← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 112

Sashe 96

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya gidan sai ya daɗa rikicewa saboda yanzu kowa ya tabbatar da cewa Aayaan ɗin ya mutu, Mummy zaune kawai take kamar itace gawar Saboda komai na mutuwar mahaifin Aayaan Sabo ya dawo mata, itakam yanzu meye ya rage mata a rayuwa da bata ganiba, ta rasa iyaye a sanda take cikin tsumman goyo, ta rasa ƙanwarta MUMTAZ, tazo ta rasa mijinta, yanzu kuma ta rasa Aayaan, shiyasa kukanma nemanshi tayi ta rasa....
Aseey kuwa har suma ta riƙa yi, ummin Nawaz ce da mummyn Sarfraz suketa kula da ita saboda suma sun rigada sunzo, Sarfraz kam zuwa yayi ya ƙanƙame gawar Aayaan ɗin yana kuka.

Allah sarki Nawaz, tanachan tana barcin maganin barci da Ayanzu ya zame mata kamar ruwansha, duk wannan abu da akeyi bata saniba, baffan Aayaan baffan Nawaz, da duk wasu dangi suna zaune kowa idonshi a kumbure Alamun sunsha kuka sun gaji,

Baffa ma cewa yayi, "mutuwa dama Ni kika ɗauka kika bar Aseey da ɗan uwanta, tunda Ni yanzu me ya rage min cikin duniyar"
Kowa saida maganar ta ƙara tayar mishi da hankali.

Ɗaukar gawar Aayaan akayi aka shiga da ita cikin falourn mummy saboda Anan za'ayi mishi wanka, duk wani abunda ake buƙata wanda za'ayi Amfani da shi an riga an tanada, kamarsu sabulu, turare, kafur, ganyen magarya, auduga dadai sauransu.

Cikin ƙasa da awa ɗaya an gama yi mishi wankan har ansa mishi likkafani, amma ambar iya Fuskarshi a waje saboda Yan uwa suzo suyi mishi addu'a kafin a kaishi makwanci shi.

Koda aka tawo da mummy tafe take kawai kamar gunki, Aseey kuwa gaba ɗaya ta zabge lokaci ɗaya, duk gaban Aayaan suka tsuguna kowa da Irin addu'ar da yake yi mishi, Aseey kam faɗawa jikinshi tayi, shima SARFRAZ daka ganshi zakaga ya koma kamar wani mahaukaci.

Dai dai lokacin Nawaz ta buɗe idonta, bata jira kowa ba ta fige allurorin dake jikin hannunta tayo waje da sauri, don itafa baza tayi ta zama a cikin gidan nanba ba tare data san matsayin da Aayaan yake ciki ba.

Fitowar da zatayi taga mutane da yawa a cikin falourn ga mutum kwance samɓal da likkafani, zuba wa gawar ido tayi, Aayaan ta gani cikin likkafanin idan ba gizo idonta keyi mata ba, jitayi kamar ta zunduma da gudu ta faɗa kanshi amma kafin tayi yunkurin yin hakan saboda yadda jikinta yake babu kwari taji baffa yana cewa "to yanzu a taso matarshi itama tazo tayi mishi addu'a kafin a kaishi gidan shi na gaskiya"

Mummy ce tace "baba Don Allah kada a tasheta, wallahi idan aka tasheta komai zai iya faruwa, Saboda tun bata san ya mutuba muke fama da ita balle yanzu taga gawarshi shimfiɗe"

Ahankali taja jikinta ta koma cikin ɗakin Aayaan ɗin da a yanzu ya zama nata, saboda tunda ya tafi a ciki take zaune, dayake duk sun bata baya basu ganta ba kwata-kwata.

Drowar dataga ya ajiye bindiga sanda suka dawo daga England ta buɗe, ɗaukar bindigar tayi ta buɗe cikinta don ganin ko akwai bullet a ciki, cikin iKon Allah taga Akwai bullet har guda bakwai, batayi Wata wata ba ta saita bindigar tayi falour da sauri.

"Kowa ya tashi ya fita ko na harbeku dukanku! Wato Ni kukeso ku cutar kuje ku binne min miji alhalin be mutu ba ko?

