← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 112

Sashe 91

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmmm Madina manya, mu munsan meya saki Barci ne da zamu tashe ki?, muje mu tasheki mu samu zunubi"

"Kai Don Allah wane zunubi kuma" Nawaz tace tana yin hanyar kitchen, sosai ta gyara rafiyarta saboda kada su fuskanci wani abu (Nikam nace hajiya Madina kin makaro, ai duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, balle kuma sun gani da idonsu)

"Bari ko noodles na dafa muku, kuna zaune tun tuni da yunwa"

"Mun hutasshe ki, aimu nan budirinmu mukayi a kitchen ɗin" fatima tace tana tashi don bin bayan Nawaz ɗin, buɗe mata komai tayi.

Mamaki sosai ya kama Nawaz, kuma sosai taji daɗi Don dama wata Irin baƙar yunwa ke sakaɗar ta, godiya tayi ta musu Sannan ta zuba, tumbler ta ɗauka ta zuba juice ɗin gwandar da Fatima tayi "wai kunma ci kuwa"

"A'a! Ya za'a yi muci fisbilillah? Daga gama dafa abinci sai mu diba muhau ci?"

"Au to kada kuci, har kuka iya girkawa, wato ci ne bazaku iyaba, to ku jira in zuba muku!" Fita tayi daga kitchen ɗin tana ɗan yamutsa fuska saboda mararta data ɗan ƙulle mata, a kujera ta zauna ta fara ci a hankali, sosai taji daɗin girkin barin dama ga yunwa ga jiki Babu daɗi.

Suma dai zubowa sukayi sunaci suna jefa hira kaɗan kaɗan, ita dai Nawaz da ido ta bisu tana mamakin ina Aayaan yaje da har Yanzu be dawo ba?

Bata gama tunanin ba saiga ƙarar turo ƙofa, Aayaan ne ya shigo da Sallama, yama manta da su maman sudeis sunzo, nufar Nawaz yayi da sauri, duƙawa yayi ya sumbaci goshinta Sannan ya rungumeta "im sorry dear, nabarki ke kaɗai ko? Kin kuma shiga cikin Ruwan zafin kuwa"
Toshe mishi baki tayi da sauri tare da cewa "su maman sudeis a bayanka fa" a hankaki yadda bazasu jita ba
Ware idonshi yayi, don gaba ɗaya ya manta cewa sunzo, waigawa yayi sai yaga basu suke kallo ba "Sannunku maman sudeis"

""Yauwa sannu an dawo lafiya" suka ce ita da Fatima

"Lafiya Lau Alhamdullillah, abikina be tashi ba"

"Ya tashi komawa yayi"

"Allah Sarki ai gara ya huta" Cewar Aayaan wanda yake yiwa Nawaz sign da ido na su shiga cikin daki, ita kuma sai ta nuna bata gane me yake nufi ba domin tana jin kunyar ta bishi su maman sudeis na zaune

Tashi yayi ya shiga cikin Don be so ya takurata tunda ya lura batason zuwa, ci gaba da cin abincinta tayi bata ko kalli inda yabi ba

Maman sudeis ce tace "wai kam Madina don Allah shekararki nawa ne?"

Cikin rashin damuwa Nawaz tace "ishirin da biyar"

Kallonta maman sudeis tayi tace "kodai sha biyar?"

"Kai maman sudeis, sha biyar kuma! Allah ishirin da biyar ne harda ƴan watanni"

"To lallai kam Abin naki harda iskanci, inba raini ba mijinki ya dawo babu tarba, babu sannu da zuwa, Sannan ya shiga ɗaki kin yi banza dashi, Anya kuwa madina🤔🤔 to wallahi maza ki tashi kije kitchen zakiga wanda na zuba mishi a madaidaiciyar warmer sai juice ɗinshi a jug, kiyi maza ki kai mishi, wallahi madina ko jinnul ashiq gareki saiya barki hardai ina tare dake, idan kuma so kike ya fara sha'awar ƙara Aure to."

Gaban Nawaz ne ya faɗi rass jin maganar maman sudeis ta ƙarshe, tashi tayi ta nufi kitchen ɗin don ɗauko abincin Kamar Yadda maman sudeis tace mata.

