← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 112

Sashe 40

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hmmm kadaiji dashi, sannan INASON baka shawara ka mu'amulanceta cikin kwarewa da wayewa har Allah yasa ka dasa sonka kai ma a zuciyarta, amma idan ka rusa komai to nidai babu ruwana don naga alamar ka cika gaggawa.
Focus on showing her real love And affection.

Murmushi Aayaan yayi "THANKS sis, insha Allah i will try my very best, zan kiyaye bi'iznillah, i will be getting in kinsan abinda zanyi gobe Koh?

"To ameen Allah ya bada iko, eh nasani Sweet dreams... Goodnight..

Ɗaki ya koma shima ya kwanta amma Sam ya kasa barci, yana mamakin yaushe sonta ya kamashi hakane, bayaso daidai da minti ɗaya yaga bata kusa dashi, ga kuma fargabar mezai biyo baya tunda yaga ranta ya ɓaci sosai.... Hakanan dai ya janyo pillow ya rungume yana sauke ajiyar zuciya...

Koda Aseey taga Aayaan ya shiga ɗaki sai kawai itama ta miƙe tabi bayan Nawaz...
A chukurkuɗe ta tarar da Nawaz ɗin ta cure jikinta guri ɗaya.

"Sis meyafaru? Ɗazu danace Miki Ina zuwa sai na dawo kuma naga Bakya nan,

Nawaz baza ta iya faɗin ma Aseey abinda ya faru ba saboda batason Aseey ta zargi wani abun a nata tunanin, sai kawai tacewa Aseey "waje na fita"

Murmushi Aseey tayi tana jinjina zurfin ciki da kawaicin Nawaz, kusa da Nawaz ɗin ta karasa zata zauna, aikuwa da sauri Nawaz ta mike saboda batason taji kamshin Aayaan dake tashi a jikin ta.
Tsaff Aseey ta gane me Nawaz ɗin take nufi amma saita basar kamar bata ganeba.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Kafin wannan lokacin
7hours back.

Koda hassu suka isa gidan baffa malam basu sameshiba, shine suka shiga Asalin cikin gidan wajen adda bilki don suji ina yaje..

Bayan sun gaisa ne adda bilki tace "ba nisa yayi ba, kafin ya fita ma yace min idan kunzo ku jirashi.
To hassu tace tare da zama a saman turmin dake gefe, shima SARFRAZ gefenta ya samu ya zauna yana rarraba Idanuwa.

Suna zaune hassu taga Adda tana fita da wanke wanke da alamu yi zatai, da sauri ta mike tana cewa adda ki bari inyi Miki.
Murmushi addan tayi tace "to hassu ga omon" batayi yunƙurin hana taba don tasan kome zatayi bazata iya hanata yin wanke wanken ba ɓata bakinta Kawai zatayi.

Bayan hassu ta gama wanke wanken ne tana share tsakar gida baffa yayi sallama suka shigo shida bandi....

Dena sharar hassu tayi saboda kada ta watsa mushi ƙura haɗe da Basu guri su wuce, Sannan ta gaida shi cikin girmamawa...

"Hassu na burge baffa malam domin ayanda ya lura yarinyar tanada hankali da ace yanada ɗa babba saiya aura mishi ita. Cikin fara'a ya amsa mata yana ƙara tambayarta yata kwana da mai jiki.

Bayan Adda ta shimfiɗa mishi tabarma ya zauna ne yasa ta zubo musu ɗumamen Tuwon biski Wanda aka Wadata miyar da ganyayyaki da nama.

"Ki zubowa hassu itama, idan tare zakuci kuma to! So nake idan muka gamaci mu wuce asibitin,Bandi ku wanko hannu kaida SARFRAZ kuzo muci tare.

"Nida hassu zanci" SARFRAZ yace yana hararar baffan

Murmushi baffan yayi haɗe da cewa "haba malam SARFRAZ ai abin bana faɗa bane, za'a zuba muku, bilki sa musu nasu tare kawai...

"To" bilki tace tana komawa hanyar kitchen donyin yadda baffan ya umarce ta.

