Sashe 95
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dear kinsan me! idan na kira mummy cewa takeyi ta yafe, wai tafison na kiraki saboda idan kika shiga damuwa basa iya Miki, Amma idan kina cikin farin ciki kowama haka zaki ganshi cikin kwanciyar hankali"
"Hmmm Mummy fa tace wai ita yanzu Yar kallo ce, wai nafi sonka"
Kyalkyalewa da dariya Aayaan yayi harda tafa hannu "Allah Sarki mummy, in'sha Allah idan mun samu yadda mukeso zuwa jibi ina gida, Kinga sai a raba gardama Idan na dawo, and kuma pls and pls banson wannan rakin naki domin tarba kakeso kimin ta musamman, saboda i really miss your warmth.
Murmushi Nawaz tayi "To Allah ya dawo mana dakai lafiya, kuma kada ka damu i promise zakasha mamaki"
Sosai Aayaann yakejin daɗin yadda yanzu Nawaz ke kula dashi, kuma da alamu kunyar ma ta ragu sosai.
Cikin farin ciki suka gama wayar, kwanciya Nawaz tayi ta lula duniyar tunani, sosai take tunanin tun randa ta fara haɗuwa da Aayaan a daji, yadda ya ɗauketa har zuwa inda ya Kawo mata tea, da Ruwan Alwala daya kawo mata ya yaga zanin gadonshi biyu ya bata tayi sallah, tsokanarta da yake yawanyi, zallar ƙaunar da yake nuna mata a fili, tsabar saboda beson ya cutar da ita sau ɗaya ya kuma kwantawa da ita tun bayan First night ɗinsu.
Hawayene taji zuna zuba ta idonta, da sauri tasa hannu ta goge tare da cewa "Allah na roƙeka ka taimaka ka dawo min da mijina lafiya, Wallahi nayi alƙawarin zan bashi dukkan wata kulawa, kuma zan tarairayeshi kamar jinjiri"
Tashi tayi ta shiga bayi ta dauro alwala, tana cikin Sallah Aseey ta shigo, ganin Nawaz ɗin tana Sallah sai ta fita kawai.
Koda Nawaz ɗin ta idar da Sallar zama tayi taita addu'a Daga busani ta mike ta fita falour zuwa gurin Aunty Aseey Saboda taji menene tazo ɗazu.
Film ɗin Saif Ali Khan akeyi a Bollywood mai suna *phantom* an fassarashi da Hausa *Farmakin Adalci*
Aseey na ganinta tace "zo ki zauna kusa dani, yau zamu sha kallo, yau Bollywood duk finafinan sojoji zasuyi, kinga idan aka gama wannan *Holiday* zasuyi, idan aka gama shi shima *Baghi* zasuyi..
Murmushi Nawaz tayi tana kara jin ƙaunar wannan ahalin acikin jininta, ya zama dolema ta saka musu da ALKHAIRI, kowa burinshi ya sata a Cikin farinciki.
Sosai taji daɗin kallon Film ɗin, sai dai Inda ya ɓata mata rai da akace Saif Ali Khan ya mutu a ruwa har kuka tayi, kallon Aseey tayi tace "yanzu Aunty ya Nawaz Mistry zatayi"
"Ohh Nawaz Film ne fa, to meye na kuka kuma?"
Dai dai nan mummy ta fito " su Aseey kuka ma kika sata yi? Wato an samu taji sauƙi shine zaki dawo mana da hannun agogo baya! To ki kashe Kayan kallon nan ki tashi ki bani guri"
"Mummy baf.........
Kafin Aseey ta gama magana mummy tace "ko ki mayar min tashar CNN ko ki kashe TV ɗin duka"
Remote Aseey ta ɗauka ta maida tashar zuwa CNN
A tare suka miƙe ganin headline ɗin News ɗin...
Jikin Mummy har rawa yakeyi ganin a gefen TV ɗin an rubuta *"AN JEFAWA SOJOJIN HAƊAKAR DA AKA GAYYATA DAGA KASASHEN DUNIYA BOMB, YANZU HAKA ANA HAƘO GAWARWAKIN WAƊAN DA BASU ƘONE BANE"*
Nawaz kam daki ta koma da gudu ta dauko wayarta, kiran Number colonel takeyi amma switch off, ta kira ta kira harta gaji, sai kawai ta fashe da kuka ta fadi a ƙasa.
