Sashe 42
Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ɗan daɗe a kishingiɗe yana tunanin "shin anya kuwa zai iya jurewa ba tare daya fallasa kanshiba har zuwa wa'adin da Mummy ta ɗibar mishiba? Ɗan tsaki yayi yana buɗe idonshi wadanda suka chanza kala Saboda daɗewar da suka yi a rufe, mamaki abin ya bashi Ganin har sun shiga cikin garin Abuja..
Yan mintoci ƙadan ya daukesu suka karasa comprence hall ɗin, sosai mutane sun cika gurin daga yan siyasa sai ƴan sanda da sojoji da mashahuran ƴan boko da masu hannu da shuni...
Tunda ya sauka ake sara mishi, yan jarida kuma sai suka maida akalarsu kanshi, kowa burinshi ya ɗauke shi photo domin sunji cewa da taimakon shi aka kama yan ta'addan...
Ganin an chukurkuɗe hanyar an hanashi wucewa yasa bodyguards dinshi suka matso sosai suna buɗa mishi hanya har ya samu ya shiga Asalin inda ake taron.
Sosai hankaki kowa ya dawo kanshi inda ko zama ba'a bari yayi ba speaker ya miƙa mishi mic, Barka da zuwa yayiwa kowa sannan yayi yan bayanan da zaiyi daga karshe kuma ya bada uzurin cewa Nawaz bata samu damar zuwaba saboda tayi aure kuma mijin yace bai bada iziniba.
Sosai mutane basu ji daɗin hakan ba musamman ƴan jarida da suke so su samu kuɗi ta hanyar daukar photunan ta.
Maidawa speaker ɗin mic yayi Sannan ya samu guri ya zauna tare da ɗaukar bottle water ɗin dake ajiye a gabanshi yana korawa, shiru hall ɗin yayi ba'a jin komai sai ƙus-ƙus ɗin mutane suna muhawara.
Shidai zaune yake kawai amma Sam bayajin daɗin garin, shi a nashi da so samu ne ya koma yau basai yayi wasu kwana uku ba.
Speaker ne ya Fara magana "we need your attention here"
Sosai kowa ya Dena magana ya maida hankalinshi gurinshi,
"To bisa abinda ya faru an yanke hukuncin za'a ba Captain Aayaan Muhammad mai goro duk wani abu da aka yiwa yarinyar Alkawari, an wakilta shi ya kaimata tunda shi yasan inda zai sameta kuma Munsan cewa abinda muka bashi zai isa gurin Wadda akeso ya isa cikin aminci, domin kaf cikinmu babu wanda bai san Aayaann ba.
Tafi aka fara, inda daga bisani aka kira colonel aka karrama shi sannan aka kira Aayaan shima aka karrama shi, haka dai akayita yi har zuwa inda aka ƙaddamar da kayan ciye-ciye da shaye-shaye kala-kala.
Ganin komai yaɗan lafa yasa Aayaan ya miƙe ya fita zuwa bayan ɗakin taron, tsayuwa yayi yai shiru yana tunani, sosai yayi zurfi a tunanin yaji hannun mutum ya dafa mishi kafaɗa.
Colonel ne tsaye a gefenshi yana yi mishi murmushi "Son meke faruwa?
Gaisheshi Aayaan yayi haɗe dayi mishi ya bayan haduwa ya su mummy Sannan yayi shiru be kuma yin magana ba.
"Son i said what is wrong with u?
Dan murmushi Aayaan yayi "Sir i am just not feeling well!
Murmushin manya Colonel yayi "Aayaan kenan ba iya shi bane na sanka sosai fa, dole akwai wani abu bayan shi, but zamuyi magana bayan munje gida amma pls kafin nan kayi ƙoƙarin cirewa ranka damuwa, domin har fuskarka Saida ta nuna hakan.
Murmushi Aayaan yayi Tare Da cewa "Insha'Allah "
Sannan suka dauki hanyar komawa cikin hall ɗin..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Ko bayan Nawaz ta gama abincin saita wuce bayi tayi wanka, hakanan ta samu kanta da son yin light make-up, doguwar rigar Atampa ta ɗauko tasa Sannan ta samu ƙaramin mayafi wanda kalarshi ta shiga da atampar ta yana akanta. Falour ta fita inda suka zauna tare suka ci abinci, sosai Aseey ke janta da hira hakan yasa har sun fara shakuwa da juna.