Koda suka gamacin abincin nan suka wanke hannu sannan suka yiwa adda sallama suka fita, a waje suka tarar da mai adaidaitar da baffa malam yazo dashi yana zaune yana jiransu,

Cikin motar ya koma ya zauna sannan malam ya zauna a gefen driver ɗin sukuma su bandi suka shiga baya, duk wannan abinda akeyi hassu ko kallon inda bandi yake batayi, ya matuƙar ɓata mata rai.

A hankali suke tafiya har suka fita cikin gari inda suka isa general hospital ɗin dake cikin garin azare...

Naanma baffan cewa drivern yayi ya jirasu sannan su suka shiga zuwa Cikin asibitin.

Sashen psychiatric suka wuce don Ganin Babban likitan ƙwaƙwalwa, wanda shine zai duba SARFRAZ ɗin.

Cewa akayi bazasu shiga dukansuba sai dai mara lafiyar shida mutum ɗaya, Kasancewar hassu tasan malam zai iya cewa bazai shiga ba yasa tayi saurin cewa baffa ka shiga idan ka fito sai ka faɗa mana yadda kukayi..

To baffa yace Sannan ya kama hannun sarfraz don shiga office ɗin.

Amma Allan baran SARFRAZ yace shifa baisan zance ba, idan ba tare da hassu ba babu inda zashi...

Hakanan likitan yace to a kira hassu ɗin saisu shiga tare saboda anason Babba a gurin yadda zaifi gane bayanan da likitan zaiyi....

Bayan ya ɗibi jinin SARFRAZ sai aka kwantar da shi saman wani gado, sannan aka haɗa allurori har guda biyar aka zuba a cikin normal saline aka sa mishi a hannu..

Likitan lab ne ya shigo riƙe da takarda yana goge zufa "Doctor akwai babbar matsala Wallahi.

Pls comment and share

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*Episode 41*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

Babban Doctorn ne yace "wace irin matsala kuma?"

Kusa dashi ya ƙarasa yayi ƙasa da murya sukayi magana yadda su baffa bazasujiba.
Shiru yayi yana tunanin yadda zai faɗawa su baffan wannan gagarumar magana, duba da yadda ya gansu yasan ba masu wadata bane.

Natsuwa yayi sosai Sannan ya maida hankalinshi guri ɗaya yadda zai samu abinda zai musu bayani, sannan yayi gyaran murya " Baba ansamu Babbar matsala amma dai za'a iya maganceta.

Baffa yace "likita faɗa min wace irin Matsala aka samu? Tun ɗazu kunata ƙus ƙus amma bakace mana komai ba!

"Baba majinyacinmu ba ciwon mantau bane ya kamashi, kwakwalwar shice ta goce daga ma'ajiyar ta. Amma idan akayi aiki ana warkewa sai dai ba'a nan ƙasar akeyin aikinba.

Wata zufa baffa yaji ta sauko mishi, "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Lahaula wala quwwata illah billahil Aliyul azeem! Subhanallah! To likita yanzu ya za'a yi?

Gyara zama likitan yayi yace "ai ba ita kaɗai bace matsalar! Bayan wannan akwai hormones imbalance a tare dashi, kuma bincike ya nuna ciwonma ya daɗe Abokinshi.

A Tare hassu da baffa suka miƙe " likita badai kana nufin mutuwa zaiyi ba ko?

Ɗan murmushi doctor yayi "kada ku damu bazai mutuba, yanzu dai ku koma ku zauna, abu ɗaya ne damuwar shine kudin da za'a fitar dashi ƙasar waje ayi aikin.

"To likita kana ganin zai kai nawa? Baffa yace Yana daɗa daidaita nutsuwarshi.
"Eh to gaskiya baba bazan ɓoye maka komaiba, waccan shekarar mun taɓa samun mai irin wannan matsalar, kuma gaskiya a yanda akayi lissafi sun kashe kuɗi yakai kimanin million goma sha uku.

Miƙewa baffa yayi haɗe da cewa "iye! Na'am! Miliyan nawa? Tabɗi aini a halin yanzu ko dubu ɗari ta kaina banida ita balle million.