Da sauri su Mummy sukayi kanta suna cewa "kiyi haƙuri sweetheart, yanzu fa aka fara News ɗin, ba lallai da Aayaan a cikin suba"
"Wayyooooo Allah na shiga ukuna, wallahi Idan yaya Aayaann ya mutu nima mutuwa zanyi, wallahi ko ban mutu ba saina haukace, nashiga Uku! Na shiga uku ya zanyi da raina, wayyooooo wayyooooo"
babu yadda basuyiba amma Nawaz taki yin shiru, gaba ɗaya jikinta yayi zafi sosai zazzaɓi ya rufeta.
Doctor Aseey ta kira tazo ta duba ta tace jininta ya hau kuma bugun zuciyarta ya haura ƙa'ida Sannan ruwan jikinta yayi ƙasa.
Allurorin barci tayi mata sannan ta ɗaura mata drip, inda tace zata dawo anjima.
Su kansu ji suke yi kamar zasu daɗi saboda tashin hankali, zuciyoyinsu kamar zasu fashe tsabar fargaba, ita mummy ma gani takeyi ai gara Nawaz tunda har zuciyarta ta fito da Abinda takeji.
Abu dai babu improvement saboda wayar Nawaz na hannun Aseey, ta kira yafi sau ɗari amma bata shiga, kuma lokacin daya saba kira har ya wuce.
Sosai suma suka ƙara karaya, itama Aseey kasa jurewa tayi ta fara zunduma ihu "wayyo Allah na! Dan Allah, Allah ka taimakeni kada ƙanina ya mutu, Allah don Allah ka tausaya mana halin da zamu shiga, ya Allah kaga bamuda uba, Ayanzu Aayaan shine ubanmu, ga matarshi da danyen ciki, ya Allah kada kada Abinda ke cikinta ya zama maraya tun kafin a haifeshi, wayyooo mummy na shiga uku idan Aayaan ya mutu"
"Mummy dake tsaye kamar gunki ji tayi itama kamar zata faɗi, samun guri tayi ta zauna "Aseey ku haɗu ku kasheni da baƙin ciki tun kafin a tabbatar ya mutu ko be mutu ba, yanzu fisbilillah nifa uwace, ko kuna tunanin zaku fini jin zafi ne? Yanzu ke da nake zaton zamu haɗu mu kwantar wa da baiwar Allan nan hankali shine kema kike zunduma naki ihun Koh? To kisani cewa idan cikin jikinta ya zube munyi biyu babu ko ɗaya, idan Aayaan din ya mutu cikin ne matsayin shi a gurin mu, idan ya zube kuma Shikenan babu Aayaan babu makwafin shi "
Cikin jan majina Aseey tace "To mummy wallahi damuwa ce ta kamani ganin har lokutan daya saba kiranta sun Wuce har kashi biyu"
"Ki shiga bayi ki wanke fuskarki ki fito kada ta tashi taga kina kuka, kinsan jikinta ƙara taɓarɓarewa zaiyi, kuma Ni yanzu burina kada wani Abu ya samu cikin nan."
Koda Nawaz ta tashi daga barci abu gaba ya daɗa yi Domin cewa takeyi ita a kira mata Aayaan ko itama ta mutu, har fusge fusge ta fara wai zata sauka akan gadon, Allah ya taimaka daidai lokacin Doctor ta dawo shine aka ƙara yi mata wata allurar Barcin, tasa mata wani drip ɗin wanda zai wakilci abincin da bata ciba.
Zuwa lokacin itama mummy ta karaya sosai, bayi ta shiga ta fashe da kuka tare da cewa "ya Allah ka duba halin da wannan baiwar taka take ciki, kuma muma ka dubamu ya Allah, nasan baka barin wani don wani yaji daɗi amma ya Allah mun tuba, ka taimake mu Aayaan ya dawo"
Yau dai kwana uku kenan, babu Aayaan babu kiranshi babu Colonel babu kiranshi.
