← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 112

Sashe 79

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana sauka daga step ɗin jirgin amma idon kowa na kanshi, ganin irin kallon da Turawan keyi Musu yasa Nawaz ta natsu ta dena wuntsil wuntsil din tare da rufe idonta,
"Sweetheart kici gaba mana"
"Baka gani kaja mana kallo"
"Idan har kikaga abu yaja hankalin bature to tabbas ya burge shine, don haka sha'awa muka basu shiyasa suke kallon mu"
"Ni dai yaya Aayaann don Allah ka sauke Ni"
Be kuma kulata ba har saida ya dangana da inda taxi 🚕 suke a jere, buɗewa yayi ya sakata sannan shima ya shiga, drivern ne yace "sir where will i head to?"
"Royale Shire hotel" abinda Aayaan yace mishi kenan a takaice, "yaya wai nikam wace iriyar tafiya mukayi ne? Babu komai fa sai kayan jikinmu kamar wasu Yan gudun hijira"

"Bazaki gane bane, koda mun tawo da kayan ba lallai su sawun miki Anan ƙasar ba, kinsan ba irin shigar mu dayaba, zamuje boutique ki zaɓi waɗanda kikeso Ni dama inada kaya a ɗakina"
Gyada kai kawai Nawaz tayi tana bin cikin garin da kallo ta window ɗin dake gefenta "garin yayi Miki?"
"Yea sosai, sai naga yawancin abubuwansu kamar yana alakanta sarauta"
"Yea haka garin yake sai ma kinje beckingham shine zakiyi kallo har ki gaji"
Murmushi Nawaz take tayi, a Cikin zuciyarta tana mamakin wai yau dalilin Aure itace a England, Lallai komai yanada nashi Dalilin"
Sunyi tafiyar aƙalla minti 25 drivern yayi Parking a dai dai wani damfareren hotel, babba ne sosai don a ƙalla yakai hawa 30 kuma faɗin shi ma zai kai unguwa guda, mutane ne keta kai komo, wasu suna fita wasu suna shiga, daga yadda zakaga mutanen kasan ba zallar Yan kasar bane, don wasu farare wasu jajaye wasu yellowish fari wasu kuma baƙaƙe, wasu chocolate.
masu saye da siyarwa ne keta cinikayyah a bakin hotel ɗin, don gaba ɗaya gaban hotel ɗin shaguna ne, wasu na ƴan kunne, wasu kayan sawa wasu takalma da jaka wasu kuma store ne na kayan maƙulashe.

Baza Ido Nawaz tayi tana kallon iKon Allah, lallai Allah ɗaya gari banban, idan kana wani gurin sai kaga kamar babu wasu illah ku kadai, amma ji ikon Allah wata nahiyar duniyar suke kuma kowa yanata tashi sabgar.

Kama hannunta yayi suka shiga cikin wata babbar hanya sannan yabi hannun dama inda ya danna button ɗin lifter, ƙofar ce ta buɗe suka shiga ciki Sannan ta koma ta rufe, 17 floor ya danna, ita dai Nawaz tana tsaye tana kallon ikon Allah.
Bata Ankara ba taji ya fincikota ta fado ƙirjin shi, "Sweetheart wannan shine mafarin Rayuwar soyayyar mu, anan zamu gina ƙauna da amana, inaso ki ɗaukeni a matsayin dan uwanki, kaninki, yayanki, malaminki, babanki, abokinki, mijinki, abokin wasa, abokin karatu, masoyi, abin kauna, garkuwa kuma ginshikin ki, ina ƙaunarki sosai *Madinatul munawwarah* kuma ina fatan zamu rayu cikin ƙauna da aminci.
Shiru Nawaz tayi tana sauraron bugun zuciyarshi, tabbas ta tabbatar da wannan maganar daga can Cikin tsakiyar zuciyarshi take fitowa kuma tabbas tayi na'am da soyayyar da Aayaan yake yi mata, kuma a yanzu ta fara tuhumar kanta meyasa bazata zage itama ta nunawa me ƙaunarta ƙauna ba?.

