← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 112

Sashe 100

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rungumeta yayi yana patting ɗin bayanta a hankali, Sannan ya Fara magana kamar haka "matata basai kin zauna kina bata bakinki Wajen faɗa min Irin ƙaunar da kike yi mini ba, Ni na gani kuma naji sannan na amince, kuma nayi miki alkawarin cewa indai nine hanyar zuwanki Aljannah to na yafe duniya da lahira, ki shiga Aljannah salin alin"
"Nagode sosai sweetheart Allah ya ƙara girma" Nawaz tace tanajin wani irin shauƙin mijin nata yana fusgarta.

Kwantar da ita yayi sannan yace "Sleep, Ni zan fita Masallaci Amma i will be back soon"

"Allah ya dawomin dakai lafiya habibi"

Fita Aayaan yayi yana jin cewa Nawaz so kawai takeyi ta haukatashi,

Koda ya fita zuwa masallaci haka mutane sukayi tayi mai Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba, harda masu cewa ashe dama matarshi soja ce itama, wai an basu Labarin abinda ya faru, shidai as usual haka yaita yi musu murmushi, da yake babu waya a hannunshi tana cikin kaya shiyasa mutane sukayi mishi yawa a Masallacin, sai wajen ƙarfe shida da rabi ya samu ya gudo zuwa gida.
A falour yaci karo da mummy "ina kwana mummy?"
"Lafiya Lau son! Ya ka tashi?"
"Nima lafiya Lau Alhamdullillah"

"Masha Allah, yanzu ina daughter na take?"

"Tana barci" Aayaan yace da ƴar Alamun kunya kadan a Tare dashi

"To yanzu ya za'ayi da shirye-shiryen komawar mutane gida?, Kaga duk don kai sukazo, kuma ya kamata ka haɗa wa kowa sha tara na Alkhairi Saboda mai sonkaene kawai zaizo inda kake a lokacin da ka zama gawa."

Kafin Aayaan ya bada amsa saiga Colonel ya fito daga ɗakin da ya sauka riƙe da madaidaiciyar jaka , mummyn Aayaan ya gaisar dayake sun gaisa da Aayaan tun a masallaci
"Na shirya zan tafi, son Allah ya ƙara sauƙi ya kiyaye gaba, sai yaushe kuma zamu haɗu?"

Murmushi Aayaan yayi tare da cewa "sir ai ko gobe kake son ganina i am ready to come"

"Nop bazan ma so ganin kaba, yanzu dai ka tsaya ka ƙara samun kwarin jiki sannan ka kulamin da daughter na sosai."

Har Cikin mota Aayaan ya rakashi, sosai ya lura Akwai magana a bakin Colonel Amma yaƙi yi, ganin be faɗa ba sai kawai ya basar shima ya koma gida.

Koda ya koma cikin ɗaki tarar da Nawaz yayi tanata sharar barcinta hani'an, murmushi yayi tare da sunbatar ta a goshi Sannan ya gyara mata kwanciya, kuma fita yayi domin ya samu ya gama haɗa komai da yakeso ya haɗawa yan Zaria tunda sune waɗanda zasu fara tafiya.

Fam ya cika musu Boot da kayan masarufi, Sannan yaba security Dinshi dubu ɗari ɗari yace idan sun sauke kowa ya basu, dakyar aka samu Sarfraz ya yarda cewa zai koma, amma da fir yaƙi, dama masu komawa zaria ɗin, mummyn sarfraz ce da daddy sai ummin Nawaz da Sarfraz ɗin kanshi, sai kuma wata innar hassu.

Tuni gida ya fara komawa NORMAL saboda waɗanda ke nan cikin Maidugurin duk sun tafi, kamar su baffa da sauran yan gidansu kakannin Nawaz, da waɗanda suka samu zuwa daga gidan surukan Aseey dama kakannin shi Aayaan ɗin kanshi..

Bashi ya samu sukuni ba sai wajen ƙarfe goma, koda ya koma cikin ɗakin barci ya tarar Nawaz nata sharɓa, a gefen side drawer kuma ga vacuum Flask da warmer Alamun an kawo mata break fast.