Fatima ce ta kyalkyale da dariya " maman sudeis wollah bakida dama, ji yadda kika zage kinayiwa ƴar mutane faɗa Kamar ƴar ki?"

"Ai Madinar ce sai da wuta, sam Batasan Irin damar da Allah ya bata bane, ji shekarunta amma sam babu wayau, ai inanan saina saita ta a layi tukuna"

"Ai kam kina samun lada Wallahi, tunda jiya sanadin ki an kashe basawa! Don sunfi ƙarfin boss"

Banza da ita maman sudeis tayi tana harararta irin na wasa.

Warmer da jug ɗin Nawaz ta zuba a saman tray tare da tumbler da cokali ta ɗauko na nufi hanyar bedroom ɗin ko kallon su maman sudeis batayiba wai irin ita tayi fushin nan, aikam tana shiga suma suka kwashe da dariya "Anaso ana kaiwa kasuwa"

A zaune ta Tarar dashi saman stool, yana ganin ita ce yayi saurin miƙewa tare da Amsar tray ɗin daga hannunta yana ɗaurawa saman mini table ɗin dake gabanshi "sweetheart bakida lafiya fa! Meyasa zaki wahalar da kanki haka, aida kin kirani na ɗaukar miki, zo ki zauna Anan.
Janyota yayi ya ɗorata a saman cinyarshi, a hankali Nawaz tace "Ina kwana yaya"

"Lafiya Lau Madam, kintashi lafiya? Ya ƙarfin jiki? Jiya nayi gagarumin laifi Koh?
Duƙar dakai Nawaz tayi, don itafa bataso yana yin Irin wadannan maganganun, ji take kamar ta ruga da gudu.

"Baza'a bani amsa ba?" Aayaan yace yana jan karan hancinta kaɗan.

"Ina kaje ne? Na tashi baka nan" Nawaz tace don ta kauda maganar da yakeyi mata

"Sirri ne! Amma idan za'a min kyauta zan faɗa " Aayaan yace yana kanne ido ɗaya, sai kuma ya ɗage girarshi sama.

Still dai Kanta a duke tace "me nake dashi dazan baka?"

Da sauri ya rufe mata baki tare da cewa "ai kin gama bani komai jiya, duk Abinda zan yi miki bazan iya biyan kiba, sai dai inyi mana fatan ko a aljanna mu kasance tare.

"Kaci abincin please, nasan ba Lallai kaci wani abuba" yanzu ma tace hakan ne saboda abar maganar.

Sosai Aayaann yaji daɗin Yadda ta nuna ta damu dashi, buɗe warmer ɗin yayi yasa cokali ya debo abincin ya nufi bakin Nawaz dashi, amsa tayi saboda kada ta Gwale shi sai kuma tace "yaya Ni na koshi, wannan nakane"

"Okay to Nagode, May Almighty Allah bless you with well mannered children "

Ɗan murmushi Nawaz tayi tana tunanin yaushe akayi daren da har gari zai waye.

Sosai yaci abincin Sannan ya ɗauki jug ɗin yasha juice ɗin, shima sosai yasha saboda natural ne kuma sosai yayi mishi daɗi.

"Madam zanyi wanka! Ko zaki min?"
Da sauri Nawaz ta tashi daga jikinshi tayi hanyar kofa da sauri Tare Da cewa "idan ka gama ka shirya zan dawo "murmushi yayi ya juya ya shige bathroom ɗin.

Ita kuma Nawaz ta fice zuwa falour, a tsaye ta tarar dasu maman sudeis da Fatima, Alamun sun shirya zasu tafi gida "kada kuce min zaku tafi ne?"

"Wallahi tafiya zamuyi munyi da oga zai dawo wurin ƙarfe huɗu, kuma babu Abinda nayi a gida"

"Okay to ku bari ya fito daga wanka sai ya samar muku cab ta maida ku" Nawaz tace tana murmushi

"Wai me kika maida mu ne Madinah? Komai kice sai anyi mana, to mudai kinga tafiyarmu, ki barshi ya huta, yanzu fa ya dawo" ficewa sukayi daga Ɗakin tare da Turo mata kofar suka rufe.

