← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 112

Sashe 38

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiryawa baffa yayi ya nufi gidan kakan Aayaan shida Nura da sauran fadawa don achan za'a ɗaura auren, domin duk sun gama maganar komai a waya har an sanar a masallaci cewa bayan sallar juma'a akwai daurin auren jikar hakimi.

Sosai ake taron bikin amma Sam an kasa samun wanda zai faɗa wa Nawaz, domin sosai baffan yaja musu kunne akan kada wanda ya sake ya faɗa mata har sai sun fahimci juna.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Hakanan Nawaz takejin komai ya fita kanta ga wata iriyar faduwar gaba data addabeta, a sanyaye take komai domin koda ta fito bayin sanye da hijab kasa komai tayi ta nemi guri ta zauna tana sauraron bugun zuciyarta....

Da murmushi Mummyn SARFRAZ ta shigo dakin rike da wata shopping bag sai mummyn Aayaan itama tana biye da ita a baya,. Gefen Nawaz ta zauna "daughter ga kaya kisa kinji!

Gwalalo Ido Nawaz tayi tana kallon wata iriyar shadda mai maiƙo sai kyalli takeyi tasha swarovski stoneworks da phoenix design "ni zansa Wannan?

"Eh daughter takice wadda SARFRAZ ya dinka muku har kin manta?
"Itadai Nawaz bata san wata shadda da sarfraz ya Dinka musu ba amma ko don DARAJAR sunan sarfraz ɗin da aka ambata aita saka.

Amsar shaddar tayi tana murmushi, nan kuma Mummyn SARFRAZ ta Kalli mummyn Aayaan sukayi murmushin manya wanda su kadai suka san manufarshi.

Fita sukayi daga ɗakin don ta samu damar shiryawa, abin yaba Nawaz mamaki domin kayan cif sukayi mata kuma sunyi das a jikinta, ita tadai sane don SARFRAZ amma bata jin wata walwala Tare Da ita ..

Binta sukayi da kallo sanda ta fito falour domin wani irin haske ta ƙara ga wani kyau da tayi daga ALLAH.
Aseey dai sai ido domin akwai abinda take hasashen amma mummy taki bata dama kuma ta taka mata burki.

Mummyn SARFRAZ ce ta kwalawa Aayaan kira "To Aayaan ka fito ta shirya, kuzo ta rakaku masallacin lokaci yana ƙurewa..

Koda ya fito kasa boye mamakinshi yayi haka ya saki baki yabi Nawaz da kallon yanajin kamar yaje ya rungumeta ya maida ita ciki...

GYARAN murya Mummy tayi sannan tace "ku tafi mana ko sai kun makara?
Gaba ɗaya Nawaz ta shiga damuwa wai fisbilillah yaza ayi aita hadata a Aayaan bayan Ansan basa jituwa.
Ɗaki ta koma ta dauko babban mayafin da Mummy ta haɗo mata Tare Da shaddar ta fito ta bisu parking space.

Tundaga nesa ta hango Aayaan ɗin yadda yayi wani irin mugun kyau, cikar kamala da kwarjini, haka nan ta kasa jure kallonshi duk da kasancewar suna nesa, koda ta karasa motar ta shiga bata tanka suba sannan duk suka shiga suka dau hanya ...

Masallacin Albani takaisu inda ita ta zauna a cikin motar tana jiransu, yayin da kuma ƙarfe ɗaya da rabi daidai ta tsinci wata irin karayar zuciya ga kirjinta da yayi mata nauyi kamar an ɗora mata wani Nauyi nadaban ... Sannan bugun zuciyarta ya ƙara tsananta.

Shi kuwa ta ɓangaren Aayaann yayi dai-dai da sun fito daga masallaci abokinshi Junaid Ya kirashi a waya, sai murmushi hakeyi kamar gonar auduga...

Cikin annashuwa ya shiga motar yana faman zuba wani irin killer smile,
Mamaki abin yaba Nawaz lallai duniya juyin juyi ce, ita ga halin da take ciki shikuma dariya ma yakeyi alamun Duniyar tai mishi daɗi.
Lura da Irin kallon da take mishi yayi, kashe mata ido yayi haɗe da daga mata gira "Toya maman boy ko akwai abinda kike buƙata ne Kinga yaro dan dagwas dani.

