← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 112

Sashe 16

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusa dashi ta matsa "kanada maganine ka fad'a min inda yake in dauko maka?

Can murya cikin makogwaronshi yace "kije kitchen ki dauko lemun tsami🍋 guda biyar ki yanka ki matse ruwan saiki bud'e fridge zakiga zuma, saiki zuba cokali uku....
Ki kawomin insha,

Da sauri Nawaz tayi kitchen hankalinta a tashe....

Cikin y'an minute ta had'a mishi, d'akin ta koma da sauri...

"gashi na had'a maka, tashi kasha kaji?

Gadon ta hau Ta d'ago shi a hankali, kopin ta kafa mishi a baki, tunda ya farasha saida ya shanye duka...
Pillow tasa mishi sannan ta d'ora kanshi a hankali.....

Rufe idonshi Yayi yana cije lebenshi....

"Sannu kaji" cewar Nawaz wadda hankalinta yake a tashe

Kai kawai ya iya d'aga mata, sannan ya Gyara Kwanciyarshi, yaja bargo ya rufe jikinshi....

Zaune take tanata Kallonshi har sama da awa d'aya, tananan zaune barci ya Fara daukarta...

Jin zatayi barcin da gaske yasa ta tashi ta Duba yanayin jikin nashi, Jitayi zafin ya sauka sannan kuma yanata zufa.... Sai barcin daya keyi a hankali....

Ganin yaji sau'ki yasa ta koma Saman three sitters couch d'in dake Gefen gadon ta kwanta...

Ko minti goma cikakke ba'a yiba barci Yayi awon gaba da ita....

Can cikin dare Misalin karfe uku SARFRAZ ya tashi domin wani irin fitsari dayaji ya matseshi...
Nawaz yagani kwance Saman couch Amma hannun Ta ri'ke da bargon daya rufe jikinshi dashi....

Wani guntun murmushi yayi "dama duka wannan abinda takemin kaunace tasa Haka!

Amma nasan tausayine kawai irinna malama Nawaz,,,

Mikewa Yayi ya nufi bayi, Bayan ya fito ya zauna Gefen gado ya kura mata ido "kalleta mai kyau, kuma ga yarinta nan a fuskarta, Anya ba karyar shekaru take yiba?

uhm ni wallahi ko shekararta d'ari haka nake sonta "
hannu ya had'a guri guda 🤲🏼"ya ilahi kasa wannan baiwar taka ta kaunaceni koda kuwa kwatan kaunar danake matane....

yanzu kuma gobe zata tafi, wani irin shu'umin Murmushi yayi "hmm nasan abinda zanyi, Allah ya kaimu goben Lapia...

ganin yanda take barcin cikin natsuwa kuma hankali kwance yasa shi tuna ta'asar dayaso Yayi.....

Baki ya kama 🤔oh yanzufa da bankai zuciya nesaba da yanzu wata chapter akeyi ba barcin namba....
ya Allah nagode maka dakasa nafi karfin zuciyata 🤲🏼....

itace batasan yanda nakejiba Saita ri'ka yimin shagwaba sannan kuma Inaga Anya malama tanada cikakkiyar Lapia kuwa, domin da tanada cikakkiyar Lapia data gane moves d'ina da kuma abinda nake nufi, amma Sam ni sainaga jikintama baya responding .......

Addu'a yayi ya shafa mata sannan shima yayi ya shafawa kanshi,
kwantawa yayi ya ri'ke hannunta cikin nashi, da burin Allah yakaisu safiya lapia.....

5:29am Nawaz ta tashi a firgice, da sauri ta karasa fuskar SARFRAZ, ganin Yana numfashi yasa tace "ALLAH nagode maka, naji jikin nashima Yayi sauki, Allah yasa kada ya karayin irin wannan ciwon domin ya azabtar dashi......
Gashi mummyn shima bata saniba......

Kiran sallar asbah taji,
To yanzu yaza ayi in tasheshi, ban saniba ko zazzabin da saura...

duk wannan abinda Nawaz takeyi SARFRAZ Yana jinta domin dama idonshi biyu ganin Ta tashine yasa ya rufe idonshi....

a hankali tadan bigi kafanshi, SARFRAZ! SARFRAZ!! Tashi asbah tayi...

Juyawa yayi alamun maiyin barci sannan yace 'uhhmm?

Dad'a cewa tayi "ka tashi kayi sallah an Kira kada a tayar bakayi alwala ba....

Tashi Yayi zaune Yana Mitstsike idonshi, Kallonta yayi "kada dai ace anan kika kwana?

d'aga kanta tayi "Eh anan na kwana saboda jikinka, kuma sanin kanka ne bazan iya tafiya nabarka a halin da Kake cikiba......