Nawaz na tsaye tana mamakin su maman sudeis kusan minti uku, sai kuma ta kaɗa kai tayi hanyar bedroom ɗinsu wanda suke kwana a ciki da, shima tsaff su maman sudeis sun gyara shi, samun kanta tayi da kwanciya tayi dai dai.
Takai minti Kusan goma sha biyar a keance sai kuma ta tashi zaune da sauri Tare da cewa "innalillahi wa'inna alaihi raji'un, yai sam bansha maganina ba gashi nayi alkawarin kullum saina sha.

Tashi tayi ta nufi kitchen ɗin, tana shiga ta buɗe drawer data ɓoye maganin ta ciroshi, ji kawai tayi Aayaann ya rungumeta ta baya tare da cewa "Sweetheart me kikeyi a kitchen, kuma fa kinyi alkawarin zaki dawo gurina"
Murmushin tayi saboda ta kasa cewa komai, ita damuwarta bata wuce maganin dake hannunta a fili ba, kada yace ta bashi saboda maman sudeis tace kada ta bari ya gani.

Amsar maganin yayi ba tare daya yi mata magana ba, bayanta gama karanta label Dinshi sai yayi murmushi "dear meya haɗaki da blood cleanser kuma?

"Maman sudeis ce ta bani sanda banida lafiya tace na riƙa shan biyu safe biyu rana biyu dare.

"Ashe likita ce itama" Aayaann yace yana ƙoƙarin buɗe murfin robar
"A'a kawai dai tace wai tayi Amfani dashine taji daɗin shi"

Zaro ido Aayaan yayi bayan ya buɗe murfin robar ganin kwayoyin da suke ciki, idan idonshi beyi mishi karya ba highly effective aphrodisiac pills ya gani a ciki, zazzago su yayi don ya ƙara tabbatar wa.

Ile kuwa sune, mamaki sosai ya kama shi amma be bari Nawaz ɗin ta lura ba, "yaushe ta baki"

"Sanda mukaje gidanta" Cewar Nawaz tana ɗan yin mutsu mutsu Alamun ta gaji da tsayuwar

Murmushine ya kwacewa Aayaan, kenan duk uban ciwon nan da Nawaz tayi feelings ke damunta amma taƙi ta faɗa mishi, lallai kunyarta har tayi yawa, kuma mamakin shi ɗaya shine ya akayi maman sudeis ta gane wani Abu be taɓa shiga tsakaninsu ba da har tayi irin wannan dabarar?

"Lallai kam Dole zanje inga Maman sudeis gani na musamman, kuma inaso ta faɗa min a ina tasan maganin nan, domin ni kaina ba ƙaramin taimakona yayi ba.

Ɗaukarta yayi chak tare da cewa "muje kiji Wata magana! Saura kuma ki min raki

Kuyi haƙuri da typing errors banyi Editing ba🥱

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*77*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Jin hakan daya ce take jikin Nawaz ya fara rawa, kada fa yace wani Abu zai kuma yi mata.
Murmushi Aayaan yayi "Meye kuma na rawar jiki, why are you so lazy? Kefa matar soja ce! Yakamata ki zama jaruma tako wane fanni, just yadda ake harba bindiga fa zan koya miki ba wani abuba.

"Nima fa bance wani abu ba"

"To ai jikinki yace" Cewar Aayaan yana kanne mata Ido.

Bathroom ya zarce da ita inda ya kuma gasa mata jikinta Sannan yayi mata wanka, tana gefe shima ya fara nashi wankan.
Ita dai rufe ido tayi har ya gama ya ɗaura towel sannan ya daukota ya fito harabar bedroom ɗin, dayake bedroom ɗin da kayansu yake ciki suka shiga, buɗe wardrobe yayi ya zaɓo mata doguwar riga me kyau da Babban mayafi, shima wardrobe Dinshi ya buɗe ya ɗauki farar polo shirt me gajeren hannu da black jeans,

Tsaff suka shirya gwanin sha'awa, kowa ya gansu sai sun birgeshi, "zamuje Hampton garden achan zan koya miki yadda ake operating ɗin bindiga da komai nata, kuma saura kimini raki!, Inaga daga chan ma mu biya Asibiti gurin haidar"
Chapter 91 · 0% Book details