Sashe 48
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida gudun bugun zuciyar kowa ya ƙaru jin sallamar Aayaan ta karaɗe cikin babban falourn *"ASSALAMU ALAIKUM"* Fuskarshi a sake alamun yana cikin farinciki, a sanyaye kowa ya amsa mishi jiki Babu kwari.
Shikam Aayaan duk bai lura da halin da suke cikiba yace "sannunku da gida mummies da kuma Aunty Aseey! Murmushi sosai yakeyi inda ya karasa gaban Aseey yana ja Mata kumatu "sis yau kuma Babu welcome hug Koh"
Ajiye shopping bag ɗin hannunshi yayi Tare Da cewa "Ga tsarabar passing out na kawo muku, but Bama Wani Abu bane special I think memo ne dasu snacks haka, may be kuma akwai T-shirt aciki....
Yanda yaga Babu wanda ya bashi attention ne yasa ya ɗago da kanshi yana karantar mood ɗinsu "mum meya faru? Ya naganku haka?
Kowa shiru yayi don bayaso aji mutuwar Sarki a bakinshi. I am asking Amma Babu Wanda Ya kulani, wai me ya faru ne?
Muhsien ne wanda dawowarsa daga bathroom kenan yayi fitsari yace "la Uncle ka dawo?
Waigawa Aayaan yayi yana kallonshi "Na dawo muhsien" Aayaan yace yana maida kallonshi kan Aseey "to ke ki faɗa min tunda su sunki cewa komai.
Kwakwalwar Aayaan Saida ta tsaya na ɗan wucin gadi, dalilin Muryar muhsin daya jiyo tace "Uncle Aunty Nawaz ta ɓace, har nemanta mukaje amma bamu ganta ba.
Kafin Wani ɗan lokaci har goshin Aayaan yayi ruɗu-rudu da jijiyoyi _*"shin dagaske baku ga Nawaz ba??????*_ Ya faɗa da ƙarfi har Saida dakin ya amsa.
Namma Babu Wanda Ya Iya bashi amsa sai muhsin daya Kuma cewa "Allah Uncle batanan, babu ita a gidan nan, kuma har waje munje dukanmu Amma bamu ganta ba ta ɓace"
Be kuma Kula kowa ba ya juya da hanzari Zai fita, sai Sannan Mummy tace "Aayaan dawo! Kada ka fita!.
Chak Aayaan ya tsaya a inda yake amma be waigo ba.
"Aayaann ka dawo nace!, Dawowa Aayaan yayi ya tsaya a tsakiyar faloun dai dai saitin mummy, "mummy gani" sannan yayi shiru yana kallonta
"Aayaann inaso ka nutsu ka maida hankalinka waje ɗaya yadda Zaka fahimci me zan faɗa maka, Yanzu idan ka fita ma ina zakaje? samu Guri ka zauna.
Hakanan ya zauna a kan kujera badon zuciyarshi naso ba, sai don kasancewar shi mai tsananin biyayya ga mummy.
Duka Abinda Mummy ta sani Game da ɓatan Nawaz nan ta zayyane mishi komai, ai kawai Sai Aayaan Ya juya ga Aseey.
"Ina matata take? Kada kice zaku haɗa baki Kumin Irin wannan wasan, wallahi i can't endure it! Ni kaina Yanzu na Sani kuma na saduda cewa Nawaz itace raunina!.
Tsalle Aseey tayi ta dire "haba Aayaan kaima kasan bazan taɓa haɗa baƙi da Wani don muyi maka Abinda zai Cutar dakai ba, Wallahi bro bansan inda Nawaz takeba.
Miƙewa Aayaan yayi "Allah ki fito min da matata, ninasan dole akwai abinda ya faru, ko kinyi mata wani abu ne?, Nawaz bazata gudu hakanan ba.
Aayaann abinnan fa ya fara isata, naga Babu yanda banyi akan ku zama intimate ba amma kaƙi yarda wai kai kana sonta kuma kanaso Saida yardarta tukuna..
Aigashinan, Wallahi nasan da ace ka kwanta da ita Babu yadda za'a yi ta gudu! Amma yanzufa? Tanada right a hannunta koda Auren tace batayi kaga dole a rabashi, amma da ka kwanta da ita Babu yadda zatayi dole ta zauna kodon kada ta zama ƙaramar bazawara.
