← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 112

Sashe 87

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar daga sama yaji Nawaz tace "I'm all yours kuma ko me kayi niyyar yi dani kayi na baka dama, to meye ma amfanin yin auran namu tunda bazamu iya cire juna a cikin damuwa ba? And kuma ina neman yafiya a gareka na wahalar da kai da naketa yi akan haƙƙin ka, don Allah kayi hakuri ka yafe min wallahi nayi maka alƙawarin bazan kuma ba"
Ɗagota yayi daga jikinshi sannan ya tashi zaune, kallonta yakeyi kamar be taɓa Ganin taba "sweetheart kece kikayi magana yanzu ko kuma kunnena ne yakemin gizo?
Murmushi Nawaz tayi tare da cewa "Nice nayi ba kunnenka bane, cewa nayi Ni taka ce dama kuma kayi duk Abinda kaga dama dani, kuma ina roƙonka daka yafemin cutar dakai da nayi tayi saboda nawa son zuciyar mara Amfani"

Farinciki ne da murna suka kama Aayaan lokaci ɗaya, ji yake kamar ya ɗauki Nawaz ya haɗiye ta ya huta "dama akwai ranar da zata ƙaunaceshi kamar haka? Lallai mahaƙurci mawadaci."

Janyota yayi ta faɗo jikinshi Sannan yayi hugging ɗinta sosai, Magana ya fara yi a hankali kuma cike da bata kwarin gwiwa "Sweetheart i promise you I Will be extra gentle, and kuma kema inaso ki fito da wannan jarumtar taki yau zatayi mana Amfani, kuma ki cire duka kunyarki ki ajiyeta a gefe gobe da safe sai ki mayar"

Ita dai Nawaz lafewa tayi a jikinshi tana shaƙar kamshin jikinshi, gaba ɗaya maganin ya soma aiki gadan gadan, hakan nema yasa jikinta ya mutu gaba ɗaya.

Miƙewa Aayaan yayi Sannan ya ɗauketa in a bridal Way "zo muje kiga wani surprise, it's for you alone"

A gefen store dama akwai wata ƙofa, ita ya nufa ɗauke da Nawaz a hannunshi, dayake Nawaz ɗin bata da bin ƙwaƙwafi bata taɓa tambayarshi ƙofar ina bace.

Buɗe ƙofar yayi ya shiga ciki amma sai dai ba'a iya ganin komai saboda duhu, switch ya taɓa ya kunna, aikam wani irin haske ne ya gauraye ɗakin, babu irin kalar bulb ɗin da babu a ɗakin bayan cikashi da akayi da party lights.

Nawaz da kanta ta bukaci ya sauketa saboda ta samu damar ƙarewa ɗakin kallo, komai na dakin Golden colour ne sai ɗan ratsin fari a inda ba'a rasa ba. Babban gadone design ɗin Italy girmanshi har yayi yawa, kowane bango na ɗakin photon Nawaz ne tana barci, iya carpet ɗin dake kasan ɗakin ya isa abin kallo, saboda kana takawa kafarka zata nutse a ciki, ta kowace kusurwa kuwa wasu irin crystal glasses ne kamar diamond suna haske, duk da girman gadon da wardrobe ɗinshi da side drawers din amma ɗakin wargajeje, zaka iya rugawa da gudu ma,
Frame's ɗin dataga an ƙawata ɗakin dasu ta tsaya tana kallo, love quotes ne rubuce a jiki suma suna haske kuma a jikin ko wanne sai an rubuta *_NAWAZ AND AAYAANN ✓ FOREVER LOVERS_*

Zanin gadon kanshi wasu rubutu ne a jiki ƙananu kuma da alamu tare aka saka shi dasu, data ƙura ido sai taga ashe *Nawaz and Aayaan* aka rubuta cikin style ɗin heart.