Lifter ɗin ce ta tsaya Sannan ƙofar ta buɗe, a yanda take a rungume a ƙirjinshi haka suka fita zuwa cikin harabar ɗakunan, bakin wata ƙofa taga ya tsaya, a jikin kofar an rubuta *Room 315* card ya ciro yayi swapping ɗin shi a jikin wani sensor aikuwa take ƙofar ta buɗe, direct ya shiga da ita ciki, wani babban royal falour ne babba sosai, ita dai Nawaz raba idanuwa take tayi tana mamakin abubuwan da take tacin karo dasu tunda suka sauka a garin.
Ɗakin tsaff yake, har kamshin rurare ne da air freshener Suke tashi, kuma ko kaɗan babu ƙura Kamar wani na zaune a Cikin ɗakin.

Direta yayi a saman wani tintin da akayishi da zallar katifa yana cewa "welcome to the royal home of Love, kinga tunda kika shigo gidan nan Shikenan babu ke babu kuma jin kunya ta, domin mun riga mun zama abu ɗaya, tare zamu riƙa yin komai, kamar su girki, wanka, ke Komai ma.
Kirjintane ya bada dararam, ai kuwa Aayaan ya ɗage gira Tare da cewa "bari naje na haɗa mana ruwan wanka sai inzo muje muyu ko?
Ita dai Nawaz na zaune Kamar gunki tana duba yadda abubuwan da Aayaan ya lissafa zasu yiwu.

*Don Allah a ƙara yi min afuwa na Rashin jina da kukeyi na kwana biyu, ina fatan kowa yana Lafiya*

*MATAR RASHEED* ✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*68*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Tayi nisa cikin tunanin har yaje ya haɗa ruwan wankan ya dawo, bata ankara ba sai ji tayi ya sureta yayi corridor ɗin bayin da ita.
"Don Allah Don Annabi ka taimaka ka saukeni kaga ko Kayan ban cire ba, kuma Allah zanyi da kaina...."
"Nop bazan bari ba, meye amfanina? Duk zanyi Miki da kaina fiye da yadda ma ke zakiyi"

"Wayyo don Allah kayi haƙuri yaya!"
Dariya Aayaan yayi "gaskiya bazan iya hakuri ba, kuma as from today Nayi cancel ɗin yaya, dole kice Aayaan ko kuma ki samin wani sunan na daban.

Rigar jikinta yake ƙoƙarin cirewa ita kuma ta fara ƙankame jikinta tana girgiza kai "yaya kunya nakeji wallahi, don Allah ka taimakeni ka kyaleni!"

