Sashe 59
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawa yayi ya zauna sannan yace bandi ya hau baya, ganin hassu na tsaye tana kallonsu yasa sarfraz yace kema zakije? Ɗaga kai tayi alamar eh.
Aukuwa yace zo kihau gaba, amma ki rungumeni saboda Kada ki fadi.. jan keken yayi da gudu yahau titi, aikuwa mutane sai kallonsu sukeyi Kasancewar a dokar ƙasar ko Mutum biyu ba'a yarda su hau keke ba balle uku, sai kuma gashi su uku sun hau....
Saiya miƙa hanya da gudu saiya cire hannunshi akan keken yana dariya.
Sosai mutane suka taru suna kallonshi Inda acikin masu kallon aka samu wani ya kira Yan sanda...
*MATAR RASHEED* ✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*53*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji ✍️*
Sam SARFRAZ beji zuwan ƴan sandan ba sai ganinsu yayi a gabanshi, ai kuwa duka suka sauka a motar tare da zagayeshi.
Daya daga cikin su ne ya kama hannun sarfraz ɗin tare dasa mishi handcuffs, tasa ƙeyarshi akayi har cikin mota sannan aka tasa su bandi da Hassu, sosai SARFRAZ yake roƙonsu akan su bari ya kira yayanshi, amma fir Yan sandan suka ki yarda.
Haka SARFRAZ yanaji yana gani aka tafi dasu, wasu daga cikin turawan kuwa sunata dariya, dama akwai waɗan da Sarfraz ɗin ya addaba a cikinsu.
Haidar ne shima tafe akan titin domin komawa gida saboda yau beda shifting ɗin rana, har ya gifta motar Yan sandan sai kuma yayi reverse ya juyo saboda wasu ya gani aciki kamar su Hassu...
Da gudu yabi motar, ai kuwa su ya hango a ciki, tsaki yayi "wallahi idan Aayaan bezo ya maida yaron nan gidaba wallahi nasan tsaff zaisa nima a koreni a ƙasar nan, ko yanzu me yaje ya aikata Oho..
Ƙarawa motar gudu yayi tare da shan gaban Yan sandan, parking driver ƴan sandan yayi tare da dirowa daga cikin motar yana jaraba.....
Ganin haidar da yayi sai ya dena fadan ya fara tambayar shi meyasa ya tsare musu hanya? Saboda yasan haidar ɗin, kasancewarshi babban likitane a fannin abinda ya shafi ƙwaƙwalwa.
Hakuri ya fara bashi tare da cewa laifinshine daya manta be rufe SARFRAZ a cikin gida ba.
"Kamar ya laifinka? Bayan mu mun kama shine da laifin karya mana dokar hanya!
"Eh yallabai, abinda yasa nace maka haka shi ɗin majinyaci nane, kuma yanada matsalar kwakwalwa ba'a saiti yakeba sha tara sha tara ne.
Girgiza kai ɗan sandan yayi Sannan yace tabbas da alama, don Nasan me hankali bazaiyi wannan abin da yayi ba, amma don Allah ka riƙa kula dashi sosai kada wata rana yaje yayi abinda zai Cutar da kanshi..
Sosai haidar yayi mishi godia tare da cewa in'sha Allah zai kula dashi dakyau.
Sakinsu akayi aka cirewa SARFRAZ handcuffs ɗin sannan aka fito Musu da kenen su, su kuma Police ɗin suka tuƙa motar su sukayi gaba.
Suna tafiya haidar ya fara yiwa SARFRAZ faɗa "kai bakajin Magana Koh? Nayi maka nasiha nayi nayi amma kaƙi ɗauka, wai ya kakeso nayine?
So kake a koreni daga garin ko? Yanzu in banda abinka ya za'ayi mutum uku suhau keke guda ɗaya, ko tsoron lafiyarku bakwa yi ko?
Shidai SARFRAZ tunda haidar ya Fara fada ya duƙar da Kai yayi shiru kamar faɗan yana ratsashi.
Hassu haidar ya kalla Sannan yace "kema kina matsayin mace amma kina biye musu Koh? Kici gaba idan wata Rana suka karyaki ke kika sani..
Keken ya gungura ya sakata a Mota sannan yace musu " ku Wuce ku shiga mota mu koma gida.
