← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 112

Sashe 109

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakin ta yayi yana daɗe babbake hanya wai duk don karta wuce "pls mehtab uzurin ya isa haka, hakurina ya ƙare akanki, kullum kice saboda Madam ɗina ne bazaki Aureni ba, to yanzu ma babu ita amma kin ƙi yarda dani a matsayin miji, anya kuwa zaki taɓa kauna ta??

"Wai ni nace bana kaunar ka ne?" Maganar ta kufce ta fito daga bakin mummy ba tare data shirya ba, saurin cewa tayi "Ni Kawai dai Auren ne banaso" don ta gyara zancen ta.

Ganin har ya samu tana yi mishi magana yasa yace "go inside we will talk later, but pls kisa lafayar ki akwai mutane sosai a gidan"

Kunya ce Sosai ta kama mummy domin ita sam tama manta haka take ziƙau daga ita sai doguwar rigarta, cikin sauri ta warware lafayar ta fara naɗa wa da sauri sauri.....

Aseey da Aayann me zasuyi idan ba dariya ba, Sosai Abin ya basu dariya, saving ɗin video ɗin da yai musu Aayaan yayi sannan ya saka wayarshi a aljihu......

Nawaz kuwa tana chan sai shiga take tana fita domin yau ta samu sake, ado tasha da wata ocean green ɗin abaya mai design a kirji da baya, ta wadatu da swarovski stones sai walwali yakeyi.
Duk wannan Abin da akeyi ita bata sani ba, tadai san Aayaan ya haɗa walimar duka dangi....

Tun kafin karfe ɗaya zancen Auren mummy da Colonel ya cika gidan, me Naufal da fudail zasuyi inba murna ba, sai nemanta sukeyi lungu da saƙo amma babu ita ba alamar ta.
Nawaz kuma sai taji gaba ɗaya kunya ta kamata, to yanzu Shikenan colonel ya zama daddyn su na gaske? Itama mummy nada miji yanzu kenan....

Ɗaki Takoma ta cire rigar jikinta ta chanza da wata cotton mara nauyi, so takeyi ta samu ta kwanta amma su hassu sunki barinta, yanzuma tana kwanciya sai gasu, shiru tayi tana tunanin ko zata gudu ɗakin Aayaan ne kawai kila idan achan ne zata samu ta huta.

Ta ɓangaren mummy kuwa suna chan ƙuryar ɗaki itada ummin Nawaz da mummyn sarfraz, faɗa sukeyi mata akan tace musu "itafa bata son auren"

"Lallai ne! Ai kuwa tun wuri ki gyara, irin wannan Babban mutum haka yace yana sonka ai abin arziƙi ne babba, kuma in banda abinki a ina yin aure ya taɓa zama laifi?kuma ki kalla kaf cikinmu waye beda Aure? Kece Kawai to ke ko irin sha'awar nan ma bama baki kullum muna samun lada ke kuma kina zaune fanko? To nidai Ina baki shawara ne a matsayin ƴar uwa, gara ki rungumi mijinki ku zauna lafiya tunda dai an rigada an daura auren" jawaban da mummyn sarfraz tayiwa Mummy kenan

Ita kuma ummin Nawaz cewa tayi "Nasan hakan yana da zafi, zakiga kamar ya nuna miki karfin iko ne, amma ba haka bane tsabar soyayyar dayake yi miki ce tasa yakejin tsoron kada ya rasaki gaba ɗaya, yanzu dai haƙuri zakiyi ki rungumi mijinki kamar yadda mumyn sarfraz tace, kuma ai mace kwanciyar hankalinta gidan mijinta, domin duka duka kwana nawa da dawowar Abban Nawaz amma saina ke jina kamar an maidani sabuwa"

Shiru Mummy tayi, tabbas gaskiya suke faɗa mata! Kota bangaren ta wani zubin idan taga mace tana yiwa mijinta hidima sai taji ta bata sha'awa, yanzu kenan idan tayi wani Abu na nuna ƙi ga auren zai zama kamar tayiwa Allah butulci kenan...

