← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 112

Sashe 1

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Assalamu alaykum brothers and sisters I am back again with a romantic, secret and funny love story....*

Hope you people will enjoy it💡

🔊🔊🔊SANARWA 🔊🔊🔊
Duk Wanda yasan idan ya karantamin littafi zai kalleni a matsayin yar iska kada ya sake ya karanta, idan kuma ya karanta ya zageni to gaskiya ban yafeba❌

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM......*
*INA MIKA GODIATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DAYA BANI IKON DAD'A KAWO MUKU WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA* 🎀ŞΔ₣ŘΔŽ🎀
Ina rokon Allah daya bani ikon gamawa Lapia 🙏(ameen)
ALLAH KAYI DADIN TSIRA GA MANZONKA ANNANBI MUHAMMAD (S, A, W)
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD, WA'ALA ALI MUHAMMAD, KAMA SALLLAITA ALA IBRAHEEM WA'ALA AHLI IBRAHEEM, INNAKAHAMIDUN MAJEED,
RABBANA ATINA FIDDUNYA HASSNA WAFIL AKHIRATI HASSNA WAKINA AZABANNNARR 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

🎀🎀 SAFRAZ 🎀🎀

Episode 1

*Written by oum aeyman*🖋

MADARASATUL TAHFEEZUL QUR'AN WA TARBIYATUL AULAD.........
🚶🏻‍♀Cikin makarantar na shiga, ban zarce ko inaba sai stairs,
Hawa stairs d'in nayi zuwa azuzuwan dake sama.

Ajin farko na kalla naga an rubuta kisa'i Auwal a Saman kofar Ajin, na biyu ma an rubuta kisa'i sani, na uku kisa'i salees.......
Haka Dai nayita wuce azuzuwa Dayawa ko wanne da sunanshi a sama.
Yawancin azuzuwan akwai malamai aciki Wanda babu kuma xakaji suna surutu sama-sama
Saida nazo Ajin karshe sannan na tsaya.
Cikin Ajin nakalla : gaba dayansu manyane, domin daga y'an sha takwas zuwa ishirin da uku za'a iya samu.....
Abinda yafi bani mamaki shine sunfi kowane aji surutu......
Saman Ajin na kalla naga an rubuta "(IBN KHATHEER)"
kubiyo bayana donjin labarin wadannan 'Daliban
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Wani kyakkyawan saurayine Wanda shekarunshi baza su wuce ishirin da daya zuwa da biyu ba, zaune yake akan kujerar da'aka tanada Don zaman malamai ya d'ora 'kafa d'aya kan d'aya ya karkace hular dake kansa wadda daka kalla zaka gane mai tsadace......
"Wallahi malam Abdullahi (shugaban makarantar) ya rainamu kuma ya Raina mana wayau, yarasa malaman dazai ri'ka kawo mana sai 'yan 'kunanan yara?!
Mufa ba yara bane anymore domin Kaf cikinmu babu under 18yrs🔞, kuma naga ko a United States d'an 18yrs yanada right ⚡balle a 9ja....
Sannan kuma dukanmu babu Wanda ba'a university yankeba......
ni abinma dayafi 'konamin rai shine maimakon ari'ka kawo mana malamai Maza sai a rika kawo mana mata, jifa wadda ta tafi ancemin ko shekara ishirin da uku dakyar in zatakai.
Dad'a gyara zama yayi "to wallahi ni kuma inanan duk wadda aka kawo saina koreta daga ajinnan.......
Raf raf raf 👏👏👏👏y'an Ajin sukad'au tafi, wani saurayine Wanda bazai wuce shekarun na farkonba ya mi'ke...
"Wow gaskiya safraz ka birgeni sosai, kuma duka abubuwan daka fad'a gaskiyane, muma kuma bazamu ta'ba watsa maka 'kasa a idoba....
kuma komai zakayi we are behind you and we will always support you dude.....
Mikewa daga kujerar safraz Yayi "badai yau akace za'a kawo mana Wata malamarba? To kabarni da ita kugani ko sati biyu baxatayiba zata gudu da kafarta...
y'an ajinne suka dad'a d'aukar tafi 👏👏👏yey safraz Muna godia.......
wani seat 💺 dake gefe ya karasa ya zauna, A'kidatul Islam ya bud'e yana karantawa....
his face look very innocent Kamar bashi bane tagama shakiyanci yanzuba.
Abdul ne ya zauna a kusa dashi "abokina kana muraji'a ne?
murmushi safraz Yayi eh Abdul, so nakeyi na haddaceta duka.....
dariya Abdul yayi "abokina ga brain ga iskanci "
tafawa sukayi 👋 sannan yaci gaba da karatun shi........