"Mummy ce tace kunga abin da nake faɗa muku Koh? Wallahi Nawaz ba'a cikin hayyacinta take ba"

Ummin Nawaz ce tace "Sarfraz Don Allah taimaka ka ƙwace bindigar hannnunta kayi ƙoƙari ka shigar da ita ɗaki ka rufe"

Saita bindigar tayi dai dai kan Sarfraz "Wallahi idan ka matso kusa Dani saina harbeka"

Kawu ne yace dalla can ka wuce ka kamata ka rufeta a dakin, kamar yadda ummin tace, don naga da alamu bazata bari a fita da gawar nan lafiya ba idan ba rufeta ɗin akayiba, mu zatayi wa barazana da wata fankon bindiga, ko yaushe ta iya harbin ma oho?

Jin Abinda kawu yace *wato bata iya harbi ba* take Nawaz ta saita bindigar dai dai BABBAN TVn DAYA MAMAYE BANGO DAYA TA SAKI KUNAMAR, JIKAKE TATSATSATSA, ƘARA SAITA WINDOW TAYI TA KUMA HARBAWA, NAMMA SAI RATSARATSA, kan ace me kowa ya mike tsaye yana raba ido.

Dawo da bindigar tayi saitinsu tace "yanzu kun yarda na iya harbin ko saina harbe ɗaya daga cikinku?"

Shiru kowa yayi yana tsoron kada ta saita shi, "dukanku ku fita ku bani guri"

Sifsif kowa ya wuce harda masu rugawa da gudu.

Binsu tayi har bakin kofa tare da cewa sauran mutanen "kowa ya kama gabanshi mijina be mutu ba" janyo Kofar falourn tayi ta rufe.
Ciki ta koma da sauri zuwa wajen Aayaan ɗin, jikinta sai rawa yake yi, jijjigashi ta fara yi tana cewa "Don Allah yaya ka tashi, kada kayi min haka, don Allah karaimaka mana katashi, ka manta cewa kamin alƙawari cewa in jiraka zaka dawo gareni muci gaba da rainan cikinmu! Don Allah ka tashi!!!!
Fashewa tayi da kuka, "wallahi idan baka tashiba kaika zasuyi su rufe a cikin kabari, na roke ka daka dubi darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ka tashi.

Duk wannan abin da takeyi a banza, domin Aayaan yananan a sanƙame cikin likkafani, tashi tayi ta koma cikin ɗakin da gudu, wardrobe ta buɗe ta ciro Brown ɗin jallabiya da gajeren wando ta koma gurin Aayaan ɗin, a hankali ta nutsu tanata cire mishi likkafanin, saida ta gama cirewa tabi duk inda aka sa mishi auduga nan ma ta cire, wandon ta fara sa mishi sannan da kyar tasa mishi jallabiyar, kwashe duka likkafanin tayi ta jefasu gefe, fridge ɗin dake faloun tabude ta ciro ruwa me uban sanyi ya riƙa shafa mishi a fuska tama kuka tana rokonshi akan ya tashi, ganin bafa zai tashi ba yasa ta zauna ta zuba wa kyakkyawar Fuskarshi ido, kallon da take yi mishi kallo ne na ƙurillah, tunda take babu wanda ta taɓa yiwa irin wannan kallon. Fashewa tayi da kuka, ganin yadda Aayaan ɗin ya kara kyau da haske sosai, "yanzu wannan jikin za'a saka a cikin rami tsutsa su cinye?, Innalillahi wa'inna alaihi raji'un!!! Ya Allah mun tuba ka yafe mana!!!!

Zama tayi ta miƙar da kafarta Sannan ta ɗauki kan Aayaan ɗin ta ɗora a saman cinyarta tana shafa gashin kanshi, a yadda takeji yanzu game da Aayaan ɗin, ta yarda tayi ta zama dashi a haka da ta yarda aje a binne shi.

Tanaji anata buga kofa ana bata haƙuri akan ta taimaka ta buɗe kofar ta bada shi a tafi a kaishi duk mutane sun taru.

