Sashe 35
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki ta kumayi "taya ma zan yarda na auri mutumin da nakejin tsoro da fargaba duk sanda ya tunkaroni?
Wani irin ɓacin rai ne ya tunkarota, "gaba ɗaya yanzu ma naga kamar an maidani kamar kwallon tamola ne, daga wannan ya jefani chan sai wannan yayi chan Dani..
Kuma ummi ta zuba ido "tsaki ta kuma yi tana daɗa shiga Duniyar tunani, "duk sanda kaganka a cikin wata rayuwa to ka godewa Allah domin da za'a canza wani abuu ƙalilan a cikin rayuwar sai kaga komai ya jagwalgwale maka.
Tunda nake a rayuwata ban taɓa tunanin akwai ranar da zansan gidansu SARFRAZ ba balle har inje cikin gidan nasu na kwana ba, sai gashi ƙaddara takaini har hidima sukaitayi dani, kuma dalili na yanzu babu sarfraz ɗin.
Ba'a barni haka ba yanzu kuma na fada gidansu Aayaan, daga ayi nan sai ayi chan, still yanzu kuma ga wani sabon zance "taɓ wallahi ma bazai yuwuba, tiburewa kawai zanyi a maidani gurin ummina.
Rayuwata tada tafi daɗi, da ace ana tambayar mutum kafin abu ya sameshi, to wallahi nidai da nace gwara abarni yanda nake ada koda kuwa su safraz ɗin zasu kasheni da tambayoyin rashin kunyar sune..
Acikin ƴan mintoci ƙalilan ta haɗawa kwakwalwar ta waɗannan tunanin...
Zufar data tsatstsafo mata a goshi tasa gefen mayafinta ta goge.
Buɗe ƙofar motar dataji za'a yi ne yasa ta daɗa murtuke fuskarta, don anata gani take inba haka tayiba to Aayann zai gama rainata ne, duba da dama ya rigada ya rainata ɗin.
Zama Aayaan yayi a driver seat bayan ya zaunar da muhsien a back seat. Ganin Yadda Nawaz tayi kici-kicin da rai sai abin ya bashi dariya, amma baiyiba ya kanne.
Gyararriyar ƙasumbar fuskarshi ya shafa yanajin wani irin feelings deep inside him. Be taɓa tunanin wannan zancen na mata da miji ba Sai yau tabbas wannan fitar tazo mishi da Alkhairi.
A iya tunaninshi shidai yasan yanajin daɗi idan ya ganta sannan yana samun nutsuwa muddin suna cikin inuwa ɗaya, sannan yasan ko kaɗan bayaso ya buɗe ido yaga batanan duk saiyajishi incomplete...
Kallonta yayi yana mamakin wai me take daurewa fuska hakane, sai kuma yayi murmushi mai sauti "maman boy meya faru naga kamar bakya cikin mood me kyau?
Ɗaga Kai tayi ta kalleshi "sai mene don kace mini maman boy? Ai dama kowace mace uwace koda yau kuwa aka haife ta, balle kuma Ni da a ƙalla na wuce shekara ishirin, kuma dama ko baka faɗa ba muhsien ɗa nane tunda ɗan Aunty na ne....
Dariya abin ya bashi yanda ta dage tana sako mishi sharhi, "nifa ban faɗa don wani abuba kuma ba faɗa nake nema ba, i am sorry please 🙏
Dago da Kai tayi ta kalleshi charaf kuwa suka haɗa Ido, aiba shiri ta kauda kanta gefe sakamakon wani irin kwarjini da taga yayi mata fiye da kowane lokaci.
Murmushi ya kumayi tare dayin igniting motar "ina fatan za'a nuna mana gurin ice cream ɗin?
Duk sai ta nemi kwarin gwuiwarta ta rasa, tanaso tace bazata nunaba ya kaita gida amma Sam ta kasa sannan zuciyarta ta cika da fargaba... "Muje zan nuna" ta samu bakinta da furta haka.
Shiru motar babu motsin kowa harta muhsien shima ya natsu, "nan ya isa! ga chicken republic ɗin chan, ka tsallaka ka siyo mishi ko kuma kayi Uturn saika shiga da motar.