Murmushi SARFRAZ yayi "oh Ashe dole nayi mafarki, Ashe da Mace na kwana, ....

A yatsine ta kalleshi kamarya da Mace ka kwana? Kuma wane mafarki kayi?

TASHI yayi yabi hanyar bayi sannan ya waigo "mafarki Nayi na kwanta dake, kuma gaskiya ya kamata ki Duba kanki kiga badai da gaske nayiba koh? Domin mafarkin yafi kowanne dad'i Dukda dai naga Ke Bakida service....

cikin bayin ya shige yana dariya....

wani makokon abune yazowa Nawaz wuya "wannan yaron bazai ta'ba iya dena rashin kunyaba, ace naji tausayinshi nazo na kula dashi shine zai kalleni yace yayi mafarki Dani, a tunaninshi ni sa'ar shice?
Yanzun nan zan had'a kayana, idan na bar mishi gidan zanga wadda zai gani arha balle har ya ri'ka fad'an mata abinda yaga dama.....

fita tayi daga d'akin ta nufi na mummy, tana shiga mumy tana shigowa,
Murmushi mummy tayi "daughter keda bakya sallah Aida kinyi barcinki baki tashiba, barin ga tafiya mai tsawo a gabanki....

Murmushi Nawaz tayi "uhhmm mummy dama cewa nayi yanzu zanyi wanka sai in shirya, zuwa shida in tafi gida sai in had'a kayana saboda sammako nakeso nayi.....

mum ce ta dafa kafadarta "calm down my dear duk wannan hanzarinfa? kin manta cewa SAUKA LAPIA AKESO BA SAUKA LAHIRABA?

yanzu abinda nakeso dake shine kiyi kwanciyar ki, kuma gida da kike cewa zakije basai kinjeba domin anan zan had'a miki komai da kikeso.....

pillow mummy ta janyo ta kwantar da Nawaz sannan tasa mata duvet ta rufeta.....

Dayake dama ba wani barcin kirki tayiba yasa batafi minti biyarba Ahaka ta shiga duniyar barci...

Misalin 7:30am SARFRAZ ya shiga d'akin dad domin gaisheshi....

murmushi dad yayi "A'a Kace fabulous d'ina ne yazo mu gaisa!
Murmushi SARFRAZ Yayi "Eh dad....

Bayan sun gaisa dad yace....

ai jiya mummyn ka tayimin bayani akan Nawaz, Ashe y'ar y'ar kawartace, tacemin mahaifiyarta taje MAIDUGURINE shine ta kawota nan gidan zuwa ta dawo...

kuma saigashi naga har kun saba....

Dadne ya kashewa SARFRAZ ido 😉 my son Kodai da ita zaayi.....

Murmushi SARFRAZ Yayi yana Sosa kai,

Dai dai nan mum tashigo rikeda waya....

Alhaji kaji wai kakannin Nawaz sun matsa wai Lallai ta tafi yau, wai sai fad'a suke yi....

'Toh yanzu yaza ayi? Cewar dady yana kallon hajiya....

Ehm ina tunani kawai SARFRAZ ya kaita, inaga zaifi data yita jigila a hanya, koya Kace Alhaji?

murmushi Alhaji yayi Eh hakan Yayi, kinga dama shima ya dad'e beje gurinsu kakaba kinga saiya biya can koh?

SAF6RAZ kuwa ji yayi Kamar anyi mishi bushara da gidan Aljannah domin mummy ta shirya komai....

Mummy tace "SARFRAZ tashi muje inyi maka list kaje kasuwa ka siyowa su mama tsarabar dazaka Kai musu....

Binta Yayi abaya, suna fita ya daka tsalle ya rungumeta Ta baya" gaskiya ina kaunarki mum, Ina Fatan Allah ya biyaka da gidan Aljannah.....

murmushi mum tayi "ni nayi wannanne kawai domin Kai, yanzu muje inyi maka rubutu, domin inaso kayi siyayyya da yawa, kaga zaka siyowa nawaz dogayen riguna da hijabs da waya dasu takalma harda jaka da pause koda guda biyune, kuma sannan inaso kaje gidan hajiya Bilki ka amso mata atampopi da lace dinkakku koda material ko shadda

Wallahi bani da Lafiya ne kwana biyu, ina barar addu'ar ku.

