← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 112

Sashe 31

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani daɗi Aayaan yaji domin dama saboda ita ya fito sai gashi kuma Allah ya haɗasu...

Kitchen ɗin ta shiga yana biye da ita a baya kamar jela,
Babban deep freezer ɗin dake cikin kitchen ɗin ta buɗe ta ɗebo iya fruit ɗin da zatayi amfani da shi...

Yana tsaye yana kallonta har ta gama haɗa mishi, mika mishi tayi "gashi na gama Saida safe....

"Nagode, good night and sweet dreams.....

Bata bashi amsaba ta wuce ya fita daga kitchen ɗin....

Cewa Aseey dake zaune tana kallon zee world tayi "auntie Saida safe zanje na kwanta.....

" Okay dear sweet dreams, good night.

Ɗakin ta shiga sannan ta samu Guri taci abincin ba Wani da yawa ba saboda tana fargaban me gobe zata tarar a zaria....
Kuma tana tunanin kada mummyn sarfraz tace ita tayi sanadiyar ɓata ko mutuwar ɗanta ...

Ahaka Sarkin ɓarayin duniya ya lallaɓo ya saceta bata saniba ...

Tunda Nawaz ta tashi sallar asuba bata koma ba, kitchen ta shiga ta haɗa musu break fast da kuma snacks ɗin da idan suna hanya zasuci, tunda tafiyace me nisan gaske ....

Saida ta gama sannan ta shirya tanata addu'ar Allah yasa Kada Mummyn sarfraz ta tsaneta....

Aayann ne ya fara fitowa, ganin warmers yayi manya a saman center table, zuwa yayi ya buɗe yana tunanin meye kuma a ciki?
Egg roll ne da meat pie 🥧 harda cake 🍰 cike a cikin warmer ɗin..

Ɗayar kuma soyayyen Irish ne da plantain sunata turiri....
Be jira komaiba ya nufi dining ya ɗauko mug da karamin plate ya dawo, Black tea ya haɗa sannan ya duba abubuwan da suka mishi ya Fara ci yana murmushi, ko ba'a faɗa mishi ba yasan wannan aikin Nawaz ne, domin yasan Aseey bata cika tashi da wuri ba balle kuma yau jiya ta iso ƙasar dole tayi barcin gajiya....

Hamdala yayi bayan ya gamsu da abincin sannan ya miƙe ya koma ɗaki don shirya wa,
Aseey ce ta fito a firgice "Wallahi sam na manta zamuje wani guri, gashi har takwas ta kusa ba'a dafa komai ba balle mu tafi, muda zamuyi sammako....

Turus ta tsaya ganin Manyan kuloli a Saman table sannan ga mug da plate a gefe alamar anci wani abu, da sauri ta ƙarasa ta buɗe kulolin.

Da gudu ta koma dakin mum tana cewa mummy Wallahi she is the perfect match, Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi....

Mum taji daɗi sosai bayan Aseey ta faɗa mata ai Nawaz har ta gama komai.

Sai shi mata albarka takeyi taba ƙara jin wata kaunar Nawaz a Cikin zuciyarta...

A gurguje suka ci abincin sannan suka shirya zuwa falour, oga muhsien kuwa ihu ya riƙa yi waishi Aunty ce zatayi mishi wanka da kyar ya yarda...

A falour suka tarar da Aayaan ya zuba uban ado sai ƙyalli da tashin kamshi yakeyi,
Aseey ce ta kalli mum suka haɗa Ido sai kuma suka kyalkyale da dariya a tare ..

Tsaf yasan dashi suke amma sai ya basar be tanka musu ba tunda ya lura kwana biyu sunsa mishi ido.
Da gudu muhsien ya ƙarasa gurinshi Yana cewa "Uncle kayi kyau,

Aseey kuma taje ta kira Nawaz...
Godiya sosai mummy tayi mata na abincin data dafa.
Ita dai Nawaz nata iya murmushi ne...

Tsaff suka tarar da securities ɗin sun shirya, har sun buɗe musu kofofin motar da sauri Aseey ta shige baya tana murmushin da ita kadai ta san manufar shi.
Mummy ma zama tayi abayan.

Nawaz kuma sai ta tsaya tayi shiru ita gaskiya batason zama a gaba barin tasan Aayaan ne zai tuka motar ..