"Okay" kawai yace sannan yayi Uturn ɗin, parking ɗin motar yayi a harabar inda aka tanada don parking ɗin.
"Madam muje" dum zuciyar Nawaz ta daɗa bugawa, Wannan kuma wane suna ya kuma nemowa? Amma saita basar "bazan shigaba" tace a takaice.
"Inahh bazai yuwuba saikin shiga, kefa mayyar ice cream ce, Kinga sai ki zaɓi duk wanda kikeso tunda Kinga nibansan wane flavour kike soba...
"A ina kasan Ni mayyar ice cream ce? Murmushi me Kamar dariya yayi "A hanyar Kano da muka tsaya lunch"
Shiru tayi sai ta samu kanta da buɗe motar tana fita, shima fitowa yayi ya buɗe wa muhsien sannan ya ɗauke shi a kirjinshi. Hakan nan yau yake jinshi cikin wata Irin annashuwa...
Nufar cikin gurin yayi yana takunshi na kasaita kuma ingarman namiji, wanda shi baima san yanayi ba, Nawaz na biye dashi kamar jela sai dai daka kalleta zaka gane jikinta a sanyaye yake..
Guri ya samu ya zaunar da muhsien sannan yaja mata kujera "ku zauna bari nazo"
Kai kawai ta ɗaga mishi haɗe da zaunawa, muhsien ne yace "Aunty bakida Lafiya ne?
Ɗan murmushi tayi mishi "eh muhsien, banajin daɗi ne!
"Sorry Aunty! Idan Uncle ya dawo zansa siyo Miki magani.
"No muhsien kabarshi naji sauki "
Bece komaiba amma shima idan ka kalleshi zaka ganshi wani sukuku kamar bashida lafiya.
Sunfi minti goma a gurin sai gashi ya dawo riƙe da manyan shopping bags niƙi niƙi, a gefe ya ajiye su sannan yace" na manta ban tambayeki wane flavours kikesoba.
"No kada ka damu inashan ko wanne ma.
Lura da yayi da yanayinta sai kawai ya kyaleta bece komaiba.
Koma wa yayi ya kuma kwaso wasu ledojin harda staff Guda ɗaya shima riƙe da wata babbar leda.....
Suna zuwa dai dai su yace "kuzo mu tafi"
Mikewa Nawaz tayi da nufin zata kwashi ledojin daya fara kawowa.
"Kada ki kuskura ki dauka, kinsan fa bakyida lafiya kawai ki tawo zan dawo na dauka .
Hakanan duk saitaji wani iri, gaskiya ita bata saba da haka ba taga mutum yana aiki ta kasa tayashi balle wanda ya girme ta, Komawa tayi ta zauna .
Staff ɗinne ya dawo yana yi mata murmushi "Madam gaskiya mijinki yana sonki sosai, Allah ya kara muku danƙon soyayyah, yace kitawo ku tafi zan dauki sauran kayan nakai motar.
Ƙala bata ce mishi ba ta mike riƙe da hannun muhsien ta nufi hanyar kofar fita, don ita ta tabbata cewa kaddara ce yau ta fito da ita da daren nan ake ta ce mata matar Aayaan....
Koda ta fita direct Parking space ta karasa, a tsaye ta ganshi kofar motar a buɗe.
Tare da muhsien ta shiga ta ɗora shi a cinyarta.
Rufe musu ƙofar yayi sannan ya buɗe booth don staff ɗin ya zuba kayan daya kwaso.
Zagayawa yayi ya shiga driver side ya zauna, a hankali taji ya karantar addu'ar hawa mota sai kuma taga yayi igniting motar sun dau hanya....
Tafiyar kurame aketayi inda Nawaz taketa tunanin hanyar da zata bi ta koma gida cikin sauki, domin itafa Wannan asha Ruwan tsintsayen da akeyi da ita ya isheta don a yanzu ma gani takeyi itafa babu wata Abuja da zataje, sai dai duk abinda za'ayi ayi, sam ta gaji, tanaso ta zauna ta nutsu ko ta samu damar yin addu'oi masu yawa akan sarfraz.