"Nagode sosai sosai Allah ya saka da mafificin alkhairi, Allah ya bar ƙauna da zumunci, gaskiya inajin daɗin yadda kuke daukata a matsayin ƴar uwa, ada ina tunanin na rasa komai da kowa amma a yanzu da Allah ya haɗamu sai nake gamin na samu komai da kowa" amsar da Mummy ta basu kenan.

Dariya sukayi Tare Da cewa "Amarya ta tashi ta shirya kada Ango da abokansa suzo bata shirya ba.

Taro ya watse Lafiya inda Aayaan yasa aka maida kowa gida tare da sha tara na arziƙi, yanzu gida ya zama saura Mummy da Nawaz sai su Naufal saboda itama Aseey ta koma kamar yadda baban muhsin ya buƙata, Colonel shima ya gudu tun washe garin da aka Daura Aure, yayi hakan ne don ya bata iska har zuwa sanda zata sauka daga fushin da tayi, abinda be sani ba shine ummin Nawaz da mummyn Sarfraz basu tafi ba Saida suka tabbatar sun cusa mata son Auren a cikin zuciyarta.

Kwance Aayaan yake yayi flat a Saman gado inda Nawaz ke kwance saman ƙirjin shi sai faman shagwaɓa take tsula mishi "Nifa sweetheart mara ta ciwo takeyi, ji nake wani abu ya cure min a guri daya duk ya dameni."

"Sweetheart kece fa kika riƙa yawo saboda kinga bana kusa dake, hannu yasa a daidai marar ta don ya duba, mamaki ne ya kamashi jin tudu sosai a gurin gashi yayi ƙarfi , tsabar firgici besan sanda ya tallafota ya tashi zaune ba, sauke ta yayi a jikinshi ya kwantar da ita yana duba cikin.
A fili babu komai amma idan ya taɓa sai yaji yayi mishi tauri, "dear ko asibiti zamuje?"

"No! Bazanje ko ina ba bayan kwanaki haka ka ɓata kusan awa biyu kana Abu ɗaya amma ya nuna babu komai, ashe kuma akwai, yanzu tunda ba komai nake jiba kuma yana motsi kawai mu barwa Allah komai"

"But dear......

Bata bari ya ƙarasa fadar abinda yayi niyya ba tace "Allah nace fa"

"Okay to! Allah ya tabbatar mana da Alkhairi"

"Ameen" Nawaz tace tana ƙoƙarin tashi, "dear please a barni in gaisa da little Aayaan"

Chuno baki tayi Alamun itafa babu dama "Ni dai gaskiya yaya yanzu zaka hana mutum sakat, kuma ko nace ka dena ba denawa kake yiba don zama kake kamar kurma."

"Haba sweetie na! Kinga fa rabon da mu gaisa tun sanda mukaje gidan Daddy colonel fa, kuma kinga lokacinma bamusan yana nan ba sai daga baya"

"Ni dai yaya gaskiya so kake kawai ka tayar min da hankali ina zaman zamana"

"Dear pls mana! Bakiga ƙoƙarin dana yiba ne? Ko so kike inada mata na riƙa ciwon mara kamar gwauro"

Shiru tayi, tasan Aayaan yana matuƙar ƙoƙari akanta, daga yanayinshi kawai tasan me yawan bukata ne, amma duk don kada ya sata a damuwa yake kyaleta, itama fa yau ya kamata tayi wani abu da zaisa shi yaji eh itama fa tana sonshi.

Samun kanta tayi da haɗe bakinsu guri ɗaya, French kiss ta bashi sosai, shuko Aayaan gaba ɗaya mamaki ya kamashi na ganin abinda Nawaz tayi, be gama wannan mamakin ba yaji tasa hannu tana cire mishi boturan riga, tana gama wa tasa hannu ta zage zip ɗin wandon shi.
Shi dai Aayaan a wannan rana dai kasheshi ne kawai mamaki beyi ba, amma ya firgita da lamarin Nawaz domin ita taja ragamar komai, sosai ya samu gamsuwa fiye da ko yaushe.
Sai bayan komai ya lafa kuma kunya ta rufe Nawaz, kasa motsawa daga inda take tayi, lura da hakan da Aayaan yayi sai yaketa tsokanar ta yana cewa shifa tayi matuƙar burgeshi sosai, kuma ta sashi farin ciki matuƙa, idan da hali ma shi yana buƙatar ƙari.