Daɗi ya cika Nawaz rasa me zata yi ma tayi, sai kawai ta daka tsalle ta maƙale wa Aayaan Tare Da cewa "I LOVE YOU"

Kamar mutum mutumi haka Aayaan ya koma, shikam dai wannan juma'ar da wace Irin Sa'a tazo mishi ne? Ace wai yau shine tsaye a gaban Nawaz har ta furta mishi cewa *She love's him*
Rungume ta yayi da karfi Kamar zai maida ita cikin ƙirjinshi har saida tayi ƴar ƙara kaɗan Sannan ya sassauta mata rungumar"
Wayar tafi da gidanka dake saman chest drawer ya ɗauka tare dayin dialling Number reception Inda yace a kawo mishi ko wace kalar nau'in kaza da suka girka yau sai kalolin Madara suma.

*Ni kam matar Rasheed cewa nayi bari na leka Zaria kafin a kawo wa Aayaan kajin, nasan zuwa lokacin na dawo*

*DON ALLAH MASU TSALLAKE ZARIA YAU KU TAIMAKA MIN KADA KU TSALLAKE DOMIN IDAN KUKA TSALLAKE NA YAU BAZAKU TAƁA GANE ME LITTAFIN SARFRAZ YA ƘUNSA BA, SABODA KADDARAR KOMAI TANA CIKIN NA YAU NE, NAGODE 🙏🙏🙏*

*ZARIA NIGERIA.........*

A firgice umma ta tashi daga barcin data fara wanda bazata wuce minti Talatin da fara Shiba, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi Dalilin marfarkin datayi yanzu, "Fauziyya! Fauziyya!! Fauziyyah!!! Umma ke ƙwalawa Fauziyyah kira, wadda itama yau a gidan zata kwana saboda mijinta yayi tafiya kuma ya yarje mata tazo nan ta kwana saboda dama yaranta suna wajen surukarta.

Ganin fauziyyah tayi nisa sosai cikin barcin da takeyi yasa umma ta fara jan jikinta har saida ta sauka daga kan katifar ta nufi inda fauziyyah ke kwance, bubbuga cinyarta ta fara yi tana ci gaba da kiran sunan ta.
A firgice fauziyyah ta tashi tana mutsika ido "umma wa ya kawoki nan? Menene?"

"Tashi Fauziyyah barcin nan ba namu bane domin Allah ya nunamin abinda Ni sam nama manta ba aikata"

"Umma me kika aikata da bazaki bari gari ya waye ba? Yanzu fa Kusan karfe 3:30am na dare ne, (saboda tazarar awannin dake Tsakanin Nigeria Da England)
"Fauziyyah idan nace zan bari Saida safe to komai ma zai iya faruwa, don wannan lokacinne nake ganin zan fara yin Abin Alkhairi ga Nawaz "

"To umma menene?" Fauziyyah ta tambayi umma cikin zaƙuwa

"Fauziyyah Ni mahaifiyar kice, don haka bazan ɓoye miki komai ba saboda kin riga da kinsan halayena Marasa kyau, cigaba umma tayi da cewa "Fauziyyah gaskiya Allah yana sona da Rahmar shi, amma daba hakaba da tuni Mutane dayawa sun mutu sanadi na"

"Umma ki faɗa min menene yake faruwa? Don Allah ki dena jamin rai"

Cigaba umma tayi da cewa "in zaki tuna lokacin bikinki Abban ku yaso ya haɗa Auren Nawaz da naki Koh, to kinsan wani mashahurin me kuɗi ya samo mata, Ni kuma a Lokacin sai hassada ta kamani akan idan aka yi Auren Rahama zata huta ta Dalilin ta gashi kuma ke ba wani me kuɗi zaki auraba.
To alokacin dama wata ƙawata kande tanaso na rakata wajen wani boka amma bayarabe ne, to da mukaje ne naji tana faɗawa bokan cewa tanaso ne a fasa Auren yarinyar kishiyarta da za'a yi, to sai bokan yace mata Gaskiya bazai yiwu a fasa ba dole sai anyi bikin.
To alokacin ta shiga damuwa sosai saboda itama yarinyar me kuɗi ne zai Aure ta Gashi kuma ita yarta batada ko saurayi.

Ganin tashiga damuwa yasa bokan yace mata Akwai hanya guda ɗaya, hanyar itace zai turawa yarinyar aljanu waɗanda zasusa bazata taɓa bari mijin ya kusance taɓa, Kinga kuwa babu wanda zai yarda da Hakan, idan kuma mijin yayi taurin kai yace zaisa mata karfi to kuwa duk randa ya sake yayi kwanciyar Auratayyah da ita ai kuwa sai dai wani bashiba.

