← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 112

Sashe 63

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigaba da haɗa kaya SARFRAZ yayi saboda ATM ɗin da Aayaan ya bashi a hannuñshi ba karamin kaya ya siyaba shi dasu bandi da Hassu, yasai wasuma yace na Nawaz ne, harda mummy aka siyawa sarka da ɗan kunne, sosai yayi ɓarnar kuɗi.

Shikam Aayaan dama Babu wasu kaya dazai shirya in banda back pack dinshi guda ɗaya.

Waje ya fita Tare Da ciro wayarshi a aljihu, Number Mummyn shi yayi dialling, da Sallama ta ɗaga tachan ɓangaren, gaisheta yayi cike da ladabi yana tambayarta ya ta tashi? "lafiya lau Alhamdulillah". mummy tace.

"Mummy Naga SARFRAZ! Kuma Yanzu haka muna Tare dashi...

"Eye Aayaan! Kasan me kace kuwa? SARFRAZ fa kace? Ɗan ƴar uwata?

"Eh mumy shi nagani, amma yanzu abinda nakeso shine zanyiwa securities ɗina magana, zasuzo su ɗaukeku su kaiku chan Zaria gidansu SARFRAZ ɗin, Nima gamunan yanzu zamu tawo..

Muryar mummy har ta Fara rawa "Aayaan ka turosu yanzu saimu tafi" kuma Don Allah ka kulamin dashi sosai.

Tsabar zumuɗi bata ma tambayeshi suna inaba sukayi sallama ya kashe wayar.

Faloun ya koma ya tarar su SARFRAZ har sun gama haɗa komai suna zaune alamun shi suke jira.
haidar da madam Dinshi suma sun shirya dayake Tare zasu kaisu airport ɗin.

Duk da Cewa sarfraz ba ƙaramin tashin hankali yasa haidar a cikiba na ɗan zaman da sukayi Tare, amma da zasu rabu Saida Kowa yaji Kamar ya zabga ihu, dama shi haka sabo yake (sabo turken wawa) hassu Harda ƙwalla taketayi Don ma tanata rufe idonta da mayafi.

Ita kanta Madam haidar ɗin sai taji idonta yana kawo ƙwalla, amma tayi saurin gogewa saboda kada su hassu su lura da hakan.

Allah ya taimaka suna zuwa jirgi na shirin tashi, a gurguje aka musu clearing ɗin komai suka shiga ciki, dayake Aayaan yafi zama a VIP, tsaff Hassu ta zage ta zama wayayyah kamar ba itaba, ko Irin ɗar dinnan ma batayiba.

Madam haidar kam Saida suka koma gida gaba ɗaya ta kasa kataɓus, sai taga gidan yayi mata wani irin fili kamar an kwashe wani uban kaya masu yawa.
Haidar keta kwantar mata da hankali (kada ki damu, kwanan nan zamuje ganin gida ai, duk zamu kai musu ziyara in'sha Allah, kuma ai dama haka baƙi suke, duk daɗewar da suka yi wata rana Dole za'a rabu, shiyasa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace mu Mu'amulan cesu da kyakkyawar Mu'amula kuma mu kyautata musu)

A haka dai ya samu ya kwantar mata da hankali.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Mummy kam tana gama waya da Aayaan ta samu Aseey tayi Mata magana akan maza su shirya ita da Nawaz Aayaan zai turo motoci yanzu akaisu zaria gidansu SARFRAZ.

Ƴar fargaba ce ta kama Aseey "mummy meya faru haka da zamu tafi Zaria urgently?

Yanzu muka gama waya da Aayaan wai yaga SARFRAZ kuma yanzu haka suna tare, zasu tafi chan Zaria ɗin.

"Ikon Allah! To yanzu suna inane?

Mummy tace "kedai kije ki shirya kayan naku na manta ban tambayeshiba, kuma kiyi sauri saboda Yanzu motocin zasu iso.

Ɗakin Nawaz Aseey ta shiga ta faɗa mata cewa ta shirya yanzu zasu tafi Zaria. Sosai abin ya bata mamaki amma dayake batada bin kwakwkwafi bata tambayi Aseey meya faru dazasu tafi zaria yanzu ba, sai kawai tace "to" tare da miƙewa tana nufar wardrobe.

Kaya kala uku ta zuba a cikin wata madaidaiciyar traveling bag, sai na jikinta guda ɗaya.

