← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 112

Sashe 39

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma Aayaan ganin nawaz ta tafi yasa yacewa Nafisa "bari mu tafi, kinsan Madam ɗin tawa Sarkin shagwaɓace, kuma dama tunda ta samu Wannan cikin tace wai ita kunya takeji.

"Hum aidama tun muna makaranta Nawaz Sarkin shagwaɓace, komai akayi sai tace umminta.

Hannu Aayaan yasa a cikin aljihu ya ciro sababbin Yan dubu dubu wanda baisan adadinsuba ya mikawa Nafisa gashi a siya wa yara biscuits dukda ban gansuba.
Da kyar Nafisa ta masa sannan tace eh ai basa nan duka suna gidan kakansu.

"Masha Allah, Allah yayi musu albarka, a gaida megidan, saimun kuma waiwayoku nida Madam, Aayaan yace yana kama hannun muhsien zuwa cikin mota.

Itama Nafisa ta koma gida tana mamakin Wannan mutum me sakin fuska haka, lallai Nawaz ta dace.

Wiwiw ya tarar da Nawaz tana kuka gaba ɗaya idonta yayi ja, hakama fuskar tayi ja kamar kosai kasancewarta fara sosai

"Haba maman muhsin meyasaki kuka?

Wata uwar harara da Nawaz ta balla mishi Saida yayi murmushi Sannan tace "malam babu ruwanka dani kuma wallahi kaci gaba da tsokanata, Sannan na rantse da Allah bazanje abujarba kasan yanda zakayi dasu.
Kuma ko kaƙi koh kaso gidanmu zan koma.

"🤔 Ooh Nawaz ɗin tawa dama tana fushi? Ikon Allah aini Nasha Bakya fushi.

Janyo ta yayi zuwa kirjinshi ya rungumeta tsam yadda bazata iya kwacewaba, mutsu mutsu ta rikayi tanaso ya saketa amma yaƙi Sakinta gashi ta kasa kwace kanta.
Sai Kawai tayi shiru ta hakura donta lura wahalar da kanta zata yi.

Kamshin turarenshi ne ya cika mata hanci gashi tanajin sound din bugun zuciyarshi da sauri da sauri, sai ɗumin jikinshi da a hankali ya fara ratsa nata jikin.

Shima ta bangaren Aayann hakane, yana sauraren nata bugun zuciyar, ta ɓangaren shi kuma wata irin natsuwa yaji tana saukar mishi a hankali...

Motsawa Nawaz ta kumayi "kaga gaskiya ya Aayaann ka sakeni kasan cewa hakan dakamin haram ne, kuma Nima nasan hakan.

Cikin raunatarciyar murya yace "amma ai yin hakan ba haram bane a gurin ma'aurata ba ai.

"Kaga kabar wannan wasan yaran da kakeyi, nidai ka rabu Dani, yaushe ka zama mijina? Nida banfi sati biyu da saninkaba...

"Kasa Sakinta yayi don kasancewar su a hakan ya mishi daɗi sosai a zuciyar shi.

*Auncle menene ya samu aunty Nawaz taketa kuka*? Muhsien yacewa Aayaan ganin anyi Banza dashi...

"Batada lafiya ne shiyasa"

Matsowa kusa da ita MUHSIEN yaayi yana taba bayanta a hankali "sannu mummyna kiyi hakuri Uncle zai kaiki asibiti kinji.

"Yaya Aayaann pls ka sakeni na hakura" Nawaz tace jin abin yayi mata yawa

Murmushi yayi "ashe kin gane abinda nake nufi, Sakinta yayi tayi baya tana gyara mayafinta amma duk jikinta yayi sanyi ..

Kunna motar Aayaan yayi yana murmushi sannan yace "Madam yanzu gidan wace ƙawar taki zan rakaki.

Kasancewar tana jin dan nauyinshi yasa tace "ai Ni inaga har abada nida in kuma cewa ka rakani wani guri.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

A chan gida Mummyn SARFRAZ ce zaune tare da Mummyn AAYAAN suna hirar aurensu Nawaz da aka Daura..

Mummyn sarfraz tace nifa tunda naga Aayaan wallahi naji kewar sarfraz ta ragunmini da kaso 40%
Sunyi kama sosai kuma yanayin Mu'amular su iri ɗaya...

Nidai fatana Allah ya nuna mana sarfraz a raye saboda inaso inga gudan jinin Yar uwata. Cewar mummyn Aayaan

shiru Mummyn sarfraz tayi ta kasa cewa komai saboda jimami.