Sif sif suka shige seat ɗin baya suka zauna suna raba idanuwa.
Koda suka isa gida a waje sukaga Madam haidar itama ta fito zata shiga Mota.
Da sauri ta ƙarasa gunsu tare da cewa "sweetheart Ashe ka amso su? Wallahi yanzu Florence yazo yake cemin wai Yan sanda sun kama baƙi na sun tafi dasu. Bakaji zuciya taba, Yanzu haka na shirya ne zan tafi station ɗin.
Cewa yayi "Wallahi basa ji sam, ace kullum daga wannan sai wancan Nidai na gaji Gaskiya, Aayaan Zan kira wallahi yasan yanda zaiyi su koma gida Kafin susa a koremu gaba ɗaya, yanzu haka da kika ganni dasu karya na shararawa cp ɗin shiyasa har ya bani su cikin Salama, amma da Wallahi sai munsha wuya zai bamu su.
Su sarfraz suna gefe Duk sunyi tsulu tsulu kamar tsintsaye sai raba idanu sukeyi.
Gida suka shiga duka, kowa yayi nashi gefen, haidar da Madam sukayi sama, bandi da sarfraz kuma sukayi dakin da aka basu a Matsayin nasu, itama hassu tayi nata.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Nawaz kam tun daga ranar data san ita matar Aayaan ce ta fara wasan ɓuya da mummy, koda wasa bata bari su haɗu sai dai bisa kuskure, shima suna haɗuwa zata gudu, ita kuma Mummy Sai dai tayi murmushi ta wuce, kuma kunyar Nawaz sosai take birgeta, fatan ta ɗaya wata rana su saba sosai.
Aseey kuma tuni ta maida Nawaz kakarta Domin kullum cikin tsokana take, daga tace matar ƙanina kishiryawa amarci don yana dawowa da sai an wuce gurin, sai kuma tace wannan kibar da kikayi ƙanina zai kwashi garaa.
Ashley kam ta tsani Nawaz kamar ta buɗe ido taga Babu ita, gani takeyi kamar ta kwashe komai, saboda tafita kyau nesa ba kusa ba, gashi ta lura su mummy suna matuƙar kaunarta sosai sosai, komai suce Nawaz.
Abinda yafi ƙonawa Ashley rai shine yadda kullum Aseey zata zauna tana bata labarin irin ƙaunar da Aayaan yakeyiwa Nawaz.
Ita kuma Nawaz ko a kwalar ta domin bata samma tana yiba, ita abinda ke gaban tama ya isheta.
Mummy ce zaune Ita da Aseey suna hirar wadda za'a kira tayiwa Nawaz gyaran jiki kafin su tare, dukda sun lura Nawaz ɗin ta chanza ba kamar daba.
Aseey ce tace "Mummy kawai ki kira Aunty Koutume kawai tazo tayi mata, kinga lokacin bikina datayimin Saida kowa yace nayi kyau sosai.
To in banda abinki Aseey kinsan Koutume tana Sudan kuma ba Lallai tazoba, tunda a chamma kullum a tsaye take bata zama saboda aiki. Cewar Mummy tana kallon Aseey don jin wace amsa zata bata.
"Haba mummy! Ƙawar kice fa, kuma nasan idan kikayi mata magana zatazo, kinga daganan nima sai tayimin kafin in koma England.
Harara Mummy ta balla mata "au kice kanki kike yiwa campaign dama"
"A'a wallahi ko nata ma aka samu Ni ya wadatar dani sosai.
Haka suka ajiye akan Mummy zata kirata taji ko zata samu damar zuwa.
Ita kuma Aseey ta miƙe Tare Da fita tana rawa, dakin Nawaz ta shiga tana cewa "lovely sis Ina kike ne? Fito kiji abin Alkhairi!
Nawaz dai daga kai kawai tayi ta kalleta ba tare data ce mata komai ba domin tasan bazai wuce zancen Aayaan zatayi mata ba.
Kusa da ita ta zauna sosai ta naniƙe mata kamar zata shige mata jiki "sister yanzu muka gama Magana da Mummy akan za'a kiramiki mai gyaran jiki daga Sudan wadda zata maidake ki koma balarabiya duk da kema ba baya ba, lokacin da tayimin na biki wallahi nima kaina saida na koma sha'awar kaina, hmmm dama ace baya na dawowa.....
