← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 112

Sashe 82

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƴar taƙaitacciyar tafiya sukayi suka isa wani classic and unique boutique, tundaga waje yake ƙyalli, harta ƙofar shiga cikin boutique ɗin designer ce, Komai nagurin me ajih ne.
Ɗaukar ta yayi in a bridal way suka shiga ciki, tunda suka shiga ma'aikatan wajen ke gaishesu.
Guri me kyau aka tanadar musu sannan aka Kawo musu ruwan roba Tare Da tambayarsu ko suna buƙatar wani abun.
Ɗaga musu hannu Aayaan yayi Alamun basa buƙatar komai, "where is Affiah Aliyuo" Aayaan ya tambayi ɗaya daga cikin staff ɗin wajen.
Ai kuwa da sauri tabi wata hanya tana ƙwalawa Affiah kira.
Cikin ƴan daƙiƙu Affiah ta karaso tana murmushi tare da gaishe da Aayaan ɗin cikin sanayyah, Sannan ta gaishe da Nawaz itama cikin girmamawa daga bisani kuma ta buɗe wata kofa ta shiga ciki, fitowa tayi janye da wasu akwatuna manya guda biyu Sannan wasu yan mata suma guda biyu suna janye da guda bibbiyu suma, That means guda shida kenan
"Sir ga kayan da aka haɗa mata, yanzu abinda za'ayi kafin ta tafi ta duba taga Idan Akwai abinda beyi Mata ba sai a chanza mata"

"Nop i trust you Affiah, idan ma akwai wanda beyiba zansa a dawo dasu, duk da harshen Nasara suke wannan zancen.
Ɗibar akwatinan wasu ƙatti majiya ƙarfi sukayi tare da kaiwa cikin motar da su Aayaann suka zo da ita, tashi suma su Aayaan din suka yi suka fita, saida ya saka ta acikin motar ya rufe Sannan ya koma ya shiga ɗaya gefen don yin driving.
Ita dai Nawaz ta zama mutum mutumi, mamakin wannan lamari takeyi "wai ita wa ta aura ne?"

Cikin wani super store suka shiga wanda ya haɗa Komai na kayan rayuwar duniya, bayan su abinci ga kayan sarrafa abincin nan su kayan makaranta irinsu littattafai dadai sauran abubuwan buƙata.

Gefen laptop sukaje Yace ta zaɓi wadda takeso, kasa zaba tayi saboda kunya, wata Apple ya zaɓar mata golden colour me ɗan banzan kyau ita Kanta saida taji cewa tayi Sa'a matuƙa "kinga wannan tayi Miki?

"Cikin zumuɗi Nawaz tace "tayi min sosai sosai"
"Are you sure? Taki ce fa wannan, Ni tawa tana gida, don haka ki zaɓi Wadda tayi miki bakida Matsala"
"Allah tayi min sosai, thank you very much, may Almighty Allah bless you and All your family, especially mummy"

Wani irin daɗi ne ya rufe Aayaan, yana matuƙar jin daɗin irin addu'oin da Nawaz take yi mishi, Gashi ita bata raina abu komai ƙanƙantarshi.

Daɗin dayaji yasa ya riƙa jidar mata abubuwa kama daga jaka, takalmi, mini hijabs, veils, turaruka, mayukan sa taushi da santsin jiki irin na turawa sarƙa da Bangles masu kyau kamar wanda zai buɗe wani madaidaicin boutique.
Haka ya gama haɗa kayan duka Sannan ya basu Master card dinshi sukayi debiting ɗin kuɗin siyayyar suka kai musu mota.

Yanzun ma dai ciccibarta yayi ya sata a motar shima ya shiga suka ɗauki hanyar komawa gida.
Yana lura da Nawaz sosai, tunda suka fito take hamma, yanzu haka idonta har kadawa yayi Alamun barcin takeso tayi hani'an
Shiyasa ya ɗan ƙara speed ɗin motar kada ta chutu da yawa, har sun kusa isa gida ya tuna cewa yaga wani text da mummy ta turo mishi na cewa ya siya wa Nawaz fresh milk da yawa a zuba a fridge saboda dasu zata riƙa shan magungunan ta, Sannan kuma ya nemar mata injin yin kunun Aya saboda shima zata riƙa yi...
And ta kara da cewa ya tabbatar tana cin Kayan itatuwa sosai musamman dangin su Apple, kankana, gwanda, inibi da ayaba, kuma ya riƙa siyo mata gasashshiyar kaza kullum.
Reverse yayi ya koma wani store dake kusa dasu, Carton uku na fresh milk ya siya sai fresh chicken pack biyu Wadda da safe zasuyi Amfani da ita, anan bakin gurin yasa akayi mishi packaging ɗin fruits iri iri Saboda umarni Mummy..

