Sashe 43
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Muryar kuka Nawaz tace "umminaa don Allah kisa baki Adawo dani gida Wallahi na gaji da zaman nan, ke kawai nakeso na gani.
Ajiyar zuciya ummin tayi "akwai wata Matsala ne ko akwai wani abu da suke yi Miki?
"Ummi babu wata matsala Wallahi suna sona kuma suna kaunata fiye da zato, kowa burinshi ya kyautata mun, amma Ni kawai nagaji ne kuma ke nakeso na gani...
Sosai ummin Nawaz taji daɗi jin ɗiyarta tana cikin kwanciyar hankali, har Saida murmushi ya kufce mata "to Nawaz abinda nakeso dake Yanzu kiyi hakuri, saura kwanaki ƙalilan komai ya daidaita.
"To ummi shikenan nagode, yasu amma da kawu? "Duk suna lafiya" cewar umma
Sai ta kuma cewa "Nawaz don Allah nasanki da ladabi da kunya da kawaici da son Duk Wanda ya raɓe ki, to don Allah kici gaba a haka koda wasa ban yarda kiyi wani abu dazai ɓatamusu Raiba, Mutanen nan ƴan halal ne, musamman Aayaan wallhi Yaron kirkine bakiga abinda yayi mana ba, sai kinzo mamaki zai kamaki.
" Ummi Aayaan ɗin yazo nan ne?
"A'a ba kuna tareba? Ummi tace Cikin mamaki
"Ummi Bama tare kuma tun shekaran jiya da dare ban kuma ganinshiba.
"To wannan wayar waye kika kirani da ita?
"Shi ya siyan mini rannan da muka fita, Nawaz tace cike da kwarin gwuiwa.
"Allah sarki Wallahi yaron Akwai hankali, to me zai hana idan mun gama waya yanzu sai ki kirashi kiji ko lafiya!
"Ummi banida numbershi fa.
''ki amsa gun mummy mana yanzu idan mun kashe wayar..
"To" Nawaz tace haɗe da cewa ummi Don Allah kice ina gaida baffa da amma da kawu...
Haka dai suka gama magana sukayi Sallama.
Ajiyar zuciya me nauyi Nawaz ta sauke "ummi batasan meyake faruwa bane shiyasa zatace na amshi numbershi, cigaba da danna wayar tayi, ta shiga nan ta fita nan, aikuwa saita shiga contact gwalalo Ido Nawaz tayi ganin wata number anyi saving ɗinta ta "Aayaan your husband"
Shiru tayi tana tunanin Lallai Aayaan Akwai ƙarfin hali, ko yaushe yayi saving ɗin number Oho.
Tunani ta fara yi akan ta kirashine ko kuma ta share? To idan ta kirashi ma me zata ce mishi?
Wata zuciyar ce tace mata kiyi text message kawai, aikuwa sai yaji tayi na'am da hakan, message ta shiga ta fara rubutu kamar haka
```ASSALAMU ALAIKUM```
```Barka da war haka! Fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ban san wane laifi nayiba da har yasa kayi tafiya ba tare da munyi sallama ba, sannan kowa be faɗa minba, babu wanda ya taɓa yimin maganarka...```
```ina fatan a duk inda kake ka kasance cikin aminci da farinciki, abokiyar faɗan ka Nawaz```
Sai bayan ta tura kuma taji wata fargaba ta kamata, "to idan ya kirata kuma me zata ce mishi? Sai kawai tayi sauri ta kashe wayar ....
Aayaann yana zaune yaji ƙarar shigowar message, be damu daya duba ba domin ba wannan bane a gabanshi, shi yanzu damuwar shi taya zaiji daga gurin Nawaz...
Miƙewa yayi da nufin ya shiga ciki ya watsa ruwa, daukar wayar yayi ya duba Lokaci ai kuwa idonshi yayi tozali da number da yayi saving da hayaahtih ta turo message, ba shiri ya danna, yama ƙosa ya karanta abinda message ɗin ya ƙunsa, aikuwa yana gama karantawa ya daka wani irin uban tsalle tare da rungume wayar "Alhamdulillah! That means itama ta fara damuwa dani, kenan zata soni, ya Rahman, ya Rabb Nagode, Nagode.......