Itadai Nawaz kallonta takeyi batare datace komai ba, saida ta gama maganar sannan tace "Ni dai abar wani gyaran jiki Gaskiya, wallahi batun Auren nan sai nake gani Kamar mafarki wallahi.
Kama baki Aseey tayi 🤔 "Eh Lallai tunda ya barki kisha iska ba, da ace aikin gama ya gama Aida kin tabbatar Auren gareki, ƙilama Yanzu da ciki gareki!
Rufe fuska Nawaz tayi "Gaskiya Aunty Aseey kidena min irin wannan maganar kunya kike bani wallahi.
"Hmmm Nidai na faɗa miki, kima shirya kafin ya dawo wallahi don bazan yarda da wannan zaman banza da kukeyiba.
Gaba daya kunyace Ta rufe Nawaz, tama rasa yanda zatayi, itako Aseey ko a jikinta kuma ita har zuciyarta da gaske takeyi.
Koda Aseey ta fita Nawaz kasa fita faloun tayi, sai kawai ta janyo wayarta ta kunna don ta kira umminta, saboda tun Ranar da suka gama waya da khadija ta kashe wayar.
Tana kunna wa message"s suka riƙa shigowa, kuma duk Aayaan ne ya Turo mata, Harda su voice messages.
A hankali ta riƙa bi tana buɗewa tana karantawa, sai murmushi take yi, domin duka sakonnin ƙorafine akan ta taimaka ta buɗe wayarta domin yanason yaji muryarta, inba hakaba zuciyarshi zatayi bindiga.
Tunani ta fara yi akan ta kirashine ko Kada ta kirashi, chan dai Wata zuciyar tace ki kirashi mana, ko Babu komai ai ka gaida me gaisheka..
Dialling ɗin number tayi sai kuma taji Kamar ta yanke domin ji tayi zuciyarta ta Fara bugawa da ƙarfi da ƙarfi.
Bata ankara ba sai jin Muryar Aayaan tayi yana cewa "sweet heart kin wahalar Dani Wallahi, kin sani a damuwa, na rasa mekeyimin daɗi a Duniya.
Ko Babu komai ai ya kamata ki kunna wayar ki koda ke bazaki kiraniba Ni zan kira, amma saiki shareni kamar baki damu daniba, ko Bakya sona ne?
Duk kunya ta kama Nawaz, kasa cewa komai tayi sai dai murmushi da takeyi ƙasa ƙasa...
"Bakice komai ba Sweet love, ko Bakya sona ne?
"Um-um kayi hakuri bazan kuma kashewa ba...
Wani dadine ya ziyarci zuciyar Aayaann Domin ya fara Ganin alamun Nasara "kada ki bani hakuri Domin kece zuciyata kuma bazan taɓa yin fushi dakeba har abada. Yanzu dai jibi zan dawo don wallahi na kasa tabuka Komai achan ɗin, kinsan fa kinbi jini da duka jijiyoyin jikina kin zuba musu gubar sonki, bana iyayin second ɗaya ban tuna dake ba. Amma Ni nasan ba'a sona Kawai dai ana yimin kawaicine, koba hakaba?
Shiru Nawaz tayi kamar Wadda Ruwa ya cinye, ita dai wallahi su Aayaann da Aseey suna bata mamaki, Sam basa ɓoye abinda ke Cikin zuciyar su, Sannan basajin Kunyar faɗar Komai..
Aayaann ne ya Kuma cewa "sweetheart bakice komai ba! PLS Nidai Ina roko a taimaka a ajiye Kunyar Nan gefe guda, domin nifa Babu Wata kunya a tsarina Don Cutar dani zatayi saboda nine ke kuma kece Ni, To meye wata kunya zata shigo ciki.
Namma dai Nawaz shiru tayi ta kasa cewa komai.
" Shikenan sweetheart tunda tsanar da kika yi min takai haka babu komai, Ni nasan matsayina yanzu.
Da sauri Nawaz tace " wallahi ya Aayaan ban tsanekaba kawai dai kunya kake bani.