Ko bi takanta beyiba ya cire rigar, itakam saita rufe idonta gam kamar wadda taga dodo, tanaji ya cire mata sauran Kayan jikinta duka babu yadda ta iya.
Ƴan seconds taji shiru Alamun yana cire nashi kayan, ai kuwa sai jinta tayi tinjim ya ɗauketa duka sun afka cikin jacuzzi ɗin daya haɗa ruwan wankan, duk tabi ta ƙanƙame kamar wadda ruwan sama yayiwa dukan tsiya da daddare, jikinta har rawa yake yi.
Duk yana ankare da ita amma ko a jikinshi domin yasan idan ya biye mata babu ranar da zasu zama ma'aurata na haƙiƙa.
Ita ya fara yiwa wankan sannan shima yayi, towel guda biyu ya ciro a towel rack, ita ya fara lulluɓewa sannan ya ɗaura nashi a ƙugun shi.
Cicciɓarta yayi suka koma bedroom ɗin, tanajinshi har ya gama shafa mata mai yasa mata kayan da batasan wane kala bane domin har zuwa yanzu ta kasa buɗe idonta.
Ji tayi ya ɗauketa ya ɗora ta a saman kujera, nan taji ƙarar hand dryer, gyara mata gashinta yayi sosai, sannan yayi Parking ɗinshi in a messy bun.
Maida ita yayi ya zaunar a gefen gadon Sannan taji alamun shima yana shiryawa.
Zuwa ten minutes taji ya kuma cicciɓarta, tsaida ita yayi akan kafarta sannan yace "soulmate pls open your eyes and rate my work"
Yanda kasan gunki haka Nawaz ta koma domin ko motsi ƙwaƙwara ta kasa "pls my reality nace ki buɗe idonki ki ba aikina marki"
Nan ma dai Nawaz tsit tayi babu respond "Okay tunda bazaki buɗe idonba bari nayi mai gaba ɗayan danasan kinajin tsoro, sai inga me zakiyi, Ni dama wallahi daurewa kawai nakeyi san.......
Ai bata bari ya ƙarasa maganar dayayi niyar yiba ta buɗe idonta amma ƙasa-ƙasa, dariya ce ta suɓuce wa Aayaan be shirya ba "wai itakam wannan wace irin tsana tayiwa Mu'amular Auratayyah ne? Ace zata iya yin komai idan aka yi mata barazana da shi"
Koda Nawaz ta buɗe ido ganinsu tayi tsaye gaban standing mirror, sanye take da wata designer ɗin doguwar riga Pink anyi mata spachs da ɗigo ɗigon baƙi.
Shima yasa NORMAL T-SHIRT Pink me V neck sai baƙin wando chinoz.
Sosai taga sunyi wani irin masifar kyau da matching, gashi ya jajjera mata wasu irin shining beads a jikin gashinta masu ɗaukar ido.
Ɗage gira yayi Sannan yace "Toya kikaga salon nawa? Fatan yayi Miki?
Ɗaga kanta tayi alamun eh"
"Okay to abani marki"
Nauyi bakinta yayi mata ga matsananciyar kunya data rufeta sam saita kasa buɗe laɓɓan ta tayi magana.
"Okay kawai bari a wuce gurin domin na fara lura kema fa kinada buƙatar kasancewa da mijinki kamar Yadda shima yakeda buƙatar kasacewa dake"

"Ba haka bane yaya! Wallahi munyi kyau 100%"
Wani irin smirking yayi na ganin tsantsar wauta da yarintar Nawaz a fili "Okay to yanzu wace kyauta za'a bani tunda aikina yayi kyau?

Nan ma dai shiru ta kumayi batace komai ba, "yanzu dai abar zancen nan tunda naga kina shiga takura, and kuma Ni nafison na ganki cikin walwala"
Hannunta ya riƙe ya jata falour zuwa dining area, wasu irin haɗaɗɗun royal lunch sets tagani jere a saman dinning ɗin wanda batasan sanda aka jera su ba.
Kujera yaja mata ya zaunar da ita sannan shima yaja guda ɗaya ta gefen ta ya zauna, bubbuɗe abincin yayi tare dayin serving ɗinsu a plate guda ɗaya, cokali ma guda ɗaya yasa, harda drink ɗin daya Zuba a tumbler ɗaya ya zuba.
One spoon yayi sannan ya ɗibo wani ya nufi bakinta dashi, babu yanda ta iya haka ta buɗe bakin ta amsa.
A haka dai sukayi ta cin abincin tare, harta drinks ɗin Idan yayi sipping saiya sa mata tumbler ɗin a baki itama tayi.

Tace ta ƙoshi amma da kyar ya barta, cicciɓarta yayi suka koma kan gado, kwantawa yayi ya ɗora kanshi a saman cinyarta tare da cewa "dubamin ƙwarƙwata"

Zaro ido Nawaz tayi "hu'um ƙwarƙwata fa kace? A wannan gyararren gashin naka ne za'a ga ƙwarƙwata?

"Eh mana baza'a rasa ba" cewar Aayaan Yana daɗa gyara kwanciyar shi"

"Kazanta ce fa take kawo ƙwarƙwata, kuma yanzu duk gyaran kan nan naka saikayi tunanin za'aga ƙwarƙwata?"
"To Shikenan duba ki gani Idan bakiga ƙwarƙwata ko ɗaya ba ki zaneni "
Chapter 79 · 0% Book details