"Assalamu alaykum"
Wata siririyar murya sukaji tayi sallama a Ajin
Dasauri suka d'ago suna Kallonta, sanye take da dogon light blue d'in hijab har kasa sannan kuma fuskarta sanye da niqab.
Idonta 👀ne kawai a Waje ta 'bulin niqab d'in...

Atare suka Amsa "wa'alaikumussalam"
gefen white board d'in dake manne a jikin bangon Ajin ta matsa "sunana NAWAZ MUHAMMAD" ni aka turo a matsayin wadda zata ri'ka yi muku QUR'AN da fiqhu .
KUTUMAR UBAN CHANN.... cewar safraz, amma idan ka kalleshi zaka rantse bashi yaceba domin ya maze.....
cewa tayi "waye yamana ashar a ajih?
dukda y'an Ajin sunsan Wanda Yayi amma sai sukace "malama zagi kuma?
gaskiya mudai bamujiba.
shiru tayi sannan taci gaba "to yanzu inaso Kowa ya mike ya fad'a min sunanshi domin musan juna.....
babu musu suka mimmike suka fad'a......
"to Alhamdulillah, yanzu wace sura kuke?
had'a baki sukayi duka Abdul yace RUM fatima tace QASAS, zainab tace AL IMRAN , safraz yace ANKABUT,
Osman yace BAQRAH......
cewa tayi "to to to ya Isa, kuna nufin Kowa surarshi daban?
had'a baki sukayi Eh malama!
Kujera taja ta zauna "to babu komai Insha Allah zaku sameni me hakuri da sau'kin Kai, Abu d'ayane banaso shine idan na koyawa mutum karatu yacemin be iyaba.... Sannan kuma inaso muhad'a kammu domin tsintsiya d'aya bata Shara....

cewa sukayi "to malama....
QUR'AN ta ciro a Jakarta ta bud'o suratul baqrah "Wanda yake a baqrah a wace aya yake?
Usman yace aya ta 25
cewa tayi "OK karantawa tayi sau Hudu sannan tace" wanda yace ankabut a wace aya Yake?
safraz ne yasha mur "aya ta 400,
ido ta zaro, aya ta 400 fa Kace?
cewa yayi Ayyah sorry malama Ina nufin aya Ta sha hudu...
"cewa tayi worry not, sannan ta karantamai shima sau Hudu.....
haka tayita binsu har saida ta karanta surori sha tara.....
agogon hannunta Ta kalla 6:30pm ta gani,
cewa tayi "time d'in tashi Yayi "sallu alal nabiyul Kareem!
da sauri safraz yace malama Don Allah Inada tambaya kafin a tashi...
"OK inajinka Menene?
malama dama jiyane nayi mafarki
yankeshi tayi "Ayyah saidai ban karanci fassarar mafarkiba!
da sauri safraz yace malama ba Haka nake nufiba...
cewa tayi to inaji 👂
karkace kanshi yayi gefe Kamar me shirin yin kuka sannan kuma duk Yayi squeezing din fuskarshi 🙎‍♂Kamar mai shirin yin kuka,
"malama dama jiya da dare ne nayi mafarki wai na sadu da Mace kuma dama tashi daga barci sainaji wandona a ji'ke...
dad'a mutstsike fuskar yayi Kamar ze rusa ihu ''shikenan malama yanzu nazama d'an wuta kenan tunda nayi zina koh?
ha'ki'ka malama nawaz taji nauyin tambayar amma yanda taga fuskarshi dauke da tashin hankali sai ta daure tace " haba kada kayi kuka mana, ba zina kayiba domin abin a mafarki ya faru ba'a gaskeba, Abu d'aya nakeso ka gane yanzu shine ka zama baligi kuma an bud'e maka littafi domin yanzu duk abinda kayi za'a ri'ka rubutawa me kyau ko mara kyau....
dad'a 'bata fuska yayi "malama kina nufin babu komai kenan?
"Eh babu komai wanka kawai zakayi Sai kacigaba da sallolinka,
to malama kenan idan na koma gida inyi wanka da sabulu 🛀🧼..
cije lebenta tayi sannan tace "nifa wankan janaba nake nufi..
dad'a karkace kai yayi nifa malama ban iya wankan janababa shida omo akeyi ba sabuluba?
aranta cewa tayi wannan wane irin bagidajene?
"bada omo akeyiba da zallan ruwa akeyi me kyau Wanda Bai chanza daga kalaba ko danndano ko kamshi, maana dai tsarkakakke me tsarkakewa ...
zaka karkata bokitin ruwan ka fara wanke hannu saika wanke Al'aurarka sannan kuma kayi alwala amma karka wanke kafa, saika wanke kanka sau uku kuma ka tabbatar ko wane gashi ya ji'ku da ruwa kuma kagaka ri'kayi kana chud'awa zaka iya fara wanke bangaren jikinka na dama sannan saika wanke na hagu, zakuma ka iya wanke Saman jikinka sannan kayi kasa kahada da kafafuwan ka wanke ....
murmushi yayi to malama nagode ...
addu'a sukayi sannan tace to sai gobenku!
Ta fita daga Ajin cike dajin nauyin tambayar da safraz yayi mata, had'e kuma da mamakin irin halinshi na rashin jin kunyar kalamnshi...