"Amma gaskiya ki hana Aayaan zuwa da Nawaz Abuja ko Babu komai Kinga yanzu ita matar aurece bazai yiwu a baza hotonta a kowace kafar sada zumuntaba gaskiya" Mummy sarfraz tace.

Wani irin tsallen murna Aseey wadda ke laɓe a bayan labule tayi, wato hasashen ta ya zama gaskiya kenan, Auren Aayaan da Nawaz aka Daura ɗazu kenan farinciki fall zuciyarta.

Aayann ne rungume da muhsien sai Nawaz a gefe suka shigo cikin falourn, Assalamu alaikum barkanku da rana.

"Sannunku da dawowa, kunga yadda mukayi matching kuwa Kamar mata da miji cewar Aseey tana ƙunshe dariya.

Ita dai Nawaz batada Burin daya wuce taganta a ɗaki ta cire kayan jikinta saboda gaba ɗaya kamshin Aayaan takeyi Kuma gani takeyi za'a gane ya rungumeta....

*Bayan awanni shida...*

Nawaz na zaune a falour kasancewar yau Aseey ta hanata sakat daga wannan sai wancan, mummy kuma suna chan sasan daddy kasancewar yau yayi tafiya.

Tashi Aseey tayi"sweet sis bari nazo kinji?
To Nawaz tace tana kallonta har ta shiga ɗaki.

Aayaann dake labe a gefene ya fito ya nufi Nawaz a hankali, Saida yazo gabanta sannan ta ganshi...

Tsugunawa yayi gabanta "dear inaso muyi magana dake me muhimmanci Please zo muje?

"Waye zai bika? Malam kaga gaskiya ka fita harkar fa, ehe.

Be jira komaiba ya suntumeta yayi hanyar ɗakin SARFRAZ rungume da ita sai wuntsil wuntsil takeyi

Please ayi comments

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 40*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Saman gado ya ɗora ta yana murmushi "wai ke meyasa komai saikinyimin jayayyahne? samun sauƙi na daya shine zan iya ɗaukar ki, amma dabadon hakaba dana wahala ainun.

Shiru Nawaz tayi tare da ƙarewa ɗakin kallo tana tuna ranar data fara shiga cikin shi, komai yayanan yadda yake illama ɗan gyare-gyare da aka samu, sai kuma ƙamshin Aayaan daya gauraye ɗakin saɓanin da kamshin SARFRAZ ne.
Hakan ya daɗa tabbatar mata cewa Aayaan ba baya bane a wajen tsafta.

"Hmmm kazo gidan mutane ka wani hakimce Koh? Sai kace ɗakin ka, to mai ɗakin dai yananan dawowa. Nawaz ta faɗa tana daɗa gyara zama a saman gadon

Gabanta ya karaso ya ɗora hannuwanshi a saman cinyarta sannan ya tallabe haɓarshi dasu
"ɗaki nane mana! Tunda ai ɗakin ƙaninane Koh? And kuma ni sainafi kowa jin daɗi muddin SARFRAZ ya bayyana.

Ture hannuwanshi tayi daga kan cinyarta " Sannu malam! Allah duk jin daɗinka bazaka kaini ba, domin yanzu kaf cikin rayuwata babu abin dana sa agabana kamar fata da addu'a akan Allah ya nunamin SARFRAZ...

Saida zuciyar Aayaan ta buga jin maganganun Nawaz, take ya fara zancen zuci "kada fa Nawaz son SARFRAZ takeyi? Idan kuwa hakane Nasan na makara ba lallai tasoni ba gaskiya.
Amma a fili sai yace "Ni kike turewa daga jikinki Koh?

Chuno bakinta tayi "nifa yaya Aayaann Wallahi banaso kana taɓa min jiki, amma naga kai hakan ya zame maka jiki Koh.

Wani irin ƙayataccen smirking yayi Sannan cikin tausasasshiyar murya me kama da raɗa yace "yap i am addicted to your body, kuma kece kika sabarmin da hakan.

"Kamarya? Nifa banason ƙage. Cewar Nawaz tana haɗe fuskarta

"Wallahi ke kika koyamin, ki tuna fa duk sanda muka hau mota saikinyi barci a jikina kuma aƙalla ba'a ƙasaraba sai kinyi barcin sama da awa biyu.
To ta ina kike tunanin jikina bazai saba da ɗumin jikinkiba?

