz cikin ɗakin tayi saurin haɗe hannuwanta guri ɗaya "Rahma don darajar Alqur'ani ki yafe min, kila dalilin haka na samu wani sauƙi a cikin hukuncin da Allah zai yanke min"

"Umma nifa tun tuni na yafe miki, sannan ki dena cire rai da rahmar Allah Domin shi me yafiya ne kuma yana son masu tuba idan sun yi laifi''

"Kaico na!! Dama ace nice me wannan kyakykyawar zuciyar da bata rama sharri da sharri, Rahma kin tsira, kin tsira!" Cewar umma tana kaɗa kai cikin ciwo da tsantsar nadama.

Inna talatu ce tace "Naji daɗi da Allah yasa kika gane kuskurenki tun kafin lokaci ya ƙure miki, yanzu abinda ya rage miki shine kiyi tabbatacciyar tuba me cike da nadama, sannan kisa a ranki cewa bazaki kuma yin wani abu makamancin abubuwan da kika yi a baya ba, to In'sha Allah sai kiga Allah ya yafe miki"

Jinjina kai Umma tayi Sannan tace " yanzu talatu kece kike bani shawara akan yadda zanyi Allah ya yafe Min bayan irin muguwar tsanar danayi miki ba tare da kinyi Min komai ba?, Lallai ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA"

"Umma kenan! Ai kowa da Irin tashi kaddarar, kawai dai abar maganar domin komai ya wuce in'sha Allah"

Ummin Nawaz ce takai dubanta ga jamila daketa risgar kuka bilhakki, ita kuma fauziyyah ta cure guri ɗaya da alamun kukan zuci takeyi wanda yafi na fili illata gangar jiki da ruhi da kuma jidata zuciya, "Jamila ku bar kukan nan haka mana, addu'a ya kamata ku riƙa yi a cikin zuciyarku sai Allah yasa kuji sanyi a ranku"

*Jama'a yau dai dubun umma ta cika*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Koda Aayaan ya koma ɗakin sai ya tarar har Nawaz ɗin tayi barci, zama yayi ya zuba mata idanu yana kallonta.
Murmushi ne ya kufce mishi sanda ya lura da irin haske da taushin da fatarta ta ƙara, Lallai shima ya tafka shirme! Ya kamata ace ya lura da chanzawar da jikinta yayi a Matsayin shi na likita, koda dai ba yarda takeyi dashi sosai ba.
Cikin barcin Nawaz ta juya alamun barcin nayi mata daɗi zata gyara kwanciya, da sauri Aayaan ya kwanta a gefen ta take ƙoƙarin juyawa, tsaff ta shige cikin jikinshi ta cure kamar kwanciyar jinjiri a cikin mahaifa.
Murmushi kawai Aayaan yayi, wai yau shine cikinshi ke jikin Nawaz? Shine zai zama uba nan da wani ɗan Lokaci, ya rasa me yasa duk sanda yaga sauyi a cikin rayuwarshi saiya tuna *sanda ya fara ganin Nawaz a cikin daji wajen ƙarfe biyu da rabi na dare nannaɗe cikin zanin gado.*
Samun kanshi yayi da shafa gefen fuskarta sannan ya furta "I Love You Madinah" a fili.

Ta chan gurin su mummy kuwa Aayaan na fita itama ta miƙe ta nufi masaukinsu domin ita zaman gidan ma ya fara isarta yanzu, har ta kosa ayi Bakwai su koma nasu gidan, kuma ba Komai bane sanadi sai Colonel daya ke ƙoƙarin karya mata zuciya.

Tana tashi kuwa colonel ya kalli Wadda tafi kowa tsufa a gurin yace goggo zuwa injima inaso muyi magana in'sha Allah"

"Kada ka damu ɗan lele, Allah ya kaimu anjimar lafiya"

Sauran ne suka amsa da "Ameen Allah ya amsa"

Murmushi kanwar marigayiyar tayi tare dayin gyaran murya Alamun zatayi magana me ɗan muhimmanci, sai hankalin kowa ya koma kanta "Ni kuwa yaya soja (haka Yawancin dangin shi suke ce mishi) me zai hana ka auri wannan balarabiyar, tunda kaga itama batada Aure kuma kaima yanzu ga taka kaddarar! Ni a ganina gara kuyi Auren sai ya zama duka an haɗu an zama dunƙulallen iyali da ayita zama a rarrabe"

Charaf yayar Colonel tace "Wallahi Nima naga sunyi mugun dacewa, kuma koba haka ba naga akwai sabo sosai tsakanin ta dasu Fudail, sannan shima naga ya saba da nata yaran sosai, kunga ko iya haka ma zai alamta mana cewa za'a yi zaman lafiya idan an haɗu waje ɗaya domin kowa yanason kowa."

Jinjina kai goggo tayi haɗe da cewa "tabbas wannan shawara ce me kyau duk da Ni naga alamar ba Lallai ita balarabiyar ta yarda ba"
"Amma goggo me yasa?" Kanwar marigayiyar tace

"Ni dai a nawa tunanin ne naga Kamar ba zata yarda ba" cewar goggo tana gyara mayafinta daya zame daga kanta.
Chapter 105 · 0% Book details