Mummyn AAYAAN da Mummyn SARFRAZ Sun zama kamar tagwaye, duk inda kaga ɗaya to lallai zakaga ɗaya, haka suke yini hira.
Aseey ce ta Kalli mummy tace "Mummy don Allah sister Nawaz nakeso ta rakani inga gari"
Harara mummy ta balla mata "lallai Aseey so kikeyi Aayaan ya ƙare min tanadi Koh? To wallahi babu inda zakuje.
Mummyn SARFRAZ itama cewa tayi"gaskiya ku hakura kawai.
Gaban Nawaz ne ya faɗi, domin sam ita tama manta yau bataga koda gilmawar Aayaan ba, shiru tayi tana tunani domin itadai tunda suka zo gidan bata taɓa kaiwa koda karfe goma ba face sun haɗu sau yafi a ƙirga, amma yau kusan ƙarfe uku amma shiru.
Duk saita jita wani iri tana tunanin Allah yasa lafiya, gashi bazata iya tambayar kowa shiba, haka gaba daya yinin ranar a falour tayishi saboda tanaso tasan meya faru amma har kusan karfe goma na dare babu Aayaan babu dalilinshi kuma bataga alamun damuwa a tattare dasu ba, lallai kam ashe mutum koh faɗa kukeyi dashi watana saikayi kewarshi idan baka ganshiba.
Hakanan ta kwanta namma Saida takai kusan awa biyu bata rintsaba, haka dai har zuwa barcin yazo ya dauketa yayi gaba da ita.
Haka Aayaan sosai yake kewar gida, yanaso ya ganta koda hararar shi zatayi, yanaso yaji muryarta koda bashi zatayiwa maganaba.
Duk tsayin daren haka Aayaann yayi shi ido farai, babu koda guntun barci daya daukeshi, shi kanshi abin ya bashi mamaki, be taɓa tunanin soyayyar da yake yiwa Nawaz har takai hakanma.
Washe gari haka ya tashi wani iri bawai don barcin da baiyiba a'a sai don tunanin daya kwana yi, ya saba da rashin barci Saboda wani zubin har kusan kwana uku yakeyi beyi barciba idan suna filin daga🫣.
Dayake a gidan colonel ya kwana, suma yaran Colonel da matarshi Saida suka tambayi colonel ɗin wai me yake damun Aayaan ne? Saboda ya saba idan yazo haka zaiyita tuna yaran wasa yana basu labarai, amma wannan karan ko dinner beyiba ya tafi ɗakin daya saba sauka ya rufe kofa.
Koda garin ya waye babu abinda ya sauya, domin Aayaan jin wani irin ƙunci yakeyi ya cika mishi zuciya, duk sai ƴan muskilancin nashi suka dawo suka maida mishi hular sarauta,
Be cewa kowa ƙala, ko colonel ne yamishi magana sai dai ya ɗaga mishi gira ko ya girgiza kai.
Colonel ɗin be damuba kasancewar yasan halin Aayaan ciki da bai, gefe ya jashi suka zauna yasa aka kawo musu Black tea saboda yasan shine favourite ɗin Aayaan.
"My son please ka faɗamin meke damunka? Abin yayi worst ban sanka da irin wannan ɗabi'ar ba sam!
Ɗago da kai Aayaann yayi yana tunanin me zai cewa colonel, domin gaba ɗaya bakinshi yayi nauyi kuma yana tunanin ta ina zai soma cewa ya auri Nawaz kuma tunaninta ne ya hanashi saƙat.
"Sir banida lafiya ne, and is serious saboda ko barci bana iyayi and kuma damuwa ta isheni, burina kawai naga na koma gida.
Murmushi colonel yayi " Son kullum burina inga kayi aure kaima kana tare da naka iyalin, amma hakan yaci tura, bansan meyasa bakason yin aureba!