Jin hakan ba ƙaramin daɗi yayi wa kande ba, ta tambayeshi kuɗin aiki ya faɗa mata ta bashi muka dawo gida, to dayake dama sai an fara yin nasu bikin Kafin naku, aikuwa a Daren da aka kaita washegari akace mijin ya mutu, ita kuma yarinyar aka kamata, saida akasha fama sannan aka gane ba ita ta kashe shiba aka saketa daga baya.

Nikuma ganin abin ya faru da gaske shine naje gurin bokan nace inaso nima yamin irin aikin a kan Nawaz , maƙudan kuɗaɗe ya tambaye Ni, aikuwa nabashi saboda lokacin idona ya rufe da hassada.

To dazan tawo ne ya bani wasu kwai guda uku yace sune suke ɗauke da aikin, ɗaya zaisa mata baƙin jini, ɗaya kuma zai hana ayi Auren ta koda an samu miji, na ukun kuma shine koda ma anyi Auren mijin mutuwa zaiyi muddin ya kusanceta.

To kinji makircin da nayi, wallahi sam na manta da nayi wannan mugun abin, sai yanzu Allah ya tuna min, kinga kuwa da ace lokacin nan dana sasu suyi mata fyaɗe da sun samu Sa'a sunyi mata fyaɗen da mutuwa zasuyi, gashi yanzu tayi Aure, tsorona ɗaya kada mijinta ya kusanceta ya mutu.

"Kai umma wai yanzu kina nufin kicemin mijin Nawaz be taɓa kwanciya da ita ba?"

"Fauziyyah kada ki raba ɗaya biyu, be taɓa ba, saboda nifa ganau ce ba jiyau ba a wannan Abin, don yayinyar nan yanzu haka aurenta uku kuma duka mazajen a Daren Aurensu suke mutuwa, in takaice miki zance dai yanzu taƙi auruwa.
Kinga kuwa dole hankali na ya tashi kada inyi silar mutuwar bawan Allah, nauyin rai ya hau kaina, banda cikin Rahma da nasa akayita zubarwa saboda Kada ta kuma haihuwa.

"Innalillahi wa'inna alaihi raji'un, yanzu umma duk kishi ne yasa hakan?, Don Allah umma ki dage da tuba kila Allah ya yafe miki"
"Ba wannan ba fauziyyah, yanzufa mafarki nayi wai mijin Nawaz ɗin ya kusance ta harya mutu ita kuma an kamata ance za'a kasheta ta Hanyar rataya, tsoro nakeyi kada hakan ta faru, duk alhakin ransu a kaina zai rataya tunda nice silar komai, Ni yanzu uban zunuban ma dake kaina sun isheni ba saina ƙara wa kaina wasu ba"

"To umma yanzu ya za'ayi?"

"So nakeyi in faɗa Miki inda na binne ƙwayayan sai kije ki haƙosu ki fasa su duka"
" Umma don Allah ki bari gari yayi haske mana!"

"Fauziyyah ki duba darajar haihuwar ki da nayi kitaimakeni kije ki haƙe su, wallahi ji nakeyi kamar mafarkin nan danayi Allah ne ya turomin da saƙo, inajin idan ban fasa ƙwayayan nan ba komai zai iya faruwa zuwa gobe."

" To umma faɗa min gurin da suke inje in haƙosu in fasa"

"Yauwa fauziyyah Allah yayi miki albarka yasa ki gama da duniya Lafiya, kije bayi dai-dai dutsen da ake wanka akai, ki matsar dashi zakiga sashin sumunti, to shi zaki haƙe, idan kika cirosu ki tabbatar kin fasasu duka Don Allah."

Miƙewa fauziyyah tayi tare da cewa "to" Sannan ta fita, a zahirin Gaskiya tsoro ne fal zuciyarta amma kodon chanjin data gani daga mahaifiyar ta zata daure ta haƙe ɗin.
Chapter 87 · 0% Book details