Ta ɓangaren Aayaan kuma tunanin yadda zai shawo kan Nawaz yakeyi ta yadda zasuyi tsabtatacciyar soyayyar da zata kaisu ga aure, domin tun daga sanda mutumin ɗazu yace mata naman boy zuwa yanzu ya tabbatar yana son hakan ta faru ..
Muhsien ne yace Uncle baza muje Apple white ɗin bane?
"Zamuje" Aayaan yace a takaice yana maida hankalinshi zuwa kan titi.
"Gaskiya muhsien kayi hakuri kawai mu tafi gida gobe sai ya kaika, cewar Nawaz tana ɗan ɓata rai domin ta fara gajiya da yawon....
"To Aunty" cewar muhsien ba tare daya nuna wata damuwa ba.
Tsaki Aayaan yayi haɗe dasa hannu a aljihu yana ciro waya, a cinyar Nawaz ya ɗora "ga taki na manta ne" sai kuma ya maida hannun daya aljihun ya ciro ipad ɗin muhsien yace "my boy ga taka" da sauri ya amsa yana dariya..
Ita kuma Nawaz saita haɗa girar sama data kasa nifa bance ka siyan mini wata waya ba domin banida bukatarta.
A ɗan zafafe yace "ai dama bance ke kikace na siyan Miki ba, ra'ayin haka nayi sannan ko bakida bukatarta hakanan zakiyi Amfani da ita.
Jin yadda muryarshi ke fita yasa babu shiri Nawaz ta dauki wayar sai kuma wata zuciyar tace mata Nawaz baki kyautaba, be kamata Mutum ya siyan Miki abuu haka me uban tsadaba kuma ki Gwasale shi ba, ko babu komai ai dama kinason ki koma gida, yanzu kin samu hanyar da zaki riƙa magana da umminki duk sanda kikaga dama har ki samu ta baki shawara.
ɗan ɗago da kanta tayi ta kalleshi "Nagode sosai ya Aayaan"
Mamakine ya kamashi domin be taɓa tunanin zata yi mishi godia ba duba da yadda ta gwasaleshi da fari.
Murmushi ne ya kufce mishi, be kalletaba be kuma amsaba be.
Haka suka isa gida bayan yayi Parking ya fito itama ta fita ta tsaya "ku shiga ciki mana"
"Zamu tayaka kwasar kayan ne"
"A'a bakyada lafiya so just get in kada ki wahalar da kanki, babu yadda ta iya haka ta kama hannun muhsien suka wuce ciki.
A falour ta tarar dasu duka sunata hira da alamu har sun saba saboda duka basuda wuyar sabo.
Suna ganinta suka fara murmushi "har kun dawo daughter, sannunku da zuwa, ina Aayaan ɗin Mummyn sarfraz ta tambayi muhsien
"Yanzu zai shigo ya tsaya kwaso kayane....
Be ida rufe bakiba Aayaan ya shigo riƙe da ledoji niƙi niƙi, ko wane hannu leda huɗu, ko achan ɗinma abinda ya hanashi dauka saboda kada mutane su kalleshi amma shiba nauyi sukayi mishiba ..
Aseey ce tace"soja mazan fama, soja marmari daga nesa! Yau kuma an tuna da filin daga kenan?
Ita dai Nawaz abin be wani Bata mamakiba tunawa da tayi sanda ya ɗauketa a daji ya ruga da gudu, juyawa tayi ta nufi daki,.
Muryar Mummyn sarfraz taji tace "daughter kizo mucigaba da hirar tare mana...
Ɗan marairaice fuska tayi "wallahi mum zazzaɓi ne ya rufeni, kuma barci nakeji..
"Subhanallah, sannu duka suka haɗa baki wajen faɗa..
Da ido Aayaan ya bita domin yasan saboda shine ta gudu hakanan saiya tsinci kanshi da rashin jin dadin tafiyar Tata "to ice cream ɗinki fa" yace yana nufarta da babbar leda guda ɗaya.
Ai da sauri ta shige ɗakin don batason ya cin mata da wannan mayen turaren nashi dukda yau ta shaƙeshi har Saida ya cika mata ciki......
Ƙofar dakin ya tura ya shiga, firgigit tayi saboda batayi tunanin zai shigo ba, ai bata jira komaiba ta buɗe bayi ta shige da gudu ta rufe tana sauke ajiyar zuciya .....