Saurin zuwa gaban mummy tayi tace mummy bari naje waccan motar kawai kinga nan bazai ishemuba kinga ya Aayaan zai zauna a gaba Sannan ga driver kuma kinga ga muhsien..

"Haba daughter kizo mu zauna mana anan, ya za'ayi ki tafi ke kaɗai ...

A'a mummy kada ki damu, saurin buɗe motar bayansu tayi ta shiga Domin ko banza ta samu ta sake tayi baccinta son ranta.
Tana shiga shima Aayaan ya mikawa Aseey muhsien ya Kalli mummy yace Nima bari na shiga waccan ɗin kawai kada a barta Ita kaɗai kinsan baƙonka annabinka...

Be jira me zataceba yaba driver's ɗin umarni sannan ya buɗe baya inda Nawaz take ya shiga, daskarewa Nawaz tayi tana kallonshi cikin mamaki...

Suma can mummy da Aseey ne ke mamakin wai yaushe Aayaan ya zama haka, Lallai kam soyayya bata ɓuya, mummy kam sai farinciki takeyi domin zatafi kowa jin daɗi idan Aayaan da Nawaz sukayi auren soyayya..

A ɗaya motar kuma Aayaan ne yaketa yiwa Nawaz wani shu'umin murmushi "nasan Saboda Ni kika gudo wannan motar shiyasa Nima na biyoki, kuma yanzu ina sauraren ki ki bani amsar tambayar danayi Miki juya inba hakaba kuma na.........

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 33*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Jin abinda Aayaan yace yasa Nawaz tayi saurin matsawa gefe ta bashi tazara sosai.

Matsawa kusa da ita ya ƙarayi "so kin yarda inyi Miki duk abinda naga dama kenan?

Kwaɓe fuskarta tayi "nifa ya Aayaan don Allah kayi hakuri, Ni bansan meyasa ba, kuma Ni wallahi kunya kake Sawa inaji. Ta karashe zancen cikin Muryar shagwaɓa Wadda ita batasan ma tayiba.

Murmushi kawai Aayaan yayi "shikenan nabarki yanzu but ya zama assignment, zaki nemomin amsar bayan mun dawo gida.....

Nawaz kuwa mamaki abin ya bata "wai inmun dawo gida, sai aka ce mishi a garin zanta zama kenan.

Komawa tafiyar kurame akayi saboda babu Wanda ke cewa ɗan uwanshi ƙala. Kowa akwai abinda yake saƙawa a zuciyarshi.....

Cikin husky voice dinshi taji yace: naga kamar kinajin barci, ko in gyara Miki kirjina ki kwanta akai naga you feel safe there, saboda rannan ma har muka dawo gida baki tashiba.

Ruɗewa Nawaz tayi, sam ita bataso yanayi mata haka, a yanzu gani takeyi ma Aayaan yafi SARFRAZ rashin ta ido....

"Ni banajin barci, Nagode. Shiru Aayaan yayi ganin beci sa'ar neman zance ba, saboda katse maganar tayi bata yarda Tayi tsawo ba....

°
Achan ɗaya motar kuma mummy ce keta murmushi.

"Mum what's good? Naga kinata murmushi ne, cewar Aseey wadda ke sonjin ƙarin bayani daga bakin mummy.

"Wallahi daughter wani ci gaba naga yanata samun mu.

"Mummy wane cigaba ne, cewar Aseey cikin son jin amsar mummy ta gaba.

Mummy tace "Aseey Kinga tun randa Allah ya haɗa fuska ta data Nawaz naji wata irin ƙaunar ta acikin zuciya ta, kuma take nayiwa Aayaan sha'awar ta a matsayin mata kuma cikin ikon Allah da mukaje chan gidan kakanninta sai na lura kakanta baffa yanamin hannunka mai sanda, yana nunamin zai ba Aayaan ɗin Auren Nawaz amma sai an shirya...

"Kai kai kai Alhamdulillah, Allah yasa hakan ya faru, domin idan haka ya faru sainafi kowa jin daɗi domin naga Nawaz ɗin akwai hankali da kunya.

Numfasawa mum tayi "kuma abinda yasa nakejin daɗin, baya wuce ganin Aayaan yana nuna zumuɗi akanta. To amma dai bansan manufarshi ba.