Dialling ɗin number yayi amma bisa rashin Sa'a sai aka ce switch off, hakan ya kara mishi zaƙuwa akan ya koma gida dukda yanzu kashi tamanin da Biyar na damuwar ya nemeta ya rasa, ai kuwa idan ya koma ko me Nawaz zatayi wallahi saiya rungumeta na minti biyar, ai yaci a tausaya mai, cikin gida ya shiga ya cewa su Naufal (yaran Colonel) su shirya zai kaisu shopping inda shi kuma ya wuce gefenshi ya faɗa bayi yanata murmushi.... So yake yaje ya jidowa Nawaz kaya a mall ɗin idan sun fita......
*_~"GASHI NA MUKU DA YAWA SABODA KWANA BIYU BANYIBA, KUMA DUBADA ABINDA YA FARU BA LALLAI KU RIKA SAMUN UPDATE KULLUM BA, MASU BINA PRIVATE DA MASU YIMIN JAJE A GROUPS NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR KAUNA."~_*
*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*Episode 43*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Sosai Hassu take fama da SARFRAZ, domin abin nashi ma kamar ƙara gaba yakeyi, don a halin yanzuma mummy yake cewa Hassu.
Kuma kullum sai dai ya kwanta a cinyarta, tun bandi na hanawa har ya gaji ya Dena.
Zaune Hassu take ta Miƙe kafa sarfraz yana kwance a cinyarta, ita kuma tana Amfani da metilated Spirit tana wanke mishi ciwo, shikuwa sai raki yakeyi akan idan bata denaba babu ruwan shi da ita, kuma bazai sammata biscuits din Shiba idan bandi ya siyo mishi.
Da sauri bandi yace "a'a sarfraz rabani da shirginku babu ruwana domin Nima ba kyaleni kayiba"
Sosai Hassu tayi dariya "babban yaya ayi hakuri muna neman sulhu ne...
Haka dai suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'awa Kamar yadda suka saba kullum.
Tsintar SARFRAZ sukayi amma Yanzu ya zame musu wani sashi na rayuwa, sun san cewa idan SARFRAZ yaji sauƙi Dole ne ya koma Cikin ahalinshi, to amma yaza suyi tunda ba gida ɗaya suke ba, hassu duk tafi shiga cikin damuwa idan ta tuna cewa wata rana ko tanaso ko bata so dolene su rabu da sarfraz, har hawaye takeyi idan ta tuna hakan....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sosai Aayaann yayi ƙawalliya sannan ya feshe duka jikinshi da turare, cike da kuzari ya shiga babban falourn Colonel Yana kwalawa su Naufal da fudail kira.
Mamakine ya kama Colonel wanda shigowar shi kenan "son what causes the sudden change? Wow gaskiya naji daɗi my real Aayaan is back.
Dariya Aayaan yayi "sir ka bari in dawo zan faɗa maka abinda ya faru yanzu zamuje shopping ne dasu fudail.
"A lallai! Masha Allah haka nakeso na riƙa ganinka kullum cikin karsashi da kuzari.....
Su Naufal ne suka karasa suna murmushi "Auncle mun shirya mutafi.
Sallama suka yiwa colonel Sannan suka fita daga faloun zuwa harabar gidan.....
Ɗaya daga cikin securities ɗinshi yayiwa magana akan ya tuka su, sannan Dukansu suka shiga baya suka zauna
Wayarshi ya ciro yana murmushi sannan ya daɗa buɗe inbox yana fldaɗa karanta message ɗin da Nawaz ta turo mishi, daɗi sosai yakeji, kuma sosai zuciyarsa take ƙara mishi kwarin gwuiwa akanta yanzu.
Samun kanshi yayi dayi mata reply da.
*_Wa'alaikis salaam matar Aayaan_*
*_ina lafiya lau Alhamdulillah kuma kema ina fatan kin yini lafiya, ya Bayan rabuwa?_* *_wato bakima san abinda kika minba ko?_*
_*Shikenan babu komai nakusa dawowa, ki tanadar mini tarba me kyau*_
_*Mai sonki ba abokin faɗan kiba AAYAANN*_
Bayan ya tura mata sai murmushi yakeyi, bai ankara ba yaji su fudail suna cewa Uncle "munzo sharaton mall ɗin"
Namfa ake yinta! Duk Abinda hannun shi yakai sai dai ya saka a basket, yayi siyayyah ta wuce tsammani, suma su Naufal sai jida sukeyi saboda dama yace musu su zaɓi duk abinda suke so....