Shiru Aayaan yayi Kawai ya tsaya yana kallon Aseey domin yama kasa cewa komai, Mummy Dake gefe kuma cewa tayi "kinci uwaki aseey, muna gurin nan amma kike wannan fitsarar? Laillai wuyanki ya Isa yanka.
Shiru Aseey tayi domin sai yanzu ma ta lura da ɓaramɓaramar data tafka.
Saida Aayaan ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya Sannan yace"to wallahi Aunty Aseey wannan Maganar ma da kika yi ta daɗa tabbatar min da cewa kinsan inda Nawaz take.
_"Wai mu zama intimate!_ _wai in kwanta da ita! to ance miki Ni namijine?_ _*Toni macene!!!*_ *_i am impotent!!!!_* Kuma dama Ni ban auri Nawaz don ina sha'awar taba, sai don ina ƙaunarta....
Mum kam Kusan suma tayi a tsaye " meyasa Aayaan zaice shiba namiji bane shi mace ne? It means fa gabanshi baya aiki kenan😳 kada fa ace da gaske yake shiyasa all this while yaƙi yarda yayi aure....
Tawowa gurinshi tayi "haba my son! Pls kacemin kaiba impotent bane Please!.
Juyawa kawai Aayaan yayi ya shiga ɗaki batare daya kula kowaba ya Maida kofar ya rufe.
Ni dai matar Rasheed cewa nayi "wanga wace iriyar masifa ce?😳😳 Aayaann ɗinne mace kuma? To duk wanga rusheshen jiki nashi ya tashi ga banza kenan🤣🤣.
Mummy kan faɗi take "lahaula wala quwwata illah billah, ya Allah kasa ba Gaskiya bane, nikam idan hakane ya zanyi da raina?.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Ta ɓangaren SARFRAZ kuma Ganin wasu Masu kiwon raƙuma yayi sunzo wucewa ya bisu yanata kallon raƙuman domin sun bashi sha'awa.
Chan dai Hassu ta fito Daga bukkar da suke dafa abinci taga bata ganshi ba, ɗaki ta duba namma babu shi.
Sai kawai ta nufi tirken shanu don Yawancin lokuta Anan take samun shi.
Abin ya ɓata mamaki Ganin babu shi Anan, miƙar hanya tayi tana kwala mishi kira "SARFRAZ! SARFRAZ!! SARFRAZ!!! Amma ina aiko keyarshi babu.
Ganin da gaske babu shi yasa Hassu ta rushe da ihu tana Bin Hanyar gidan malam tana zunduma ihu......
Namma dai Ni matar Rasheed cewa nayi 😳😳😳 chakwakiya.
°°°
Nawaz kam Saida yamma tayi taji duk kewa ta kamata, ji takeyi ma meyasa ta gudo tunda dai Basu Aseey bane sukayi mata laifi Aayaan ne, take taji bata kyauta ba ko ya Mummy da Aseey zasuyi idan suka buɗe Ido basu gantaba?
Shi kanshi Aayaan ɗin Saida taji kewarshi, hakanan ta kasa sakin jikinta, domma Inna tanata janta da hira....
Himma bata ga rago! Domin inna harta hada Wasu saiwoyi da sassake dasu kayan kamshi da mazarkwaila ta dafa ta juye a bokiti, jira takeyi ya huce taba Nawaz tace ta maidashi Ruwan Shanta....
Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Nifa har na ƙosa naji yadda za'a yi a shafin gaba, domin akwai tirƙa-tirƙa da yawa.
Gashi nan dai Inna harta fara tsuma Nawaz 😂 gashi kuma Aayaan Yace shi macene😳, Toya abin zai kasance????
Shi kuma SARFRAZ yabi raƙuma! Ga hassu na zunduma ihu 😳😳😳😳
Koya Aseey zasu ƙare da Aayaan kuma🤣🤣🤣 shidai ya dage akan saita fito mishi da matarshi...
🧐🧐Anya Mummy zata iya Bacci ma kuwa? Gata mayyar ƴaƴa gashi kuma Aayaan yace babu kayan aiki🤣🤣🤣🤣🤣🤣
Don haka saiku zage kuyi comments da sharhi yadda zanji daɗin kawo shafin gaba, Idan ba haka ba kuma kuji wayam, har sai zuwa sanda naga zan iya turo muku..