"Calm down baba! Kada ka tada hankalinka, kasan komai Allah ya tsara ma bawa baya iya kauce mishi, yanzu abinda nakeso dakai shine ayita addu'a, saikaga Allah ya kawo wanda zai biya kudin aikin cikin sauƙi.

"To Allah yasa! ta malam bata wuce Ameen, amma a ƙarnin nan waye zai iya biyan million goma sha biyu don ayiwa wani aiki?

"Numfasawa Doctorn yayi "baba nace ka kwantar da hankalinka kuma kuyita addu'a, kuma inaso inyi maka albishir cewa akwai Wani babban soja da yake biyawa mutane kuɗi idan basuda hali, to shine nakeso idan yazo zanyi mishi bayani kila Allah yasa ya biya mishi.

To shikenan likita mungode, amma yanzu babu wani abu da za'a bashi wanda zai iya taimaka mishi gurin lafiyar shi? Kaga kuma yanada ciwo a jikinshi.

"A'a duka wannan babu matsala zan haɗa ku d wanda zai wanke mishi ciwon kuma zai baku magani.

Miƙewa baffan yayi "to likita mungode!

Tare suka fita duka zuciyarsu babu daɗi barin hassu da take ganin kamar bazai taba warkewa ba.

Kamar yadda likitan yace haka aka yiwa SARFRAZ dressing ɗin ciwon aka basu magani suka tafi gida.

Sai bayan sun koma gida ne baffa yayi wa bandi bayanin yadda sukayi da likita, shima bandi baiji daɗi ba, Sannan ya ƙara tausayawa sarfraz halin dayake ciki ..

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Kallon Nawaz ɗin tayi tace "sis don Allah kada ki tafi ki barni!

Take hankalin Nawaz ya koma kan Aseey "sis meyasa kikace haka? Ko wani yace Miki zan tafi gobe ne.

"A'a Kawai dai ina rokon Alfarma ne akan ki zauna tare damu har zuwa sanda zan koma England, saboda duk sanda naganki ji nake kamar ke ɗin jini nace domin nida mummy munyi burin samun yar uwa mace amma dayake Allah ya riga da ya gama tsara komai sai bata kuma haifar maceba sai Aayaan da marigayi..

Kusa da ita Nawaz ta ƙarasa ta rungume ta, tama manta cewa batason taji kamshin turaren Aayaan daya gauraye jikinta kamar ita ta shafa "sister i feel your pain, Nima inada wannan tabon a zuciyata inaga har gara ke kinada ƙani nifa banida kowa.

"Yea kin faɗi gaskiya, amma Nawaz me zai hana mu zamewa juna sisters! Kinga shikenan Ni sai na zame Miki yayar da kika daɗe kina nema, ke kuma saiki zamemin ƙanwar da na daɗe ina nema.

Murmushi Nawaz tayi "yea big sis Nagode da wannan dama da kika bani, i really appreciate..

Sakin juna sukayi Sannan Aseey ta fara magana.
"Sis Nawaz kinsan cewa mummy bataso ta haifi Aayaan ba, taso ta haifi mace ne saboda asa mata sunan biyuninta wato maman SARFRAZ.. dayake Ni sunan mahaifiyar daddynmu aka samini.....

In faɗa Miki sanda ta haifi Aayaan har kuka tayi wai ita taso ace mace ta haifa, shiyasa zakiji wani zubin Aayaan yana cewa muda ba'a sommu tunda munzo a maza, to yaza muyi tunda kaddara ta riga fata.
To daddyn mune ya bashi labarin yadda Mummy tayi bayan ta haife shi kafin ya rasu ... Kuma har yau har gobe Mummy bata dena ƙulafucin ƴa mace ba
Sai dai yanzu taci burine akan matar Aayaan....

Gaban Nawaz ne yayi wata irin faɗuwa amma saita danne bata nunawa Aseey ba.

Cigaba Aseey tayi da magana " kuma sis kullum banada addu'ar data wuce Allah yaba Aayaan mata ta gari wadda zamu haɗu mu rufawa juna asiri, saboda Al'amurran duniyar nan sun gama lalacewa, tsorona kada yaje ya auri wadda zatasa ya manta damu, Wallahi idan haka ta faru bazamu iya juraba musamman mummy.
Chapter 40 · 0% Book details