Aseey tace "mum amma gaskia akwai matsala.

Da sauri mum tace"Aseey wace matsala ce kuma?

" Kada ki tada hankalin ki mum, bawai wani babban abu bane, na lura da wani abune daga gurin Nawaz ɗin.

Mum ce tace "Ƙaniyarki Aseey wato Ni kike jawa rai koh? Come"on zaki faɗa min ko kuwa saina saɓa Miki!

Wai dama gani nayi Nawaz na mugun jin tsoron Aayaan, kuma ko yanzu ma saboda shi taƙi shigowa motar nan, Gashi kuma ya bita....

"Tsoro kamar ya? Cewar mum tana kama haɓarta

Gyara Zama Aseey tayi "mum Nasha ganinsu tare, sai inganta ta firgita shikuwa yayita murmushi, nifa gani nakeyi kamar daɗi yakeji idan yana bata tsoron.

"Oh shikuma Aayaan irin tashi soyayyar kenan, Lallai Amma Allah ya zaɓa mana Abinda yafi Alkhairi....... Mummy tace tana gyara zaman muhsien wanda tuni yayi barci a cinyarta...

Ƙarar shigowar kiran mijin Aseey ne a waya yasa mum yin shiru ita kuma Aseey ta ɗaga fuskarta cike da murmushi.....

°
Aayann nanan yanata faman neman hanyar dazai tsokani Nawaz amma Sam taƙi biye mishi,

Murmushi ya saki sakamakon wani abu daya tuna.

Gyaran murya yayi "sister nifa ban yarda cewa sarfraz ba saurayinki bane, duba da abubuwa da yawa, bayan nan kuma da Yadda kika damu dashi.

Wata lukutar harara ta zabga mai "me kake nufi? Nifa naga ka damu da zancen sarfraz ne, ina ruwanka dashi? Kuma ko da shi ɗin saurayinki ne meye ruwanka?

Hamdala Aayaan yayi azuciyar shi, shi dama so yake suyitayi, sai gashi cikin sauki Allah ya kawo mishi mafita.

Niko nakeda ruwa kuwa, sannan inason nayi investigation ne akan shi,. Domin Ni sam banma yarda dashiba, ya za'a ayi ace ba'a ga mutum ba sam...

Ran Nawaz ne ya ɓaci "kanaji Ni babu ruwana idan munje can gidan nasu sai kayiwa iyayenshi bayani, pls kabarni da iya fargabaar da take damuna.

"Fargaban me kikeyi?

Hawayen da taketa riƙewane suka zubo a saman kumatun ta "babu ruwanka dani"

"Haba sister daga tambaya? Nifa banyi haka don in ɓata Miki Raiba, pls i am sorry kibar kukan.. beso kukan nata ba shi yayi hakane don ya tsokaneta tayi magana

Kara fashewa da kuka Nawaz tayi "nifa tsoro nakeyi kada Mummyn sarfraz tace Ni na batar mata da yaro, kuma Ni bansan ta yadda zan iya shiga gidansuba.

Aayann ya fahimceta sosai kuma yasan tabbas ko shine haka ta faru saiyaji fargaba bare Nawaz daya lura tanada sanyin hali "ki kwantar da hankalinki, Insha Allah babu abinda zai faru zanyi Mata bayani kinji.

Gyaɗa kai Nawaz tayi,

Hannu yasa a aljihu ya ciro wani farin hankie me kyau sai kamshi yakeyi " amsa wannan maza ki goge hawayen cry cry.
Amsa tayi tana rufe fuska dashi...

Sai motar tayi shiru kowa da abinda yake tunani....

Sai wajen ƙarfe daya suka isa Kano, driver's ɗin ne sukayi parking saboda ganin lokacin sallah yayi, kuma sunsan oga Aayaan baya wasa da Sallah....

Wani store ɗin Rufaidah yogurt Aayaan ya shiga ya kwaso musu yoghurt dasu ice cream....

Su kuma su mummy suna cikin Masallacin dake gefen store ɗin duk sunyi Alwala suna jira Aayaan yazo ya jasu sallah, dayake an riga an idar a masallacin..
Chapter 31 · 0% Book details