Taɓe baki Nawaz tayi "kai ɗin ne dagwas? Lallai kana kallon ka kamar wani basmude zaka ce wai kai ɗin dagwas ne, ina tausaya matar ka Wallahi Donna lura ka cika salo da salsala.....

Wace matar tawa kike n........

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 39*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️

Wace matar tawa kike nufi?
Balla mishi harara Nawaz tayi "au matan naka har nawane da zakace saina banbance maka wacce daga ciki..

" Hmmm yarinya zaki sani ne, wato kin fara rainani Koh?

Murguɗa Baki Nawaz tayi "niba yarinya bace"

"Au ashefa sunanki maman boy ko? Sorry na manta"
"Eh sunana haka ɗin saime?" Wajen muhsien ta waiga "muhsien ɗana zoka zauna a cinyarta kaji daga yau sunana mummynka"
Cinyarta muhsien ya dawo yana kallon fuskarta "Aunty da gaske kema mamana ce?
Murmushi tayi mishi "eh muhsien, Nima mamankace kaji?"
Aayann kam sakin baki yayi yana kallonta "wai ɗan ta bata min rai take wannan? Murmushi yayi kawai be kulataba ya tada motar yayi gaba..

Dai dai sunzo zasu wuce layin baaba Ahmad Nawaz tace "Please anan gaba kaɗan akwai gidan wata ƙawata Nafisa tare mukayi Junior secondary school da ita idan ba damuwa dan Allah inaso kaɗan tsaya zan shiga mu gaisa.

"Okay babu matsala nunamin inda zamubi.

Dai dai Kofar gate ɗin gidan yayi Parking Sannan Nawaz ta fito riƙe da hannun muhsien, shima sai ya fito ta ɗaya ƙofar ya jingina da motar yana kallon Nawaz ɗin, wacce tayi wani irin shu'umin kyau, "ku shiga Ni zan tsaya daga nan in ɗan ga gari.

"To" Nawaz tace tare da tura gate ɗin suna shiga ciki.

Durkushe Nafisa take tana Alwala taji an buɗe gate an shigo, da sauri da ɗago kai don ganin waye, Aikuwa da gudu ta saki butar ta nufi Nawaz ta ruƙunƙumeta "wayyooo Allah yau juma'ar ta musamman ce, Nawaz kece? Wallahi nayi kewarki.
Babu abinda Nawaz take yi sai murmushi, Sakinta Nafisa tayi Sannan ta Kama hannun muhsin suka shiga ɗaki, a kujera ta zaunar dashi sannan ta kwaso kayan ciye ciye kala kala na yara ta miƙa mishi, ita kuma Nawaz ta kawo mata drinks.

"Oh Nawaz ashe rai kanga rai? Aini Nasha munyi hannun riga bazamu sake haɗuwa ba, kinsan rabonda mu haɗu tun bikina, Gashi dama Ni bansan gidankuba kuma numberki bata shiga.

Hmm wallahi kuwa, Nima abubuwane sukamun yawa kinsan fa bayan Nagama NCE Saida na ɗora da B.ED.

"Ikon Allah kice kunbarmu a baya, nida nayi aure a jss3 kinsan bebari naci gaba ba.

"Haka ne Allah kinsan wasu mazan basason suga matansu suna zirga zirga cikin maza. Cewar Nawaz tana daukar ruwa

"Wallahi kam, Allah dai ya bamu zaman Lafiya a gidajen aurenmu ya kaɗe fitina.

Nawaz tace "Ameen tana ajiye Ruwan bayan ta kurɓa, "wai kuwa yaranki nawa yanzu?

Dariya Nafisa tayi "yarana biyar"

😳 Eyee wai wasa kike ko gaske? Amma Nafisa kece da ya'ya biyar? Nawaz tace cike da mamaki.

"Wallahi dagaske nake, saidai haihuwata huɗu, saboda Akwai ƴan biyu shiyasa ƴaƴan suka zama biyar.

Murmushi Nawaz tayi "haba koda naji amma ko a huɗun ma sunyi yawa, inasuke?.

"Kai Nawaz ko don ke haihuwar ƴan gayu kikeyi? Suna gidan kakansu.

"Hmmm aini banyi aureba har yanzu, sai dai ku taysamu da addu'a. Da suna nan Aida na gansu

"Harara ta balla mata, lallai NAWAZ aiko makaho ya shafa fuskar ɗan nan ya shafa taki yasan kece mamar shi balle Nida Nasan yawan shekarunki, tundama shekara biyu na baki Kinga kuwa yanzu ina 27 Kinga ke kina 25 kenan.