Kowa yanzu karfin hali kawai yakeyi, itakam Nawaz kullum tana cikin allurar Barci, don a tashinta na ƙarshe window ta buɗe tace zata faɗa.
Wayar Mummy ce ta fara ƙara, koda ta duba Number ƙasar waje ta gani, jikinta har rawa yake yi ta daga tare da karawa a kunnen ta.
"Mummy please i am sorry to say, Ni colique ɗin Aayaan ne kuma team ɗinmu ɗaya, he is such a very nice man, caring, kindness, Love in fact he is the best person I have ever meet in life, what i want to say is that, Don Allah kiyi haƙuri, haka Allah ya tsara.
Sunje wajen aikin da zasuyi a ƙarshe sai aka mamaye su aka jefa musu Babban bomb ta sama, kuma gaskiya mugun bomb aka jefa musu Irin wanda hayakinshi ma kawai kashe mutum yake yi.
An duba daƙyar aka samu gawar mutun 79 a cikin duka adadin da suka tafi, amma cikin ikon Allah an samu harda Aayaan ɗin a ciki, sai dai koda akaje asibiti babu irin Binciken da ba'a yiba amma an tabbatar ya mutu, yanzu haka ance in kira in sanar miki da cewa yanzu zamo tawo da gawarshi nan Nigeria Saboda ayi mishi sutura kamar yadda addininku ya tanadar, I'm very sorry mum.
Aje wayar mummy tayi a gefe sannan ta haɗa hannunta guri ɗaya tare da cewa "Alhamdulillah ya Allah, Nagode da Ni'imar ka agareni ya Allah,"
Sosai zuciyarta ta bushe neman wani abu wai kuka tayi ta rasa, inda ita kam Aseey miƙewa tayi tanata tsalle tana ihuuu (Rayuwa kenan, Allah sarki Aayaan)😭😭😭😭😭
Ɗaukar wayarta Mummy tayi tanata kiran Yan uwa tana sanar dasu Abinda ya faru, kan kice me duka ko'ina ya dauka, dayake Aayaan akwai sauƙin kai ga damuwa da mutane...
Cikin awa uku gidan ya cika fam da da mutane kala-kala, dayake wajen ƙarfe takwas ya kirata ya sanar da ita mutuwar Aayaan ɗin, wurin ƙarfe 3:36pm helicopter ɗin daya ɗauko gawar Aayaan ya iso harabar da helicopter ke sauka a cikin gidan, koda aka fito da Aayaan a cikin akwatin da akeyi na karrama sojoji an nannade shi da tutar Nigeria, miƙewa kowa yayi yanaso ya taba kamar wata gawar sahabi.😭😭😭😭
Banyi Editing ba saboda ina cikin tashin hankali😭😭😭
*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*80*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
*Ina ƙara ba masoyan Aayaan haƙuri, kunsan shi littafi yadda yazo haka yake tafiya, ban taɓa zaton Aayaan yanada masoya ba sai jiya daya mutu, to haka ma a rayuwar duniya Akwai wanda zakaji baka son shi amma wata rana sai yazo yafi wanda kakeso ma, Saboda a sanda na kawo Aayaan cikin littafin nan kowa baya sonshi, kowa haushinshi yakeji, amma jiya naga zahiri*, *To saboda haka wannan ya zama Aya a garemu, idan zamuyi so muyi ɗan dai dai, haka idan zamuyi ƙiyayya itama muyi ƙadan*
Kuma inaso Don Allah ku jure kuci gaba da karanta littattafin nan saboda akwai sauran darussa a gaba. Nima banso Aayaan ya mutu ba, Nagode 🙏🙏🙏🙏🙏.
*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA AMINA HARUNA (MEENASH COOL) INA FATAN ZAKI YAFE MIN, SABODA KE BABBAR FAN ƊIN CAPTAIN AAYAAN CE, KUMA IN'SHA ALLAH NAWAZ ZATA HAIFA MIKI WANI SABON AAYAAN ƊIN*
Haka akayi kama-kama aka shigar dashi Babban falourn gidan daƙyar, saboda Saboda yawan mutanen da suka cika gidan.