Itama Aseey bata Wani dibi kaya da yawa ba, sai dai na muhsin ta ɗiba da ɗan yawa Saboda shi zai iya ɓata wa.

Cikin abinda befi minti talatinba har sun gama shirin su sun dau hanya zuwa Zaria, kuma har a lokacin Nawaz na cikin duhu saboda ba'a faɗa mataba kuma bata tambaya ba.

Ashley Kawai aka bari a gidan, dayake tana Chan tana barci har suka gama shiri, saida zasu fita ne Aseey ke cewa Mummy "Ashley fa tana ciki!

"Shareta Kawai, Don bazani da itaba, idan ta tashi nasan zata nememu, idan ta kira a waya zan faɗa mata ta jiramu ko ta tafi, duk wanda takeso.

Dayake yau babu Aayaan tare dasu ai kuwa securities ɗin suka samu dama sai uban falfala gudu sukeyi, kuma su mummy duk sun rufe windows sannan hankalinsu baya titi shiyasa ma basu lura ba, kuma har da yanayin motar, domin idan kana ciki Bama ka gane ana tafiya.

Cikin ƙanƙanin Lokaci suka isa Kano, koda Aseey ta gansu saman gadar kwankwaso Saida abin ya bata mamaki, don bawani dadewa sukayi da fitowa ba..
Sosai suka ɗauki hanyar Zaria,bayan securities din sun tambayesu za'a tsaya ne?

Mummy tace "a'a" Domin babu abinda ke zuciyarta a yanzu illa zumuɗi ganin SARFRAZ.

Ita dai Nawaz tana gefen Aseey ta jingina kanta da bayan seat ɗin motar ta rufe idonta kamar tana barci.

Karfe huɗu a cikin Zaria tayi musu, dayake sun rigada sun san gidan sai kawai suka sauka daga Express way suka koma cikin unguwa.

Mamaki fal cikin Mummyn SARFRAZ, farin ciki ma ya hanata yin magana, sai dai kawai ta rumgume mummyn Aayaan tayi shiru.

Cewa su Aseey da Nawaz tayi "ku tafi dakinku kuje ku samu kuyi wanka ku huta, yanzu zansa a Kawo muku abinci.

Muhsin kam saiya choge waishi a gun mummy zai Zauna, tafiya sukayi suka barshi anan.

Tunda suka shigo gidan ƙirjin Nawaz ke bugawa kamar Zai fito waje, ga wata fargaba data cika mata zuciya.
"Yau fa Aayaann yacemin ze dawo, ko dai wani abunne ya faru? Dole Akwai wani abu domin Babu yanda za'ayi hakanan mu tawo Zaria ba tare da wani dalili ba.

Ganin batada amsar duka wadannan abubuwan sai Kawai ta watsar da tunanin taci gaba da sabgar ta dukda bata dena jin faduwar gaban ba.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Su Aayaann kuma a Nnamdi Azikiwe airport dake abuja suka sauka, securities ɗin shi na Abuja ya kira, babu jimawa kuwa suka iso, nan suma suka ɗauki hanya Don zuwa Zaria.

Hassu tunda taji cewa sun iso Nigeria sai ta riƙa jin gabanta na tsinkewa tare da tararrabin kada a rabata da sarfraz tunda Yanzu ya samu lafiya, Idonta Sai cika yakeyi da ƙwalla tana gogewa a fakaice..

Sarfraz kam harya gaji da zama, tun yana kalle kalle sai ya koma ya kifa kanshi a cinyarshi.

"My brother ko baka farincikin dawowarka gida ne?" Aayaann ya tambaye shi tare da dafa gadon bayanshi

"No bro inayi sosai ma, Kawai dai na gaji da zaman motar ne, cewar sarfraz tare da ɗagowa daga duƙon da yayi.

Sosai Aayaann ya kalli Fuskarshi Sannan yace "kada ka damu mun kusa ƙarasawa kaduna, idan muka isa zansa a tsaya mu huta kuci abinci sai mu wuce.

Ɗan murmushi SARFRAZ ɗin yayi.

Sam Aayaan beji daɗin Ganin sarfraz ɗin a haka ba, sai yake Ganin Kamar idan suka isa gida Mummy zata tuhumeshi..

Gyaran murya Aayaan ɗin yayi Sannan ya fara magana.