*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 47*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Koda Aayaan ya shiga ɗaki kasa zama yayi, yama rasa me zaiyi yaji daɗi! Idonshi gaba ɗaya ya kaɗa ya koma jaa, jikinshi kuma har wani irin huci yake fitarwa.
Bathroom ya shiga ba Tare Da ya cire ko ɗaya daga cikin Kayan jikinshiba ya sakarwa kanshi shower 🚿, yafi ƙarfin minti Talatin a tsaye Ruwan yana zuba a jikinshi Sannan ya samu ya cire kayan yayi normal wanka, babu Abinda ya ragun mishi daga raɗaɗin dayake ji a cikin zuciyarshi illah zazzaɓi da yaji ya rufe shi likaci guda.
Bathrobe yasa Sannan ya fita daga bayin zuciyar shi na tunani kala kala, yama kasa ko shirya wa, ko mai bai iya shafawa ba, komawa kan gado kawai yayi yaja duvet ya rufe jikinshi Sakamakon wani Irin sanyi dayaji yanaji, Sannan ya dau wayarshi wadda ke ajiye a gefe, Number Nawaz ya nema ya kira, Amma sai akace switch off.
Sosai yake mamakin wai me akayi wa Nawaz da har ta yanke wannan tsatstsauran hukuncin? Shi Yanzu ko nemanta zaiyi baisan ta inda zai Fara ba.
Shiyasa yaso sanda Mummy ta faɗa mishi cewa Nawaz matar shice da an sanar da Nawaz ɗin itama.
Gallery ya koma inda ya nuno photon Nawaz ya ƙura mishi ido, "why did you choose to run away? Why did you not think of what will happen before going, how i wish you were here when I'm back..... Haka dai Aayaan yaketa magana shi kaɗai sai kace Nawaz ɗin tana zaune a gaban shi..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sosai Hassu ke ihu tana tafe kuma tana kwalawa SARFRAZ kira ga duhun dare ya fara sauka, saura kaɗan ta ƙarasa gidan baffa ta hango wani Cikin raƙuma kamar SARFRAZ, ai kuwa da gudu ta kwasa zuwa gurin tana kwalawa SARFRAZ kira....
Waigowa SARFRAZ yayi yana dariya "Hassu zo kigansu Masu kyau, mu bamuda irin wadannan sai dai irin su gwalbo...
Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya turniƙe hassu "Wato yanzu da Ban fito ba da Shikenan binsu zakayi, Ni na taɓa ce maka idan kaga Wasu ka bisu koda mutane balle raƙumi!
Saroro SARFRAZ ya tsaya, exactly dai Kamar yadda yara sukeyi idan sunyi laifi, harara ta balla mishi "ba tsayawa zakayi ka zuba min ido ba, daka ɓace daka gane kuranka....
Juyawa tayi ta tafi ba tare data ce zo muje ba, ai kuwa shima saiya bita da gudu yana cewa "kijirani mu tafi"
Hassu da baƙin ciki ya dameta akan Cewa da Yanzu sarfraz ya ɓace data shiga uku duk saitaji haushin shima takeji, ƙin kulashi tayi taci gaba da tafiyarta.
Aikuwa SARFRAZ Yana ƙarasawa kusa da ita ya faɗa jikinta yana cewa "inata cewa kijirani anma kikayi banza dani!
Taga-taga Hassu tayi zata faɗi sai kuwa ya taro ta suka faɗi ƙasa tare yana dariya, Cikin kwayar idonta yake kallo itama Haka, Sanin cewa a Banza "wai an yakushi kakkausa" tasan shi bema san meyakeyiba, ta tashi tana kakkaɓe zaninta.
Daɗa riƙo ta yayi ta faɗo jikinshi yana ƙara cewa "meyasa baki jirani ba?"
"Don Allah SARFRAZ ka kyaleni mana" hassu tace tana tureshi daga jikinta, "kaso ka kasheni wallahi, fisbilillah da Allah besa na fito yanzu ba Shikenan ka ɓata kenan?
"Ni dai Gaskiya har dai kanason in cigaba da zama ƙawarka kada ka kuma bin koma me kagani"
"To bazan kumaba"; SARFRAZ yace yana riƙe hannun Hassu tare da haɗa su guri ɗaya da nashi yana sarƙafe yatsunshi cikin na Hassu, sannan suka dauki hanyar komawa gida.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°