Haka aka cika Boot dam da kaya sannan seat din baya shima haka, dole suka koma daya motar securities ɗin da suke binsu a baya domin gurin bazai isaba.
Bayan sun koma gida ne Aayaan yasa securities suka kwashi siyayyar su Naufal suka kai musu ɗaki, inda shi kuma yabar nashi a Cikin motar...
Sosai colonel yake farinciki domin ya lura Aayaan ya warware sosai, sai dai besan silar warwarewar tashi ba.
Kallon Aayaan yayi Sannan yace "Son zo ka zauna a kusa dani! Zamuyi magana.
Kusa dashi Aayaann ya ƙarasa ya zauna yana murmushi ba tare da yace Komai ba.
"Son kasan cewa munada passing out a N.M.S Nan da kwana biyar?
Muskutawa Aayaan yayi Sannan yace "No sir Wallahi ban saniba.
"Okay to shikenan yanzu koda an gama meeting ɗinmu bazaka tafiba, ka tsaya saimu tafi tare chan Barack ɗin Koh?
Wani Irin saukan aradu ne me kamar guduma ya dirarwa Aayaan a zuciya _ya za'a yi yadda naketa murnar komawa gida ace kuma saina ƙara wasu kwana huɗu a gaba?_ abinda Aayaan ya raya a zuciyarshi kenan.
Aikuwa baiyi ƙasa a gwuiwa ba yace "sir gaskiya I can't wait that long"
"Amma meyasa? Abinda yasa nace ka tsaya shine saboda naga garinku da nisa sosai bazai yiwu daga komawarka ace zaka kuma ɗauko hanya ka dawo Zaria ba, kuma kaga Zaria hanya ce, ana gamawa saika wuce gida kawai.
Murmushi Aayaan yayi "sir na manta ban faɗa maka ba, ai ko wannan zuwan danayi daga Zaria nazo saboda dukanmu nida mummy da Aseey munzo gidan yar uwar mummy ziyara.
"Au Masha Allah, to ai Shikenan ma faɗuwa tazo dai dai da zama, yaushe Aseey tazo?
"Bayan mun rabu dakai mun tafi gida, inaga washe gari tazo.
Gyara zama Colonel yayi "Masha Allah, sunzo lafiya dai ko? Ina muhsien abokina..
Aayann yace "sunzo lafiya, Muhsin ɗan rigima yana can nabarshi da Nawaz.
Sai Sannan Colonel ya tuna da zancen Nawaz "Aayaan namanta sam in tambayeka meyasa bakazo da daughter ba, kuma ka bada uzurin ƙarya?
"I'm so sorry sir, wallahi Nawaz ɗin ce tace ita bata son zuwa, sai Mummy tace to na kyaleta kawai....
Miƙewa colonel yayi "hakanma yayi, bari na shiga ciki barci ya fara rinjayata saboda kwana biyu ban samun yin barci isasshe..
"Okay Sir goodnight" Aayaan yace shima yana miƙewa.
Ɗaki ya shiga ya kwanta, yanajin daɗin cewa ya kusa zuwa yaga hasken rayuwarshi.
Numberta yayi dialling amma switch off, murmushi yayi Kasancewar yasan kashe wayar tayi bawai chaji bane babu, kunyar Nawaz tana matuƙar burgeshi shi yasa ma take ƙara shiga mishi rai.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Nawaz ce kwance gefen Aseey da wayarta a hannunta tana jijjuya ta, bayan ta gama shirin kwanciya,
Aseey tayi nisa sosai a chatting ɗin da takeyi da baban muhsien, sosai takejin daɗin hirar tasu saboda yana faɗa mata yanda yayi missing ɗinta, shiyasa ma yau basuyi hira da Nawaz ba.
Shahada Nawaz tayi ta kunna wayar tana salati a cikin zuciyarta.
Aikuwa wayar na gama booting message ɗin Aayaan ya shigo, ta daɗe tana wasi-wasi akan ta buɗe ne ko ta barshi.