Dai dai kunnen ta yasa bakinshi inda yace mata "dear nifa wata sugar naji kin ƙara ne! Pls meye sirrin?"
Tsabar kunyar data kama Nawaz bata san sanda tayi ƙundumbala daga kan gadon ba tayi cikin bathroom da gudu, tashi yayi shima ya rufa mata baya yana dariya
°°°°°°
*Aseey*

Ko bayan ta koma england rasa sukuni tayi, tanaso Daddy colonel yasan cewa har yanzu shi mutum ne duba da dadewar da marigayiya tayi tana ciwo, kuma bata tunanin Mummy zata saki jiki dashi sosai har ta faranta mishi.

Samun kanta tayi da tuna Aunty khatoume, babu jinkiri kuwa ta kirata ta faɗa mata cewa mummyn su tayi aure sai dai ga yanda Auren ya kasance, duk Abinda Ya faru ta bata labari sannan daga bisani tace tanaso ta kira mummyn ta bata shawarwari sannan ta tura mata da magungunan gyaran jiki na musamman kuma emergency, sai dai ta roƙe ta akan cewa don Allah kada ta faɗa wa Mummyn cewa ita ta faɗa mata, tace Kawai ji tayi itama.

Sosai Aunty khatoume taji daɗi jin cewa Mummy tayi Aure, domin dama tun tuni take fama da ita akan tayi aure Amma taƙiyi, Hakan yasa taci alwashin tura mata magunguna na musamman domin ta rikita colonel.

°°°°

A chan Zaria kuwa ko bayan sun koma Abban Nawaz baya wani kula umma, sam ya fita sabgar su ita da Jamila, ita ko umman bata damuba sam illah istigfarin ta data dage dayi, tuba kuwa harta gaji dayi.
Basu samu sauƙin abun Abban Nawaz ba har saida ummin Nawaz ta sameshi tace mishi jamila fa fyaɗe aka yi mata a makaranta kuma da dare ne shiyasa koda akabi kadu ba'a gane waye ba, ta ƙara dace mishi sun bar maganar ne saboda kada sunan jamilan ya ɓaci.

A Ranar kuwa Abban Nawaz ya shiga ɗakin umma, har zama yayi a gefe tare da tambayarta ya jiki.
Tun daga ranar suka samu sauƙin abubuwa da dama, jamila kuwa ta warware sosai domin duka aikin gidan ita takeyi dukda cewa ummin Nawaz na hanata yin wasu abubuwan.

Ranar da Umma taji ƙaryar da ummin Nawaz tayiwa Abban Nawaz akan cikin Jamila Saida tayi kuka, wato ita ada kullum neman hanyar da zata tozarta ta take amma yanzu itace ke nemar musu sasanci a gurin kowa.

°°°°°°°°°°

*Bayan wasu watanni*

Abubuwa da dama sun faru, ciki harda tarewar Mummy da Colonel, sosai colonel ya samu kanshi cikin wata sabuwar duniya, hakan yasa ya dage wajen kula da Mummy yana ririta ta sosai, kullum yana nakiƙe da ita kamar ya cinye ta, datayi motsi kuwa zaiyi saurin tambayarta meya faru, itama Mummy ganin yadda colonel ɗin ke kula da ita, ga kuma su Naufal suma kullum cikin yi mata hidima suke yasa itama ta kwantar da hankalinta ta saki jikinta suke farantawa juna.

Yauma kamar kullum suna zaune a dining suna yin lunch, Naufal na gefen Mummy yana cewa ta bari yabata a baki tunda Daddy yau be fito da wuri ba.
Chapter 109 · 0% Book details