"Dariya Nawaz tayi kinsan Aure lokacine, har yanzu dai munanan Muna jiran rabbil izzati, amma Allah banyi aureba har yanzu ki yarda dani.

"Wai Nawaz meye abin jin kunyata? Inkinyi aurenmu meye? Kallon muhsien tayi "yarona ya sunanka?

Haɗiye biscuits din daya cika bakinshi dashi yayi Sannan yace "sunana muhsin"

Murmushi Nafisa tayi "Nice name! Kuma da alamu kaima irin kwakwalwar mamanka kayi.

Dariya Nawaz tayi "wai kinƙi yarda da magana ta Koh?

"Yaza'ayi in yarda, Muhsin waye mamanka?
Nuna Nawaz yayi Sannan yace "wannan ce"

Zaro ido waje tayi "muhsin banason ƙarya, Ni mamanka ce?

Murmushi muhsien ya daɗa yi yace "wallahi kece"

Kyalkyale wa da dariya Nafisa tayi "to kindaiji yaro baisan karya ba, kada ki koya mishi.

Mamaki gaba ɗaya ya cika Nawaz shiko meyasa muhsien yace haka, "Nafisa inaga zamuzo mutafi yaya Aayaann yana jiranmu a waje!
"Subhanallah Nawaz bakida mutunci, ashe tare kuke shine ko ruwa baki kaimai ba?

" Mtsewwwss inaga koda nakai bazai wani shaba, yauwa muje wajen saiki tambayeshi waye mamar muhsien ɗin, kila idan shi ya faɗin miki ki yarda.

Kama hannun muhsin tayi suka fito tsakar gida Sannan ta ɗauki hijabinta dake saƙale a igiya tasa, Nawaz kuma tana binsu a baya.

Mamaki abin yaba Nafisa sosai, yadda taga Aayaan ɗin itama Saida ya burgeta matuka "inayini surukina"

Murmushi Aayaan yayi "lafiya lau Babbar ƙawa, yau dai zan huta kuma za'a barni nayi bacci lafiya.

"Murmushi Nafisa tayi tana daɗa mamakin a ina Nawaz ta samu mijin nunawa Sa'a irin Aayaan Sannan tace "sabodame kace haka?

"Ai baki saniba tunda muka haɗu da ita ta faɗa min tanada wata kawa Nafisa tare wai kukayi jss da ita amma waike kinyi aure, wai kun shaku sosai.

Baki da hanci Nawaz ta saki tana kallon Aayaan wanda ya zage yana haɗa karya.

Ita kuma Nafisa sai tayi dariya jin dadin maganar da Aayaan yayi, wato tanada matsayi kenan.

"To ai baki saniba, Lokacin biki ma haka ta matsamin, to amma dayake ba'a nan akayi bikin namuba shine na samu sauƙi, kuma in faɗa Miki ko data haifi muhsien bata barni na hutaba musamman ranar suna, to Kinga dole nace yau za'a barni na huta.

Wata dariyar Nafisa ke daɗa yi "ikon Allah, Wallahi Nima inanan kusan kullum saita faɗo min araina wallahi, ashe nima ina maƙale a zuciyarta.
Rungume Nawaz ɗin tayi "inasonka ƙawalliya" sannan tayi ƙasa da muryarta tace "Allah ya tona Miki asiri gashi tun ban tambayeshiba ya faɗamin da kanshi. Sannan ta saki Nawaz ɗin tana kashe mata ido.

Itadai Nawaz tsaye take kawai tana kallon ikon Allah " wai dama haka Aayaan ɗin yake, Cikin ƙanƙanin Lokaci ya haɗa labari kamar a cinema.

Shima Aayaan yana ankare da Nawaz hakan yasa ya daɗa cewa "amma kada ki damu wannan karan idan ta haihu har gida zansa azo a ɗaukeki kizo mana suna.

" 😳 Allah sarki Nawaz ashe da wani rabon ma, Allah ya raba lafiya, gaskiya naji daɗi sosai wallahi, Allah dai ya ƙara zaunar damu lafiya.

Ai Nawaz fashewa da kuka tayi kawai ta nufi mota bata kula suba, inbanda Tiƙuƙi babu abinda zuciyarta keyi, wato ita Aayaan zai haɗa wa sharri..
Chapter 38 · 0% Book details