Duƙar da kanta tayi saitin fuskarshi tanata yi mishi magana tana kuka, kamar daga sama taji Aayaan ya turnuƙe da wani Irin tari sai kace zai amayar da kayan cikinshi, aman wani baƙin abune ya biyo baya kamar wanda yasha Ruwan kwata.

A cikin dashasshiyar murya taji yana cewa "ya rabb matata da mamata da yayata" komawa yayi ya rufe ido ƙirjinshi yana sama yana ƙasa da sauri da sauri, faɗin halin da Nawaz ta shiga a dai dai wannan lokaci kamar ɓata bakine, donji tayi ta gama dace a duniya, ita ko yanzu ta yarda ta mutu tunda shi be mutu ba.
Jijjigashi ta fara yi tana cewa "yaya don girman Allah kada ka kuma mutuwa, ka tashi ka ganni, nice matarka Nawaz!! Wallahi inasonka, kuma daga yau dai abinda kace kanaso shi zanyi..

Aayaan wanda a tunanin shi har Yanzu yana cikin underground ɗin daya shiga ne yaji Muryar Nawaz kamar daga nesa, buɗe idonshi yayi a Hankali, amma be ganin komai, sai da aƙalla yakai minti ɗaya Sannan ya Fara ganin kamar fuskar Nawaz a saman tashi, yunƙurin tashi yayi amma ya ƙasa saboda yadda jikinshi ya galabaita, motsa bakinshi yayi tare da cewa "is it really you? Ko mafarki nakeyi?

Cikin kuka me haɗe da dariya Nawaz tace "wallahi nice, nice Nawaz matarka, don Allah kada ka mutu, ka zauna da Ni"
Dago da hannunshi yayi da kyar ya shafi fuskarta, jin da gaske ya taɓa ta yaji itace yasa yaji wani irin ƙarfi yazo mishi, yunkuri yayi ya tashi tare da taimakon Nawaz ɗin, jingina shi tayi da jikin kujera sannan ta kafa mishi robar ruwan data dauko ta zuba mishi dazu "sha" Nawaz tace dashi.

Saida ya shanye Ruwan tass sannan yace "sweetheart ya akayi na ganni a cikin gidanmu? A iya abinda zan iya tunawa shine na dira underground sai kawai naji hayaki ƙura da ihu ya baibaye ko ina, daga nan kuma ban ƙara sanin komai ba sai na ganni kusa dake.

Rungumeshi tayi gam tana cewa "cewa fa akayi ka mutu, har anyi maka wanka ansa maka likkafani za'a je a binneka shine na kori kowa nace baka mutuba, amma da tuni an binne ka.

Tabbas ga likkafanin nan ya gani a gefe, chan ɗaya gefen kuma makara ce a ajiye...

Kasa magana yayi ganin bindigarsa ajiye a gefe, "waya dauko bindiga ta?"

Ɗaukar bindigar Nawaz tayi tare da cewa "nifa yanzu kaf a cikin Duniyar nan idan aka cireka aka cire ummina babu wani abu daya kai muhimmancin bindigarnan a gurina, saboda itace ta taimakeni ta hana a binneka, da yanzu an cuceni, fashewa tayi da kuka ta miƙe da bindigar riƙe a hannunta ta buɗe ƙofar falourn, mutane ta gani cirko cirko, ganin ta fito ga bindiga a hannnunta yasa kowa ya kwasa a guje harda masu yin gware, "ku shigo kuga ya tashi, wallahi da kun tafka babban kuskure, be mutuba.

Zuwa lokacin Kowa yana kallon Nawaz ne a matsayin mahaukaciya, kowa watsewa yayi in banda su Ummin ta dasu mummy sai su Aseey da Sarfraz.

Haɗuwa sukayi suka tawo gurinta don su kansu baso sukeyi a binne Aayaan ɗin ba, Abinda Nawaz ɗin tayi ba ƙaramin daɗi yayi musu ba.

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃. *WANNAN RAWAR TA AAYAAN CE*

*MATAR RASHEED*✍️*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*81*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Chapter 96 · 0% Book details