"Wai ko dai har yanzu allurorin data sha basu gama sakin taba ne?, Tun jiya da dare fa take barci"

Daƙyar ya tasheta ya bata Abincin Sannan sukayi wanka, laptop ya kunna yana nuna mata wasu sabbabin site da yakeso ta zaɓi wanda take so, ji yayi yanata magana amma shiru babu Amsa, waigawar da yayi sai ganin Nawaz yayi tanata kwasar barci abinta.

Girgiza Kai yayi yai murmushi sannan ya kashe laptop ɗin, gyara mata kwanciya yayi Sannan ya fita zuwa falour.

Anan yaga muhsin wanda gaba ɗaya ya manta dashi, da gudu ya tawo ya faɗa kanshi yana dariya "Uncle yanzu uncle saddam ya dawo dani daga gidansu gwoggo (surukan Aseey) yace ma wai yanata kiran wayar ka bata shiga, kuma wai in gaishe ka.

"Ina ansawa dear, zakasha chocolate?"

Aseey ce tace "Babu wani chocolate da zaisha Don Nima inaso na zauna da dan uwana mu tattauna, da yanzu Shikenan bazan Kuma ganinkaba da Nawaz bata hana a kaika ba, gaskiya bro Nawaz mutum ce, kuma Rahma ma ce a tattare dakai da muma baki ɗaya, wai kam kaga yadda ta fiyace ranar da aka sanar cewa an saka muku bomb?" Haka Aseey ta zauna ta zayyanewa Aayaan komai da Nawaz tayi. Shi dai shiru yayi yana ƙara yiwa Allah tasbihi a Cikin zuciyarshi

Mummy ce ta fito da sauri kamar zata tashi sama, fuskarta cike da tashin hankali "Aseey je kira Aayaan" ta faɗa ba tare data lura da Aayaan dake zaune cikin sofa ba

"Mum gani nan" cewar Aayaan da alamar damuwa shima tattare dashi, saboda yadda yaga Mummyn nashi cikin tashin hankali

"Yauwa Aayaan! Yanzu na gama waya da Naufal wai mummyn su ta Rasuu"

A zabure Aayaan ya miƙe tsaye cikin tashin hankali saboda zuwa yanzu yasan meye mutuwa "mummy shi colonel ɗin yana ina?"

"Yana gefe shima amma dai bamuyi magana dashiba" mummy ta faɗa cikin kololuwar tashin hankalin da yake nuna taji mutuwar ƙawar Tata.

Aseey ma tsaye take ta rungume hannayenta tana tuna irin alkhairin matar a gareta, "mummy wai dama batada Lafiya ne" Aseey ta tambaya cikin jimami

"Eh batada lafiya paralyzed ya kamata bayan kin koma England."
ALLAH sarki rayuwa, Allah ya jikanta yasa ta huta, wallahi naji mutuwar baiwar Allahn nan, akwaita da haƙuri da kawaici ga mutunta ɗan adam.

Shiru Aayaan yayi yana nazari inda daga bisani yace "zuwa Abuja fa ya kama mu yau ɗin nan,"

Mummy bata hana ba saboda itama tanaso taje gaisuwar ƙawar tata, "kowa ya shirya kafin karfe huɗu Flight ɗin yamma zamu hau" Aayaan yace yana nufar dakinshi.

Zare ido yayi ya tsaya yana kallon Nawaz da mamaki ganin ta tana..........

Kwana biyu kun jini shiru ko, Ammin rasuwa ne, ina yiwa kowa Fatan Alkhairi.... Allah ya yafe mana kurakuran mu

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*84*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Zare Ido yayi ya tsaya yana kallon Nawaz da mamakin ganinta tana Sallah, "dear jinin ya tsaya ne?" Sai kuma yayi shiru sanin babu me bashi amsa tunda Sallah takeyi

Gefe yaja ya ɗauki medium ɗin luggage ya fara zuba musu kayansu, yawancin na Nawaz duka Abaya ya zaɓar mata, shima dai ba wasu kaya bane na Azo a gani ba.

Yana gama shiryawa itama dai-dai lokacin ta idar da Sallar "my soulmate Naga kana haɗa kaya a akwati?"

"Dear wallahi zuwa Abuja ne ya kama mu urgently, yanzu mum ta gama waya da Naufal wai mum ɗinsu ta rasu?"