"SARFRAZ duk abinda kakeso a duniya inaso ka faɗa Min ko menene kuma ko nawa ne in'sha Allah, hardai befi ƙarfina ba nayi maka alƙawarin yi maka shi.

Da sauri SARFRAZ ya kalli Aayaan "sir dagaske kake?

Jinjina kai Aayaan yayi tare da cewa"Eh dagaske nake, kuma Alkawari nayi maka...

Sosai sarfraz ya gyara zama "zaka kaini China?

"Har India idan kana so"

Zaro ido sarfraz yayi "woo ni woo ni, wayaga sarfraz a China? Kutmar!🤭 Sai dai kuji ina cewa "chan cheng wei, jiang xian miing🤣🤣🤣

Sosai Aayaann yayi dariya sannan yace "idan har kanaso, zan neman maka makaranta achan saika karanci Yaren china ɗin tunda naji ma ka iya!

Kwal kwal SARFRAZ yayi da Ido Kamar zaiyi kuka sai kuma yace "Ni Wallahi Daddy nake tsoro, sam bayaso nayi nesa dashi, dakyar idan zai yarda ma, ita ma mummy bason na matsa kusa da itan takeyiba zugawa zatayi a hanani zuwa.

Shafa kanshi Aayaan yayi, "ka manta Kanada Ni? Nace ka dena jin komai Ni zan zame maka kamar garkuwa ne a duka lamuranka.

Hannunshi SARFRAZ ya sargafe dana Aayaan Sannan yace "promise me brother"

"I promise" cewar Aayann yana murmushi.

Sai misalin 7:30pm suka isa Zaria, tashinsu bandi da Hassu Aayaan yayi sannan suka nufi masallaci don bada farali. Duk ba yunwa sukejiba Kasancewar madam haidar ta haɗa su da kayan ciye-ciye kala-kala, komawa motar sukayi Sannan suka nufi gidan su SARFRAZ.

Sosai SARFRAZ ya ƙosa su Isa gida, ganinshi a saman titin layinsu yasa yaji Kamar motar bata gudu, sosai zuciyarsa ke bugawa Kamar zata fito fili, duk abinda yake yi Aayaan yana lura dashi.

Bandi ma daɗi yaketaji yau SARFRAZ zai koma ga ahalinshi a Matsayin me cikakkiyar lafiya, ita kuwa hassu kukane yake neman kwace mata, domin gani takeyi korarsu za'ayi, kuma ita ta rigada ta saba da Sarfraz, ta rasa meyasa takeji Kamar idan aka rabasu mutuwa zatayi..

Har cikin gidan suka shiga da motocin Kasancewar dama ansan da zuwansu...

Alokacin Nawaz ta daɗe dayin barci saboda wani Irin ciwon mara daya kamata dalilin period da takeyi, shine Aseey ta saman mata Diclofenac tasha, bayan tasha ne taɗan samu relief har barci yayi gaba da ita.

Mummy kuwa da Aseey sun kafa sun tsare a main falour yadda zasuji ƙarar shigowar motocin idan sun ƙaraso.

Da gudu mummy tayo waje yayin da Aseey tayi dakin daddyn sarfraz saboda ya dawo wajejen magrib
"mummy da Daddy pls ku fito gasu sarfraz sun dawo.

Duka suka miƙe sukayi waje yayin da kowa na ƙoƙarin yadda zai isa zuwa parking lot ɗin, rungume suka tarar da mummy da sarfraz, sai zub da ƙwalla mummy takeyi tanajin zuciyarta kamar mumtaz ɗinta ta rungume....

Sosai Aayaann yake murmushi saboda yadda yaga ƙaunar sarfraz tsantsa cikin zuciyar Mummy, mamaki abin ya bashi ganin ga kowa amma babu Nawaz, yana so ya ganta kafin sarfraz ya ganta.

Mummyn Aayaan na sakinshi mumynshi ta rungumeshi, gaba ɗaya sun babbake sun hana Daddy koda hannunshi ya riƙe....

Ko su hassu ba'a lura dasuba sai daga baya, shi kuwa sarfraz sai ya zama mutun mutumi ganin wasu tare dasu kuma yana ganin alamun kamanshi a fuskarsu gashi kuma be taɓa ganinsuba.

A haka dai suka isa main falour ɗin, aka zazzauna, nan mummy ta bukaci jin a ina Aayaan ya tsinci Sarfraz.
Chapter 63 · 0% Book details