Miƙewa Nawaz tayi "Gaskiya ka shahara, nidai bani guri in wuce"

Shima Aayaan sai ya Miƙe Kamar zai matsa ya bata guri sai kuma charaf ya rungumeta yana hadata da jikin bangon ɗakin.

Kasancewar shi mai faɗin jiki da murdewa yasa duka ya rufeta, sannan a tsawo bata wuce iya kirjinshiba..

Tsoronshi data ɗan samu sauƙin shi ne ya dawo mata sabo fili, fat fat fat haka kirjinta ke bugawa, gaba ɗaya jikinta saiya kama rawa, cikin dasasshiya kuma shaƙaƙƙiyar murya tace "Don Allah yaya Aayaann kabari, Wallahi banaso.

Shima ta bangaren Aayann bugun zuciyarshi ne ya karu kuma a hankali yakejin numfashin Nawaz yana sauka saman kirjinshi ga sautin bugun zuciyarta daya ƙaru alamun tsoro ƙarara ya kamata. "Nikuma inaso!" Abinda Aayaan ya iya cewa kenan cikin low tune.
Cikin abinda bai wuce second hamsinba numfashinsu ya gauraye da kamshin turaren Aayaan da wanda itama Nawaz tasa, saiya bada wani irin romantic scent. Hakan yasa daƙyar Nawaz take iya jan nunfashi tanajin wata iriyar kasala na saukar mata a hankali, shikuwa goga Aayaan ji yake kamar a dauwama a haka saboda wani irin feelings Dake ratsashi Lokaci guda wanda be taɓa Experiencing ɗin irinshiba, hakan yasa jikin shi ya mutu tare da wata kasala shima data saukar mai.

Kusan a Tare suka sauke wata iriyar raunanniyar ajihar zuciya.

Tanaso tayi magana amma Sam bakinta ƴaki buɗuwa ya bata dama, sai kawai tayi yunkuri ta tattaro ragowar karfinta ta turashi baya. Cikin ikon Allah sai kawai taga yayin bayan kasancewar jikinshi daya saki gaba ɗaya.

Aikuwa da sauri Cikin rashin kwarin jiki Nawaz tayi hanayar waje, sai Sannan shima yayi sauri don ya cin mata amma ina ta rigada ta buɗe ƙofar ta fita falour.

"Madam please ki dawo, bamuyi maganar da nakeso muyi ba! wallahi i seriously need your support and Du'a.
Kota kanshi Nawaz bata biba tayi hanyar dakinsu tanajin wata irin fargaba a zuciyarta. "Gaskiya zata dena ba Aayaan fuska, kada azo tsautsayi yasa wani abuu ya ratsa tsakaninsu ta shiga uku...

Tana jiyoshi yana cewa "i promise bazan kuma hugging ɗinki ba, amma Please ki tsaya ki saurareni.

Koda ta shiga dakin bataga Aseey ba, sai kawai ta nemi guri ta zauna kirjinta na cigaba da bugun tara-tara, hakanan takeji kamar har yanzu tana cikin jikin Aayaann ne, gashi duka jikinta ma kamshinsa yakeyi.

Shi kuma Aayaan takaicine ya kamashi "meyasa na kasa control ɗin kaina ne, ohhh da kaina kuma nake shirin ɓatawa kaina Budget, amma naso muyi magana ko don naji ra'ayin ta. But never the less zanyi abinda ya dace kawai.

Juyawa yayi da niyyar ya koma ɗaki sai yaga Aseey zaune tana murmushi.
Ɗan daburcewa yayi "ehmm sis Ashe kina zaune?

"Ina zaune tun ɗazu amma tsabar yanzu kazama mara kunya baka lura ma daniba, hmmm ai Wallahi na godewa Allah, domin ko yanzu ALLAH yabar ka Nasan ya ramawa tulin ƴan matan daka riƙa wulakantawa a makaranta... Bakada abinyi sai tozarta Mata musamman waɗanda kaga sunaso suriƙa shiga sabgarki.
" To yanzu gashinan matar kace amma tsoronka takeji.

Kusa da ita ya matso "sis wai don Allah dagaske mummy takeyi an daura mana aure yau? Nifa jin abun nakeyi Kamar a mafarki

"Au dama mummy ta taɓa yi maka ƙaryane ban saniba?

"No sis ba haka nake nufiba, kawai dai abin ne is very very amazing, ace wanna beautiful damsel ɗin tawace!.
Chapter 39 · 0% Book details