Duhu Nawaz ta shiga domin bata gane inda zancenshi ya dosa ba "dear waye Naufal?"

"Au na manta baki sansu ba, yaran colonel ne Naufal da Fudail, Amma dama ba wannan data rasun bace ta haifesu, tun suna jinjiraye maman su ta rasu bayan ta haifesu, to shine a garin su aka bashi auren wannan data rasun, Matace mai karamci da mutunci sosai, munsha zuwa gurinta muyi hutu sanda daddyn mu yake raye, ƙawar mummy ce sosai."

Rausayar dakai Nawaz tayi, irin Alamun tausayin nan, "Allah sarki, Allah ya jiƙanta yayi mata rahma yasa ta huta, mu kuma Allah ya bamu ikon yin Abinda mukazo duniyar yi"

"Ameen dear thanks, yanzu muje muyi wanka saimu shirya saboda su mummy na jiranmu,"
Tsayawa yayi yana kallonta sai kuma ya kanne ido ɗaya as usual "ko na tsaya na Angonce tukuna? Kinga sai muyi wankan mu me hujja koh"

Ita dai Nawaz shiru tayi kanta a ƙasa batace komai ba, shima be kuma cewa komai ɗinba ya sunkuceta zuwa bathroom, "wasa nakeyi miki fa, ai yaci na barki kiɗan huta koda na kwana uku ne, kada naje a kuma yin tuntuɓe da wani cikin a bakin ƙofa"

Duk da cewa Nawaz ba wani kunyarshi takeji yanzu ba amma Saida maganar shi tasata rufe ido tana dariya ƙasa-ƙasa.

Bayan wasu Yan mintoci har sun shirya abinsu, tsaff sukayi gwanin ban sha'awa, sai tsokanar Nawaz Aayaan yake tayi barin ya lura tanata ɗan kannewa "yasan tsoron haɗuwarsu takeyi domin yasan da tasan zai shigo ya ganta tana Sallah da batayi lokacin ba.

Ta ɓangaren Nawaz kuma duk sai take Dan jin fargaba na kamata kaɗan saboda yadda taga yanata nan-nan da ita, gashi dama an daɗe ba'a haɗu ba, kuma tasan Aayaan har dai ya chafke ka saiya ƙureka duka sannan zaice zai fara komai.
Tunawa tayi da second night ɗinsu yadda tasha fama, Saida tsigar jikinta ta tashi saboda tunawa da tayi da irin aika-aikar da yayi mata, har kuka tayi wiwi akan ya dena amma ko'a jikinshi (wai an yakushi kakkausa).
Ita ba komai ke damunta ba irin yadda yake tasa ta da taɓe-taɓe, taɓa chan taɓa nan, matsa nan, matsa chan, tsotsi nan tsotsi can, duk saiya ƙureta tass taji kamar numfashinta zai ɗauke, dama ace idan yazo Abinda yazo yi zaiyi ya wuce amma ita tasan ta shiga ukunta, duk abinda yasa jikinta yin sanyi kenan, barin dataga duk motsi saiya kashe mata ido tare da ɗaga gira.

A falour suka haɗu dasu mum duka don tafiya Airport, mummy na matukar jin daɗin Yadda Aayaan da Nawaz suka fahimci junansu, Aseey ma haka.

*Some hours later....*

Su mummyn Aayaan ne da Aayaan ɗin da Aseey da Nawaz sai Muhsin, zaune a Babban falourn baƙi na gidan colonel, falourn cike yake da masu Amsar gaisuwa, kowa kagani kasan ba'a cikin kwanciyar hankali yakeba.
Mummy ma sosai hankalinta ya tashi ganin da idan suka zo gidan ita marigayiyar suke gani taita hidima dasu.

"Lokacin sallar magrib yayi, bari muje masallaci" cewar colonel yana miƙewa tare da dafa kafaɗar Aayaan, ita dai mummy na zaune sanye da hijabi tanata jan chasbaha.

Aseey da Nawaz ma haka suna gefe a zaune sunyi jugum-jugum, bayan su Colonel sun fita ne suma suka tashi don gabatar da tasu sallar.
Chapter 100 · 0% Book details