A wahale Nawaz ta isa gida domin wani wahalallan barci ne yake cinta a Ido, kamar zata faɗi haka ta riƙa ji, Gashi kuma Aayaan ya tada fitina akan saiya yi mata wanka kafin su kwanta, ita dai ta rasa wannan jafa'i, wanka wanka wanka kamar kwaɗi, banza tayi dashi don ta fara gajiya, tanaji ya ciccibeta ya cire mata kaya Sannan ya zunduma ta a cikin jacuzzi, haka ya gama kiɗanshi ya gama rawar shi bata ko buɗe ido ba balle ta tanka mishi.
Tanaji yasa mata kayan barci ya feshe ta da turare ya ɗora ta a ƙirjinshi yaja musu duvet, kusan ince daga ɗaya Nawaz Neman barcin tayi ta rasa domin Aayaan ya isheta da taɓe taɓe, daga ya taɓa chan saiya ja chan, ya tsotsi chan ya matsa chan har sauke numfashi yake yi da sauri da sauri, ganin yadda ya matsa da yawa yasa tsoro ya kama Nawaz,. Aikuwa take jikinta ya fara rawa, shi kuwa Aayaann jin jikin Nawaz ɗin yana rawa ya gane Cewa ta tashi.

"Sweetheart kin tashi?"
Shiru tayi tana tsoron kada tace eh ya zarce

Murmushi Aayaan yayi "wai duk tsoron ne haka?, To ki saki jikinki babu abinda zan yi Miki, kin manta na Miki alkawarin sai kinaso? And I always keep my words.

Bata tanka mishi ba saidai jikinta ya dena rawar, a haka dai tana jinshi har barci ya kuma kwasheta.

Yauma koda suka tashi da asuba shi yayi mata wanka ya shirya ta sukayi Sallah sannan suka koma barci, sai wajejen ƙarfe tara suka farka, kamar jiya haka yauma taga abinci kala kala jere a dinning batasan wa ya jera ba, bayan sun gama break fast ɗin ne Aayaan ya dauko sabuwar laptop ɗin daya siya mata jiya ya saita mata Komai tare dayi mata subscription na shekara ɗaya.

Bayan ya gama haɗa komai na laptop din yace ta shirya suje Makarantar Kawai yayi mata registration ido na ganin ido tunda jiya Allah beyi za'ayi ba, "to ai a shirye nake"

Hararar wasa ya balla mata tare da cewa "Nifa bana zama da ƙazami"

Zumbura baki tayi " to Amma yanzu dai don Allah ka bari nayi wankan da kaina tunda kaga sauri mukeyi "

"To kije kiyi, amma Ni zan shirya ki"
Batare da tace komai ba ta juya ta shige bathroom ɗin.

Kafin ta fito ya buɗe ɗaya daga cikin akwatinan da suka amso jiya ya zaɓo mata wasu irin designers ɗin riga da wando ƴan Turkiyya, rigar sakakkiya ce Sannan tsayin ta har gwuiwa sai wandon shima dogo me faɗi.
Babban veil ya ciro mata me ruwan madara Irin me haɗe da hula da mini hijab ɗin nan, dayake kayan peach colour ne.

A Saman gado ya ɗora su sannan ya miƙe ya fita falour don ya haɗa Mata magungunan ta, yanaso ta fara sha daga yau har zuwa Lokacin daya ɗibarwa kanshi...
Kofuna guda Uku Ya ɗauko tare da robar madara guda biyu sai magungunan kala kala, harda gumba da Tsumi....