*MATAR RASHEED*✍️🎀🎀 *SARFRAZ*🎀🎀

*episode 19*

*✍🏻written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*

*SUPREME WRITERS ASSOCIATION (SWA) .... We write with the ink of era, that's era is our ink..... We satisfy, entertain and touches our readers mind.....*

Inaso kaje gidan hajiya Bilki ka amso mata atampopi da lace dinkakku koda material ko shadda,
Saika wuce kasuwa ka siyowa su inna Suma atampopi dadai sauran abun Bukata, yanzu dai zauna in gama rubutamaka.

Zama yayi a Gefen mum Don babu yanda ya iya, saboda shi yasone yaje d'akin mummy yaga Nawaz saboda bega giftawartaba ....

A Saman table ta dauki jotter, na Nawaz ta fara rubutawa sannan ta rubuta Wanda za'a kaiwa y'an uwa.....

Cewa SARFRAZ tayi biyoni d'akin daddyn ka...

Kumbura baki Yayi sannan yabi bayanta, suna shiga mum tacewa daddy "kaga abubuwan dana rubuta sunyi?

Amsa dad yayi ya Duba "Eh sunyi amma sainaga baki wani rubutawa ummanki abubuwa da yawa ba, gaskiya Ki kara.....

Murmushi tayi "to Alhaji nagode Allah ya saka da Alkhairi!

D'aga mata hannu Alhaji Yayi "dakata! Wai so nawa zance miki ki denamin godia ne?
Gaskiya banso ki dena.

Murmushi mummy tayi "to Allah ya huci zuciyarka, kuma naga ai duk Wanda bai iya godewa mutumba bazai iya godewa Allah ba.

SARFRAZ ne yace mummy bari nazo....

Da sauri mum tace "A'a babu inda zaka, amshi takardar nan kawai ka tafi yanzu, inyaso saika fara zuwa gidan hajiya Bilki tukuna....

Amsar takardar yayi ya fita, dad ne ya kwala mishi Kira "fabulous zo mana.....

Dawowa SARFRAZ Yayi Amma ranshi a had'e, "gani dad"

Murmushi dad yayi "kafita banbaka master card 💳 ba, to dame zakayi siyayyar?

Dad akwai kudi a account d'ina ai.....

Hmm wannan ai nakane, yanzu amshi wannan saikayi siyayyar, idan kagama komai saika ajiyemin a drawer....

Amsa yayi "to dad nagode "

Girgiza Kai dad yayi "kaima mummyn taka ta koya maka Dabi'ar ta ta godia koh?

shi dai SARFRAZ fita yayi, parking space ya wuce ya shiga mota ya fita daga gidan, daka kalleshi zaka gane yana cikin damuwa......

Bai wuce ko inaba sai gidansu ABDUL (abokinshi na islamiyya)

yana shiga kuwa yaci Sa'a, dashi ya Fara haduwa.......

D'akin ABDUL suka koma, ganin ABDUL Yayi duk shashin bulala a jikinshi Dayake singlet ce a jikinshi......

Mamakine ya kama SARFRAZ 🤔😳, Kai kuwa ABDUL waye yayi maka wannan danyen aikin?

murmushi ABDUL Yayi "SARFRAZ Allah yasoka kabi malama Nawaz ka tafi gida ranar nan, wallahi dabansan yanda jikinka zaiyiba barin gaka fari!

Ai in takaice maka zance, katuna sanda zaku fita ai malam bilal ya shigo ajinmu koh?
SARFRAZ ya daga kai alamun "eh

Abdul yaci gaba da cewa" to wallahi daya fara dukanmu Kai kazata Allah ne ya aikoshi..
domin maganar danake maka yanzu haka Zainab da uthman suna asibiti harda Karin ruwa akayi musu......

tausayine ya kama SAFyRAZ ganin irin yanda y'an ajinsu suka shiga halin ha'ula'i kuma duk sabo dashi.....

cewa Yayi "ABDUL amma ya fad'a muku abinda kukayi mishi.....

Girgiza Kai ABDUL Yayi "A'a wallahi baice mana komaiba....

Kai in banda abinka SARFRAZ waye baisan mugunta irin ta malam bilal ba?

Dafashi SARFRAZ Yayi "Dan Allah kayi hakuri, wallahi be kyautaba, ai duka ba hauka bane......

Hmm SARFRAZ Idan banyi hakuriba to me zanyi? Cewar ABDUL yana Mikewa "bari na kawo maka flask ka hada tea domin nasan baka karyaba....

Cewa Yayi to abokina...

ABDUL na fita SARFRAZ yace "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, yanzu abinda malam bilal yayi musu kenan, wallahi danasan abinda zaiyi kenan daban Kira shiba....
Fisbilillahi ji yanda ya illata musu jiki!
Chapter 16 · 0% Book details