Shekarunka sunkai ace kana da yaro ma ko yarinya but you're still single, yanzu wannan damuwarma da kake ciki waya sanima ko harda matsalar rashin mace kusa dakai, shifa Aure Rahma ne, idan Kanada mata duk damuwar daka shiga zaka faɗa mata kuma zata baka Shawara ko ta tayaka Neman mafita, nidai Aayaan nagaji pls kayi aure na roƙe ka.
Tabbas Maganar colonel Gaskiya ce, Ni ɗin ma ai saboda tawa matar na damu, amma Ni matsala ta guda biyu ce, ya za'ayi Nawaz ta yarda da zancen aurenmu kuma tasoni batare da taga anyi mata karfa karfa ba?
Na biyu mummy bazata bari na ɗauketa zuwa wata ƙasar ba, balle ƙila idan munje mu saba sosai da ita, ta gindaya min sharadin sai dai Nawaz ta zauna a gabanta har zuwa lokacin da ya dace tasan cewa nine mijinta.
Duk acikin ƴan sakwanni yayi wannan tunanin.
Dafashi da colonel yayine ya dawo dashi daga nisan kiwon da yayi "my son zan fita Amma pls zanso kafin na dawo ka warware..
Murmushin ƙarfin hali Aayaan yayi "Yes Sir Insha'Allah, amma meyasa bazanyi accompany dinkaba?
Murmushi colonel yayi "No Aayaan bakajin Dadi, just saina dawo.
Ko bayan colonel ɗin ya tafi Aayaan be tashi a gurin ba sai kawai ya ciro wayarshi ya zubawa photon Nawaz ido "ko yanzu tana ina? Me take yi? Ta nemeshi? Tayi kewarshi kamar yadda yayi Tata? Duk bashida wannan amsar.
Tunawa yayi da wayar da y siya mata ranar da sukaje chicken republic, ai kuwa take yaji wani irin farin ciki ya lullubeshi, nuno number yai sai yayi dialling, amma abin haushi is switch off.
Kuma shi ya rasa meyasa Aseey da mumy suke mishi haka, ya kirasu yafi sau a ƙirga amma babu wanda yayi mishi Maganar Nawaz, kuma ko muryarta bejiba alamun batama kusa dasu..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Itama yinin ranar haka take sukuku da ita, amma su Mummy basu ganeba Kasancewar dama ba wani sakin jiki takeyi sosai dasuba, ita kuma Aseey koda taga Nawaz ɗin ta kuma zama so cool itama bata kawo komaiba sai ta ajiye hakan a matsayin kotanaso ta koma gida ne...
Mamaki abin yakeba Nawaz sosai, ace babu Aayaan babu alamun shi kuma ko dai dai da rana ɗaya Babu wanda yayi maganar shi, kokwonto ta farayi tana cewa ko dai sun gane Bama shirine? Kada fa suma su tsaneni saboda banason Aayaan.
Tsoro ne yaɗan kamata "inaga fa hakane shiyasa yatafi be mini Sallama ba, kuma suma basu faɗamin ba. Kwalla ce ta cikawa Nawaz ido "Wallahi Ni Ban tsane shiba, kuma Wallahi bana ƙinshi, kawai Ni taɓa min jikin da yakeyine banaso...
Haka da daɗe zaune tana takanta wasikar jaki, idan ta gama wannan ta ɗauko wannan... Lokaci ne yayi nisa bata saniba....
Hakanan taji tanaso tayi magana da umminta kila ta samu sauki a zuciyarta, to amma tana tunanin taya zata ce Aseey ta kira mata ita bayan suna kallonta a wadda ta tsani ƙaninta.
Cikin azama ta miƙe tunawa da tayi da wayar da Aayaan ya siyan mata, aikuwa jikinta har rawa yake yi sanda take kunna wayar, bayan ta kunna ne ta rubuta number umminta tayi dialling, ai kuwa ƙara biyu ta daga da sallama.
Jin sallamar ummin sai ya ƙara karya wa Nawaz zuciya ta fashe da kuka, tachan ɓangaren ummi ta fara magana cike da damuwa "Nawaz faɗamin me akayi Miki? Sun faɗa Miki wata magana ne data bata Miki Rai? Ko Wani abunne ya faru?