Mamaki Abin ya bashi sanda ya dawo ganin daga fitarshi wai harta fito daga wankan ta shirya, murmushi yayi "Anya ba sai kin koma an chanza wankan nan ba? Naga kamar ojoro kika yimin"
Dariya tayi "Allah yaya na fita"

"Ooh Nidai nace a taimaka adena ce min yayan nan asa min wani suna na daban amma anƙi"

"Zansa maka In'sha Allah Kawai dai ban gama tunanin wanne ne ya dace dakai bane"
Murmushi yayi "shikenan to pls idan an tashi zaɓowa a zaɓo min me daɗi"

Rufe fuska tayi alamun jin kunya, kusa da ita ya matsa ya mika mata magungunan tare da cewa "kiyi sauri kisha saimu tafi"
Babu musu ta amsa, tasha da yawa saboda basuda ɗaci kuma barin ga madara,

Goge mata baki yayi da tissue sannan ya Gyara mata mayafin ya fesa mata turare ɗan daidai sannan ya zaɓo mata wata Yar ƙaramar jaka me kyau wadda zata shiga da kayan haɗe da takalminta.

Tsaff suka fito gwanin sha'awa, tsaff tsaff dasu kamar ka sace ka gudu....

Sanda suka isa makaratar Saida ya tabbatar Komai Saida ya biya kuɗinshi har zuwa sanda zata dena zuwa Makarantar, har aji ya kaita Sannan ya juya ya tafi da alƙawarin zai dawo ƙarfe huɗu ya ɗauke ta, dayake ƙarfe biyu ake shiga ajin a tashi huɗu.

Nawaz taga ikon Allah, mutane kala-kala iri-iri haka ta gansu, iya kallonka dole kaci karo da halittar da baka taɓa cin karo da irin taba....

Dayake karatun ana yi musu na awa ɗaya da rabi ne to sauran minti talatin ɗin sai a barku Ku tattauna da sauran ƴan ajin yadda zaku saba dasu sosai.

Malamin na fita wata mata ɗauke da jinjiri wanda a ƙalla bazai wuce wata Uku ba ta ƙaraso kusa da Nawaz ta zauna "ƴar uwa wallahi tunda mijinki ya shigo dake nake Allah Allah malamin nan ya fita saboda inyi hausa inɗan ji daɗi, tunda mukazo ƙasar nan bana ko wane yare sai turanci"

Murmushi Nawaz tayi mata tare da amsar yaron "to mijinki fa? Ko baya kusane?"

"Hmmm ai dogon labari ne, bayajin hausa sam"

"Allah sarki! To yaudai Allah ya haɗa mu"

"Wallahi kuwa, Allah dai yasa zaku daɗe a ƙasar " cewar matar tana kallon Nawaz cikin jin daɗin haɗuwa da ita.

"Eh inaga zamu jima In'sha Allah"

"Masha Allah naji daɗi sosai, To Nidai sunana Zainab Ibrahim s lame, Ni Yar jahar kano ce a Nigeria, wannan ɗan naki kuma sunanshi sudeis, mijina kuma ɗan Sudan ne, mun haɗu dashine a jahar Jigawa sanda naje ganin kakannina"

"Allah sarki, gaskiya naji daɗin haɗuwa dake maman sudeis, Allah ya ɗorar da ƙawancenmu" ɗaga sudeis ɗin Nawaz tayi tana mishi wasa shi kuma sai ɓangala dariya yakeyi.

"Iyye ashe Sheikh sudeis baka ƙyuya" cewar Nawaz tana daɗa ɗagashi sama.

"Aikam dai bai fara ƙyuya ba tukuna, har roƙon Allah nakeyi akan Allah yasa kada yayi ƙyuya wallahi"

"Allah yasa kada yayi"

"Ameen" Cewar maman sudeis

Gyaran murya Nawaz tayi Sannan tace "Ni sunana Madinatul munawwarah Muhammad, amma anfi cemin *Nawaz* Ni yar Zariya ce, amma iyayena Yan Maiduguri ne, shima mijina da surukaina duka yan Maiduguri ne, achan Maidugurin ma muka haɗu, and kuma bamu daɗe sosai dayin aure ba.

"Masha Allah Madinah, gaskiya naji daɗin haɗuwa dake, ashe Amarya ce!

"Sunne kai Nawaz tayi Alamun jin kunya.
Chapter 82 · 0% Book details