tana fita daga Ajin sukadau ihu yeeyyy Sai namu safraz......
kujerar data tashi yaja ya zauna "ya kukaga wannan salon?
cewa sukayi wallahi yafi nada ma....
safraz yace ai tunda naga Kowa ya fad'i surarshi daban kuma naga bata damuba sannan kuma ta karanta daidai na fara tunanin mezanyi mata....
sai wannan tunanin ya fadomin, Amma PA ta bani tsoro domin naga ta Amsa hankali kwance.....
kunsan meye "had'a baki sukayi A'a oga safraz "
cewa yayi naso ta cire niqab d'in saboda Mufi gane yawan shekarunta domin nidai a yanayin muryarta nasan bazata wuce 17-zuwa-18 ba.....
y'an Ajin sukace Eh wallahi...
"murmushi safraz Yayi dukda haka kubarni da ita saina koreta duk hakurinta...
Mikewa Yayi zuwa hanyar Waje sauran y'an Ajin sukabi bayanshi suna tafi duk fuskokinsu dauke da annuri.....
Wata compressor blue black naga safraz ya bude driver seat ya zauna,, igniting dinta yayi sannan Yayi reverse yafita daga gate d'in makarantar ...
y'an ajinsune keta d'aga mishi hannu suna cewa boss sai.
2MO shima d'aga musu hannu Yayi sannan ya Kara speed d'in motar,,
d'an gaba kadan yaga malama nawaz tana tafiya a nutse, rage gudun motar yayi yanata binta a hankali.......

kubiyoni donjin meyasa safraz yakebin malama nawaz,
wai shin zai iya korartama kuwa..
kumama wai to waye safraz ne????????? ?????

TAKU AKULLUM HAFSAT ALIYU SHUAIBU CHIKAJI WATO OUM AEYMAN..... 😎*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

🤳by oum aeyman

Episode 2

Binta yaketayi har suka shanye street d'in duka, layin dake dama tabi, shima yana biye da ita Amma Yayi d'an nesa da ita saboda kada tagane ana binta..
Gida na hudu ta shiga, babu laifi gidan yanada kyau domin duk Wanda yaga gidan yasan megidan irin masu kudin Da ne....

Murmushi safraz yayi ''Ashe gidansuma babu Nisa. Wani Murmushin ya kumayi "ai kuwa tunda tabari nasan gidansu ta shiga uku Dani...
Wayarshi ya ciro a aljihu, security ya cire sannan ya shiga contacts,
Wata number da'aka yi saving da "MY WORLD" yayi dialling...
daga can bangaren naji ance "sweetheart yakake?
Murmushi yayi "Ina Lapia mummy, dama nakirane na fada miki zankai Abdul gida saboda yau bezo da machine ba.
"to sweetheart kayi sauri ka dawo saboda banaso dadyn ka ya dawo bakanan....
Cewa Yayi "to mum as u said Insha Allah....... Sannan ya yanke wayar...

Masallacin dake d'an gaba kadan ya karasa domin gabatar da sallar magrib....

✨✨✨✨✨✨✨

Ita kuwa malama nawaz tana shiga gida ta tarar da umma (uwargidan babanta)
zaune a tsakar gida..
Chapter 1 · 0% Book details